DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

Jin Fu'ad ya kwana a police station Abbi da sassafe yabi ta sama manyansu ya kashe case din gaba daya,aka Kira su momy aka ja musu kunne Nan ma gwiwarsu tayi sanyi,Bamu San anyi ba muna kulle sai gani Mukayi Yan Sanda an bude mu Ana ta Bamu Hakuri,na fito nace da karku bude mu Mana wallahi ku gani,wani katon ciki cikin Yan Sanda yace Iyyeee kaji Yar fici har da ke Wato kin Isa ko? Nace ae har nayi yawa,Wayoyinmu da komai namu suka Bamu muka fita Uban Izzar Ana ta takama Yana wani kumbura,Taxi Muka Shiga sai gida.

Bayan komai ya lafa Abbi duk tafiya aikin Hajjin ma fasawa yayi a gida kowa zaiyi Azumi,wannan Azumin shine Azumin da zanyi talatin cif a duniya,tunda aka fara Azumi a garden dukkan Yan gidan suke taruwa kowa da kowa Kuma kowa da carpet dinsu daban,Nan sunyi rukuni can ma Haka,wacce ke da girki itace ke Zama a shimfidar Abbi, Fu'ad kuwa shi kadai ne a carpet dinsa Kato,Yanzu Yan gidan ganin Basu da sauran abin da zasu Yi min sai dai tsangwama da hantara,ko da na fito wajen na nufi carpet din Yan matan tun kafin na karasa Safna da Naila Suka min alama da hannu na koma,Umma tana tare da Abbi,matansa su Momy nasan ma bazan rabe su ba Kawai sai na juya na koma wajen Fu'ad shima Ina tsoro kar ya Kore Ni sai kuwa gashi Bai ce komai ba na zauna kasan kafafunsa.

Zamu fara cin abinci kenan Khaleesat Tace je ki karbo min yaji,to nace na Mike Zan tafi Fu'ad ya daka min tsawa zauna idan ta Matsu taje da kanta,ai kuwa na koma na zauna,Na fara cin abinda nake so a cikin kayan Shan ruwansa kowanne abinda ke so yake ci,idan Ina son wani abin ma wajen Su Islam nake ebowa ba ruwansu Dani har Hira mukeyi da su,a nutse kowa ke ci Amma Ni sabo da bana jure yunwa kamar yaki Haka nake ci,in cinye wannan in shanye wancen,duk abinda Fu'ad yaci ya Kara ragewa Haka Zan dauke na Kara dannawa ciki na,Su Hakeem suyi ta min dariya,Islam yace shi yasa kullum buleliya kike Zama kina ta cika gaki har kin Zama Yan Mata sai Aure Wanda ya aureki ya Dace,kalarki bakwa tsufa, Fu'ad ya Harari Islam,Islam yace sorry Babban Yaya na manta na Yaba maka Mata,Ai sai Fu'ad ya dinga bala'i shi ba matarsa bace,Ni dai Ina cin Dankali na nace Kai kudi sunyi a rayuwa dole Iya taso kudi Ashe Iya ta Gama gano kan kudi,Yanzu Fadila ma tana can tana soye soyenta,Iyata Allah ya Baki halin yin soye soye kema,aka dinga dariya har su Khaleesat naji girki harda tuno da Fadila,na Bude farfesun kaji nace to jama'a su Fadila ko Ana can Ana soye soye ko Kuma Ana ta fada da Miji Bata iya girki ba,nasan ma tana can tana ta shirga Masa kwaba a gidansa,wlh ayi Sauri a Kai Mata me Aiki kar ya sako ta da wuri akan girki kadai ya Isa a koro Fadila bare sauran munanan Halayenta,wa ya sani ma ko yanzu Mari ta Sha Guda Uku oho,Momy ta jefe Ni da takalmi karya kike Munafuka,Abbi Basu San me akeyi ba, Fu'ad Yace dazu da Rana a kasan tiles kika kwanta kina ta birgima Akan kina Azumi ko magana bakya Yi,Makarantar safe data Yamma duk Baki je ba Akan Azumi Amma yanzu an Sha ruwa kinfi kowa surutun masifa.

Nace Ina ma da Iyata yanzu Muna mutunci da sai na Kira ta naji wacce wainar take toyawa ita da Ali Shagali me shayi,au bakwa ma mutunci kika ce?Muna magana su Momy suna gulma mama Tace kinga suna Hira shegu,Momy Tace Ina kallonsa Yana ta wani kashe Mata Ido daya da alama yau tare zasu kwana Dan Kira yake mata.

Ni kuwa ban sani ba naci gaba da surutu na nace da gidan talakawa ne da yanzu Mata Ana ta kishi Ana masifa da bala’i har makwafta Ashe kishi ma an fi Yi a gidan talaka,Kai tsiya tana gidan talaka,Amma Nan kowa da kudinsa Ina ruwan wani da wani,Habaici na fara yiwa su Momy Ina Waka nace Alhmdllhi naci na Sha yanzu ko me za ai ayi,gida Ana Zaune lfy akan Yar yarinya an hargitse Ana ta yaki Ana kashe Kudade Ana tashin hankali,Allah ya Zabeni, Waliyiya Rumaila,na zama Waliyiya,Mikewa Fu’ad yayi yace ke kin dameni wlh bana son surutu dazu bakya iya cewa komai an Sha ruwa kin Dame mu,Nima binsa nayi nace ai har Kai a Sel fa ka kwana sabo Dani,ka Mari su Fadila ka murdewa Khaleesat hannu sabo dani,ka bini Sel lailahaillallahu Kamar Fu’ad a Sel sabo da Rumaila,kuma ka bada kudi, wayyo Ni… Na kyalkyale da Dariya nace ka bani abinci a Baki Ashe kana da tausayi Kai mashaallah,Ahhh Baki Ahh bakin Subhannallahi,Allah so na kake Yi Kawai gwara ma ka fada min ka huta,ko sai Watarana idan ba kowa sai ka rada min kace Kawai Ina sonki , Fu’ad Yana tafiya Ina ta Shan gabansa Ina surutu.

 Yanzu Ya Fu'ad cinya ta da laushi Sanda ka kwanta? Dariya ce ta kamashi na takura Masa gaba daya,Yana Dariya yace kamar dutse Ni Azumi nakeyi Ramadan ban San wani laushin cinyarki ba,Zan sake magana ya fisgo hannu na zai min mugunta na kwace da kyar na gudu na barshi Nan Yana ta Dariya.

Yace Allah ya kawo wani abu ya sameta bazan sake ceton ta ba tunda yanzu na zama abin tsokanarta har tana ji da kanta Wai Ina sonta,har ya koma bangarensa idan ya tuno sai ya kama dariya shi kadai.

Haka tare muke Shan ruwa,Tarawi ma duk Muna zuwa,tahajjud tazo idan Muka tafi sau da dama ba a gamawa Dani bacci zai sa na gudu gida,sai yaga Ana fitowa Dani baya ganin Ana komawa Dani yasan guduwa nakeyi,kullum Ina karatun Boko Dana Addini na goge sosai na waye haduwa da kawaye   duk na canja Nima na rage wani Haukar Kauye.

 Ranar da za ayi azumin karshe zobo na hada lafiyayye me kauri yasha pineapple da Banana a ciki yayi dadi matuka,Muna Shan ruwa yau ma Ina shimfidar Fu'ad na zuba Masa a glass cup ya dauka banyi zaton zai Sha ba ya kurba ya dago da fuskarsa Muka hada Ido ya Bata Rai ya balla min Harara yace da tun farko kin San kin iya wannan Dan mugunta sai da kika Bari an Kai last Ramadan an Gama Zaki fara hada wannan,Dariya nayi da farko nayi zaton Bai Masa dadi bane,Abbi na kaiwa a juck ya dinga Santi,Su Islam ma na Basu Amma su Momy da yaransu suna kallo Ana ta Sha Ana dadi nace ku kuyi Hakuri bakwa kaunata Nima bana kaunarku baza kuji dadi na ba Sam,Safna Tace zobon banza wa zai Sha kazantarki,nace Nima bazan baku ba,baza ma Ku Gane kurenku ba sai na zama Antynku Nan gaba zaku sani,Kuna kallo dangina zasu zo suyi ta wadaka da kayan Dan uwanku ku kuwa sai dai ku zauna a palon Baki ko kitchen Dina baza ku samu matsayin shiga ba,sai dai ku hango su Rukayyatu Yaya ta da kannena su Basira da Basiru a kitchen suna ta dafa Indomie da kwai ku kuwa sai dai mu gaisa na koma daki na barku a Palo ku bushe anan  ko ruwa baza ku samu daga wajena ba,Kuma Yan uwana su dinga saka super super ku kuwa sai dankwali irin na tsofaffi me Asabari,
Dariya aka dinga Yi Banda su Momy da su Safna,Abbi yace Rumaila kema tsokanar fada ne da ke kullum sai kin kulasu ki kyalesu Haka nace magana ta wuce Amma kinfi so kullum ki tsokane su,Dariya Umma tayi tace ai Wasa takeyi itama ba aikatawa zata Yi ba...Inji uban waye wannan muguwar aikatawa zatayi Mama ta bada Amsa Kai tsaye.

Duk an Mana dinkunan Sallah sai abinda ka gani Kawai kala biyar na samu, Fu’ad ya min kala biyu,Abbi ya Mana da Yan gida kala biyu na samu Umma ta Kara min wata Arabian gown ta zuwa Idi,kala biyar takalma na kala Uku da jaka kala Uku da mayafai kalar kayan Guda biyar,Inner wears sababbi kala kala,harda kana Nan Kaya wata na yo Order daga Dubai masu shegen kyau Umma tasa na zabi kala hudu ta siya min,na makalewa Fu’ad sai da ya bani kudin kayan kwalliya dubu goma da kaina naje na siyo har da wasu rigunan Yan kanti na Karo abina.

 Washe gari Idi masu Aiki tuni gida ya dau kamshi yasha gyara na musamman, kowa yaci wanka Muka tafi masallacin Idi Allah yasa Bamu da nisa, Fu'ad da abokansa Suka shigo wajen su bakwai palon Umma a Nan zasu ci abincin Sallah,fitowa nayi na shiga kitchen na fito da nama a plate Ina Kiran Yar Aiki Tasalluwa Ni tuwo zanci ki kawo min Ina fada na zauna a palon Mazan sai kallo na suke yi,na gaishe su suka amsa, Tasalluwa ta kawo min tuwon shinkafa miyar Egusi na karbi tuwon nace ke Tasalluwa me Zan gani Haka Sallah guda wannan dan tuwon kamar tsaiwar wata shi Zaki kawo min,kin San fa bani kadai bace mu biyu ne ya kike Haka ne sai kace wata bakar kadara Baba Jummai,ai a Yan aikin gidan Nan ba kamarki ko Sarkin Izzar gidan Nan Dole sai ya iya cin girkin ki,Haba Tasalluwa Uwar tuwo,tuwo da Miya sai Tasalluwa.,Tasalluwa tana washe baki ta Karo min tuwo Leda Uku na karba na tafi dakina Ina cewa ki sa Abula ta kawo min ruwa da lemo da Red Apple Guda biyar.

Fu’ad a ransa yace Bari Baki su tafi tunda Habaici kike min Zaki sani,su kuwa abokan sai Dariya sukeyi Wai Dan tuwo Kamar tsaiwar wata.

Masu Sharhi Kuna birgeni Ina Jin dadi Kuma Ina godiya.

AsmaBaffa
????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

        NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

            31-35

Official

By
AsmaBaffa

PAGE NAKU NE

Ummy Manga
Momyn Sultan
Rukayyatu
Maryam

Bayan Na shiga Bedroom Dina cikin abokan Sayyeed yace gaskiya ta hadu tunda na taba ganinta a gidan Nan nake sonta Dan Allah Friend kayi min hanyarta ko na samu na fita a gwaurantaka, Tsaki Fu’ad Yaja yana Danna wayarsa,na fito na fito na Manta Umma tace karbo Mata wasu flasks a kitchen,na fito a kitchen Na tsinci Muryar Fu’ad yace Ke Ina Ummata? Nace banji me kace ba na karaso kusa da shi na duka Ina tambaya me kace,Tsaki Yaja yace Umma ta nace,Oh tana can taje karbo dinkunanta da Suka rage,a hankali nace kayi kyau,Bai kula Ni ba.

      Masu aiki ne Suka cika musu gabansu da kayan Alatu suna ta hira,kunya ta kamani Ni kadai tashi nayi tsam na shige bedroom da kwanon Abinci na,Ina tafiya Hakeem da Adam suka shiga yabon kyau na da hankali na,Hakeem yace Ina sonta idan Zaku bani Dan Momy da gaske nakeyi irin kalata ce,Sayyeed yace ai na Riga ku, Adam yace Nima Haka Ina ciki, Fu'ad ya kalle su yace to tana da aure matar wani ce ciki ma gareta mayun Mata sai a ajiye Zalama gefe,Hakeem yace waye wannan yayi min shigar sauri ya Gama Dani wlh,Tsaki Fu'ad yaja yace Allah ya shirye ku da son Yara irin wannan in Banda shirme da hauka me irin wannan zata maka ta birge ka,ai ka nemi babba wacce da kadan ka girme ta wacce tasan ya kamata me Ilimi,tasan jiya ta San yau kaga love,Amma irin wannan yaran in Banda hauka me zasu Yi maka,kana magana tana cewa sai ka rantse zata yarda komai sai ka koya Mata Amma idan ta mallaki hankalinta to Ka Gama dacewa kawai.

Suna jinsa sun San Halinsa suce ba daidai ba ayi fada sai Suka barshi,Hakeem ne kadai yace Kai Dalla baka San Mata ba bazan tsaya jayayya da Kai ba,Umma ce ta shigo cikin Wata arniyar Shadda tana kwala min Kira na fito Ina tsotse miyar Dake yatsu na,Je ki shirya aikenki zanyi gidan kawata Hajiya Haule,to nace na koma bedroom,Wanka na sake sallawa nasa Atamfa ta Golden and black,dinkin Riga da skert sun kamani Surata ta fito,kayan Sallah kenan nayi Daurin Yan birni me kyau,na shafa powder tare da zizara tozali kadan na shafa jambaki maroon,Na daura agogo da sarka ta na fito Shar kamar rainon birni,Takalmi na Half cover na saka Golden da mayafi da Jakata Golden na fito Ina kwambo,Umma ta kalle Ni tayi Murmushi tare da Furta kinyi kyau nace na gode,Mazan Nan Suka bini da kallo yuuu Banda gogan waya yake latsawa,Kaya ta bani a Leda Tace gashi idan kinje kawai ki Bata munyi waya tasan Zancen,to nace ta bani kudin Taxi na tafi Zan fita kenan na tsinci Muryar Fu'ad me shegen Dadi yace

  Ana ta kidnapping a Gari Gashi yanzu na karanta a News an sace mutane Saba'in a kusa da layin unguwar Nan Bayan anyi batakashi da musayar wuta da Yan Sanda,Umma tayi tunanin gaske ne sabo da yanda kullum bashi da abin ji sai Labarai,Tace Innalillahi Kai Dan Allah? Fu'ad yace sosai ma yanzu Haka Sojoji ne ko Ina,Nan take Umma Tace ke Rumaila dawo na fasa Aiken hanyar lafiya a bita  da Shekara Bari na bawa Driver ya Kai,Nace Umma Ni dai zanje Allah ya kiyaye,Umma Tace to jeki Allah ya tsare.

Fu'ad yace an dakatar da masu taxi ance yau Kar a ga me Taxi a hanya,Kai wannan Bala'i na kasar Nan da me yayi Kama Wai da me zamu ji ne haka,Dagewa nayi Ni sai naje sabo da yawo nake so Naga Gari nima,da sauri na tafi abina tunda na fita normal naga Gari ba abinda ya faru,Address din da Umma ta bani a takarda shi na mikawa Drivern taxi ya karanta,har kofar gida ya kaini wani katafaren gida shima ya gaji da Haduwa,Masu gadi Basu tare Ni ba Suka Bude min,Mutum Daya na roka ya rakani har Palon Hajiya Haule, wani matashi ne wankan tarwada Kyakyawa zai Kai sa'an Fu'ad Yana kwance a kujera kannensa sun zagaye shi suna hira.

 A mutunce Suka amsa min sallama Muka gaisa,tunda na Shiga Matashin ke kallo na Kamar Maye,Hajiya Haule tace sakon Umman Fu'ad ce ko?nace ae tare da Mika mata ledar,lemo aka kawo min da snacks ga fruits a gefe,Matashin ya kalle Ni yace ki ci Mana bakuwa,Haka na Dan tsakura na mike Zan tafi Hajiya Haule tace Anwar je ka Mika ta gida ba sai ta shiga taxi ba,murna ta kamashi ya mike da sauri tare da cewa taso muje,Lafiyayyar motarsa baka na shiga gaba,Duk kunyarsa ta kamani sabo da yanda yake Bina da mayen Kallo.

 A bakin gate din gidan ya tsaya tare da Danna Horn Nan take gate man ya Bude gate har ciki ya Shiga tare da yin parking,Na balle murfin Mota Zan fita yace Ban San sunanki ba? Rumaila na furta,wayarsa me tsada ya Mika min tare da Furta sunana Anwar please sa min number dinki,Ban karbi wayar ba nace saka Bari na fada maka,Yana wani murmushi ya shigar da number wayarsa mukayi sallama ya wuce Ni Kuma na wuce part din Umma,Da sallama na Shiga na Iske ba kowa ciki sai Naila tana kwalliya Fu'ad Yana kwance Yana kallon News,Naila ta kalle Ni ta sake Kallo na tare da Furta Lallai kauye ta Fara gogewa,Mayafi na Dana rike a Hannu na ajiye a saman kujera tare da Zama nace Ina Umma? Sun fita yarinya sai dare zasu dawo mu gidan Nan manya da Yara bama Sallah a gida yawon shakatawa muke fita kullum har a gama Sallah,Wayyo Dana sani nace Anwar ya kaini yawo yanzu ya kawo Ni gida Kuma sai da yace na rakashi naki Amma ai nasan zai kirani a waya.

 Baki Naila ta tabe Tace shi Kam Anwar ya cuci kansa dan Bai San Yar kauye bace ke shi yasa har ya dauko ki a motarsa, Anwar yaro ne me tashe me zaiyi da ke yaudarar ki zaiyi kawai ya barki ba abinda zai ci da ke,Murmushi nayi nace Wanda yafi Anwar ma Wlh nasan sai ya kula Ni bare wani Anwar Mikewa tsaye nayi nace Ni na San nafi duk Yan Matan gidan Nan komai kalla Kutiri yarinya a palon na shiga Taku dai dai tare da shanye Hannu Daya nace ke nasan idan Kika sa skert dina fadowa zaiyi sabo da kugun sauro gareki,Dariya Naila tayi tare da Furta ya Fu'ad kaga abinda takeyi a gabanka kayi maganinta Wai Kutiri ne Duwawu fa, Munafuki ya kalli komai Amma sai yace me aka Yi? Baka gani yanda take murgude deniya a gabanka wayarsa ya ci gaba da latsawa ko kula ta Bai Yi ba,Dariya nayi na juya Ina murguda Mazaunai na nayi kitchen a Haka, Fu'ad ya girgiza Kai yace Dole ayi Mata ciki fitsararra ko kunya ta Bata ji,

Ina Fitowa lokacin Naila ta Gama Cakarewa ba karya ta Sha kyau ta Gama tsukewa Kamar a sace ta,Kallo Daya ta min tana wani yatsina Tace ayi a Haifo Mana Dan shege mu Sha kallo,A zuciyata nace Zaki ga me Kama da Yayanki a fili kuwa nace Allah ya kawo shi lafiya sunansa Fu’ad idan Namiji ne,ai da Sauri Ya Fu’ad dake kwance ya juyo yace Zan balla ki Dan shegen naki Zaki sa Masa sunana? Nace yo Kai kadai ne Fu’ad a duniya Wanda yayi Cikin ma ai sunanku Daya Kuma Ni Allah Fu’ad Zan sa masa,To ki sa ki gani yanda Zan tatsile jaririn ya mutu,idan mace ce Kuma Sunan Khaleesat Zan saka Mata ko Fadila na sake furtawa Ina Murmushi me tafiya da Imanin me kallo na,Umma ce ta shigo ta Sha kyau Tace yawwa dama Ina wajen Nene ke nake Jira Rumaila Zo mu tafi kema ki kalli Gari,murna Ina washe Baki nace to Umma, Fu’ad yace Umma wlh bakwa kiyaye lafiyarku kasar Nan Babu lafiya ba tsaro Amma ku ba ruwanku so kuke Dole sai Kun jawo Mana Maraici da kukan rashi,Harara Umma ta watsa Masa tace Kai nifa ka ishe Ni yanzu kullum ka tare min a part Dina sai Iyayi kala kala kake zuba min,Ni ban San yaushe ka nacewa Zama a Nan ba ka koma part dinka ka ishe ni,ka Hana Yara sakewa gaba Daya haba.

 A dawo lfy Umma Shawara na Baku...Bama so Umma ta furta,Lace Dina me kyau yasha dinkin Riga da skert na shirya na fito ko Dankwali ban daura ba Yana a Hannu na saman kaina Kuma na yafa mayafi na Karami na fito Ina yanga Ni a Dole na waye tare da Umma muka fita Ina ta Santi Ina kalle kalle, da ka kalle Ni kasan ban waye ba sutura ce kawai irin ta Yan birni ta Dan rufa min asiri,Amma sai zare idanuwa nakeyi Ina waige waige,Umma da Naila suna ta min dariya,Umma ta kalleni taga na zurawa wani waje Daya ina ta faman kallo Tace kiyi dai a hankali karki karya wuyanki irin wannan juye juye da kallo Dan Allah ki dinga rage idanuwanki jiba duk sun Kara girma akan kallo kawai,Ni dai Ina ta kallo na ko kulasu banyi ba hankali na yayi gaba,wata budurwa na hango ta gaji da Haduwa ga wani saurayinta Dan charas suna tafiya cike da Nishadi da gani kasan masoya ne, Nan take Fu'ad ya Fado min na Shiga tunanin inama ace Ni da shi ne tunani na koma Yi Ina kallon Masoyan a nice da Fu'ad Ni kadai nake Jin Dadi Ina nishadi abina su Umma suna ta kallo na da mamaki sai ji nayi Naila ta kwala min Kira,firgit na dawo hayyaci na sai Naga Ashe ma sun min nisa sosai da sauri na tafi na Karasa Inda suke,Umma ta rankwashe Ni tare da tambaya tunanin uban me kikeyi sai wani dariya kikeyi ke Daya Ana kallonki a kwarkwar, Baki na bude da niyyar yin magana kenan kawai sai ga wasu masoyan daban sun fito da take away suna farin ciki,ai hankali na ne ya sake kwacewa na bisu da kallo Ina haskowa a Raina nice da Fu'ad Baki na a Bude,Umma haushi yasa tayi gaba Suka barni har Suka siyo abinda zasu siyo Ina Nan inda Suka barni Ina tunani da kallon masoya,Cikin fushi Umma tasa Driver ya maida Ni gida ta fasa yawon Dani,Hakuri na Bata Amma Tace wlh sai kin Koma gida,Dole na shiga mota Ina ji Ina gani Driver ya figi mota Ni kadai ya kaini gida shi Kuma yayi tafiyarsa wajen su Umma,Ina ta Jin Haushin kaina,maza na gani sun cika Palon Umma nasan friends din Gogan ne Fu'ad,sallama nayi kawai Ina fushi na wuce su ko kulasu banyi ba na wuce Bedroom Dina, Fu'ad a ransa ya dinga dariya yasan Dole akwai abinda nayi aka fasa zuwa dani,Abokansa Suka ga Kawai ya sheke da dariya shi kadai kallon kallo suka fara tare da tambaya lafiya? Fu'ad yace wata ce Yana ta Dariya.

Abokansa Basu tambayi wace ba sabo da sun San Suna da Mata da yawa a gidan,Islam ne ya shigo Yana Kira na mayafi na yafa tare da Fitowa Hannuna ya rike Yace fito muje yawo tunda Allah yasa har yanzu mu tuzurai ne anki ayi Mana aure muje ko na rage Tuzurantaka, bani da budurwa muje ki Dan rakani yawo,Ya Fu'ad Yana kallon mu na janye Hannu na Nace to Bari na fito...Muryar Fu'ad Muka tsinta da Gadara ya furta Umma ta hanata fita sabo da shirmenta,Kai kaje Kai daya ko ka tafi da budurwarka ko dole sai da it? Islam yace Zan sa ta gyara,Baki Fu'ad ya tabe Suka ci gaba da hirar su Ni Kuma Muka fita da Islam Ina ta murna.

Shi yake Driving da kansa Muna Hira Ina gaban mota me kamshi Haka Ina ta kauyenci Yana min dariya har muka Gama yawon mu har dare 9pm bamu dawo ba,lokacin Muna wajen Shan Icecream na kalle shi nace Ya Islam ya kamata mu tafi gida sabo da Umma zata min fada Kuma Bata San na fito ba,Ke matsoraciya ya Furta Yana dariya ba abinda zata Miki matukar taji tare muke,Umma kuwa sai Magrib Suka dawo ta iske abokan Fu'ad suna ta Hira an cika gabansu da kayan ci da Sha,Umma Tace yau Kuma a Nan aka ya da zango Kai Dan Momy Ina Rumaila? Sabo da munafuncin Fu'ad sai cewa yayi sun Fita da Islam yace sai dare zasu dawo idan anga Shuru a rufe gida yau idan ba dare ba sai ta Fadi,Umma ranta ya baci tace Amma tafi karfin ita Rumailan ta sanar min zata fita ,Umma tana ta fada ta Haura sama tana cewa bazan kirasu a waya ba Bari naga hankalinsu.

Abinka da Family friends Basu ce komai ba hirarsu Suka ci gaba da yi,11pm Muka dawo gida lokacin Fu’ad ya raka abokansa sun shiga motocinsu,Umma kuwa Bata Yi bincike ba ta sa key tare da kulle part dinta gaba Daya, Fu’ad Yana ta dariya a ransa,ko da na Karasa ba irin bugun da banyiwa kofa ba aka ki Budewa,na shiga Kiran wayar Umma Bata daga ba,Hannu na Dora a Kai nace wayyo Naga ta kaina ya zanyi,diri diri na farayi a wajen har na gaji na tafi sashen Nenen kauye itama nayi Rashin sa’a tayi bacci ta kulle ko ina.

 Rasa inda zanje nayi sai kawai na wuce sashen Yan aiki tare da shiga dakin Tasalluwa,Da fara'a ta ce Rumaila Hala dai kinyi dare Umma tayi fushi? Kai na daga Mata alamar ae Ina zama a saman gadonta, Hmm ya kamata dai ki kiyaye kina cin arziki karki wuce gona da iri kina gani yanda ake ta munafuncin cikin Dake jikinki kadan Su Momy suke jira sunce wlh sai kin bar musu gida,Da mamaki na kalli Tasalluwa nace yanzu Zancen cikin Nan har yanzu ba a daina ba? Waye ya fada?Murmushi Dattijuwar tayi tace Babu Wanda Bai sani ba har makwafta wlh ki taka a sannu a banza ake kallon ki ya kamata ki boye kanki sabo da Baki da daraja a Idon kowa,Allah ya kyauta na Furta cike da kunyar kaina,Tasalluwa Tace ke yarinya idan ta sake kacamewa ki Fadi gaskiya Fu'ad shine ya Miki tunda ai Fyade ya Miki Yan fashi Suka Sanya shi Dole,A Raina nayi Murmushi nace Lallai Tasalluwa Bata San gaskiya ba,ai daga baya sace Ni yayi ya min ciki ranar da Yan fashi Suka Zo ba abinda ya faru sai Bayan sun tafi ya cuce ni,a fili kuwa nace Zan fada Inshaallah ai ma kowa  na gidan ya sani tunda ai kin San rigimar da aka Yi,Dan dake ciki na zai nuna za a ga da wa yayi Kama,Allah ya kyauta a Nan na kwana.

 Washe Gari da hantsi sai Dana Yi wanka naci Abinci 11am na shiga part din Umma,a bedroom dinta na sameta wani mahaukacin sabon kamshi ya daki hanci na Ina Shiga na Iske Fu'ad a ciki yasha farar Shadda Yar gaske komai fari yayi kyau har ban San da ya Zan misaltashi ba,Umma ke taje Masa Sumar sa tana sa Masa mayuka masu tsada na maza sai sheki da kyalli take Yi,Yana ta Shagwaba Yana Kara Wai Umma tana Jan gashin da karfi,Naga Alama so kake Yi ka makara a meeting din Nan kasan Kuma Abbinka wlh sai kasha fada,Banyi zaton Umma zata kula Ni ba Amma sai Naga da Fara'a ta amsa min hakuri na Buda Baki Zan Bata ta katse Ni ba damuwa ki kiyaye gaba kawai ban son kina shiga sabgar Yaran su Momy kin San Halinsu so kike a kulle Miki wani sharrin kenan, Inshaallah na daina na furta tare da kallon Fu'ad kadan Yana ta uban kwalisa nace Ina kwana ya Fu'ad ba tare da ya kalle Ni ba yace karki sake kulani matukar Umma Bata Miki komai ba na hukunci kina abinda Kika dama,Dariya ce ta kamani nace ta yafe min,Umma ya kalla yace ayi Mata hukunci wlh Umma jiya ta Bata min Ranki Kuma kina bacci ta Kira Wayarki,sannan ta buga Miki kofa cikin dare sai an hukuntata .

 Karka dameni duk ba Kaine ka rura wutar ba,ficewa Yayi Yana cewa sai na dawo, tunda ya fita Bai dawo ba sai dare wurin 9pm lokacin Ni kadai ce a Palo  Ina kallo na Mike Zan dakko ruwa a kitchen Ina Mikewa duf ba dalili wuta dauke duf,duhu ya mamaye ko Ina bana Iya ganin komai Ni Kuma ban San Fu'ad ya dawo ba sai kamshinsa naji daf Dani ba zato naji ya min zazzafar runguma tare da kwanciya a jikina Yana cewa Umma na dawo,jiki na ya dauki rawa da sauri nace Ba Umma ba ce Rumaila ce fa,wuta ce ta dawo fal haske ya bayyana sai ga Umma ta fito daga kitchen da sauri ya sake ni ya tsuguna a kasa ya fake da gyara takalmi,Ka daina batawa kanka lokaci na ganka cewar Umma,yace ai nayi tunanin kece Umma karya kakeyi Fu'ad kana sani kasan Rumaila ce Algungumi,na sanka fa ba abinda za a gaya min a halinka,Fuskewa yayi shi fa ba Haka bane,Kallonsa nayi Muka hada Ido nace to nesa ta matso kusa kenan? Ka fadi Soyayyarka wa zai hanaka,Ni Zan rike maka sirri a sirri zamu Yi soyayyar mu bazan Tona ma asiri ba,Baki ya tsuke Allah ya kiyaye naso me cikin shege yarana su gado halin banza,Ka nemawa yayanka Uwa ta gari,ke ai ba ta gari bace,da ta gari ce Zan Iya manage dake kafin na Karo ta biyu,yanzu kuwa Nan da kwana Uku zaki ga Budurwa ta matar da Zan Aura zata zo gaida Umma,Allah ya kaimu na fada Ina Jin wani kishi a Raina.

 Banyi tunanin da gaske bane Wai Ranar Saturday Uku ga Sallah sai ga Budurwa katuwar gaske Yar gayu ga tsayi ga jiki wankan tarwada,ta Gama hadewa tana ta kamshi Wai tazo gaida Umma Kuma Wai Fu'ad ne ya kawo ta,lokacin naci kwalliyar Sallah Ina niyyar zuwa gidan kawata Yar makarantar Islamiyyarmu,Ina ganin Naila tana ta wani ji da ita ta rasa inda zata sa kanta,tana cewa budurwar ya Fu'ad ce Rumaila zo ki gaishe ta kuyi Hira kafin Umma ta dawo,Yar gidan matemakin Shugaban kasa ce Amal ce,Me gidauniyar tallafin marayu.

 Raina ya baci kishi naji kamar na kashe su har Nailan,Karasowa nayi na zauna Ina fushi nace kika ce Yar gidan matemakin Shugaban kasa ce? Naila tace ae Amal ba,Nace to matemakin Shugaban kasar yaci kan Babarsa,dama ke nake Nema wallahi ki fadawa Ubanki da shi Shugaban kasar hakki na Dana Iyata da hakkin Affa,Dana Kanne na da hakkin Yayye na ya fito Mana da shi,bafa za mu yafe ba,Allah ya Bamu kudinmu ta hannunsu har ga Allah a fito min da  hakki na,Amal ta Bude Baki tana kallo na,Ae nace kalli da kyau,Bayan hakki na dake hannunku har wani gaishe ki zanyi? Wannan wanne irin Rashin mutunci ne Rumaila? Bakuwa ce fa Cewar Naila,nace ki cire Fu'ad a ranki yafi karfinki baza ki same shi ba,ba kalarsa bace kin Masa tsayi da fadi,kin cika Fadi kinyi banga banga,Ya akayi kika sake kika cika mudun jikinki Amal? Mudunki yayi yawa,Amal Tace ke wallahi ki kiyayeni Dan nayi kanwa biyar dake sai na bubbuga ki da kasa,nace yanzu kika Yi bayani me kyau Ashe tsohuwa ce, na dake Ina ta masifa,Naila ta Kira Fu'ad a waya ta fada Masa abinda nakeyi,gashi Naila tace na tafi naki tafiya nace sai na ga kwal Uwar daka,Nace wa aka Isa ayiwa ciki ace za a auri wata wallahi Tallahi Bai Isa ba,ya min ciki ya auri wata,to yazo ya kawo Likita a daura min ruwan nakuda na Haifo Masa bakwainin Dansa na tafi abina,Amal ta Bude Baki taga da gaske nake Bata ga Wasa ba,Tace Ciki? Nace kwarai muje asibiti a gwada ki gani da kanki,kalle Ni da kyau ba Yar Nan gidan bace zuwa nayi.

Amal Tace kina da gaskiya dama Ni kawarsa ce Muna Business da juna ne,gaskiya Ina sonsa Kuma yanzu yace Dama auren dole za a Masa gwara ma ya aure Ni,shine fa zamu yunkuro da soyayyarmu,nace ba yunkurowa ba kuyi Aman soyayyarku ma baza a samu Result na
Aure ba,Ahhhh nace kuyo Amanta ma ba yunkuri ba kinji,Amal taji masifa ta isheta sai masifa nakeyi nace Haka kawai,Tace to ya aure mu biyu Mana? Murmushi nayi nace kina ganin kishi Dani zata miki kyau? Ni Rumaila Zama da kishiya babu,Amal Tace sabo da me? Sabo da ba son zaman lafiya nake ba Ni,Dariya Amal tayi tana kallo na banfi ta min dukan tsiya ba Yar karama Amma sai ji da Kai nakeyi,Mikewa tayi Tace Ki gaida Umma in ta dawo na tafi,ta tafi Na zauna Ina masifa Ina hararar Naila,ta fita tabi kawarta.

 Umma tana dawowa nace Umma Sannu da Zuwa,Umma Zaki ji labari yau nayi tijara a gidan Nan,Wai wata tazo budurwar Fu'ad Amal,Zata min Yanga da kuri akan Wai soyayyarta da Fu'ad tazo Nunawa a gidan Nan sun Yunkuro zasu Yi amanta,ba kunya fa Ni Kam gaskiya na ci Mata mutunci,Umma tasan zancen Naila ta Bata labari Tace to ai ba budurwar sa bace shashasha meeting tazo sukayi su gomane Mata da maza tsokanarki Naila tayi,Wani jiki nane yayi sanyi naji kunya ta kamani,nace Zan dinga bincike daga yau na daina gaggawa Allah ya Bata Hakuri ai nayi tunanin Umma ke tazo zata yiwa rashin kunya a gabanki shi yasa nayi maganinta kafin tazo ta fara cewa Fu'ad I love you a Gaban ki,Dariya Umma tayi tasan wayancewa nayi,Tace ke da Fu'ad Kuna Raina min Hankali Rumaila a gidan Nan,zamewa nayi na gudu.

Fu'ad kam shigowa yayi ya juyo muryata Ina ta Dariya muna waya da Jauro,Nace Kai Jauro ka rage karya Kai Jauro yaushe ka Zama Dan Sanda?

Fitowa nayi Ina waya na wuce shi a Palo tare da Umma kafa ya sa min a hanya na Fadi,Kuma ya fuske Kamar ba shi yayi ba,Umma Tace kyale shi Rumaila Allah ya saka Miki,Umma Tace ke Rumaila wannan cikin naki yaki girma Abu ya tafi wata bakwai Kai gaskiya sai na kaiki babban asibiti an duba,Kina gani yarinya ta lugwigwice ta Gama lafkewa duk kamannin masu ciki gashi Nan Umma Amma kice wani babban asibiti Zaki kaita,asarar kudi dai cewar Fu’ad,Kai da kace baka kallon Mata kafi karfin ka kalle su me ya kaika har kasan Rumaila ta Gama Lugwigwicewa,Umma yanzu sabo da Allah bazan kalli mutum by mistake ba,Yarinyar da ta rainani duk abinda take min sai ace bazan Bude Ido ba sai na rufe a gabanki jiya kina gani zata wuce Ina bacci ta ja min gashi tare da kwalla min Kara a kunne,Kai kuma rannan mintsininta kayi ko ban ganka ba? Cewar Umma ta furta tana Mikewa ta haura sama,Tana tafiya yace Ke bude cikinki na gani Yana girma ko baya Yi? Nace Ni bazan Bude ba,yace to karya kike dama ba Wani ciki,nace wallahi Ina da ciki,to Bude na gani,Rigata na dage sama,shi Kuma harda Kanne Ido daya Wai duk salon kallo yakeyi Kamar wani me kallon Kallo-kallo,Yace Kai…..ya girma gashi Nan ya fara kumbura,nace Allah da gaske?Yana ta faman kallon cikin Yace a hankali da slow aeeeee….ka….Mar…..Haka……nake……ga……ni,naja rigar Zan rufe yace tsaya ban Gama gano gaskiya ba matso kusa da Ido na sabo da idona Watarana baya gani sai nasa medical Glass shi yasa Ni bana son farar mace sai baka sabo da Ido na yafi iya kallonta sosai,Harararsa nayi na matsa gaba, ban Gane wayonsa ba Ni Wai dole sai ya kalle Ni tunda yace baya Iya kallon farare,na matsa sosai nace kalli,yace da slow Yana Kanne Ido daya ai….ke….haskenki….na kashe Ido Ne dishi dishi nake gani,Tafiyar Umma mukaji da sauri yace a hankali rufe gobe Zan karasa kallo na tantance,na rufe da sauri na Fadi a kasan carpet na kwanta Kamar kallo nake Yi,Allah yasa Umma Bata ganmu ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button