DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

Part dinsa ya koma yanda ya gaji da Tsafta a ransa yasan Lallai ko wace ta gyara Masa part din Nan ta San makamar tsafta ya kamata yasan wace ta gyara,Tasalluwa ya Nemo sabo da itace shugaban ma'aikatan gidan,Bata fuska yayi Yana muzurai yace Uban wace ta shigar min part har ta samu damar gyara min part Dina?bana ce Kar a bar kowa ya shigar min part ba,Tsoro ya Kama Tasalluwa tace kayi hakuri Alhaji Wlh nacewa tayi ita jikinta ciwo yake yi ta Saba da aiki a gidansu a barta tayi aikin ko ta Dan Wasa jininta, what? Nufinki wace ta shigo min sashe? Sunanta dai Rumaila cikin bakin Yan kauyen Nan da Suka Zo Amma kayi hakuri baza a sake ba,Fu'ad ya dinga mamaki a ransa yanzu wannan gajar ce ta iya gyara Haka? Ko dai karya ne?tunawa Yayi ya ganta a kusa da sashensa tana buya Amma ba komai zai gano gaskiya sannan ma Bai yarda itace ba,Tasalluwa ya nunawa kofa da Hannu yace Out Kar na fusata na koreki daga aiki Baki daya,Tasalluwa Kamar walkiya ta bar sashensa,kudinsa Daya ajiye yaje ya duba harda sake irgawa yagansu cif cif ba a taba ko sisi ba,a fili yace Zan kureki yarinya.

 Ni kuwa harkata na Shiga a bangaren Nene na Shiga kitchen,Nene Tace yawwa ko kun iya fura? Na kalli Nene tare da kyalkyalewa da dariya nace harfa tallan fura nayi ai nayi mugun iyawa kawo kayan aiki kiga aiki Nene,Nene Tace Alhmdllh dama wannan uban Yan iyayin ne yace nayi Masa shi Bai Shan ta siyarwa Kuma Ummansa da dukka Yan gidan ba Wanda ya iya, Gero na karba na maida turmin can ta Bayan kitchen anan nayi surfe tare da daka Gero cikin Tsafta sabo da nasan Halin Ogan nasu,tsaf nayi furar lafiya na Gama na Gama Dakawa Zan Fara lailayawa Nene tazo Tace rufa min asiri ai matukar Kika lailaya to fa Abban Momy bazai Sha ba zaice anyi kazanta,Banga laifinsa ba nace yayi dai dai Haka na zubata a wani Glass Bowl aka ajiye a fridge dama Already lafiyayyen Nono Yana ciki.

 Wanka mukayi Bayan munyi kowa yayi Sallah Amma Banda Dani domin sai Naga dama Kuma yau banyi Niyya ba,doguwar Riga ce a jikina wata dark Green kalar Yan fulani duk da ta tsufa Amma tayi min kyau,Su Rabi sun rigani cin Abinci suna daki suna kallon cartoon sai dariya suke Yi Ni kuwa bana son Cartoon shi yasa na fito Palon Nene ko Dankwali Babu a kaina kitsone guda biyu a kaina jelar murtukekiya Tana yawo a gadon bayana me tsayin gaske.
Kitchen na shiga tare da ebo Abinci Jullof taliya ta Sha nama zuku zuku,a kasa na zauna na mike kafafu tare da saka plate din a tsakiyar kafafu na ga ruwana na roba a gefe da lemo Fanta,Muna kallo Muna Hira da Nene,Kamshi ne ya daki hancinmu,Nene Tace ga uban Iyayi an shigo,Murmushi yayi kadan Yana uban gadara yayi Sallama Muka amsa nace Ina Yini? Ciki ciki ya Furta lfy ya Shiga harkarsa,Nene ce ta Shiga kitchen ta fito da Fura da Nono a gabansa ta dama Masa sannan ta Mika Masa,Ni kuwa Tv na kafe da Ido na saki Baki ganin an nuna Salman Khan a tallan Indian film,Baki na washe Ina faman tsotse yatsuna da nake cin Abinci da su,Nene ta kalleni tace oh Rumaila wannan kallo Haka rufe bakin Mana Haka Nan,Nace Nene Salman Khan ne fa,To a kansa wani banza Bai ma sanki ba kike wannan kallo kamar idanuwanki zasu Fado ga Baki kin Bude,Nene na kalla nace Yasin Nene da ki zagi Salman Khan gwara ki zagi Malam Haruna yayan Iyata Kawu na,Dariya Nene tayi tace akan wannan din? Nace yo ai Ni gwara ki Mari Malam Haruna ko a jikina,Nene Tace Allah ya shiryeki wlh.

Sharukhan aka sake nunawa,nace wohoho Ina gwanin wani ga nawa kaga Kauna da kanta, Soyayya ce da kanta a Nan wajen,shugaban masoya na duniya kenan Nene,Dariya Nene ta sake Yi tace shi Kuma wannan soyayya ya iya?nace ae Nene ai da ace Zaki dauki salon wannan bawan Allah a soyayya to wallahi duk tsufanki sai kiga Gomna ko Minista yazo zai aure ki,sai ki hada goslow a gidan Nan masu motoci ne zasu dinga layi,Dariya Nene ta dinga Yi shima Fu’ad da kyar ya danne dariyar sa Sai da ya murmusa,ai duk Wanda kika ga baya soyayya to Sam Bai hadu ba,Bai ma San me yake ba, Fu’ad a ransa dai yasan baya soyayya sai yaji Kamar shi nayiwa Habaici ya wani Bata Rai Kamar zai ce ya Shiga Uku ya lalace.

Nene Tace duk a Ina kike kallon? A kauyenmu akwai gidan kallo na kudi can muke zuwa,Ana Haka sai aka hasko Ajay debgan,Tafi nayi nace ga Babansu yazo wannan duk iya soyayyarka idan yazo da Salonsa sai ya kwace Budurwar ka,akan wannan Na zazzagi Saurayina Iro Muka Bata kaca kaca sabo da Zaginsa yayi Yana kishi da Ajay sabo da ina sonsa,Fu'ad ne ya kalli Tv din tare da dauke kansa yaci gaba da Shan furarsa me sanyi Yana ta Santi a ransa yace Wai Nene a Ina Kika koyi furar Nan ne? Ga wacce ta koya min ta nuna Ni,Ni Kam tsoronsa nake ji sai naji Bai ce komai ba yaci gaba da Shan abarsa, ina kallo na abina ina ta Jin dadi.

Ina cin taliya Ina Santi nace wanne mahaukaci ne zai dandana zaman birni ya koma kauye,Nene tace akwai Mana Ana samu nace Amma sunyi asara Allah wadaran Halinsu ace na zauna a birni na koma kauye hauka nake Yi,ai daga Jin sunan ma Kau..Yana nufin wani bala'i da masifa idan kuwa aka karasa da shewar Nan ace Yeeeee....to kasan jahilci ne zalla,Amma ko a birni kaji kasan fadarsa a Baki da dadi,Amma Kauye harda shewa a karshe yeeee,Kau..yeee,Wani bakin talaucin da wahala da muka Shiga a bana watan satumba idona Babu Kalar da Bai koma ba tun Yana fari Kamar Madara ya koma ja,ya koma Kore ya koma shudi na Iyata kuwa dake babu kuruciya Allah sarki ruwan shanshanbali ya koma (purple),kidan General ba Wanda ba mu karba ba,munji na goge,munji na kukuma,Algaita,na kwarya,kalangu,ganga....Nene ce sai Dariya take Sha,Nace ko me gadin gidan Nan Nene Ku aura min mu zauna a Birni, Fu'ad shi dai Bai taba Shan Dariya ba irin ta yau daurewa Kawai yakeyi a ransa yace sai kace Radio Bata gajiya da surutu.

 Rabi ce ta kwala min Kira tana cewa kizo ga Salmankhan dinki Rumaila gashi an saka film dinsa,da sauri na mike na wuce Dakinmu tare da shigewa dakinmu Muka ci gaba da kallonmu mun Dade bamuyi bacci ba.
Washe Gari da safe Haka na shiga ko Ina na gaishe su Banda su Rabi,Momy da Mama Haka Suka min wulakanci Amma ban kula su ba part din Umma na koma na shige cikin Yan aiki mukayi aikin komai tare,Umma sai Godiya take min Ina birgesu su sosai,Bayan mun Gama aikin Amma ban gaji ba sai ma aiki da nake bukatar yin wani,Ganin Fu',ad ya fita sai na lallaba na shige part dinsa domin gyarawa,kayan sawa na gani da Dan yawa a saman bed dinsa da Alama wanki za a Kai,Kayan na hada bangare Daya sannan na fara duba Aljihunsa Ina fito da kudade masu yawa na zube Masa a kasan pillow, Haka nabi ko Ina da gyara Yana kamshi da sheki sai da na Gama zan fita mukayi Ido Hudu a bakin kofar palonsa,tsoro ne ya kamani,hankali na ya tashi.

Sharhi fans banda godiya da stickers,gwara Sharhi ko Yaya ne.

AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

NA KUDI NE

DARI BIYU 200 SHIGA GROUP.

Account number
0175487861, Asmau Garba Muhammad,Gt bank.

Masu tura katin mtn ko vtu ga number da zaku tura
08033933642

‘YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39

             4

Official

By
AsmaBaffa

Page naku NE

Rukey Muaz
Mummy Sani
Nafee
Hafsa
Mamu Galadima

       Cike da tsoro jikina Yana rawa kamar mazari,zufa tana karyo min ta ko Ina duk kuwa da AC Dake Dakin,cikin Ina Ina na Furta Dan Allah kayi hakuri wallahi karambani na ne ya kaini,bana Jin magana shi yasa nazo gyara maka makwanci Wanda matarka ce ta Isa yin Haka,Dan Allah naci darajar Bakunta Ni Bakuwa ce, Ni Bakuwa ce ka taimaka min bazan sake ba,Fuskarsa ba Rahma cike da gajiyawa sabo da Bai son Yawan Hayaniya yace ki maida min part Dina inda Kika ganshi tun farko,Tsoro ya kamani na zaro Ido nace yayi Kura fa ta ya Zan dawo da kurar yanda ka sani? Tsaki yaja yace Idan kina son zaman lafiya ki dawo min da bangarena inda Kika ganshi bana bukatar gyaranki,tunowa nayi ance baya son Hayaniya tunani na Zan sa Masa cuta sai na Fara Masa kukan Jiniyar mota Kamar an dakko Ambulance wiwiwiwiw.......gani Yana kallona da mamaki sai na canja kukan Akuya mehhhh....mehhhh...sai nayi na Kare wan...wan..wan...da karfi yanda zai ji Hayaniya ta Masa yawa,wani mugun kallo da ya min ban San sanda nayi tsit ba ya min kwarjini cikin maganarsa ta Gadara yace Zo ki dawo min da Dirtyn dakina har kurar glass ki dawo da ita idan ba Haka ba yau sai nasa an Zane ki a gidan Nan,Jiki na Yana Bari nace to na bi na zage ta bayansa Ina bin bango na fita da gudu tare da furta gani Nan zuwa,Direct kitchen din Yan aiki na wuce tare da dakko rariya karama ta tace Shayi,Garden naje na ebo kasa a farar Leda na dawo part dinsa,a Palo na Iske shi yana zaune a saman kujera ya harde kafafu ya daura Daya Kan Daya a saman Center carpet.

Ban kulashi ba na nufi Plasma Tv da Yar kasa ta  na zuba a tafin Hannu na na shiga hura kasar a jikin tv Ina busa Mata,Shi kuwa wayarsa yake latsawa Yana satar kallon abinda nakeyi,Na koma center table Nan ma na zuba a cikin rariyar nace gyara kafarka kurarka ta dawo kuma ta nan yawa gareta na shiga zazzagawa Kamar me tankade na Ni kujerunsa kawai Ina busa musu,a ransa takaici ya kama shi yace lallai Yarinyar Bata da mutunci daga cewa ta dawo da kura sai ta samo dabara ta dawo da ita kuwa,Ina ta faman hura kasa yace kaga kuwa da gaske take yi Ta dawo da shi,Bari ta Gama inci unanta na balla ta gida biyar, center carpet kuwa Gongonin malt ne a Kai guda biyu Haka naje cikin Dustbin na ebo biyu na zube a Kai nasa Gongonin daya ya a kalli gabas dayan rabinsa a kasa Rabi a saman carpet,tunawa nayi nace au na koma Dustbin na dakko robar ruwa na karaso gabansa nace wannan robar dai dai inda kake zaune take matsa na ajiyeta,ko kulani baiyi ba na ajiye a gefensa Ina rera Waka Kamar Haka:

wani….. fushi da…. kumburin mutum mu baya tsora ta mu….a ransa yace Wato Habaici take min,ni kuwa Haka har bedroom na koma na maida kurar jar kasa na fito kenan daga bedroom dinsa shi Kuma zai shiga,saman mirror dinsa ya hango kasa sosai na zuba ai kuwa ba zato ya dauke Ni da mahaukacin Mari yace Are you mad?

Kumatuna na dafe Hawaye ya biyo baya zirrrrrr.....Get out of my side Nonsense, Da Gudu na fita a bakin kofar palonsa na ci uban Birki sanadin ganin Momy Dana Yi ta shigo part din Ita da Yarta Fadila,Salati Momy ta saki tana tafa Hannu,Fadila tace tirkashi me Zan gani Momy Kinga katuwar kauye,da gudu na fice gaba Daya a part din,Hawayena na goge sannan na nufi part din Nene,kumatu Daya ya tashi da shatin hannayen Fu'ad abinka da Fara fuska ta tayi ja duk da farin nawa ba irin Kal Kal bane Amma dai Dole Fara ce Ni tas.

 Direct Momy sama ta Haura Fadila tana Palo sabo da indai ba iyayen gidan ba Babu Wanda yake Shiga bedroom din Fu'ad sabo da duk Wanda ya Shiga ranar sai ya Sha Mari ko duka shi yasa Babu Wanda ke rabarsa,Momy ce tayi Sallama tare da knocking   cikin yangarsa yace yes,Shiga tayi ya amsa sallamarta Yana Shirin shiga wanka Ganin Momy ya zauna a gefen bed da ladabi yace Momy lafiya? Akan bikin Fadila ne kaga biki Yana matsowa saura wata hudu ya kamata aje kasar waje ayi Mata siyayya,cike da salonsa na magana yace Ina sane Momy Abbi ma munyi Zancen dashi karki damu I will follow-up with the case Inshaallah,Alright ta furta komai dai ka sanar Dani, Inshaallah ta juya ta tafi,Yace Momy ki turo min Khaleesat zata gyara min part Dina,Okay Zan sanar Mata,Haka Khaleesat taje ta gyara Masa duk kuwa da cewar ba wani me kyau tayi ba Sam su Basu iya aikin komai ba ko girki duk Basu iya ba sabo da basa Yi Yan aiki ke Yi daga yawon biki da guraren Hutawa zuwa kasar waje sai makarantar Boko da Islamiyya suna da Ilimin Addini Dana Boko sosai gashi a gida Saturday Sunday Ana musu lesson har manyan gidan su Kuma karatun Addini ake Kara musu yaran Kuma Boko tunda suna zuwa Islamiyya.

Ni kuwa Dana koma part din Nene su Rabi suna ta tambayata Ina naje? Sannan kumatuna Kamar Nasha Mari nasan dariya zasuyi min,Saude na kalla nace ai wallahi bazan fadawa kowa ba Fu’ad ya mareni ba,Dariya Suka dinga Yi Rabi Tace banza Kamar Yar fari ai kin fada Mana to,Ranar kwana sukayi suna min dariya,washe Gari Saturday ba Aiki ba school kowa Yana gida tun safe,mudai gani mukayi gida ya hargitse Ana ta shige da fice Yan aiki suna ta girke girke iri iri,Ni dai naje ko wanne part din Matan na gaida su,Rabi Tace tunda ke Rumaila kin fimu shiga ko Ina ki jiyo Mana Mene ne Wai za ayi a gidan Nan yau ko Ina ya dauki kamshi,Nace ai Dole naje wajen Tasalluwa uwar gulma na jiyo labarin,dama banje part din Abbi ba Haka naje nayi sallama a nutse Yana Palo kuwa Yana karyawa Mama tana kusa da shi a gabansa na durkusa na gaida shi ya amsa da fara’a yace wannan yarinya Mama tana da hankali tunda Suka Zo kullum sai ta gaishe ni Rabin ma Bata zuwa ita da take Yar dangi Allah ya Miki Albarka,Ameen nace Ina murna an yabe ni,Mama kuwa tabe Baki tayi tace tana kokari Kam tafi su Rabi shishigi Dan kuwa wannan shishigi ne da cusa Kai ba kwar jini,Abbi yace ku daina Haka fa Wai me yasa kuke Raina Dan Adam ne musamman ke da Momy Haba ko kune akewa yaran Cikinku Haka baza Kuji Dadi ba,Mama canja hirar tayi Dan Kar ya dameta ma,yace jeki abinki kinji,Wai ya sunanki ne yarinya? Cike da ladabi nace Rumaila yace madalla jeki abinki Kinji,zan juya kenan Muka hada Ido da Mama na saci kallon Abbi nayi Mata gwalo,da bala’i ta Bude Baki zata Yi masifa tafiya ta nayi ban tsaya ko Ina ba sai wajen su tasalluwa.

Da sakin fuska Muka gaisa dasu sabo da kowa Mata da maza na gidan Ina girmama su Ina gaishe su,nace Inna Tasalluwa Wai yau me za ayi a gidan Nan ne Naga Ana ta gyara Kamar sarki ne zai Zo, Tasalluwa kadan take jira tace ke ai duk Asabar din karshen wata Family dinsu na kusa na jini suke Haduwa  a Nan gidan,anjima zaku Sha kallon daukan wanka har da mu Yan aiki sabon dinki ake Mana za aci a Sha suyi hirar su ta zumunci masu matsala su fada yau Yan gidan ko Islamiyya baza su je ba Haka me lesson bazai Zo ba yau ranar zumunci ce,Kuma wallahi duk kusan Yan uwansu daga kasar waje zasu Zo Zaki Sha kallon gayu,ance ma wasu sun sauka Drivers sunje dakko wasu,kuje kuyi wanka kuyi kyau idan ba Haka ba wallahi zaku Sha wulakanci yau,Ai Ina Gama ji da gudu na nufi sashen Nene Ina haki na Fado palonta turus na ja na tsaya ganin Fu'ad kwance a palon Nene Yana latsa waya Nene tana Masa surutu,Lafiya ke Kuma kin Fara Zama budurwa kina famfara uban gudu Haka yanzu maza Yan aiki duk sun kalli nonon ki suna tsalle sama,Kunya naji Kamar na nutse Nene Bata kunyar fadar magana,har nayi Shuru sai Kuma na Fara kokarin Kare kaina nace Nene ai ban girma ba Ina abin yake,Nene Tace kaji yarinya da karya uban mene wannan....kafin ta karasa na gudu Bedroom,Shi kuwa Fu'ad Kamar ma bai San Muna Yi ba ya mike yayi waje abinsa,Muna zaune Ina bawa su Rabi labarin Abinda za ayi a gidan sai ga Khaleesat ta shigo da katuwar Leda har Uku,ko magana Bata Yi Mana ba tana wani Yi Mana kallon banza ta Fara ajiye min ledar Daya a gabana sai ta ajiye Saude ma ta ajiyewa Rabi sannan tace kuje kuyi wanka ku shirya cikin Daya daga kayan nan naku,ku tube kayan jikinku ku daura towel ku hada da kayanku na kauye ku bani su yanzu.

Da sauri mukayi yanda Tace duk Muka daura guntun Towel ta kwashe ledojin kayanmu na kauye Muna kallo ta tafi dasu ta bawa masu aiki aka zubar dasu a shara,Kayan Muka hau dubawa kowaccenmu panties kala Shida,bra kala uku uku masu kyau,Tight 3qtr kala uku,vest uku,sai lace kala biyu biyu kowacce kalar nata daban ne,dinki kuma doguwar Riga da Riga da skert,sai Shadda kala Daya doguwar Riga me kyau,sai Atamfa kala uku duk Riga da skert,dinkin ma da kayan kowacce style dinta daban,sai Readymade Arabian gown kala uku,sai flat shoes kala biyu black and milk,ko wacce Design nata daban,harda Yar hand bag guda Daya,sai kuma kayan kwalliya,maroon jambaki,jagira,powder lipstick tare da body cream Kato me kamshin gaske kowacce nata daban,sai man shafawa a gashi da Kuma shampoo murna muka dinga Yi Kamar mahaukata,sai dai kayan gaba Daya Wanda aka dinga sun dame mu dai dai jikinmu cif cif.

  wanka mukayi tare da shafa man mu kaina yasha wanki da shampoo,Ina shafa Mai nace Saude shafa min a gadon bayana Saude ta lakuta tana shafa min Ina cewa yarba shi da yawa yaji sosai yanda fatata zata murje,Allah yasa man Blitching ne sai na Kara Dashewa na kode,wata Atamfa Red na zaba na saka Riga da skert dinkin ya dameni matuka nayi wani caras Kamar ba Ni ba kamar a jikina aka dinka,Rabi doguwar rigar lace ta saka Saude kuwa ta saka shaddarta Muka fito fes duk Sunyi kwalliya irin ta kauye,Ni Kuma bana kwalliya powder kawai na shafa sai lipgloss dina nace Daurin Dana gani a wakar garzali Miko zanyi nanfa na coka ture kaga tsiya kamar wata Yar birni,Rabi kuwa Tace Ni da nake Yar dangi Zan shiga family ai Illi gogoro zan zuba,Muna gani tayi wani uban gogoro Kamar Matan yare masu gasa masara a gefen titi ko masu siyar da manja, Saude ma Tace yanda za a Sha Baki ai Ni bazan daura dankwali ba Naga sunayin acuci maza Bari nayi abina,Nan Saude tayi acucinta da tsohon ribbon dinta Wanda ya Gama tsufa Kuma ba Babba bane ta yafa gyalenta siriri milk,mu bamu Saba yawo da gyale ba bamu saka ba dama ba wani Abu bane a wajenmu,muna Fitowa Palo Muka ga Nene ta Sha wani sabon lace me Arnen kyau da tsada tana zaune,Da kallo ta bimu ba karamin kyau Muka Mata ba, na fara yabon kyan da Nene tayi Nace Nene na Baki Gomnan Kano Ganduje,Dariya Nene tayi tace me zai ci Dani,muma Nene tace munyi kyau musamman Ni da banyi kwalliya ba bare ace nayi Kama da Yar kauye.

Masha Allah Nene ta furta Rabi ce kawai zata Shiga cikin Yan Uwa tare da Nene Suka tafi Palon da aka tanada Ni da Saude Muka Yi zamanmu  sai motoci Muka ji suna ta shigowa lokaci daban daban,sai da Muka tabbatar sun gama Zuwa kaf Ana Palon taro,Wajen Yan aiki Muka shiga nace Tasalluwa Zamu tayaku Kai Abinci da zuba musu, Tasalluwa Tace ba matsala ku dauki abinda zaku iya muje,Da kyar nake tafiya sabo da kayan jikina sun kamani Kuma ban Saba ba,wani flasks na dauka kato me tsananin kyau da tsada,Saude Tace nifa tsoron Fu'ad din nan nakeyi kullum cikin kunci yake ga uwar yanga da Iyayi ga Uwa uba Gadara ban son wulakanci a rayuwata wallahi,Ni dai bance Mata komai ba ta dauki Bowl na fruits Muka bi bayan su Tasalluwa da wasu Yan aikin Mata su biyu,Cike da nutsuwa Muka Yi musu Sallama tare da Shiga.

    Rabi Muka hango a zaune gefe Daya ta rabe tayi wani tsilli tsilli kamar tayi karya,Yan Mata Muka gani Baki sunfi su goma ga na gidan,matasan samari sun Kai su bakwai ga Kuma na gidan,Dattijai kuwa manyan Mata su wurin goma ne ga Karin na gida Haka manyan maza irin Abbi sunfi su Tara,ga Yan Yara kana na da yawa ba laifi sun cika sosai gaba dayansu Yan gayu ne na gaske kowacce tana na fiki  wannan tana na fiki Haka mazan ma,da Addua Suka Bude taro sannan manyan Suka Yi bayani akan darajar zumunci,Abbi ya gabatar da Rabi a wajensu sannan mu da muke tsaye Muna jira a bamu Umarni Abbi ya nuna mu yace kawayen Rabi ne,Zo Yar Albarka Abbi ya Furta tare da kirana,gaba Daya hankalin kowa ya dawo kaina Suka zuba min Ido duk sai na duburburce,mazan Nan Suka bini da kallo musamman yanda Suka ga nayi mugun kyau gani da sura me kyau,a gefen Abbi na durkusa tare da gaisar da dangi suna ta wani dauke min Kai musamman Yan Matan,Abbi yace sunanta Rumaila yarinya me hankali kenan,Ameen na Furta Ina dagowa mukayi Ido hudu da Fu'ad,da sauri na janye idanuwa, Momy ce Tace Tasalluwa kuyi aikinku,Mikewa nayi tare da komawa wajensu muka zubawa kowa abinda yake so Zaici 

sai wasu kallo na sukeyi wata Mata cikinsu tace wannan tayi kyau tana da kyau kamar ba Yar kauye ba,dariya Yan Matan Suka saki tare da furta Haba Aunty kalle ta fa ko Alama Bata Yi Kama da birni ba,Khaleesat Tace gyara na ce Ni na fito da su,su Rabi duk sunji Haushi musamman ita da take cikinsu suna ta Mata kallon banza,Ni kuwa ko a jikina,Saude sabo da takaici barin Palon tayi abinta, Ni kuwa banji haushi ba ko Daya sai ma Murmushi da nayi nace ai Allah ya rufa Mana asiri Anty Khaleesat ta kawo Mana Kaya Amma ai da baza ki so ganin mu ba a kusa da ku ba ai Kauye masifa ce,Umma Tace Allah sarki to Wai ba a dinka muku Kaya ne a gida? Nace cab yo Allah na tuba ai Gara Saude da Rabi Yan gata ne su duk kayan Sallarsu suka Zo da su ai kure wanka muka Yi zamu Zo Birni,Dariya suka kwashe da shi har manyan Matan da mazan matasa da Yan Mata kuwa har da rike ciki Banda Fu’ad shi fuskar Nan a murtuke take, Sai da Suka Gama dariyar Khaleesat Tace tabbas Kam kayansu sunfi naki kyau gaskiya ne to ke ba Yar gata bace?
Baki na Bude nace bani da gata ko na digo maraya ma ya fini gata a kasar nan nice shugabar Agololi ta Nigeria, Ni a Agololin ma ta karshe ce gida sunfi takwas na zauna Ina Agola,to idan mun koma ma wani sabon gidan Mijin Iyata Zan koma da Zama yanzu Haka Iyata Amarya ce a gidan Wani me Shayi,Babana kuwa ba ruwansa Dani sabo da Babata ta Masa ba Dadi kafin ya sake ta,Wasu Suka ce eyyaaaaa….Umma Tace aure aure takeyi? Kai na daga nace ae duk inda tayi Aure Kuma tana da Yara wani gidan mace wani gidan Namiji wani gidan Mata da maza,Ni Kam Ni kadai ce ta Haifa da Affa na Amma Ina da yan Uba,Abbi yace ikon Allah me zatayi da aure haka? Nace ai da Allah zai sa na kawo Iya gidan Nan sai ta kashe aurenta akanka Abbi tace sai Kai,Momy da Mama kishi ya cake musu zuciya, ko Wanda kuwa yafi kowa Gadara a gidan nan nasan tsohuwa zai aura tunda ba wata soyayya ya sani ba, Fu’ad ya kalleni da Sauri yasan da shi nake Ina Masa Habaici shine zai auri tsohuwa,nace yo ai sai a godewa Allah ma da Kamar Iyata zata so mutum.

Nace duk Nan Wai gidan kudi take nema inda zamu Huta Amma Bata taba Dace ba daga me shayi sai me noma,ai Iyata ko sarkin Makka ne zai Aureta karewar kudi to sai ta fito Haka kaddararta take.
Abbi yace Allah kyauta nace Ameen duk gidan Nan Abbi Khaleesat ce farin gani Kaya ta dinka Mana mun Zama Yan gayu,Fadeela ce ta tabe Baki tace ke dalla to ba ita ta siya muku ba Yaya Fu’ad ne kike wani damun mutane,dama na tsani Fadeela Bata da mutunci nace Ni dai ita na San ta bamu Kaya waye ya bada kudi ba ruwana kishi kikeyi da ita Dan Allah Abbi ko kayan daki Kar ayi Mata na kasar waje ga na gida Nigeria iri iri wannan ko taje gidan miji me ta iya Sai bacci,Dariya akayi wasu dattijan suka ce oh wannan yarinya da surutu take.

Fadeela kuwa tace wlh sai naci ubanki a gidan Nan,Mama da Momy suka galla min Harara,Ina sani nace Bacci zata dinga Yi a gidan miji ta Zama kazama dama duk me bacci kazami ne dakin miji ma masu aiki zata Bari su gyara Mata Kuma girki ma Bata iya ba,Yan gidan Sunyi mamaki da sukaji Bakuwa har tasan Halinsu,Abbi yace yawwa Rumaila Yi musu Nasiha ko zasu gyara kunji yarinya karama ta fiki hankali,nace a Haka suce suna da degree,to a wajen miji wallahi zero zaku samu,Umma tace ai kuwa dai ya kamata ku gyara,Momy ranta ya baci Ana kushe Mata Yara Tace a gidan ubanki Kika San Haka shegiya munafuka,Nace ai Ni kwana Daya nayi da mutum Ina Gane Halinsa mutum Daya ne a gidan Nan na kasa Gane Ina ya nufa,samarin suna ta dariya,Shi kuwa ya sake Bata fuska a ransa Yana cewa Lallai yarinyar Nan sai naci Ubanta ta Raina ni.

 Ni dai cewa nayi a tashi lafiya ganin kowa ya Bata Rai Ana Shirin cin Ubana sai na sulale na gudu,matasan sai kallo na sukeyi suna yaba surata,Islam yace gaskiya wallahi tana da kyau matuka ga kyan sura,Shima Hakeem yace sosai ma tunda ta shugo nake kallonta dukkan su suna da kyau Amma ita ta fisu har wayewa kullum sai ta gaishe mu Kuma zaka ganta Kamar Yar gida tana harkokinta,Dariya Sa'ad yayi yace Ni Kuma Excersise dinta ne ke birgeni Yar kauye tasan motsa jiki,idan munayi da Sassafe zaka ganta ta fito watarana ma tana Riga mu Fitowa da ita muke buga tsere,dariya Suka dinga Yi har Matan wata tsohuwa Tace wannan yarinyar dai? Ae ita fa Zan Fara koya Mata wasu kalolin na Mata ma,cikin bakin mazan Suma suna ta Yaba kyawu na,Hisham yace wlh ta shiga Raina daga Nan Fu'ad yace Ni Kam Bata birge Ni ko kadan na tsaneta ma,Islam yace ai Kai dama baka layin mutane,Shut up Fu'ad ya Furta Wai shi babba,yace ayi a gama taron Nan Ina da wajen zuwa Abbi.
Anci ansha anyi Addu'a aka saurari matsalar kowa sannan aka rufe da Addua duk masu tafiya ko kwana basuyi ba sabo da kudi kawai Suka Kama gabansu Yan gida Kuma Suka tafi inda zasu,Yan aiki Suka gyara ko Ina again.

  Ranar nasan na batawa Yan matan gidan Rai ko Fitowa banyi ba Dan Kar su kamani su Zane Ni,Muna zaune a palon Nene sai ga Khaleesat ta shigo da fara'a nace sannu da zuwa farin gani ta balla min Harara tare da Mika  mana karamar waya kowa Daya irin kana Yan Dubu bakwai kowa Tata kalar daban,Ihu Muka saki da murna sai tsalle mukeyi,ita kanta Khaleesat sai da tayi dariya ganin Haukar da mukeyi, Nene tana ta dariyar haukarmu,Fu'ad ne ya shigo da Sallama ganin na Fadi a kasa Ina ta birgimar murna Khaleesat Tace Wai akan wayar da kace a Basu tunda suna neman wayar aro zasu Kira iyayensu,Na tsaya cak nace wannan ma shi ya siyo Mana? Khaleesat Tace ae ai kuwa muka dinga zuba Masa godiya,nace kayi Hakuri kaji kasar Dana zuba maka a daki,ban San Haka kake ba,Kuma Ba tsohuwa zaka aura ba irin Iyata, Suleliyar Balarabiya ta kasar Afghanistan Yar shekara Sha shida ita zaka auro ko Yar Italy kaci taliya ka more wace Guda daya sabo da tsayinta sai ta cika plate,ko Yar China ka sharbi Dafgen kwadi lafiyayyu masu Zaki,kullum da safe ka karya da Kaguwa ko hantar kadangare.

Kuma Allah yasa cikin shekara uku ta Haifo maka yara biyar,duk wata biyar nasan zata dinga Haihuwa, Nan take Fu’ad ya sake cukulewa ya hada girar sama da kasa yace a ransa Wato ta maida Ni ayu Ni jarababbe ne zanta XXX da mace ba ji ba gani, Allah sarki Ni Kuma ban ma San komai akan ya abin yake ba a ganina yabonsa nayi.
Muna zaune Khaleesat ta koya Mana komai tare da saka Mana layi ciki,kowa da katin MTN na dari biyar aka saka Mana ta bamu tayi Tafiyarta.

 Fu'ad Yana zaune a kujera suna Hira da Nene kadan kadan,Number Iyata na saka na Kira Bugu biyu ta daga, Salamu'alaykum waye,Da karfin gaske Kamar Ina magana da duniya nace Allahu Akabar Kaji Muryar Iyata,Iyata nice Yarki Rumaila,Iya itama da Karfin gaske tace Dan gidanku sai yanzu Zaki neme Ni? Hankalina Yana tashe,nace Iya yanzu na Samu waya ne,duk wayar dake garin a rasa me Baki aro? 
Nan fa na Fara bawa iya labarin Alatu da abin Dadi dake gidan Iya tana ta dariya,Fu'ad Yana jina nace iya kullum da kaza muke karyawa wallahi Allah, nama muke ta faman ci Baki ga yanda na murza kiba ba Iya baza ki Gane Yarki ba na Kara ja, fari na ya dawo Kamar sanda Ina jaririya,ki fadawa mijinki kafin na dawo ya Sara Kofar Dakinki ta Kara Fadi sabo da kibar danayi Kofar tayi min kadan sai Fadi na ya cika ta taf, Fu'ad dai da Nene suna ji Haukar Yarinyar Nan ta isheshi shi kam, Yar karama da ita kwaila tace wani kofa zata Mata kadan,Gashin kaina na na jawo tare da Karawa a jikin wayar nace Iya gashi na kamshi Yasin shinshina kiji iya laushi,Amma sanda Ina kauye fatar jikina kamar Bayan Kada (crocodile) dariya Sai da ta kwacewa Fu'ad yayi kadan,Nace Iya babban Dan gidan ne yake ta Mana Alheri,A Haka Zaki ce Bai da kirki Ashe abin a zuciya yake Iya Imani ne dashi da Tausayi ya dinka Mana Kayan gayu ga waya kyauta me tsada iya wayar fa idan aka siyar da ita sai ta siya min Kayan kitchen na Aure,ko katuwar Akuya me ciki, Dariya ta sake kwacewa Fu'ad yayi kadan Nene Tace idan Rumaila ce zaka gaji da dariya.

Nace Iya Bari na Baki shi ku gaisa ki Masa godiya,Iya tace to,na Karasa gabansa da sauri na durkusa a gabansa tare da Mika Masa wayar cikin sigar rada nace Iyata ce Dan Allah fitar Dani kunya ku gaisa,Harara ya watsa min da mugun kallo Wanda sai da jikina ya dauki rawa Nene Tace karbi Mana karka Bata kunya,Da kyar ya karba Amma nayi mamaki cike da girmamawa ya gaida Iya ta dinga zuba Masa Addua da ruwan godiya sannan ya Mika min wayata na karba mukayi sallama,su Rabi duk sun Kira iyayensu Suma.

Washe Gari ma banje gaida kowa ba Ina tsoron Yan Matan Kar su Duke ni, Zama mukayi a dakinmu muna ta Hira, Nene Tace Yan Mata kuzo Palo kuyi a gabana ko ba komai nayi nishadi, bamu Dade da Zama a gefe ba can ba,wani kamshi na musamman ya dake mu mun San ma Fu'ad ne ai kuwa shine kullum sai yazo wajen Nene Yana sonta,yasha wata arniyar Shadda ruwan toka yayi azabar kyau ko wanne shiga yayi  kyau yake zubawa,     Kallon jikina nayi yanda Kaya Suka dameni Suka fito min da sura nace kalli gangare Ashe Ina da tudu da gangare Haka?ga tudu kalli Rabi ya Kika ga idan Muka koma kauye? Rabi Tace ai ta kofar Yamma zamubi Majalisar su Ubaliyo su kalla Haram shegu duk a rubuta musu zunubin kallo,Dama ba kallon Musulunci sukeyi ba ga gulma munafukai ai sai na sa sun dauki Alhaki suyi ta kallo mala'iku suna rubuta musu,a sanadiyar wannan sai kiji su Ubaliyo an ja su Jahannama,walakiri ya dinga buga musu guduma a tsakiyar kansu,dama sun ishe mu da munafunci munki Yin aure.

 Fu'ad Yana jinsu Yana jinjina iyashegen yaran kauye kamar manya,Nene Tace tunda kuke Hira tun kafin Sallar Azahar Banga Kun tashi kunyi Sallah ba har anyi La'asar ga Abban Momy har ya dawo daga Office banji kunyi Sallah ba biyar ta wuce Shuru na lura Baku damu da addini ba fa ko bakwa zuwa Islamiyya ne? Nace Ni dai yau Allah ya gani bana Sallah na Sharo karya Dan Kar nayi bayan ko period ban Fara ba,Saude ta Dan fimu kokarin Sallah tunda tana yi sau biyu sau Uku a Rana,Sai tace karya sukeyi Nene wlh bama wata Sallah sai munga dama ko ta ganin Ido to karatun ma bamu Iya ba ko Al'ada bamu Fara ba Rabi ce ta Fara duk kawayen mu,Mamaki ya Kama Fu'ad,Nene ta saki Salati tace to me kukeyi a Kauyen? Talla Saude ta Furta wlh ba abinda Muka sani sai sirrin waken siya wajen soya Awara,Fu'ad ya girgiza Kai sannan yace su Fara zuwa Islamiyyar yaran gidan Nan wacce malami ke zuwa kullum da yamma Yana musu karatu Zan Masa magana Akan abinda ya Dace na addini su Fara sani ko ba komai kafin su koma zasu rage jahilcin Dake damunsu,Kuma Duk wacce Bata Yi sallah ba Nene ki fada min wlh sai nasa Guard ya Mata dukan tsiya a gidan nan,Ido na zaro Ni dai bana son yin Sallah,nace Alwala ce wahala kullum komai sanyi sai ka taba ruwa, Amma Haka muka yi mukus.

Washe Gari karfe Uku muka je part din da ake koyawa Yan gida karatun Addini Muka zauna can baya Muna ji kowa Ana Kara musu karatun Qur'ani da sauran littafai na musulunci,Malamin yace kune Fu'ad ya min magana a kanku ko? Ae mune Rabi ta furta,A gurguje ya dorawa Yan gidan karatu ya sallame su saura mu Uku kacal..

Malamin yace yanzu zamu fara daku daga farkon muhimman abubuwan da Addani ya gindaya da kuma abinda ya wajabta ko wanne musulmi ace ya sani. Zamu fara bayani ne akan abinda ya shafi tsarki tunda Addini baya yiwuwa sai an tsarkaka Kamar yanda Annabinmu Annabi Muhammad (SAW) ya koyar damu a cikin hadisi cewa: “Allah (SWA) mai tsarki ne tsarkakakke kuma baya karbar Aiki sai mai tsarki….” Har ya zuwa karshen hadisin. Tsarki dai kamar yanda aka koyar a cikin littattafai na Addini kala biyu ne, akwai tsarki na jiki sannan akwai tsarki na tufafi. Kafin musulmi ya aiwatar da ibada karbabbiya sai ya kasance ya hada biyun nan duka.

Da Sauri na Mike tsaye nace Malam tukur Aradu ka koma makaranta tsarki biyu kacal ai tsarki da yawa zaka ce biyu,kaji karya Yaya Malam kana Babba zaka dinga zugo karya,Saude tace kyale shi Rumaila Billahillazi da a garin mu ne Yasin sai su Garbati sun goce maka kashin kafada,Rabi tace Alqur’an kuwa Saude,Kai Malam Tukur kake me dalla dalla ko Malam tukuro to ba dalla dalla ba ko filla filla kake Yi Yasin Mun ci gyaran ka a nan,Malam ya kalle su yace to Ku sanar Dani kalolin tsarki,ke Rumaila kawo min su,Mikewa nayi tsaye nace akwai tsarkin bandaki,shi bayi Yana bukatar a dinga wanke shi kullum da ruwa da Omo,akwai tsarkin dakin bacci shima Ana share shi fes,akwai tsarkin kwaryar nono da fura,akwai tsarkin ludayin Shan koko,kokon da ake lailaya tuwon shinkafa duk a dinga wanke su fes kai baza su Irgu ba,Rabi ta kyalkyale da Dariya tace Malam a koma Maiduguri a Karo Ilimin Addini,Saude tace Ko za a samu ilim kulunboto ko ka samu kudi,Kai Malam ka zauna a banza gidan masu kudi Ana biyanka kudi kadan ba gwara ka koma malamin soro ba kana yiwa masu kudi aikin tsubbu Ana kaika Makkah a siya maka gida da mota da tuni ka zama me kudi gashi nan haddarka tana ta gogewa a banza.
Dariya Malam yayi yace baku da hankali ku saurare ni zan fara muku karatu ko nayi tafiyata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button