DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

    Ina kallon Yan Mata suna ta Hada hada,Dangin Nigeria Dana kasashen ketare duk sun zo,Sai Yamma Kawai aka fara cakarewa masu tafiya make up sun tafi wasu Kuma duk a gidan ake tayi musu,Umma ta Neme Ni har ta gaji ba a San Ina Garden ba,wurin magriba aka fara tafiya Event center inda za ayi wedding Dinner, Ina ta kallon gayu iri iri suna ta birge Ni,duk wacce taci gayu a Yan matan Amarya zata wuce sai na buya a Bayan bishiya suna tafiya Ina cewa ke Siiiiiiiiiiii.....Baki Yi kyau ba,ko nayi ta musu ba'a,idan fara ta wuce nace bature ya daina hada Mai,an rufe kamfanin man Blitching a duniya,Idan baka ce nace ke kuwa duk wayewar Nan da tazo kika tsaya aka barki a baya ga mayuka can sun fito Amma jibe ki kamar Bayan tukunyar Iya ta,idan Siririya ta wuce sai na fara Waka Ina cewa cokali a saka a dadi,idan me kiba ce nace kaga marga margan Toro.

Wata Yar sukuta tazo wucewa nace Sannu kifi sukunbiya da sauri ta juyo taga ba kowa taja Tsaki tayi gaba,Wata ma lukutar zata wuce nace a dawo lfy Dorinar Ruwa Allah kiyaye,sai Dana gaji na tashi nayi sabo da zanje nayi Sallah,Duk gidan an tafi saura Amarya da wasu tsirari,Har su Rabi sunci gayu an musu kwalliya dake An musu anko ma da wasu kalolin kayan na cin biki,Zasu shiga mota Driver zai kaisu Muka hadu suna ta Iyayi ganin ban shirya ba sun San ma bazan je ba sunyi tunanin ma bani da kayan sawa Dariya suka dinga yimin ko kallonsu banyi ba nayi tafiyata.

 Ina Shiga na iske Umma zata tafi tare da Naila sunci gayu karshe,Umma Tace Ina kika tafi Kuma Ana ta tafiya babu Neman da ban Miki ba? Ina wajen Hutawa,je kiyi Sauri kiyi wanka kayanki suna kan gadonki,ga me make up zata Miki,da gudu na fada Bedroom dina naga Kaya kala Uku Shadda lace da Atamfa kalarsu sun birgeni harda mayafai da takalmi na me Dan tudu kadan harda jakarsa da murna na Shiga wanka ba Bata lokaci na fito tare da shafa Mai na zabi lace Dina sky blue and Black na saka sannan na fito aka Yi min kwalliya sama sama nace bana son kwalliyar hauka tana Gama min ta daura min dankwali me kyau, ka Rantse ba Ni bace sai yabawa akeyi,Daki na koma na dauki bakin mayafin da takalmi da jaka bakake Nasha kyau sai da na Dade Ina kallon kaina,su Umma Suka gaji Suka tafi,Islam Umma tayiwa waya yazo ya dauke Ni mu je tare.

 Fitowa Nayi Ina taku dai dai zan fita kenan sai ga Fu'ad yasha wata Gezna Yar gaske milk color tana maiko,ba karamin kyau ya zuba ba,kamshi Yana tashi,kallo na yayi sau daya yasan Nayi kyau ba karya a Ransa yace an fara gogewa,Ina Umma? Nace sun tafi,ke Baki da hankali duk kowa ya tafi waye zai tafi da ke? Nace Kai Mana,Baki ya tabe yace kinyi kadan yarinya yayi tafiyarsa,shuru shuru banga Islam ba Ashe Momy ce ta hanashi zuwa Tace Indai ta ganni da shi sai ta Masa Baki,Ni kuwa ganin ba kowa na fita abina na Shiga Taxi dama da gate pass a Hannuna Kuma da Address din wajen,har can me Taxi ya kaini na bashi kudinsa na shiga wajen, kida ne Kawai ke tashi Ana rawa.

Kowa ya hallara aka zuba min Ido kunya ta kamani,duk naga Wanda na sani Amma babu wajen zama kusa da su,ga kida ya cika min kunne,Amarya da Angon ta An Sha kyau shiga na Alfarma, suits ya Sha black ita Kuma white wedding gown Wai su turawa,Fu’ad na hango shi kadai a wajensa ga kujeru har uku ga table a tsakiya an cika shi da abinci iri iri,wajensa na nufa a tsorace Ina Addua Allah yasa kar ya kunyata ni Amma Haka na tafi Ana ta kallon inda na nufa,Momy ta kalli Mama Tace kinga shegu ko gashi can ta tafi wajensa,tayani kallo ai Ina sa Ido sai asirinsu ya Toni Mama ta furta.

Kafin na karasa wajen Cikin Sauri Lubna ta koma ta zauna a dayar kujerar tana hararata,Su Rabi Suka saki shewa Ahayyeeeeee lokacin kida aka kashe dif sai ga iya muryar su Rabi a dubban jama’a wajen Yan gayu anji Ahayyeeeeee cassssss……aka kwashe da Dariya gaba daya kallo ya koma kansu Mata da maza,Ni kuwa naja kujera zan zauna wata kawar Fadila da take son Fu’ad Wato Fauziyya itama da sauri ta bangaje Ni ta janye kujerar ta zauna tana cewa me cikin shege,Baki na saki Ina kallon su Kawai na juya zan koma wani wajen,Hannu na naji an rike na juyo da sauri a tsorace sai Naga Fu’ad ne ashe,Lokacin Ido na ya ciki da Hawaye Ni kowa ya tsane ni kenan,Jawo Ni yayi jikinsa sai ji Nayi yayi sama Dani ya Dora Ni a cinyarsa,Kallo ya sake dawowa kaina naji kunya ta masifa Ina nokewa Ina so na gudu Amma sai yace ke dalla zauna ke ba Yan Mata ba kwaila me zakiji Ni ba irin Wanda ya Miki ciki bane,Ni kadai naji Maganar,Nace wallahi Ni ba kwaila bace cab Kaine dai kwaila wanda ko soyayya baka iya ba,ae ai naga alama shi yasa kika Yi ciki ko? Nace ai yaron ma me kama da Kai ne Kuma Ina son dana,Sunanka zan saka Masa idan namiji ne,idan mace ce kuma Sunan Fadila ko Naila,Da kuwa kinci Ubanki a gidan Nan cewar Fu’ad,ki rasa Wanda Zaki sawa sunana sai Dan shege,Murmushi Nayi Ina wul wulla kafafu na Ina Wasa da su by mistake na taba kaurinsa,yace kar ki Bata min Kaya fa,Su Lubna Kawai kallon ikon Allah sukeyi takaici da kunya ya Kama su an disga su,Gashi Basu San hirar da muke ba sabo da kida,tashi sukayi da haushi zasu bar wajen na kalle su Ido cikin Ido na dinga antayo musu gwalo,Ina ta rawa Zaune a cinyarsa har da daga Hannaye sama,Ashe Fu’ad yaji gulmar ance shi yayi min ciki shi yasa ya Nunawa kowa nasa dinne suyi abinda zasu Yi ai Allah ya San gaskiya.

Koma kujera sun tashi kin dameni,na kyalkyale da Dariya sabo da wani irin farin ciki na tsinci kaina ciki na manta duk damuwa ta Baki daya,kafada na makale tare da furta dadi,Momy da Mama tare da sauran Yan gida sai kallon mu sukeyi Kamar idon su zai Fado yau sunga zahiri cikin Fu'ad ne ya ma daina boyewa, Fu'ad duk Yana kallon abinda sukeyi,Amarya sai harara ta takeyi,Umma itama Naila ta fada Mata gulmar da akewa Fu'ad cewar cikinsa ne, Umma taji haushi Amma Bata saurari kishiyoyinta ba,sannan ita abinda Fu'ad yayi Sam Bata ga laifinsa ba,da Hannu Umma ta yafito Fu'ad yazo,Nima na gani sai na koma kujera yaje Kiran Umma,Yana zuwa Tace Ina kudin likina? Ya zaro raper Yan dubu dubu ya Bata Dana Naila,Umma Tace ka bawa Rumaila Bai amsa ba ya tafi ya dawo inda muke Zaune daga Ni sai shi,Yan matan Amarya da dangi Ana ta kiransu suna rawa da liki,Amarya da Angon sun fito fili sai da Fu'ad ya Bari duk an Gama rubibin ruwan liki sannan ya bani Nima Yan dubu dubu yace je ki min liki,na karba tare da Mikewa Yar dagwas Dani Ina tafiya cakwas cakwas Ana ta Yaba kyawu na da kyan surata,Fadila ta balla min harara na share su Waka tana tashi na Balle raper a Raina Ina cewa wayyo Iya ga kudin-Ga kudin a Nan,Iya dadi ya barki,Iya ba Rabo Allah sarki Iyata sai dai ki samu naki a darul salamu, na fara liki far far,Dj ya saki sauti su Rabi sun Ware murya da karfin gaske sabo da karar kida suna cewa wayyooooo Allah Alqur'an Yan Dubu take likawa duf Kake Dj ya tsaya da kida aka sake Jin muryar su Rabi ta cika Hole din suna cewa Alqur'an Yan Dubu dubu take likawa,aka sake kallonsu aka dinga Yi musu Dariya,Hajara Tace yau Bamu da sa'a Kawai mu daina magana idan an koma sai muyi gulmar,Saude Tace tsinannen Dj ne wannan sai kunyata mu yakeyi to wallahi kwandala bazan lika Masa ba Dan ubansa,Rabi Tace wannan kwai jarabar Rumaila tazo dangina daga bakunta tazo ta kwace Mana dangi wallahi da nasan Haka ne wlh bazan zo da ita ba,Kawai na dauki wuka na dabawa kaina.

Momy da Mama Suka girgiza Kai tare da kallon juna Suka ce ta Gama tabbata zasu ci ubansu wlh Bari a Gama biki hankali ya kwanta,Ina yiwa Amarya da Angon liki Fu'ad yazo Ni Kuma Yana lika min sai da ya gaji,Ina tsaye Safna ta wuce fuuuu ta fadawa Mc ya min tambayoyi na wulakanci ya kunya ta ni kowa ya min ihu, Amarya akace su koma su zauna,zan tafi Mc yace Yar fillo ga kyau ga kwalliya ya sunanki? Ya Kara min speaker a Baki,Allah sarki ban sani ba nace Rumailan Fu'ad me murmushin Naira,aka kwashe da Dariya har Fu'ad Wanda ya koma tuni ya zauna,Mc yayi Niyyar abinda aka Umarce shi Amma ganin Fuad sai ya Masa kwarjini Yana Tsoronsa,yace waye Fu'ad a wajenki ko kema kanwarsa ce? Nace ka daina rage min daraja mana ai nafi kanwa matsayi a wajensa,Uwar gidan sa Kuma uwar 'yayansa Inshaallah, me Zaki cewa makiyanki? Nace ba abinda zance face na zaro harshe waje na kalli ko Ina a hole din nace wannan gwalon shi zancewa da makiya na, har Yan bakin ciki sai da suka dinga Dariya,Mc yace Dj sa Mata kida Uwar Gidan Fu'ad ce,ai kuwa aka saki kida me shegen dadi ko baka so sai ka taka,Momy na kalla Muka hada Ido na Mata girgiza,Mama ta Bude Baki Tace wannan tsagera ce,Islam ne ya fara zuwa Yana min liki Banda girgizar da nayiwa Momy ba abinda na sakeyi na rawa Ni ba wata rawa nakeyi ba,a wajen na tsaya kawai maza Suka dinga tururuwar Yi min liki, Fu'ad nake kallo Ina masa inkiya da Ido akan yazo ya min liki,Bai taso ba sai da na gaji na fito zan bar wajen rawar sannan ya Iso da Izzarsa ya sake bani sababbin kudi Yan dari biyar shi Kuma ya fito da Yan dubu Yana lika min Nima Ina lika masa,Umma tazo  ta Mana liki,Haka Naila,Sai mazan gidan kaf dake maza ba irin Mata bane Basu fiye shiga harkar wani ba bare su suna da aikin Yi gasu da Ilmi,Kamar bikin mu akeyi Haka Muka Sha ruwan liki,Naila ma tazo tayiwa yayanta Ni kuwa hararata tayi Nima na rama.

Muna Gama likin muka koma Muka zauna Yana wani basarwa ya wani Bata Rai nima na share shi na shiga cin abinda aka cika table din da shi,abinka da me ciki sai da na koshi Ina gamawa na Mike tare da daukan jakata na kalli Fu'ad nace na gode Allah ya Kara arziki,Ina Zaki je? Nace gida na Gama biki na ai kasan Dan ciki na kida ya dameshi sai motsi yakeyi Kamar kifi a ruwa,bacci Kuma nakeji,Hade Rai yayi yace ke baza ki Fadi Wanda ya Miki cikin Nan ba ko? Nace Hmm Kawai na juya Nayi tafiyata,Ina fita na tare taxi na shiga sai gida,Ina komawa wanka Nayi na shirya cikin kayan bacci na Bayan Nayi Sallah na kwanta abina bacci yayi gaba Dani.

Sai wurin 3am Yan Biki Suka fara dawowa,Abbi ya Hana ayi Event da yawa yace daya ta isa,washe gari za a daura aure zuwa dare akai Amarya shike Nan an Gama biki.
Washe gari Saturday ranar daurin Aure,da wuri aka fara Shiryawa,Nima Ina jefa gyada a bakina har Nayi wanka na shirya cikin Shadda ta Yar gaske fara Kal da adon dinki Kuma peach and dark blue,Me Daurin dankwali ta daura min dark blue dankwali sai na koma Kamar wata Amarya Nasha Yar make up kadan,Palo na fito Umma Tace Masha Allah kinyi kyau iri daya ke da Fu’ad sabo da Yadi goma ya siyo ya Masa yawa shine ya kawo min yardi Uku aka Dinka miki,naji dadi shike Nan za a ce shine ya Dinka Mana zasu sake sabuwar gulma,Umma kuwa wani material ta sha,Amarya lace me tsada Haka kowa gida ya cika da Yan gayu sai kamshi da kamshi,duk mazan Sun tafi daurin Auren Fadila a masallacin Unguwar,Angwaye sun zo,11am aka daura auren Fadila Suffiyan jawa da Angonta Engineer Sadeeq Igabi,Umma Tace Rumaila bani wayata wannan hoton ya Isa Haka kinyi kyau jeki wajen Fadila kice su zama Ready Angwaye zasu shugo,naga duk Yan bikin basa saka Mayafi Nima ban saka ba na tafi gaba na Yana faduwa nasan zan Sha wulakanci.

 Ba karya Nayi kyau sai kallo na akeyi,su Rabi Dan Iyayi suna wajen Kawayen Amarya Ana ta tsokanar su suna kauyenci Ana musu Dariya,sannan sai aiki suke sa su suna Aiken su,Inda Fadila take Yar Aiki ta nuna min na shiga da sallama na iske Ana Mata kwalliya an ma gama nace Anty Fadila Umma tace Ki shirya Angwaye zasu shigo,Yan matan Amarya sai gayu ake Sha kowacce da Kalar nata haduwar,Lubna Tace ke Rumaila zo Nan Dan Uwarki dama Ina so na ganki ke ga Yar Iska ko jiya Ni Zaki ki Nunawa bariki? Tunaninki sonki yake Yi akan ya Miki ciki to wlh Fu'ad yafi karfin Yar Kauye irinki banza jaka Suka saki Dariya har da su Rabi,ban kulasu ba na tafi Abina dama duk sun Gama Shiryawa,Fadila ta daka min tsawa ke Dabba tsaya ki rike min wayoyi na da jakata duk Inda Nayi ya zama dole kina wajen sabo da zan na amsa waya,Ko a jikina na karbi wayoyi da hand bag dinta na tsaya tare da Yan matan kaf Muka fito sai ga Angwaye da Yan gidan maza da abokansu Har Fu'ad shima,Shaddar mu har zanen iri daya,sai bakin ciki ya Kama masu son Fu'ad da Yan Uwansa shi Bai San ma Ni aka dinkawa ragowarsa ba,kannen sa Mata gaba daya Suka lullube Fu'ad suna ta daukan hoto da shi wannan ya ja shi can wannan ta ja shi can,gaba daya Suka hadu Ana ta ruwan pics, da tsokana nace yawwa Nawan Fu'ad haska su ka fisu ka take su,sai kafi kowa kyau,ke munafuka rufewa mutane Baki cewar Lubna,Alhajin Qarami da matarsa shine Babba a gidan Amma ba a shaku da shi ba shima Ana ta pics da shi,uban DJ ne ke tashi a gidan har an kunna sai dare zasu tashi,Abbi ma anyi da shi,naje na tsaya kusa da Abbi aka dauke mu munyi kyau, Fu'ad ya shigo Muka saka Abbi a tsakiya,su Umma ma Suka fito akayi da su Anty Samha da yaranta Amaryar Abbi,kakar su Fu'ad ta wajen Uba itama an kawota dake ta Gama tsufa duk a susuce take ma bata Gane komai,su Nenen Kauye,Da ta Kano da duk wani Dan Uwa,sai Kawayen Amarya,Sai Angwaye,,Ana Kiran Fadila na Bata wayoyinta na silale na gudu,abinci na eba Dakina na koma Ni kadai na zauna Ina ci kenan Umma ta shigo tana kwala min Kira,na fito da sauri Tace Islam da su Abdulhakeem sunce kije kuyi hoto Wai kinyi kyau,plate din fried rice and chicken na dauka na tafi a Haka aka dinga daukan mu da abinci na a hannu,har aka Gama na tafi,Angwaye suka tafi Suma aka ci gaba da shagali.

Da Yamma Nayi wanka na canja Atamfar Riga da skert sai magrib aka tafi Kai Amarya a motar Islam naje,su Rabi ma sun je,a ranar aka Gama biki washe gari duk na nesa suka tafi har su Rabi nice kadai na rage sai Babar Abbi Wai sai Nan da wata biyu za a maida ita Germany Likita yaci gaba da kula da ita, Yan aiki sun Gama gyara ko Ina Kamar ba ayi taro ba,yau na samu Umma a Palo na durkusa nace Umma gobe zan tafi gida Inshaallah,Umma Tace hmm Rumaila kenan ai kinzo kenan sai dai kije Kauye da yawo,Abbi yace karma ki tafi,ga cikin dake jikinki duk yasa kina Shan zagi ki zauna a Nan har ki Haihu Allah ya Baki Miji na gari kiyi aure, a Raina nace wa zai auri irina ,Nasan ko na koma kauye to abin takaici zan ta ji,dadi naji a Raina, Nayi ta yiwa Umma Godiya har Abbi na je nayi Masa godiya yace ba komai.

Su Momy suna Jin labarin a gidan zan ci gaba da zama suka ce ai dole tana Haihuwa ta Basu dansu tunda dama son Dan shege sukeyi,Islam Yana Zaune Momy ta zuba Masa rankwashi Tace sai na ci ubanka wlh idan na sake ganinka tare da Rumaila Wato harda Kai ta gidan Amarya ko algungumi,Islam ya tashi ya bar musu dakin gaba daya.
 Su Rabi Ana Kauye tunaninsu zan dawo sai suka ga shuru ai kuwa sai da suka bugo waya Suka tabbatar na bar zaman Kauye,Rabi ta cizi yatsa Tace ba komai zanzo ne Watarana sai na sa an Kore ki Rumaila,kinzo kin kwace min dangi Allah ya Isa matsiyaciya, Ni kuwa tuni Umma da kanta ta kaini Islamiyya ta kusa da gidan wacce a kafa ma zan dinga zuwa 4pm to 5:30,Bata ce na dinga zuwa ta gidan ba sabo da Yaran gida zasu wulakantani,Uniform kala Uku ta Dinka min da takalma,Ta Boko Kuma wata Yoruba ta dakko min zata dinga koya min turanci karatu da Rubutu,idan na fara Iyawa sai a saka Ni a makarantar Boko,Nasha murna Kamar na mutu,Haka na fara karatu kullum Umma tana sake koya min,dake Ina so sai na dage Ina naci da kokari, Fu'ad kuwa ba sosai nake ganinsa ba Yana Office sai dare,,yau ba school Toilet na shiga zanyi Alwala sai kuwa jini ya zubo zanyi fitsari,Ihu na saki me Aiki ta fado da sauri nace Kira min Umma kice tazo nayi Bari,ciki na ya zube Ina ta murna, Fu'ad lokacin Yana gida tare da Umma me Aiki ta Fadi sako na,Umma itama Tace Kai Alhmdllh ta shigo toilet din na nuna Mata taga jini kadan,ta kawo min pad Tace shirya mu tafi asibiti,Haka nayi wanka na wanke toilet dina na shirya na saka Arabian gown tare da yafa Mayafi nta Muka tafi Umma da kanta ta tuka motar Muka wuce Asibiti daga Ni sai ita.

 Wani private Hospital ta kaini Bayan bincike Likita yace ciki Yana Nan lafiya Kalau Period na fara dama wasu Ana samu ko suna da ciki suna yin period,Murna ta koma ciki,magunguna ya Bamu Muka dawo gida a Palo Muka Iske Fu'ad,Yace Umma yaya? Umma Tace ai Yana Nan daram,Dariya yayi Yana kallon fuskata wacce kadan ya rage na fashe da kuka,Magungunan na watsar a wajen nace Allah bazan Sha ba don Kawai yaron ya samu lfy to wlh bazan Sha ba ya mutu Dan shegen Banza,Kuma wlh a waje Zan na kwana Sauro yayi ta cizo na malaria ta Kama shi yaji jiki ya Sha wahala, ko na koma Shan ruwan rijiyar Typhoid ta Kama shi me karfi ta bubbula Masa hanji, Fu'ad Yace kanki kika yiwa mu Ina ruwan mu uban waye yace kiyi cikin,Umma ta haura sama ta barni tana Masa fada.

Bayan kwana Uku Umma Tace da Fu’ad ya fara kaini awon ciki a madadinta,Haba Umma so kike a ci gaba da zargina?ai zargi ya Kare tunda a bikin Fadila ka Nunawa mutane zahiri ka kiyayeni Fu’ad, tunda baza ka bi Umarni ba Ni Zan kaita da kaina, I’m sorry Umma Zan kaita ya furta Yana Bata Hakuri tace gobe Monday sai ka kaita ,Okay Allah ya kaimu ya furta.

 Ali Me shayi kuwa ya Gama ganin take taken Iya so take ya sake ta shi kuwa yace zanyi maganinki,Duk wulakancin da Iya zata Masa sai ya kyaleta ko kulata ba yayi,Iya tayi tayi Amma Me shayi yaki sakinta,Haka Kawai dabara ta fadowa Iya sai ta dinga fita unguwa baza ta sanar Masa ba, shi kuwa ko ya ganta ko ya dawo ya Iske ta a gida baya ko cewa ya akayi ta fita Bata tambaye shi ba,Kuma bazai nuna yaji haushi ba,Kamar kullum Haka Iya zata ganshi Kuma ko Zaginsa tayi dole idan yazo dakin ta ranar kwananta to fa sai ya sadu da ita,ko ta Hana ta karfi zai Danne Iya yayi abinsa,Shi har ya fi so ma Tace baza ta yarda da shi ba sai ya sa karfinsa,Iya taga da wannan tsarin nata baiyi ba sai ta fara tsanar yayansa tana azabtar da su kullum cikin fada da kishiyarta take Amma me Shayi yace hakki a kanki Kuma wlh yara ba ruwansu Dan Haka ko a jikinsa,Ah Iya ai sai taga Nan ma baza ta bulle da ita ba,Idan ya shigo sai taci kwalarsa Tace ka sake Ni idan Kai Dan halak ne,Me shayi ya samu ya wawwankawa Iya Mari ya hankade ta ya shiga harkarsa Kuma da dare ba zai fasa ba sai ya karbi hakkinsa,Iya ta sake canja plan sai ta dinga Wayar karya tana soyayya a gabansa Wai da samari shi Kam ya Gane tana Yi Yana Dariya,sai da Iya tafi sati tana Wayar Iska shuru ba saki,ita kadai ta fashe da kuka sai an sake ta lallai,da Daren ma sai ta daina bacci Sam sai ta kwana tana kuka Kamar me Aljanu,Har mamakinta me shayi yake yi,Yau ma Yana kallonta cikin dare ta fice daga gidan ta dawo zaure ta kwanta tana ta kuka,ya fito ya kalle ta Kawai sai ta bashi tausayi yace Allah ya shirye ki,Kudi ya zaro dubu Uku ya shafa Mata a fuska kafin kace me Iya ji kake luf ta Mike Zaune zumbur tare da furta kudi ne?????? Laaaa Kudi....Me shayi ya Mika Mata yace gashi,da sauri ta karbe Tace na gode duka Nawa ne? Me shayi yace ae ki siya abinda kike so,Ya juya zai tafi Iya ta riko rigarsa Tace yau kwanana ne fa,yace na sani ai,to yau baza kaje garin shagali ba ne? Dariya me shayi yace Baki ji sunana ba Ali Shagali muje na hau hanyar Shagali na,Iya ta bishi ba kunya.

 Amadu Affa na a bakin kasko yake Yana ta suyar fanken siyarwa Yana rike da matsamin Fanke daure da zanin Leshi milk, wasu Yan Fulani da suke kunna Dj a kasuwa Ana zuwa suna turawa mutane film Ana biyan kudi Suka saki Dj Yana suya Yana cashewa Yana wani karairaya tare da girgiza da kirjinsa Yana shewa,Ana sa wakar wani tsohon mawaki wato Na gwagwa,Affa da karfi yace Ahayye ah Subhanalla tare da Dora  Hannayensa a saman Kansa Yana cashewa da kugunsa Yana murgudedeniya Yana fari da ido ko kunya baya ji,Allah ya rufa min asiri na bar garin da bakin ciki kadai ya ishe Ni,Ni Kuma ga cikin shege Kai bala'in yayi min yawa.

 Washe gari Monday da wuri na shirya Fu'ad Yace na same shi a mota ya Sha farar jallabiyya Yana kamshi a wata dalleliyar motarsa fara na hango shi,sanye nake da bakar Abaya nayi Rolling,Gaban mota na bude na shiga da jaka ta a hannu,ta saman bene su Momy suna ta lekowa suna gulma suna cewa ai wlh awo zai kaita da gani matsiyaci kunga, Kai karshen duniya ya Gama bayyana sai dai mu bugawa mutanen Niger waya muce tashin kiyima yazo da Cameron da chadi ma sai dai suji a labari a wajen Yan Nigeria kafin ya karasa musu can,Momy Tace yaron Nan Mama kinga dai Ni na Raine shi wlh duk ya Gama sire min na tsane shi,Kuma yanzu ya juya Mana baya Ummansa itace Kawai Uwarsa mu Bai dauke mu Uwa ba,Mama Tace yo itama Umman tasa Baki ga ta daina shiga harkar mu ba,Dan taji munji Danta yayiwa wata cikin shege daga fadar gaskiya,Namiji munafuki ne shi Kuma Abbi yabi bayansu ya dauki son duniya ya dorawa Rumailan nan,nasan da ace ba matansa hudu ba to wlh da shi zai Aure ta,itama Amaryar tasa Samha taga Umma ta iya Munafunci tana bangarenta tare suke zumunci mu bata ganin Kimar mu,Yaranta su Suhaila gaba daya sai wajen Umma.

Baba Jummai wacce Yan fashi suka ce Fu'ad ya sadu da ita na fanshe ta,tana Mopping Tace Momy ai Ni nasan komai Nan ta kwashe labarin abinda ya faru tsakanin mu da Yan fashi ta fada musu,Tace Ina da tabbacin a Nan ya fara amfani da ita sannan daga Nan an Bude Masa hanya Suka ci gaba da mashaarsu tare har ya Mata ciki,Baba Jummai har da rantsuwa a gabanta aka Yi komai,Bayan Bata sani ba lokacin ba ayi komai ba,Momy ta rike Baki Tace cab lallai ai ke Jummai Baki da wayo Baki Gane bane na Sha kamata a part dinsa,dama na Sha Kama su shi yasa ai Tace ta fanshe ki ba Dan Allah tayi ba,Baba Jummai Tace biri yayi Kama da mutum munafuka harda kukan karya Ashe na dadi ne,Safna Tace ai Baki ga zahiri ba a Wedding Dinner Anty Fadila ba? Mama Tace kafin Azumi ai Fadila zata zo da Yan Sanda a kamata Ana zarginta da cunen Yan fashi Wai Tace Yarinyar Yan fashi ce,ranar yini sukayi suna gulma,Abbi Bai San me suke kullawa ba ya Gama shiri ya tafi Dubai daga can gaf da Azumi zai wuce Saudiyya acan zaiyi Azumi har a Gama sai Bayan Sallah da sati daya zai dawo,dama komai a hannun Fu'ad yake,Su Momy sai murna sukeyi zasu Kama Rumaila a kulle Ni.

 Ni kuwa Ina motar Fu'ad sai kamshi da sanyi kida na tashi sama sama na wakokin turawa,Yana Driving a hankali baya magana Nima bance komai ba Gyada ta nake ci kadan kadan,daga cikin garin Abuja naga Mun fita,tsoro ya kamani Yana satar kallo na,Wani kauyen gwarawa ya shiga sai ga wani Asibiti Karami na Gomnati marar kyau,kafin nayi magana yace yes shi Zaki dinga zuwa awo tunda kika Yi cikin shege ai dole ki Sha wahalar rayuwa Kin karya dokar Allah kin dinga Shan azabar rayuwa kenan,murmushi nayi nace ta Kai ta kauyen mu? Ke kika sani,nace hakan ma na gode a bakin Asibitin ya tsaya tare da furta fita kije kibi layi cikin talakawa ki Sha Ranar masifa idan Kuma ruwa ya tsuge ya zane mana ke tas, ki dawo gida Kuma mura ta kamaki kiyi ta kwala tari da atishawa,majina ta Hanci ta makoshinki,Dariya ya bani na dinga kyakyatawa sosai,Dubu biyu ya bani kudin Bude File da Kuma kudin mota ya juya yayi tafiyarsa.

Ni kuwa ciki na Shiga da tambaya nayi komai da ake bukata aka Bude min file da komai,Likita ya dubani har da scanning komai lafiya Dana Kuma Namiji ne, duk ranar laraba Zaki dinga zuwa awo,Bayan na Gama na fito naga masu siyar da kayan ciye ciye iri iri,kwadayin me ciki yasa na tsaya na siyi Data,na siya Aya,na siyi kwakwa da dabino da sauransu,wata rigar jariri ce ta birge Ni na siya na hada kayana a katuwar bakar Leda sannan na shiga Taxi na koma gida.
Umma ma Bata Nan taje biki,Na boye kayana a daki,nayi wanka tare da gabatar da Sallar La'asar na ebo abinci naci abinda nake so.

Washe gari da safe 11am sai ga Fadila Amarya da motar Yan Sanda mota Guda a gidan.

Masu sharhi Ina matukar godiya,Kuna birge Ni wlh.

AsmaBaffa.
????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.

        NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK.

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

           26-30

Official

By
AsmaBaffa
Page naku ne

BEAUTY BOSS
UMMU AYMAN
M BELLO
NANA FIDDAUSI BELLO
RAKIYA YUSUF OZEGYA
PRETTY DEEJARTH
MARYAM ABACHE
OUM SAFWAN
SHAMSIYA BASHAR
FATIMA ZAHRA BINTU

        Allah yasa naji hayaniya Kawai na leka ta window Naga Yan Sanda da yawa,Sai ga Umma ta shigo da Sauri tana cewa Rumaila bi ta Kofar baya ta kitchen ki koma part din Fu'ad ke akazo za a Kama fa, ai ban ma tsaya ji ba na fyalle da gudu na Sha kwana tuni su Safna suna hayaniya tana Ina bauraniya ki fito Ina jinsu a hankali nace baza a fito ba,Nene ta fito tana Hawaye tana basu Hakuri sunki ji Yan matan suna sai Mun daure ta Wallahi Khaleesat harda tsalle,Allah yasa ban hadu da kowa a hanya ba na fada cikin palon kasa na fita,Karo naci da mutum gaf, kamshinsa ya daki Hanci na,Ya Gama shiri zai fita Office,Ina Haki nace ka taimakeni Police dasu Fadila zasu kamani za a kaini gidan yari wayyo Masifar tayi min yawa Wallahi bazan iya daukan wannan ba,wannan dai bazan iya ba kaddarar me girma ce, Fu'ad yasan kan zancen dama, yace ke Calm down kwantar da hankalinki,Kinyi wanka? Na daga Masa Kai Alamar nayi,Ya kalle Ni yace kayan Nan naki sun min local bazan iya fita da ke ba Haka,Dan Allah ka taimaka nasan iyayinsa ne Amma shaddar bikin Fadila ce a jiki na irin tasa nayi kyau Kuma,shi kuwa kana Nan Kaya ya sha,Muje to,nace Na'am? Muje zasu kamani muje nace ko? in bakya so Zan tafi,shahada nayi na jera da shi Muka nufi inda Yan Sanda suke Ina ta cewa Yan Sanda fa wayyo,Hannu na ya rike Kam cikin nasa,Momy da yatsa ta nuna mu tana Officer gasu can,Duk Yan gidan har maza suna wajen da Yan aiki an cika, Fu'ad ba mutunci ya Bata fuska kamar Bai taba Dariya ba,Muka tako har Gaban Yan Sanda da mutane,Wani Dan Sanda ya daga min ID card yace  you are under Arrest, a Gaban Fadila Fu'ad ya tsaya Ina rike a hannunsa yace ke Dan Uwarki wannan ce Rumailan? Fadila tsoron yayanta ya kamata,Mari ya dauke ta da shi yace nace ita ce Rumailan? Fadila ta fashe da kuka da tsoro Tace a'a ba ita bace,Yan Sanda Suka saki Baki suna sallallami,Khaleesat ya murdewa Hannu sosai yace ke wace wannan fadawa Yan Sanda Khaleesat Tace Maryam ce karya muke ba ita ce Rumaila ba Wannan Maryam ce,dama mun tsaneta ne shi yasa muka Mata sharri,Momy tace karya ne Sir,Dan Sanda yace who said Sir? Momy ta daga hannu irin abin kirkin Nan Tace  nice,yace You are very stupid kun San karya ne kuka wahalar da Yan sanda,mu abokan Wasan ku ne? Dan Kuna da kudi wlh da a police station ne sai na rafka Miki Mari Nonsense Get Out Yan iskan banza kun Bata Mana lokaci, Fu'ad Yace kaji dai daga bakinsu to ba itace Rumaila ba Rumaila Yar Kano ce kuje can ku nemeta,Kuma wlh kuka Kara zuwa Nan wallahi sai na shigar da ku Kara duk aikinku sai kun rasa Kuna biyewa Mata,Hakuri Suka shiga bashi,ya zaro kudi ya Basu Suka tashi motarsu suna zage zage Suka koma.

   Murna ta kamani Ban san ma na nayi tsalle a Gaban Fadila ba nace Fuck you.....Fu'ad sai da yayi Dariya Wai Ni Yar makaranta har nasan Fuck, Umma tana kallon komai,Momy Tace Allah ya Isanki Fadila shege kwarto ta furtawa Fu'ad, Fu'ad Yace rainonki ne tarbiyyar ki ce,Iyyeeee kaiiiii Fu'ad cewar Mama,mota muka shiga ya tafi Dani,Momy Tace ai wlh Bari zamu hada plan dole Nan gaba zamu kawo wasu Kalar Yan Sanda dole fa Yarinyar Nan sai tayi zaman gidan yari,Fadila tana kuka Tace wallahi...kar...kar a barta,Nima wlh tunda ya mare Ni a kanta yanzu na fara sai Naga karshenta,Islam ya furta Dan Allah Wai me tayi muku Haka? Bai dace ba,muna Zaune lafiya Amma akan wata kun lalata zumunci gaba daya,sauran mazan ma Suka ce Bai dace ba.

Ni kuwa yau murna na rasa inda Zan sa kaina,Yana Driving ya juyo ya kalle Ni kadan tare da maida hankalinsa kan tukinsa yace Wai ya naga cikin ki kullum a shafe ne yaki kumbura,nace kaima dai ka fada Kuma watansa yafi biyar ba,irin cikin Nan  ne dani me teba kaga kibar da nayi ce ta shanye shi fa shi yasa ai naji dadi kaga na huta idan nayi aure ba Wanda zai San ciki gareni,Baki ya tabe yace uhm ke kika sani,nace Wai me yasa baka soyayya ne ban taba ganin ka Dan ko kalli wata ta birge ka ba,kwantai nayi sai ki Nemo min ai kisa nayi auren dole tunda ke Uwa ta ce,Baki na Bude nace Allah baka Hakuri daga magana,Ameen ya furta yace tunda kika zo gidan Nan kinbi kin Sa min Ido ni Ina Sa Miki Ido Ne? Kiyi rayuwarki nayi tawa aikin banza Ni fa na tsane ki Bari kiji tunda kikai cikin shege ba ruwana da ke,Naji zafin Maganar sa na Danne nace yo Dan ka tsaneni Ni dama cewa nayi ka so ni? Ni Nace sai ka so ni? Cikin waye yayi idan ba Kai ba Malam zaka dinga pretending,Sitiyari ya daka yace ke dama Haka kike da sharri? Ni a Ina muka taba haduwa har nayi Miki ciki? Tsoro ya bani yanda Naga har ya canja Yana huci,ba shiri nace Wasa nake maka,Harara ya balla min yace wlh da a Nan zanyi parking na zaneki a gefen titi,ko na maidawa su Fadila ke su daure ki,shuru nayi ban sake magana ba naga masifa yake ji,Office dinsa Muka je na Sha kallon haduwa Kai fada ma Bata Baki ne,Har wani Palo ne da bangaren wasu kujeru na Alfarma,Sanyi da kamshi ke tashi,maaikatan dage Building din suna Aiki karkashinsa sai kwasar gaisuwa sukeyi,a kujera na zauna Yana ta aikinsa ,Yar wayata na dakko Ina ta Game,1pm yunwa ta kamani dama ban karya ba sai ga Abinci Umma ta Aiko Driver ya kawo a Basket,Ni na fara eba naci na koshi sannan nayi Alwala a toilet dinsa me kyawun gaske,Sallah nayi tare da adduoi na,Yace an tsaida  Sallah ne? Tun yaushe naji wuyar duniya ban San Sanda na tsaida ta ba,ya fiye Miki ai,yaushe Jauron naki zai zo zance ne Wai? Yana magana Yana buga Stamp a takardu.

Ai kar yazo ace Ina kwashe kwashe,a’a mene ne ba ruwanki da wani Kawai idan yayi Niyya yazo mana,mamaki ya kamani ya akayi yake so yazo? a jiki na naji Kamar da matsala nace bazai zo ba sai idan naje ganin gida Kauye zamu hadu, Fu’ad da wayo yace to ba Kya sonsa Kawai Amma ai saurayi yazo zance shine magana,nace Watarana zance yazo,Bai sake cewa komai ba Nima haka.

Bayan komai ya lafa ban sake Jin komai ba bana ko fitowa daga part din Umma sai wajen Nene Ina zuwa, Har ciki na ya wuce wata biyar Amma ciki Sam Bai ko dago ba abin mamaki,Ga awo Ina zuwa ance yaro lfy yake, Umma da kanta ta sani a makarantar Boko me tsada ganin Ina da kokari Kuma na iya karatu da Rubutu turancin ne Bai zauna sosai ba sai a hankali,na Kara wani wayewa na goge,gashi Umma sai Kaya take Dinka min,ga Ready made etc,Naila ta shirya ta tafi Kano wurin kanwar Nene zata Dan Huta,Mama Kuma Ana saura kwana Uku Abbi yace ta taho Saudiyya suyi Azumi tare,Su Momy Suka ce Allah kaimu Bayan Sallah kafin su dawo sai dai suga Rumaila a prison,kafin ta tafi Momy,Mama da Fadila sun Kira Abbi sun fada masa komai akan cewar Rumaila Yarinyar Yan fashi ce,sannan Fu'ad shine ya Mata ciki, Abbi dai Bai yarda ba Amma yace bincike Yana da dadi ya fasa zaman Saudiyyan gida zaizo yayi settling komai sabo da Haka Umma ma Bata tafi ba.

Kwana daya tsakani sai ga Abbi ya dawo lokacin Kuma su Momy again sunje sun sanarwa wasu Yan Sandan daban tare da jika su da kudi,a ranar Abbi ya Tara kowa na gidan muka hallara kaf,Abbi ya kalli kowa duk Muna kasa shi kadai ne a kujera a zaune,yace ba sai nayi bayani ba kowa yasan dalilin zuwa na,Fadila ance kece kika San komai,to mene komai din akan Rumaila? Fadila har da mikewa tsaye kamar a makaranta tayi bayanin barazanar da Rumaila tayi,sai Bayan ta Gama kaf Momy itama aka Bata dama ta Mike tayi Karin bayani Tace yau Zan daina boye boye kowa yasan gaskiya,Ni dai na Sha Kama Rumaila a part din Fu'ad,sannan Bayan barinta gidan Nan da wasu lokaci ta fara laulayin ciki,Bayan an Mata test aka tabbatar tana da ciki na wata Uku,idan aka tantance lokaci ya nuna tabbas ba a Kauye tayi ciki ba a Nan gidan ne,Abbi yace waye Hujjar ki? Momy Tace a Kira Baba Jummai,Nan take aka Nemo Baba Jummai,Abbi yace Baba Jummai me kika sani tsakanin Fu'ad da Rumaila,Baba Jummai ta kwashe komai daya faru lokacin da Yan fashi suka zo fashi gidan sannan Tace ta fanshe Ni Kuma nasan fansa ta da tayi dama sun Saba masha'arsu da Fu'ad badan Allah ta fanshe Ni ba,na kalli Baba Jummai nace kiji Tsoron Allah Baba Jummai ki tuna Allah Yana kallonki,Da Ubanki ne yake kallo na,Ni zaki yiwa rashin kunya,Abbi yace Jeki Baba Jummai,Bayan ta tafi ya kalli Momy yace sauran shedunki Zaki kawo min,Nan take Momy ta Kira Wayar Rabi,Bugu daya Rabi ta dauka,Momy ta sa waya a handsFree kowa na ji,Abbi ya karbi Wayar yace Rabi Abbi ne, Nan take ta gaida shi,yace tambaya Zan Miki me kika sani game da cikin Rumaila? Dama can Momy sum Gama hada Baki da su Rabi,ai Rabi Tace Ciki Kam tayi shi Kuma Fu'ad ne yayi Mata ciki,tunda Muka zo gidan Nan kullum sai taje part dinsa tana fakewa da gyara Masa part dinsa,daga baya Kuma har cikin dare sai muga ta sace jiki ta fita cikin talatainin dare,Har binta mukeyi a baya sai muga Fu'ad da Kansa ya Bude Mata kofa ta shige,Watarana har rungumeta ya Sha Yi a Gaban mu,munyi munyi ta daina Mun Mata fada tace ba ruwan mu, Kuma ranar bikin Fadila kowa ya gani a kunna maka video din bikin zaka ganta a saman cinyarsa wannan ita ce sheda babba,.

Abbi ransa ya baci yaji kamshin gaskiya Amma duk da Haka yace a kunna Masa video dama mama ta tana da abinta a waya sai ko ta kunnawa Abbi ya kalli zahiri,kan Abbi ya kulle ya rasa ta ya zai warware abin Nan a sirri ba tare da kowa yaji ba ko ba komai Dan ya rufawa dansa asiri duk da Bai yarda ba Amma ba a shedar mutum,Amma Sam Bai yarda Dansa zai yiwa wata ciki ba musamman Fu’ad,Itama Rumaila Sam baya Jin ma ko a jikinsa zata zama Yarinyar Yan fashi Sam bazai yuwu ba Amma dai duniya ko danka ne ba a shedar sa sai anyi bincike.

Umma Kuka takeyi tun tuni,Abbi yace to duk naji Haka ya Isa,Ke Rumaila tsakaninki da Allah ya abin yake Fu'ad shine ya Miki ciki? Ina Hawaye na tausayawa Umma da shi kanshi Fu'ad a dalili na ake ta Masa sharri Ana Bata Masa suna,da suna zaman su lafiya a dalili na Abu ya lalace,Kawai Nace Abbi ba shi bane,to idan ba shi bane ya zakiyi da Maganar Jummai? Nace wallahi Jummai da kanta ita ta nemi Alfarma akan kar su Bari muyi a gabansu Suka amince Muka Shiga bargo,kayan mu Kawai Muka cire suka karba Dan su tabbatar munyi wani Abu har komai da Mukayi kamar Shirin Film Haka Mukayi, yace naji to Maganar su Rabi fa? Nace Allah shine shaida Bai fi sau Uku ba na taba shiga part dinsa Kuma Ni gyara Masa dakinsa nayi shine har Momy taga na fito daga ciki, Amma wlh in Banda a biki Fu'ad Bai taba rike ko da yatsa na ba,to waye ya Miki cikin kenan? a Nan na rasa me zance Kawai Dan na Kare Fu'ad Nace wani saurayi nane Jauro,Ina Gama fada Abbi yace zauna,Kai Fu'ad fa duk abinda Rumaila ta fada gaskiya ne? Fu'ad Yace a'a Abbi, yasan karya shima zai yiwa Abbinsa Bai San ya sadu da wata mace ba a duniya Kawai yace nine nayi yiwa Rumaila ciki kareni tayi,Abbi ransa ya baci yace Kai Ni Wai ya zanyi ne da wannan kullun masifa haka,Kai Fu'ad idan Rumaila ta Haihu dole sai ka aureta na Gama magana daga yanzu ka sani wallahi sai na Daura maka aure da ita tunda ka amsa laifinka,ka bani kunya banza shashasha kaci sa'a daya ta Umma wallahi da sai na daureka Nasa an maka hukunci me tsanani,Rumaila Ina godiya da karar da kika nuna min da Umma kin San Dan mu ne Amma kika boye gaskiya sabo da kunyar mu na jinjina Miki Allah Kuma ya Miki Albarka ya Kara shiryar mu baki daya.

Momy ba haka suka so ba burinsu a Kori Rumaila ko a kamata sai Tace to Maganar Yan fashin fa?Abbi yace wannan zancen banza ne daga bakin mutanen banza….kafin Abbi ya rufe Baki Yan Sanda masu yawa bataliya Guda sun cika palon tare da Nuna Rumaila,Ogansu yace You are Under Arrest,Rumaila ta Mike tsaye,Abbi zaiyi magana sukace baka da damar magana idan Kuna so ku bi mu station,sai ayi magana Amma ku idan kun yafe Mata mu hukuma dole sai munyi bincike a kanta sosai,idan Bata da laifi zamu sake ta Amma baza mu bada Belin ta ba sai Mun Gama bincike a kanta, Fu’ad ya Mike yace ai ba Haka doka tace ba,Abbi ya kalle ni yace kiyi Hakuri Rumaila za a dinga Kai Miki abinci Ana kula da ke Allah zai isar Miki Kuma Inshaallah zanyi wani Abu,Kawai bin Yan Sanda nayi muka tafi.
Cikin Sel suka sakani tare da kulle Ni Bayan sun karbe wayata da dankunne etc.

 Ni kadai a ciki na zauna kamar marainiya tunanin rayuwata ya dawo min na daga kaina sama Hawaye ya shiga sintiri a kumatuna, Fu'ad kuwa Abbi yabi Yana cewa Dan Allah kar a kulle ta ka bada kudi masu yawa a saketa idan kayi magana abin zai fi,Abbi Dan Allah a samo hanya,Abbi yace Fu'ad ka Dame Ni Wai ko dama son Yarinyar kakeyi ko kuwa sha'awarta kake? so kake a fito maka da ita kaci gaba da Yi Mata wayo? Shuru Fu'ad yayi yace Abbi gwara ma ka fito da ita wlh Dani za a kulle a Sel din,Abbi ya zaci Wasa Fu'ad yakeyi yace to ai dole sai anbi a hankali ta karkashin kasa kasan case din babba ne,a Bari suyi bincike Mana ai dole gaskiya zata Yi halinta, Fu'ad Yace Abbi su Momy ne fa za suyi ta Basu kudi Ana azabtar da ita,so kake kafin a Gama bincike Yar mutane ta mutu,Kuma tana da ciki? Abbi Yana sani yace to Ina ruwanka Wai? Fushi Fu'ad yayi Ya koma wajen Umminsa yayi Mata rada a kunne ta Dan murmusa ya tafi,wanka ya dauka cikin wata arniyar Shadda sea blue Yana kamshi yasa Driver ya kaishi police station inda aka kaini,Ina ciki kamar marainiya,Wurin Dpo ya Shiga ya zauna,ya buga ya buga yaki bada Belin Rumaila,Takaici ya kama Fu'ad ya zaro kudi masu yawa ya ajiye masa a saman table ya cire agoginsa me tsada ya Mika musu yace Bude min inda take na Shiga ka hada ka kulle Dani,Dpo kuwa yace Fine  ya Kira yaronsa Suka tafi da Fu'ad har cikin Sel,Ina ganinsa farin ciki ya lullube Ni tunani na fitar Dani za ayi sai Kawai naga an bude Masa ya shigo shima an maida kofa an Rufe dani da shi a ciki Dan Sandan Yana cewa Soyayya dadi,Amma fa ka birgeni a kulle budurwarka ka shugo a hada da Kai harda biyan kudi akan kulle ka kaima,to wannan a kanta zaka iya kashe kanka ma.

Duk da Haka naji dadi ko banza Ina ganinsa mantawa nakeyi da damuwa ta,Bai min magana ba nace kaima kamaka sukayi? Ae Kawai yace min,Murmushi nayi nace yunwa nake ji Allah yasa Umma ta kawo Mana Abinci sai kuwa ga Umma da kanta tazo aka fito Dani Kawai Fu’ad Yana ciki,muka gaisa Umma Tace ki Kara Hakuri kinji very soon Zaki fito Abbi zaiyi maganin komai nace Inshaallah na gode Umma,Abinci kala kala aka bani a kwando Umma ta tafi Ni Kuma na shiga da shi ciki sabo da Fu’ad ya biya kudi ba a takura Mana,Sel dinma daga Ni sai shi aka barmu ya biya kudi,Abinci na Bude na ebi yanda zai min,nace Kai fa? Yace sai dare kici naki Kawai,Zama nayi Ina ta ci Yana kallo na,tunani na tafi Hawaye ya zubo min nayi saurin gogewa,Mene na kuka Kuma? Iyata nace Ina Hawaye Ni gwara na tafi kauyenmu,Abincin ya karba tare da daukan spoon din ya ebo abincin yace Ahhh Bude bakin,Murna ta kamani har ban San ma na daina kukan ba nace Da gaske kake Yi? Yace ae kina Bata min lokaci,Nace Dan Mazon Allah fa? Yace Uhmmm Zan fasa,da Sauri na Bude Baki na fararen hakorana Suka bayyana ya zuba min jullof rice din da Naman rago,nace dake hannunka ne sai ya karawaa girkin dadi,yace kaji karyarki ko Ni baza ki yaudareni ba yarinya,Yana ta bani a Baki sai da na cinyes tas Nasha ruwan roba me sanyi,Magriba na Yi,Suka Bude mu Muka Yi Alwala tare da sallah,Har Isha Mukayi Basu ce mu koma ciki ba sai Bayan Isha sannan Muka koma Suka kulle mu,Abincin ya zuba shima zai ci nace kawo Nima na baka a Baki? bana so ya furta yaci gaba da cin abincinsa ya koshi,Kasa kwanciya yayi ba shimfida bare pillow,Kwanciya nayi ya gaji ya kwanta shima tare da Dora kansa a cinya ta Ina daga kwance shuru muka Yi a Haka bacci ya kwashe mu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button