Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
COUSINS NENOVELS

COUSINS NE 7, 8, 9

Ad

_____

PAGEā€¦.. 8-9

Bismillahir – Rahmanin rahim.

wannan shafin nakine mrs farook Allah yabar kaunašŸ„°

Aleeyu tunda yatashi yake cikin farin ciki wanda duk gdn su bbu wanda bai fahimci hkan ba Allah’ Allah yarinka yi dare yayi amma gani yake tym baya guduā€¦ Yana fita ya shiga part din iyayen shi sama ya sami hafsa da Aisha suna kallo kasancewan sunyi hutu islamiya ina umma tana daki suka ansa masa atare knocking yayi akace yashigo gaishe da ummansa yayi yace mata zaikai su hafsa shoprite adawo lfy tace masaā€¦. Fitowa yayi yace su shirya zasu fita daga hka kitchen ya wuce direct ya hada tea ya koma part dinsa yana shan tea ya shiga yayi wanka ya shirya cikin Kanan kaya black tshirt yasa da jeans blue wanda kayan ba karamin kyau yamasa ba fita yayi yasamu su hafsa da zumudi agun motarsa suna jiransaā€¦ Bude motan yayi suka shiga yajasu bai tsaya ko inaba sai shoprite suna shiga wajen wasan yara sukashiga wasa sukayi sosai kafin suka koma sukaci abinci suka yi siyayya nan Aliyu yadauki su body spray da turansa dasuka kareā€¦. Basu koma gda ba sai wajan 5 suna isa gda suka samu umma parlorn kasa tana kallo nan Aleeyu ya bata nata tsarabar A’a gadanga nima harda ni a tsaraba ne to Allah yayi albarka turaruka yasayo ummansa dan ita ma’abo ciya son kanshice nanta samasa albarka ummana ai bbu yawa, ai meyawan knan watarana za’akawo wanda yafishi Allah yamaka albarka babana Ameen yace yana mikeyewa dan komawa part dinsa, Aleeyu nashiga yawuce yayi wanka ya dauro alola yana idar da sallah wayansa tafara ringing har yakusa tsinkewa ganin saeed ne yasashi dagawa childhood frnd dinshine sun shaku sosai dan iyayensu ma abokaineā€¦.. Sallama saeed yayi yace kai kace yau kazama musulmi dariya yayi yace dani arne ne nifa bansan iskanci Aleeyu nasan yanzu ananan anata rawar kai kaman sabon ango nifa bansan iskanci in baka da wata important issue nakashe wayata dariya saeed yyi yace yaune fa ranan yanda akedamuna da lbrn khadijerh aidole nakira yau nasha lbr,infact zanzo da daddare inka dawo naji yanda kukayi dariya Aleeyu yayi yace saika matse bakina ai infada maka oho nidai nafada maka anjima zanzo kokazoma bbu abinda zakaji nansuka zolayi juna suka dan taba hira akan aikinsu suka yi sallamaā€¦ā€¦ā€¦.

Yau tunda khadijerh ta tashi take rawa da earphone a kunnenta fatima ce tace khadijerh yau lfy kuwa dan nasan bakya rawa saide inkina farin ciki dariya fatima tabata tace nidai bbu komai kawai yau rawa nake jinyi, tacigaba da rawanta itadai Fatimah na kallon ikon Allah. ā€¦ā€¦

Alhaji Ahmad ne yadawo daga kasuwa dan tunsafe yafita kasance wan akwai business din dayakeyi ko weekend baya zama gda bai shigo gda ba sai magrib ko cikin gda bai shiga ba sanda yaje masallaci yayi sallah yashigo gda a dining yasame su gabadaya suna cin abinci nan yayi joining dinsu gaishe shi duka yaran sukayi mummy tayi saving dinsa suna kamallawa yace mata zaije can gdn Alh usman akwai mgn dasuyi inya dawo zai mata bayani adawo lfy tace masa, yana tashi khaleel ya yace daddy zan bika khaleel dare yayi nima dolece zata kaini kushirya harda hajiya gobe insha Allah kuje kuyo musu wuni nanduka suka shiga murna shikuma ya wuce gdan dan uwan nasa,,yana zuwa mai gadi yabude masa gate yashiga direct parlor yashiga nanyasamu daidai da fitowan Fatimah zata shiga kitchen gashe sa tayi ya ansa yana zolayanta taje tace barita sanar da iyayenta, tare suka sauko da fatima da mahaifinta nan gaisawa suka suka dan taba hira kafin daga bisani suka soma mgn daya kawo Alh Ahmad mamace tayi min mgn akan wai yarannan sufitar da miji harda kuka takemin mgn da kyar nasha kanta nace zanzo muyi shawara, Alh yace kasan sha’anin tsoho saida rarrashi dole mubi mgn ta ai dan arabu lfy mama ta saukko suka gaisa takoma kitchen tasa hauwa ta hada snacks drinks da ruwa takaima su Alhajiā€¦ā€¦

Aleeyu na idar da sallah yayi wanka ko takan abinci ranan baibi ba yasaka shadda skye blue ta matukar mishi kyau da hula blue sai takallmi black inkagan shi inba ance ba zakazata angoneā€¦.yanagama shiri ya bugawa khadijerh waya suka gaisa inanema kikace unguwar ku sharada phase 2 kashigo ta police station second line din zaka shigo zaka wani gda milk colour up stairs ne da bakin gate kayi parking anan zan fito ok am on my way insha Allahā€¦

Yana kashe waya khadijerh takama shiri dan dama daga wanka tafito wata doguwar riga pink tasaka tayi rolling da bakin gyale bawani ado tayiba dan ita ba ma abociya make up bace powder kawai tasa da lip glow dan bakinta two colour ne saman bakine kasan kuma pink ne har classmates dinta suna tsokannanta da unique lips, kiran Aleeyu ne yashigo wayanta wanda saida zuciyanta yabuga batasan daliliba nan dauka tayi da sallama nazo ok tace masa,tama Fatimah sallama ta fita da sauri ta karasa gun da iyayen nata suke dan tana wanka lokacin da daddyn ta yazo gaishe sutayi ansawa sukayi dukansu tawuce sama gun ummanta dan sanarda ita za’azo gaishe da abba gashi yayi sa’a ya tararda suduka,dan dokan zurian sune kafin katsaya da saurayi sai iyaye sunsan shi,shiyasa basu damuda samari sai suzo gda ba dan wasu samarinma a waya ake rabuwa itada bama kulasu take sosaiba kowani tarkace ai sai Fatimah, to umma tace mata suka saukko taredan ta sanar dasu Alhaji khadijerh kuma ta wuce tashigo da Aleeyu tamasa iso ya shigo da motansa bayani da tamasa yasa shi jin dadi dan dagaji yar gdn mutunci ce, har parlor taraka sa amma saita ki shigaā€¦.

HHHH SU KHADIJERH ANGIRMA HARDA KAWO MAI GAISUWA HMM MUJE DAI ZUWA DAN JI YAZATA KASANCE TSAKANIN SU PLEASE COMMENT AND SHAREā€¦.. THANK YOU ā¤

Ad

_____

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button