AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 65-66

??65and66??

Takardar sallama yakarbo yadawo suka wuce gida,

Har suka dawo gida iyayen ameelah basu san da zancen ba,

Da isarsu gidan yawuce dakinsa, ameelah ma haka dakinta ta wuce taje tasame gado tayi kwanciyarta
*** *** ***
Acikin daren afham yahada kayansa saida ya kintaci su momy sunyi bacci sannan yafito,
Tafiya yakeyi cikin sanda, harya karsa bakin kofa fita, ya bude yafita,
Motarshi yashiga, ya kunna, a lokacin mai gadi yatashi, yabude masa kofar get babba yafita,

Yakama hanyar gombe zuwa ganin ameelah ( kujimun wauta, Allah yakaremu da shairin zuciya)

Tafiya yaketa tsala sai kusashen asuba yakarasa gombe,

Wata babbar Hotel yakama yaje ya ajiye kayansa, wayarsa yadauko yayi off dinta yacire sim dinsa yadauko wani sabon sim yasaka, sannan ya kunna wayar, a cikin sabon sim din number ameelah ce kadai a ciki, kiran number yayi yajita akashe kamar yadda yasaba ji a yan kwanakinnan,

Zauna yayi a bakin gado cike da damuwa, sannan yayi ajiyar zuciya, ya wullar da wayar saman gado yatashi yanufi ban daki yayi wanka, bayan yafito yadawo ya kwanta,

Washe gari

Sai misalin 9 nasafe yatashi, a lokacin yayi sallah,
Sannan ma ai katan hotel din suka kawo masa kayan karin safe,
*** *** ***

Acen kuwa gidan su afham, momy tagama hada kayan kari, aneesah tafito tace “momy ina yaya afham duk yau bangan saba”

Momy tace “kinsan inda yake kije kisamesa “

Aneesah ta zunbure baki, ta nufi dakin afham,
Tunda ta tura kofar dakin takejin gabanta nafaduwa, a hankali takada kafarta cikin dakin, tayi sallama shiru,

Wata yar gajeruwar takarda tagani a gefen gadon sa, takarasa bakin gadon tadauko tana dubawa, karantawa takeyi a hankali, tun kafin takarasa karanta takarda hawaye suka fara zubo mata,
Juyo tayi da gudu tafita tana kiran momy,

Tana isah falo taci karo da momy da abba zaune akan danni, takarasa tana kuka tace “momy yaya afham yagudu” a gigice momy tace “innalillahi wa inna ilaihin raju un”

Abba dayake zaune agefe yakarbi takardar datake hannun aneesah, yafara karantawa, a karshen takardar aka rubuta ” niban bazan iya auren amal ba natafi gurin wadda nakeso” edon abba sunyi jajir, ya dago kansa yakalli aneesah yace ” wacece yakeso”

Aneesah tana kuka tace “wata yar gombe ce a chart suka hadu”

Abba ya girgiza kansan cike da takaici yace ” lallai yaron nan zai hadu da fushina, wlh duniya kadai zai bari nafasa auren dazan masa shida amal, dole sai anyi wannan auren ko baya garin nan”

momy tace “aa alhaj…”

Abba yadaga mata hannu ” karkice komai hajiya, wannan shine hukuncina” yana gama maganar yatashi yabar gurin , aneesah kuka take sosai momy tana lallashinta,
*** *** ****
A gidan ameelah kuwa, tunda safe hilal yafita bayan yakarya,
Ameelah takasa samun sukuni domin tunda tatashi daga bacci takejin gabanta nafaduwa, tarasa meye dalili…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button