NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 16

BOOK 2
                      PAGE 16
Bariki gida tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi tace Umma…..
Amsawa tayi da fad’in ya akayi? Yau dai Kedai shar

Bariki tayi dariya, tare da fad’in ina son miki magana Allah yasa zaki amince….
Umma din tace name fah.?
Bariki tace akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga zaifi muku.
Umma tace aure?  Dawa Rufamin asiri, barni inyi abunda ya kawo ni.
Bariki tace kin fiso ki zauna babu aure??
Tace a’a ina so inyi mana inna samu dai dai ni
Bariki tace gashi kin samu
Dariya tayi tare da fad’in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had’awa??
Bariki tace shiya Aiko ni inyi miki magana, kuma naga Wlh auran shiya dace daku.
Tace hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, saiki fad’a mishi na amince
Bariki tace Alhmdlh, amma dan Allah Ayi bikin Kafin aurena…..  Nan dai sukai ta tattaunawa suna cikin fira habib ya fad’o kaman an jefoshi
Bariki tace miye haka ko sallama babu
Tsaki yayi tare da fita ya tsaya a kofar d’aki yana gafaranku dai masu d’aki,  tare da kuso Kai…..
Bariki tace wannan ne sallama???  Ai b….
Yace dakata Mlm, nifa ban gane miki ba, tunda Yarima ya fara soyayya dake kika koma wata iri iri, in ke kin zama ustaziya ni barni yanda nake…..
Bariki tace Allah ya shirya, ni bama wannan ba zauna kaji…..
Kallon tara saura kwata ya watsa ma bariki, sannan yace wlh Ina gab da in Tsiga miki rashin mutunci, Idan kina kaini jinsin da ba nawa ba…..
Tace Allah ya baki hakuri, zauna dan Allah
Zama yayi yana bud’e hanci wai shi a dole ranshi a bace yake
Bariki tace iyayen Yarima sun Aiko har Sun tafi
Yace haba dan Allah?? Gud’a ya saki tare da fad’in inama inada duwawu babba dana tashi nayi rawa da duwaiya guda d’aya….
Bariki dariya tayi tare da fad’a ma habib yanda aka yanke bikin nan da wata biyu
Habib yace Wlh bariki ban San mai yasa ba, ina sonki da Yarima,…
Bariki tayi dariya tace ngd kawata, nan suka shiga tsara yanda za’a gudanar da bikin da yanda za’a samo kawayen Haya duk habib yace abar komai a wajanshi……
Sannan maganan gyaran jiki irinsu dilka, maganin Mata bariki tace y’ar Maiduguri take So,da yar Sokoto
Suma habib yace duk zai Kawo, cikin satin nan dan a Fara , sunyi magana Sosai inda tabi habib suka je maraban jos domin ta Fara had’a kayanta wanda take bukata wanda bata so kuma ta bayar…..
Koda suka je sunga haulat ita da Hjy babba suna magana, ganin bariki yasa haulat ta nufi bariki Tana fad’in Indai za’aga wannan kina wajan…..
Habib yace Wlh Haulat zan miki bura uba, ban so
Tabe baki Haulat tayi tana bashi hakuri,
bariki kam wajan hjy babba ta nufa tana fad’in haka hjyta har yanzu fushin ake dani?.
Hjy babba yace kyaji dashi, ni Kinga karki batamin rai yanzu da yamman nan
Bariki tace haba hjyta kiyi hakuri mana
Hjy babba yace Wlh bariki kina bani mamaki, da kyanki da kuruciyarki da lafiyanki, amma kice zaki aure, keda ake rububinki haba bariki
Bariki tace hjyta adai yi hakuri
Hjy babba yace ya wuce yana tabe baki
Bariki tace godiya nake tare dayin gaba ta nufi d’akinta…..
Tana cikin had’a kaya haulat tazo, ganin bariki nata aikin had’a kaya yasa haulat tace badai bikin yazo ba??
Bariki tace eh Wlh, Kinga wata biyu aka sa, gwara in fara had’a kaya, in kyautar dana kyautar wa inbar na Bari
Haulat tace hakane, ni har yanzu ba’a fad’amin dan wani gari bane ko sunanshi
Bariki tace saurin Mai kike ki jira koma Waye zaki gansa in lokaci yayi
Haulat tace Allah ya kaimu, nan ta Fara taya bariki had’a kaya, haulat ta d’auko wata Leda nan kayan suka zube dan ledan ya fashe, Aiko ayabar roba suka fito……  Haulat d’auka ta farayi taga har guda biyar tace bariki dama kina dasu??  Ah ba banza ba kika daina harka da maza ba, ashe kina da abunda yake d’ibe miki sha’awa
Bariki kai ta girgiza tare da cema haulat ki d’auka duka na baki, ni ban taba amfani dashi ba, yanda aka bansu haka na ajiyesu dan banda abunda za suyi min
Haulat ta dinga godiya tare da fad’in amma wanda ya baki yasan kina son babban ayaba tunda harya baki….
Bariki tace Alh madu Yaban dan iskan tsoho, ci gaba da had’a kayanta tayi harta gama taba haulat kyautan kayanta da yawa.
Haulat tana ta mata godiya duk yanda haulat taso bariki ta fad’a mata wa zata aura amma bariki ta’ki Tadai fad’a mata dan gidan sarauta ne, abunda kawai bariki ta fad’a mata kenan……….
A kwana a tashi babu wuya wajan uban giji, bariki ta gama istabra’i,  sannan iyayenta sunyi aure, mai martaba ya siya musu Gida Mai kyau 4bedroom a u/kanawa inda anan iyayen nata na Bariki suka tare, sannan bariki tace ta bar musu gidan halak malak, domin suna Mata aiki yanda ya dace, bariki ta K’ara kyau da haske domin ana mata gyaran jiki Sosai…..
Yau bikin bariki da Yarima baifi kwana Goma ba,  Yarima yanzu ba kullum yake zuwa wajanta ba, domin aiki sunyi mishi yawa, ga hidiman biki, gana asibiti ga fitinar zinatu, abubuwa sunyi mishi yawa Sosai….. Yana office ya Gama duba patient yaji yana bukatar ganin Zainab dinshi dan haka ya tashi ya nufi gidansu, wanda yanzu in yazo ciki yake shiga dan akwai falon ba’ki a gidan, kiran Zainab din yayi yace ta sameshi a waje basai y’a shigo ba.
Fita tayi inda ta sameshi a mota ta bud’e ta shiga tare da gaidashi
Mai makon ya amsa sai yace Kai my princess Kinga yanda kike K’ara kyau kuwa?? Gskya ana gyaramin ke dakyau,
Murmushi tayi cikin jin kunya  sannan tace Kai Yarima wani kyau nake karawa?? Tayi maganan a shagwabance
Yace Zona nuna miki tare da janyota jikinshi, wani irin kamshi ne ya daki hancinshi Wanda tunda ta shigo yake ji, amma daya janyota jikinshi sai yaji kamshin ya fito Sosai, gaba d’aya yaji jikinshi ya fara weak domin kamshin turaren yasa jikinshi ya fara yin sanyi…..  Itama ta gefenta wani iri take ji domin maganin da ake bata ya tsumata Tana matukar bukatar namiji amma babu yanda ta iya dole sai mijinta Bayan tayi aure, gashi yanzu Yarima yana son tada mata bala’i…. Yarima Aliyu hura mata iska yayi a fuska da sauri ta d’ago   suka had’a ido peck yakai mata a goshi tare da furta I love you my princess
Da sauri ta lumshe ido
Ganin haka yasa Yarima ya kura mata ido yana kallonta tare dajin wani irin mugun sonta na K’ara shiganshi…. Jin shuru yasa ta bud’e ido a hankali idonta ya sauka cikin kwayar idonshi da yake kallon nata idon…..  Dukansu wani irin yanayi mai wuyan misaltuwa suka shiga……. Karan wayar Yarima yasa ya saketa ta tashi da sauri daka jikin nashi ta koma ta zauna dakyau….. Daukan  wayan yayi ya duba, ganin mai kiran yasa bai d’auka ba, zinatu ce……
Bariki kam gaba d’aya ta birkice, dan dan tabata dinnan da Yarima yayi har tana jin zuban ruwa a cikin pant dinta, lallai ya kamata Yarima ya rage zuwa, ko kuma ya daina tabata….  Domin Indai hakan zaici gaba da faruwa zata sha wuya, ido ta lumshe tasan ba komai yake sata yawan sha’awa ba sai maganin da take sha, wacce y’ar Sokoto take bata…..
Yarima ne ya Katse Mata tunani da fad’in, my princess zan gudu, bata sim yayi guda d’aya tare da cewa ta cire nata, baya son ta kara amfani dashi…..
Amsa tayi, tace toh dama tun tuni take da burin canza layi, amma tana tsoran Kar Yarima yace Mai yasa, yanzu tunda ya kawo mata, hankali kwance, sannan ya bata check na 3mil yace a K’ara gyaran jiki domin naga suna gyaramin ke dakyau……
Tace Yarima kafa ban kud’i cikin kwanakin nan, kaban a kalla wajan 7mil kace in siya kayan akwati, kuma gashi kace May be gidanku su Kawo nasu gobe ko jibi, kai kamin gashi gidanku zasu kawo, ga kud’i kuma kana karamin, gskya abun yayi yawa, ka barshi…..
Bata fuska yayi tare da fad’in in kin ciro kud’in ki zubar a bola tare da ajiye mata check din a jiki…..
Ganin yanda ya bata fuska, yasa tace Yarima kayi hakuri, wlh ba haka bane, naga hidimar tayi yawa ne Sosai, Kaga y……
Yace enough, komai na miki, kin can Canta inyi miki shi, and karki manta am your husband to be, waya kamata inyi ma Abu Inba keba??  In my life ban taba kyauta ko wani abuba a nuna ba’a soba sai ke..
Da sauri tace kayi hakuri plz na tuba, ngd Allah ya saka da alkhairi….
Jin ta fad’i haka yasa yaji dad’i…..  Ba komai yasa Yarima ya bata wannan kud’in ba, sai sanin da yayi ba masu hali bane su, and y’an uwanshi zasu Kawo akwati, ance ana bada kud’i, sai yasa ya bata wannan kud’in dan iyayenta su bada tukwici…  Ajiyan zuciya yayi tare da fad’in zan tafi sai munyi waya,
Tace OK
Yace kin dai ki zuwa kiga gidanki koh?
Tace Yarima saurin Mai kakeyi?? Ka Bari har a kaini mana
Murmushi yayi domin kin amincewanta yasa ya kara yarda damai tarbiya da kuma kamun kai zai aura, sabanin matan yanzu da suka lalace suke ganin haka shine wayewa, tab kunji Yarima shi’a dole zai aura ustaziya????
Sallama ya Mata sannan ya wuce……
Bariki gida ta shiga jiki a sanyaye lallai Yarima yana matukar sonta da yawa, hawaye ne ya gangaro daka idonta, tare da tausayin kanta yanda zai dauketa in yasan ko ita wacece……
Anata shirin biki musamman ta gefen ango, domin dai ita amarya rufa rufa take ma auran ba kowa bane ya sani, sai dai zargi da wasu sukeyi……
Ranan da za’a kawo akwati saida bariki da habib sukai hayan mata guda biyar, An kawo akwati guda ishirin da hud’u, dozen biyu kenan, kaya ne makil na Kece raini masu tsadan gaske…..  Ganin yawan kayan yasa umman bariki taga 1mil yayi kad’an dan haka ta sami bariki dake boye cikin wani d’aki, tace ya kamata a K’ara kud’in nan Kinga uban kayan kuwa?  Bariki kara 1mil tayi ya zama 2mil, nan aka basu kud’in tukwici, tare da abun ciye ciye da aka tanadar musu, bayan sun fito sis din Yarima Fatima tace Kai ance yarinyar talakawa ne amma har da bata 2mil, Aini ban d’auka zasu bada koda dubu d’ari ba, dariya sukayi sannan aka canza firan,
Bayan sun tafi bariki ta fito tana kallon kayan, itama Abun ya bata mamaki ganin kaya masu uban yawa da tsadan gaske, yanzu ga akwati ishirin da hudu, gashi kudin da Yarima ya bata itama ta siya guda sha biyu, duka talatin da shida…..
 Ummanta ta bariki tace Kai gskya ki gode Allah y’ar nan, Yaron nan yana sonki Sosai, ji uban kaya sannan kayan d’aki yace baya bukatar komai, kai Kinji dad’i wlh
Bariki murmushi kawai tayi jiki a sanyaye, domin sai yanzu ta Fara jin tsoran abunda take kullawa na auren bariki, da tana ganin abun kaman wasa, amma tunda har taga akwati yau an kawo ta tabbatar Abun dagaske ne, d’aki tayi ta Fara rusgan kuka tare da fargaban abunda zai biyo baya….. Hmmm Allah ya kyauta dai zan iya cewa
Biki ya kan Kama amma amarya bata cikin nutsuwa kullum tana cikin fargaba, harta rame saboda damuwa, kullum bata da wani aiki sai kuka tare da K’ara tsanar rayuwar bariki…….. Tana cikin wannan kukan Yarima ya kirata, da sauri ta seta kanta dan Kar ya gane sannan ta d’auka…
Gaidashi tayi
Amsawa yayi tare da fad’in ya naji muryanki haka??
Da sauri tace mura nakeyi Yarima
Yace toh fah, Allah ya sawake zan Aiko miki da magani.
Tace nasha tun dazu
Yace OK, toh ya shirye shirye?
Tace Alhamdullilah
Yace za’a Aiko miki da kayan da zaki saka a dinner sannan masu makeup za suzo suyi miki ranan, lil sis taban sa’ko in fad’a miki
Bariki tace ok Allah ya kaimu
Ya amsa da Ameen, sun d’an taba fira Kafin sukai sallama…..
Yana ajiye wayar gimbiya zinatu ta shigo, Tana fad’in yanzu Yarima saboda cin fuska a cikin gidan nawa kake waya da wacce zaka aura??? Kuka ta fashe dashi tare da fad’in haba Yarima Wlh kana cimin fuska da yawa maina maka haka da kake Yimin wannan abun??
Ganin yanda take kuka sai yaji ta bashi tausayi, rarrashinta ya farayi…..
Gimbiya zinatu ji take kaman ta tureshi Dan tsabagen kishi, Allah ya sani da badan gimbiya Amina tana kokarin hanata wani Abun ba da Wlh babu abunda zai hana tayi ma Yarima mugun tujara, amma Gimbiya Amina tace tayi hakuri ta Bari Ayi auran zata nema Mata mafita, yarda da gimbiya Amina da tayi shine yasa har take dan jurewa, amma ji take kaman zata mutu dan kishin Yarima take Sosai, bata son ganin ko wace mace kusa dashi……
Toh biki ya rage saura kwana biyu, inda a yau za’a gudanar da dinner, bariki da habib sunyi hayan kawaye Wanda sune kawayen amarya, cikin kawayen harda haulat da khairat, zuwan haulat gidan iyayen bariki yasa ta gane yanda bariki ta shirya auranta, ta gano tayi amfani da iyayen bariki, haulat ta kalli bariki tace gskya kinyi dabara, nima Ina tunanin haka zamma farhan, in samo iyayen bariki
Bariki ganin Haulat ta gano komai, yasa tace inko za kiji shawarata karki Fara yin aure da iyayen bariki, gwara ki koma Gida wajan danginki
Haulat tace Hmmm kedai kawai Ayi sha’ani,
Anyi ma amarya makeup na Kece raini, tayi mugun bala’in yin kyau, gaba d’aya makeup din da aka mata yasa ta canza, ta kara mugun kyau dama yaya balle an kara da wanka, an shiryata cikin wani tsaddan material Mai Kama da less anyi mishi dinkin doguwar riga, k’asan kuma anyishi da fad’i kaman weeding gown, an saka mata head maroon kayanta kuma golden, ba karamin kyau tayi ba, kawayenta kuma sunsa kaya red head golden, ba karamin kyau bariki tayi ba, da kawayenta, 7 dai dai aka turo motoci dan d’aukan amarya da kawayenta zuwa wajan dinner da za’ayi a cikin garin kaduna, duk y’an uwan ango suna kaduna, an d’auki amarya an nufi hall da ita, inda motarsu na zuwa na ango yazo, dan haka Yarima ya fito ya nufi motar da Zainab ke ciki, Yarima daya ganta ido ya kara bud’ewa ganin irin kyau data K’ara kaman ba ita ba, dama yasan tana da kyau gashi anyi mata makeup, lokaci d’aya kuma sai yaji yana kishin ta shiga Ayi ta kallonta, ya dad’e a motar yana nazari akan baiso ta shiga…..
Itama ta gefen amarya fargaba take, karta shiga taga Wanda ta sani, asiri ya tonu…..
Jin Yarima shuru yasa usman yazo yana buga glass din motar
Bud’ewa Yarima yayi tare da fad’in Usman gskya aje abama mutane hakuri, an fasa wannan dinner din, suci abinci kawai su wuce
Usman yace Yarima. Kasan Mai kake fad’a kuwa?? Plz Yarima ku fito mu shiga
Yarima yace kasan inna fad’a magana bana canzawa koh??
Usman shuru yayi yana nazari can yace dan Allah Yarima kayi hakuri ka duba girman Allah karka bamu kunya……
Yarima ya dakatar dashi da fad’in am telling you kayi abunda nace, wannan umarni ne…. Karan wayanshi yasa ya d’auka ganin lil sis
Yana d’auka tace Bros ku shigo mana kowa na jira, dan Allah kuyi sauri
Yace sis am sorry bazan zo ba, kuba mutane hakuri …..
Tace what? Tare da tashi ta fito waje dan taji dakyau, hango usman tayi da Yarima a tsaye da sauri ta nufesu, tana fad’in bros miye haka plz kuzo ku shiga….
Zaiyi magana tace plz koso kake ace akwai matsala ne??
Yace let people say what ever, nidai bazan shiga wannan wajan ba.
Hafsat tace bros akan wani dalili?
Yace ban son ayita Kalle min Mata, inada kishin iyali na
Hafsat hannu ta d’aura a Kai, alaman takaici, danta d’auka wani abune akayi mishi da yasa yace bazai shiga ba, motar da bariki take Hafsat ta nufa, sai gata ta fito
Ganin amarya a waje yasa Yarima ya fara yima Hafsat fad’an Mai yasa zata fito mishi da mata….
Hafsat tace bros nifa bani na fito da itaba
Kallon bariki yayi yace Oya muje in kaiki gida
Tace Yarima plz muje mu shiga, zaiyi magana tace dan Allah, karka sa mutane suyi zargin wani abu tana maganan tare da kokarin San zubar da kwalla…..
Ganin haka yasa yayi dan tsaki tare da fad’in karki Fara cewa zakiyi min kuka a nan, dan naga kina da Arhan hawaye, babu yanda Yarima ya iya dole ya shiga shida abokanan shi da amarya da kawayenta, cikin hall din yayi mugun tsaruwa, wajan zaman amarya da ango daban su biyu, y’an jarida da masu hoto sai d’auka suke, kowa yana fad’in amarya da ango sun dace dinner din ya had’a manyan mutane ciki harda Mai martaba, Yarima bai San zaizo ba saida Ya ganshi shida abokanan shi, harda Mai girma governor da wasu masu mukami a gwamnati sun halarta, anyi watsi da naira kaman baza’a mutu ba, an yanka cake daka nan akace amarya da ango suzo suyi rawa, nan suka fara rawa duk da bariki ba a sake take ba, dan tana jin tsoran ko akwai wanda ya Santa a wajan, nan aka fito ana watsa musu naira mum din Yarima tayi musu liki Sosai, a cikin masu likin idon bariki ya sauka akan Alh madu, dam gabanta ya fad’i, musamman irin murmushin da taga yana sakar mata, gaba d’aya jikinta taji ya saki babu kwari, Yarima kaman ya Lura da ita gashi kuma mutane sunyi yawa ko ince maza dan haka Yarima yaja hannun Zainab suka koma suka zauna, Anci ansha kowa ya watse, Yarima yakai bariki gida da jikinta yake a muce ganin Alh madu a wajan dinner, yanda ta gode Allah ta canza layi ma balle ya mata barazana, toh inya fad’a ma Yarima fah??  Nan taji gabanta ya fara fad’i
Bariki harta Washe gari tana cikin zullumi Kar asirinta ya tonu, haulat Dai da khairat sunyi Mata kara domin a gidan suka kwana, dasu kuma ake komai, bariki na kwance haulat tace wai lafiya kuwa naga kinyi shuru??
Bariki tace kalau nake
Haulat tace dan bani wayarki in bud’e hotspots banda data gashi Ina son tura Abu.
Password din wayar bariki ta cire sannan ta mi’ka ma haulat wayan…..
Toh rana dai bata Karya inji masu iya magana yau juma’a aka d’aura auren Zainab musa da angonta Yarima Aliyu, akan sadaki naira dubu hamsin inda dubban jama’a suka shaida……
Bariki tunda taji an d’aura take ta godema Allah, domin anyi auranta cikin nasara ba tare da Yarima yasan gaskiya ba, a hankali tace yau zan fad’a maka koni wacece Yarima Indai aka kawo ni gidanka,….. Karfe hud’u dai dai aka zo aka d’auki amarya inda aka tafi da ita Zaria a can zata zauna Kafin a dawo da ita kaduna, gefen Yarima Nada aka kaita inda aka gyarashi harta wanda suka kawo amarya bariki hayansu tayi, an karrama amarya da danginta wajan su abinci da duk abunda suke bukata, nan sukace zasu wuce tunda sun kawota, anyi musu shatara na arziki Kafin nan suka wuce……
Wajan karfe 9 Yarima ya shigo d’akin amarya ba tare da Aboki ko d’aya ba, dan yace kallon da suka mata wajan dinner ya isa haka, bariki na zaune akan gado Yarima ya shigo tunda ya shigo gabanta ke faman fad’i, inda take ya nufa tare da cire mata gyalen dake kanta yace Alhmdlh tsarki ya tabbata da Allah daya nuna min wannan ranan, janyota yayi jikinshi yayi mata wani irin runguma, har tana jiyo ajiyan zuciyarshi, lokaci d’aya ya saketa tare da d’agota ya sauketa k’asa yace my princess muje muyi alwala muyi ma Allah godiya…..  Gabanta taji yana fad’i yaka mata Yarima yasan gaskiya Kafin wani abu ya shiga tsakaninsu, wayarshi dake ajiyu yayi kara d’auka yayi yaga number kaman Karya d’aga, sai kuma ya d’auka, ban son mai aka fad’a mishi ba naga ya kashe da sauri tare da fara danna wayar duk wannan abunda ake suna tsaye shida bariki suna kallon juna amma shi idonshi nakan wayar….  Lokaci d’aya hawaye ya fara zuba a idonshi tare da fad’in today is our wedding night, the day dat I have waiting for since d day dat I have meet u, but you destroy my life, you have cheated me….. Cikin tashin hankali tace Yarima maiya far…. Yace keep quiet tare da ri’ke kirjinshi alaman yana mishi ciwo yana kokarin yin magana ya fara tari Sosai lokaci d’aya yayi k’asa……
TOH MASU MIN KORAFI IN K’ARA YAWAN RUBUTU YAU DAI NA K’ARA, AMMA KUDA KUGA WANI POSTING DIN SAI NAN DA KWANA UKU, BUT IN NAGA COMMENTS DINKU YAU YAYI YAWA MAY BE GOBE IN MUKU
not edited
MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button