A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

⋆☆A ZATO NA…!☆⋆

  *⋆©Jeedderh Lawals⋆*
             *☆⋆01⋆☆*

     Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Muna kara godiya da taruwarku a wannan zaure mai albarka, ina fata Allah Yasa mu gama lafiya kamar yadda zamu fara lafiya. 

Littafin ‘A Zato Na’ mallakin wadda ta rubuta ne, ba’a yarda wani/wata su canza kowace irin suffa ta wannan littafi ba.

Muna fata zaku rike mana alkawari, ku kuma rike mana amana. Allah Yasa mu dace.
Da sunan Allah Mai Rahma Mai jin Kai’

‘Kirr! Kirrr!!’…

Karan daya ziyarci kunnena kenan lokacin da na danna lambar wayar kawata Janan. Bata dauka nan take ba, sai da yayi kara kamar sau biyar.
Kafin ta dauka hakurina ya gama karewa, saboda haka tana dagawa, ban bari ko sallama tayi ba na tare ta da; “wai dallah can malama me kika tsaya yi ne kin tsaida mutane?”.

Tace “jeez girl, bi a hankali mana. Ina jiran Anty Raheemah ne ta dawo kafin in fita”.

Na ja dan siririn tsaki, “kawai ki fito ki bar mata gidan a haka mana. Ba maigadi yana nan ba?”. Janan tayi ajiyar zuciya, “kin fa san abinda ya faru last time da nayi haka. Tace an shiga an mata satar kudi da jewelries, kuma dole sai da Yaya Bilal ya biyata sannan aka zauna lafiya, bana son abu makamancin haka ya sake faruwa”. Nace “sai kiyi ta zama ai ta mayar da ke maigadinta. Ni dai wallahi idan baki zo nan da mintuna goma ba ko? Sai dai mu hadu da ke acan kawai!”. Ban jira ta kara cewa komi ba na kashe wayar na ajiye ta a gefena.

Browsing naci gaba da yi da system dina, sai da nayi kamar minti goma sha biyar kafin na kashe na ajiyeta a mazauninta. Janan na sake dannawa kira, tana dauka tace “gani nan don Allah, sarkin gajen hakuri kawai!”. Na tabe baki ba tare da na damu da abinda tace ba, nace “better. Idan kin iso ki kira ni kawai mu hadu a main entrance” tace “toh”.

Gadona na dan gyara kafin ta iso. Zuwa lokacin da Janan ta kirani, na gama kimtsawa. Na dauki gyale na nada shi a kaina yadda ya zagaye rabin kirjina da bayana, na dauki wayar hannu, purse da flat din takalmi ruwan goro kalar veil dina da zanen flower da yake jikin doguwar rigar gown ta atamfa da na sa, na zura shi a kafata. Aylah, roommate dina na yiwa sallama na fita.

A bakin hostel din Queen Amina dake cikin campus din ABU Zaria, na tsaya ina karewa wajen kallo cikin neman Janan. Ina kokarin kiranta a waya na hango ta acan inda ake parking motoci a gefen hostel din tana dago min hannu, murmushi na saki cike da murna da dokin ganinta na taka a nutse na tsallaka zuwa inda take. A tsakiyar wajen ta tareni, muka rungume juna cike da doki. Duk duniya, ita kadai ce naki jinta kamar wata yar uwata ta jini, kamar yadda nasan itama haka take a bangarenta.

Na kalli iNext din da naga ta fito daga ciki ina daga mata gira, “Ya Almu ya sake sabuwar mota ne hala?”. Ta girgiza kai tana murmushi, “ina Almu na yayi arzikin sayen irin wannan abun? Yaya Bilal ne”. Na dan zare ido cikin mamaki, “Holy Wow!! Yaushe rabon da in ga Yaya Bilal? Har na manta wallahi. Yau dai Allah ya nufa zamu hadu kenan!”.
Tayi dariya da tasa dimples dinta suka lotsa, abinda yake burgeni da haliitar ta kenan. Tace “sosai ma. Allah ne yasa ban samu abin hawa da wuri ba, shine yace bari ya kaini tunda shima wajen FCE din yayi. Taho muje, muna kara makara”. Na bi bayanta zuwa wajen motar.

Janan ta bude gidan gaba, ni kuma na bude baya muka shiga a lokaci guda, bakina dauke da sallama. Sansanyan kamshin freshener na cytrus da mix din strawberry ya doki hancina hade da sansanyan sanyin AC daya dumame motar. Muna tsakiyar watan May ne, saboda haka ba karamin zafi muke sha ba a garin na Zaria.

A nutse na gaishe da Yaya Bilal, ya juyo a kaikaice ya amsa tare da juyawa ya tashi motar muka bar wajen. Babu abinda na iya kararwa game dashi sai cewa faded jeans ne a jikinshi da T-shirt mai zanen zebra a jiki, sai sunglass da ya saka ya sakaya idanunshi.

A hankali yake tukin, tattausar kira’ar Sheikh Malam Minshawee tana tashi cikin suratul-Kahf, na jingina kaina da kujerar motar na lumshe idanuna, a can kasan zuciyata kuma ina bin kira’ar bi da bi. Yayin da a gefe guda, shi da Janan suke hira jifa-jifa. Har muka isa makarantar Kongo, inda zamu je, a bakin gate ya nemi waje yayi parking. Sai a baki-baki ma yayi parking din, saboda yadda wajen ya cika da mutane da ababen hawa. Muka mishi godiya muka fita, ya ja motar ya tafi, mu kuma muka tunkari gate din makarantar.

Ranar babban Shehin malami, ‘ Dr. Bilal Philips’ yake zuwa yin wa’azi. Saboda haka, you can only imagine yadda wajen zai cika da mutane wai don ma na mata ne zallah. Duk da mun zo kusan mintuna arba’in kafin a fara wa’azin, da kyar muka samu wajen zama muka zauna.

Akan Matan da zasu shiga aljanna yayi wa’azin ranar. Kafin ya gama, jikin kowace diya mace dake wajen yayi sanyi saboda yadda ya dinga zano abubuwa da mu mata muke yi, muna tunanin ba wani abu bane, either ga junanmu ko ga mazaje da iyayenmu, alhalin abubuwan nan za su iya jagorantarmu zuwa wuta. Karfe sha biyu na rana aka gama wa’azin, saboda karancin abubuwan hawa da aka yi ranar, bamu samu mun koma cikin makaranta ba sai kusan karfe daya da rabi.

A dakina muka sauka, Janan tayi sallar azuhur, kafin ta gama ni da bana yin sallah na gama dafa mana jollop spaghetti. Bayan mun gama cin abincin, kan gadon muka hau, na kunna mana film din Pick the Stars, wani Korean Film, muna kallo. Bamu jima da fara kallon ba, barci ya daukeni.

“Na’ilah!”.
“Uhmn?” na amsa cikin barci.

A hankali naji an kai tattausan hannu gefen fuskana an shafa cike da wani irin tenderness da yasa naji bugun zuciyata ya canza sosai. “I Love You, baby! So much!!”.
Aka fadi a daidai saitin kunnena, cikin wata irin tattausar murya. A hankali na bude idanuna dake cike da barci, mutumin da ke zaune a gefen gadon da nake kwance, appears very blurry, bana iya ganinshi cikin rashin hasken dakin.

“Na’ilah?” naji ya sake kirana cikin tattausar muryarshi, na saki murmushi a tausashe ina amsawa, “uhmmn??”.

“Na’ilah!!”. Wannan karon naji an kirani da karfi. A gigice na tashi zaune, kaina ya bugu da bango. Da sauri na dafe wajen na maida kaina kan pillow ina hararar Janan dake zaune a gefena, tana kallona cike da alamun tambaya.

Harara na jefa mata tun karfina, cikin tsiwa nace “dallah can Malama meye haka, zaki katse min barcina mai dadi?”.
Ta daga kafada, “maganganu kike yi cikin barci. Abin naki ya dawo ne?”.

Na kara komawa kan katifar na kwanta, “Wallahi kuwa Jan. Yaushe rabon ma da inyi irin mafarkannan? Har na manta. Sai yau”.
Janan tace “to sai ki kiyaye da addu’o’i dai. Is’haq yazo yana jirana a waje, bari in tafi”.
Na duba naga yamma har tayi.

Na mike ina lalubar mayafi na, “muje in miki rakiya to!”.

Ta tashi na rufa mata baya, dakin na rufe kasancewar abokiyar zama na bata dawo ba, muka sauka kasa ni da ita.
Har parking lot na rakata inda Is’haq yake jiranta. Ta bude gidan baya ta shiga, na maida mata kofar na rufe ina daga mata hannu, a haka suka tafi. Sai da na tsaya anan kofar hostel din na sayi yoghurt babbar roba mai sanyi sannan na koma daki.

Bayan na yi yan gyare-gyare da kimtse-kimtse na, arm chair na dauka na ajiye a gefen gadona na zauna, na dora laptop dina akan gadon na bude tare da cigaba da kallon da muka fara ni da Janan.

Sai bayan magriba Aylah, roommate dina ta dawo. Har zuwa lokacin ina kan system dina, ta min sallama na amsa, a gajiye ta zauna a gefen gadonta. Sai da ta huta, sannan tayi sallah. Taci sauran spaghetti din da muka bari ni da Janan.
Ni kam karfe bakwai tana yi, na kashe laptop din na mike. Kasa na sauka inda common room yake, na kalli serieses din da nake kallo a Zee World; Twist of Fate da King of two Hearts. Karfe tara na koma daki, ina zuwa shirin kwanciya barci nayi cikin riga da wando, na bi lafiyar katifa na kwanta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button