DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

      Motocin Amarya ne Suka danno Hancin motarsu cikin Gida,Su Momy aka gyara tsaiwa ga Sanduna a Hannu,sai motoci biyu suka Yi parking a inda ya Dace motar Yan Sanda ta shigo tsoro ya shigi su Momy za a kamasu da makamai hukunci zai hau Kansu,Da Sauri Mama Tace ku zubar sai Yan Sanda sun tafi, sai kace wasu Yan China a tare suka saki Sanduna a kasa,Yan Sanda sun Kai goma suka fito daga motar su tare da tambaya wannan makaman fa? Momy Tace ba makamai bane makamashi ne, itace ne muka ebo zamuyiwa masu kawo Amarya girki ai baza a bar Baki Haka ba,Dan Sanda ya San karya ne Amma yace Weldone kuje muma Muna jiran abincin idan mun Gama aikin mu sai muci mu tafi,dama Saddeeq yace Kar a musu komai surukansa ne sun ci Darajar Abbi,Ba shiri su Momy suka koma cikin part din Fadila,Mama Tace muyi sauri mu bawa Yan Sandan Nan su ci su tafi muyi aikin mu Kar Abbi ya dawo ya Iske Bama gida,ai Momy suruka ta dauraye tukunya babba ta daura a Gas,su Khaleesat Ana ta yanke yanke Ana Taya Momy,Mama ta wanke nama ta Dora,Ita kuwa Fadila aikin kukan bakin ciki take Yi Kawai,Momy Tace maza ki dinga kuka Gaban Amarya ta Raina ki,Wai Amaryar Yar uban wace ce? a wanne gari take? Fadila Tace ban sani ba wlh ai Baki ga kayan daya zuba Mata ba masu tsada da gani kin San Yar manya ce.

Cikin lokaci kankani su Momy suka zabga Jollof Rice ta Sha nama da kayan Lambu,wata katuwar cooler Suka cika dam,Khaleesat da Faridah Suka dauka tare da kaiwa Yan Sanda a compound,Dariya ce ta Kama Yan Sanda Amma Suka Danne,Ogan ya dakawa Faridah tsawa yace ku shiga palon Amarya ku Kai musu,Haka Suka Shiga palon sai Suka ga Yan Kauye ne gaba Daya,abincin suka ajiye suna buga tsaki,Dangin Amarya suka ce Sannu Dangin Uwar gida mun gode da wannan tabbar da gani mun San Uwar gida zata rike Amanar Amarya,kafin su Rufe Baki sai ga Dangin miji Suma da nasu abincin da ruwa na roba tare da Lemuka na tarbar Baki,sai Guda sukeyi,Farida Tace muje muga wace Amaryar,Dakin Amarya suka shiga,Rabi tana hango su ta shararan mayafinta,ai Kara nannadewa tayi cikin Mayafin ta dukunkune kanta,Suka Yi iya yinsu Amma Rabi Taki yarda su ganta,sai da suka bari Dangin Ango sun taru da mugun yawa Su Kuma su Khaleesat sunki tafiya sai sunga kwaf,Lokacin Rabi ta zare mayafinta ta dage shi sama,Kanwar ango ta saki Guda tare da cewa Allah ya yarda Amaryarmu Yar Fulanin asali Alherin Allah ya Kai Miki babbar Aunty,Salati Khaleesat ta saki,Farida Tace Rabi ce Wai ko Ido nane?Rabi tana Yanga tare da yatsina fuska Tace Allah ya yarda Na Zama matar Saddeequ, Khaleesat Kamar ta zare haka ta fita da gudu lokacin Yan Sanda sun Gama aikinsu sun tafi, Khaleesat tana Haki Tace ku fito yaki za ayi wallahi yau yakin duniya za ayi na biyu Rabi ce Amarya,Fadila Tace me? Rabin Kauye wacce aka ce mun hada dangi da su,Rabin da Saddeeq ya yiwa Fyade ita ce Amarya,Fadila Faduwa tayi kasa a sume,Mama ta Yayyafa Mata ruwa ta farfado,Safna Tace ku zo muje mu hada Mata jini da majina,gaba Daya Suka fito Dan Abin kunya,Dangin miji Dana Amarya suna kallon ikon Allah,Momy ce ta cakumi Wuyan Rabi Amarya ta fesa Mata Maruka biyu,Kanwar Babar Rabi ta Mike tare da fincikar Momy Abinka da karfin mutan Kauye Kan Momy ta Kama tare da gwarata da jikin bango ta shake Mata wuya tana naushinta a ciki,Momy tana ta ihu,Mama ta Kama wata Cikin Dangin Ango Suka rukume da Kokawa Ana ta duro ashariya da zagi Iri iri, Safna Kuwa Saude kawar Amarya tayi kukan Kura ta damki Safna Suka dinga dukan juna,Khaleesat da Farida Suma Dangin Ango Suka kama,gaba Daya dakin casuwa akeyi ba me Jin Kira,Fadila tazo ta kwakushi Amarya suka fada Kan gado,Rabi ta sauka kasa ta daura gyalenta a kugu ta samu Fadila ta kwada ta da kasa,Cikin Dangin Ango  wata ta Kira Ango ta sanar masa abinda ke faruwa,shi kanshi ta waya Yana Jin Ihun Mata da Ashariya Ana ta danno ta,Yan Sanda ya turo gidan yace duk su tattara Dangin Fadila su kaisu station,Ai kuwa da Mata Yan Sanda aka zo,Suka dinga kallon abin mamaki,wasu rigar su ta yayyage,wasu ba Dan kwali wasu daurin ya karkace sun hada Zufa sai Haki sukeyi ko wacce taji jiki,Fuskar Momy duk Tasha yakushi raunuka a fuskata ko Ina,Mama kuma kunnenta Daya ya fashe,Farida an Mata kulu a goshi,Fadila Bakinta ya fashe,Safna Lebenta ya kumbura suntum, Khaleesat gefen kafarta ya fashe sabo da an bugata a jikin gadon Amarya,Dangin Ango ma wasu duk sunji rauni,Haka na Amarya ma,Yan Sanda Suka ce Ina Dangin Uwar gida Masu daraja? Su Momy sunyi zaton gaskiya za a Basu harda warewa gefe Daya Suka ce gamu,Yan Sanda Suka ce muje cikin tsawa Har Fadila aka tasa keyarsu,cikin mota aka jefa su suka tafi dasu station,Su Momy suna ta Fargaba da tsoron tsakaninsu da Abbi,Mama Tace Mun Shiga Uku ya zamuyi idan Abbi yaji? Safna Tace mafita Daya ce ku Kira Fu'ad shine kadai zai Rufa Mana asiri ba tare da Abbi ya sani ba ya fitar damu, Khaleesat Tace tab wallahi yanzu ya tsane mu babu Maganar wacce yake ji sai ta matarsa Rumaila ce kadai zata ce yayi kiga yayi Amma Indai ba ita ba wlh bazai Yi ba,Amma kuyi sauri ku kirashi kafin a kaimu sel,Mama Hannu na rawa ta latso number Fu'ad,Yan Sandan Basu kulasu ba sabo da sun San irin kudin Abbi a kasar shi yasa suke Takawa a Sannu.

Fu'ad yayi mamakin ganin Kiran Mama,lokacin Ina kwance a jikinsa a bedroom dina, Wayar ya daga tare da gai da Mama,sabo da yaji tausayinsu Mama ta fashe da kuka tana karantawa Fu'ad komai Bata boye Masa ba har auren Rabi, Fu'ad yayi mamakin Rabi Amma a ransa Allah ya Kara yayi Kuma shi Rabi ta birge shi wlh,ta nuna wayewa tunda ya Mata Fyade dama tunda da aure tsakaninsu ta kyauta ta yiwa kanta gata,a fili yace Gaskiya kunfi karfi na,abinda kuka Yi yafi karfi na,Kun San Ashe Ina da amfani a wajenku? Har Kuna da bakin neman Alfarma a wajena? Wacce kiyayya ce Baku nuna min ba,ba sharrin da Baku Yi min ba,nayi cikin shege kuka Bata min suna a wurin dangi da mutane,gulma babu wacce bakuyi ba,tarko ba Wanda Baku Dana min ba Ni da Umma sai yanzu Ashe Ina da amfani,Ni da nake Dan Iska lalatacce me Zan iya Yi muku,Dan Iska me zai Iya,ku yanzu Rabi da ita kuke fada? Rabi kawar gulmar ku,itace fa ke Nemo muku Gulma Kuna murna Kuna kaunarta,yanzu Dan ta auri Mijin Fadila ai sai kuyi murna tunda Kuna sonta,Bai kamata kuyiwa Rabin taku Haka ba,Sannan Mijin Fadila shi ya lalatata ya Mata Fyade Dan ya aure ta sai kuji haushi,Wato kin Fi so ya dinga lalata Yaran mutane akan yayi aure? Idan za a daure ku daurin Rai da Rai Ni Fu'ad bazan taba fitar da ku ba,ku nemi yayanku maza ai Kuna da su Kuma Allah ya Baku ko ku sanarwa mijinku Amma ba Ni ba,Mama Tace Dan Alla...kit Fu'ad ya datse wayarsa.

 Kallonsa Nayi Ina Wasa da sumarsa Jin Yan Uwansa ne ban ce komai ba,Kallo na yayi yace Baki tambayeni su waye ba?nace naji matsalar family ce me zai sa na shiga,okay nufinki Bamu Zama daya ba? Abinda ya shafeni Bai shafe ki ba? Ai ba a shiga tsakanin Yan Uwa,Cizo na yayi kadan a kunne na saki Kara,Yace kawarki Rabi tayi aure,Nace wow Haka bakatatan? Yace Mijin Fadila ta aure,Na kyalkyale da Dariya nace Alhmdllh Allah na gode maka Yan Iska marasa mutunci gwara da ta musu Haka,sunje sunyi dambe da Dangin Amarya an kwashe su zuwa police station,Mikewa Nayi na dinga taka rawa Ina kida da Baki na ganji...gan....ganji...gan.... Fu'ad Yana ta Dariya yace to muguwa,nace tashi da Allah ka kaini gidan bikin Nan daga Nan mu biya ta police station nayiwa su Momy jaje Allah kiyaye gaba, Fu'ad yace bazan je ba,nace Dan Allah ka tashi mu shirya,Rokonsa na dinga Yi yace to Amma idan mun dawo Sai nayi Second Round nace har Third ma ba damuwa.

Wanka Mukayi tare ya shiryawa Cikin wata Danyar shadda peach,Ni kuwa Lace nasha me tsadar gaske Milk and Brown,takalmina me tsini da jakata da Mayafi duka milk nayi kyau, harda saka Glass brown me shegen kyau na zuba kyau.

  Fu'ad Yana Bina da mayen kallo yace dole ki mallake Ni,shi yasa Duk abinda kika ce bana musu,nace gashi zaka kaini nayi gulma,idan ba ke ba wa ya Isa yasa naje gidan wata Rabi,Muna mota Muna Hira Yana Driving ya kaini gidan Rabi yace kiyi sauri 10mnt na Baki,shiga nayi Ina Taku dai dai,Me gadi ya nuna min bangaren Amarya,na shiga,su Saude sunyi mamakin ganina,sai wani Sannu da zuwa suke min,dama Dangin Amarya sun Sanni,kauyenmu Daya sai kallo na sukeyi sunga na Zama Hajiyar birni, gaisawa Mukayi Ina musu Allah Sanya Alkhairi,Naga wasu duk da rauni a fuskarsu,Dangin Ango kuwa Yan Birni tambaya sukeyi wannan Yar gidan wannne hamshaki ce Haka? Aka ce ai matar Fu'ad ce yayan Uwar gida,sai yabo na sukeyi Yan matan cewa suke kinyi kyau Ina cewa na gode,kowa cewa yake gaskiya tana da kyau Allah yayi Halitta,ga Miji kyau matar kyau za a ga Yara masu kyau,Rabi Algunguma harda rike Hannu na Tace Amaryar Fu'ad Ashe Zaki zo min?gani Kuma na furta Tace na gode Rumaila Dan Allah kiyi hakuri,Ido na kyafta Mata nace Yi Shuru Ni bana rike mutum,abinci aka kawo min Dangin Ango suna ta ji Dani Kamar sun Sanni,15mnt Fu'ad ya dinga Kiran wayana, Sallama na musu nace Oga Yana jira,Hajara ce ta rakoni da Saude,suna ta bani labarin fada Ina ta Shan Dariya har mota,Saude Tace Gaskiya na tausayawa Safna Kinga wata hambara da na Mata a makoshi saura kadan ta Suma Muna ta dariya,suna gaida Fu'ad muka Yi Sallama sai police station.

Saddeeq kuwa tuni ya sanarwa Abbi komai a waya, Fu’ad Abbi ya Kira yace Kar ya sake yayi Bail nasu ko uban waye yazo sai idan yazo da Kansa,Suna Sel a tare gaba dayansu sunyi jungum jungum, Fu’ad ya nemi Alfarma a barmu muje Kofar Sel din mu gansu muna daga waje suna daga ciki,Kamshin mu Suka ji Basu San waye ba da sauri Suka Mike suna ganin Fu’ad rike da Hannu na Momy Tace Alhmdllh Ni San Fu’ad me tausayi ne bazai Bamu kunya ba,Dan ma Yana tare da waccen shegiyar me bakar kafa anzo birni an waye shegiya sai kiba takeyi tana Kara kyau duk ta tsafe Fu’ad ko Ina zai je sai da ita,shima shashasha ne yaushe zai biyewa wannan Yar talakawan cewar Mama,Safna da karfi Tace to Yan Sanda Dan Ubanku sai kuzo ku fitar damu,Wani Dan Sanda yace zaku ci Ubanku Bari bakin su tafi,Khaleesat Tace Yan wahala matsiyata Kun San ko mu su waye Bari mu fita sai Mun sa an Kore ku a Aiki dan Me cin babarku ta furta da Muryar Yan jagaliya wai ita tsagera yanda tsageru ke yiwa yansanda idan an Kama su.

Muna karasawa Mama Tace Fu'ad Sannu da zuwa, Fu'ad har da rusunawa ya gaida su sabo da ya sa musu Rai,Ni kuwa cewa nayi Ashe Kuma Haka Abu ya faru? Kai Abu baiyi Dadi ba,yanzu Babyna ya kaini gidan bikin naji abinda ya faru,Bai kamata ba ai Allah Yana tare da masu Hakuri, Haba Fadila da hankalinki kina Uwar gida kin zubar da mutuncinki,Na nuna Momy nace ke Kuma gododo Uwar Fadila ace anyi doke doke da ke Haba Kamar zamanin jahiliyar farko,Haba Bai Dace ba Mama a dinga Aiki da hankali,Rabin ku ce fa,Yar Uwarki

U,me dakko muku rahoto,Rabi ta bangarenku,wlh Kun bani kunya Rabi da kuka ce Yar Kauye,Bata ishe ku kallo ba Yau shine ta tsone muku Ido har da jiwa juna rauni Haka akan Rabi Yar yarinya ta Kauye wacce Bata waye ba Yar talakawa,Ina birnin naku? Ina kudin da kuke takama da shi?me gulmar Rabi ta Kara muku?Baki suka Bude suna kallo na,Momy Tace Dan Ubanki da ke muka Yi ? Ina ruwanki munafuka,ki Bari muyi magana da Danmu, Fu’ad yace lallai bakuyi nadama ba,Baku Sha dauri me kyau ba,Ku tunanunku fitar daku zanyi? Ai Abbi ne ya turo Ni Nace lallai a Kara tsananta muku dauri,Sanda kuka yi nadama sai a fitar daku,kuka su Khaleesat Suka saki Tace wlh munyi nadama Dan Allah Yaya ka taimaka,Dariya nayi nace Sajan….Dan Sanda yazo da Sauri,kudi na zaro masu yawa a jakata,tunaninsu fitar da su za ayi har sun fara murna,Dan Sandan na mikawa nace duk wacce ta fada muku bakar magana ku tura Yar Sanda ta chasa ta,Jiki na rawa ya karba Yana cewa angama, Fu’ad yace Uwar gida ta Gama magana,da ace Rumaila Tace na fidda ku da wallahi yanzu zansa a fidda ku Kuma na Bawa Abbi Hakuri ya kyaleku Amma Tace a’a,muje ke ya juyo tare da rike Hannuna muka tafi,Ina Jin Khaleesat tana cewa Dan Allah Rumaila ko Albarkacin Wayar Dana koya muku Sanda kuka zo daga Kauye,ko kulata banyi ba musamman idan na tuna wulakancin da suka dinga min da zagi,da abinda Suka yiwa su Iya.

Sai washe gari sannan Dangin Amarya Suka koma Kauye lafiya,Dangin Ango ne Suka Kara gyara ko Ina na gidan sai dare suka tafi,10pm Ango ya shigo,bata ji wani dar ba sabo da ya rigada ya mata Fyade tun farko ta Gama Shan azabar ta,Kaji ya Bude Musu da kayan Sha,Rabi ta cikin Mayafinta sai kyallo Ido daya takeyi waje tana kallon kaji wani farin ciki ya kamata yau zata ci dadi Haka abinka da ba a saba ba,Mayafin ya cire Mata Yana kallon Amaryarsa cike da farin ciki da kauna,daukanta yayi ya zaunar da ita a carpet Suka sa Naman a tsakiya Rabi sai satar kallon Kaji takeyi ta Matsu ma ya fara Bata taji irinsu taga sai wani maiko sukeyi sun Sha Mai, Bismillah ya Furta Rabi tayi Bismillah Amma kunya ta hanata ci,shi ya ballo Cinya Guda da Kansa ya bawa Rabi a Baki ta kafa Mata hakora tare da yaga,tana ci wani Dadi taji har kwakwalwarta,Ya Bata na biyu tana ci Tace Wai Gurguwa ce Kazar? Yace ban Gane Gurguwa ba? Tace Kajin gidan gona Wanda ake kiwatawa na bature Wanda ake cewa  Brolas  zaka ga idan Suka girma da yawa kasa tafiya sukeyi sabo da kiba wasu har karyewa sukeyi sabo da kiba tasa sunyi nauyi da yawa ai su ake cewa Gurguwar kaza, Saddeeq Dariya ya dinga Yi yace lallai kinji dadin Kazar Nan harda Santi,Rabi tana boye fuska Tace ai Ni dai ba Santi nake Yi ba Allah,yace sabo da Allah Naga Abu a gashe Ina Zan tantance Gurguwa ce ko me kafa? Rabi Tace gaskiya ka tambayo min me gasawar Nan.
Suna ci Rabi Tace Nan gaba idan Allah ya hore maka Dan Allah ka Bude min wajen kiwon kaji gidan gona Ina so na dinga kiwatawa kaga mun huta idan zanyi Miya Watarana Kawai sai mu kamo daya na dannewa shegiya wuya na yankata mu jefa a Miya, Saddeeq Yana ta cin dariyar Santin Rabi yace to Princess za a bude Miki Inshaallah,Rabi Tace na gode Allah Kara budi Amma karka Bude min a garinmu Yan Uwa su yo min caaaa kowa yaji kwadayi yace Rabi Dan Allah Gurguwa Daya, Saddeeq yace to a Nan za a bude Gina miki kusa kusa Tace to.

Cike da nishadi Suka Gama ya Bata Yogourt tana Sha Tace an Dade Ana cutar mu Muna can kauye,Anya wannan da nonon Saniya akayi? Saddeeq yace Rabiat da bakya zuwa Nan garin ban San ya zakiyi ba ma,Dariya tayi Tace to ai abin ne Ni naka na musamman ne ko Dan Ni Amarya ce ne? Saddeeq yace ai sai abinda kike so Rabi kiyi ta Addua Allah yaci gaba da Buda Mana Zaki Zama Kamar kawarki kema Rumailan Fu'ad Rabi Tace to ai zanje na Bata Hakuri Watarana tunda ka min fadan Nan abinda nayi naji nasihar ka na canja Hali na, Saddeeq yace yawwa shi yasa kaddara ta fada Mana na Miki Fyade hakkin Rumaila ne zamu je tare Watarana ki Bata Hakuri,Rabi Tace to na gode Nima da kayi min nasiha,duk abinda kaga nayi ba daidai ba ka dinga sani a Hanya kaji yace to Rabina,Wanka tayi sosai da Brush,Ta sa kayan baccin da Kanwar ango ta zabo Mata gaba Daya tsirara take,Rabi kunya tasa taki dawowa dakin Saddeeq,sai da ya gaji yaje ya riko Hannunta ya dawo da ita dakinsa Dake part dinta,Hijab da zani ta daura ya jasu Sallah Suka idar tare da adduoi,Sannan ya dauki Rabi Kamar tsinke yayi saman Bed da ita,yace ya naji kinyi Shuru gimbiyata? Rabi Tace tausayin kaina nakeji,murmushi yayi yace Haba a hankali Zan bi Dake,Rabi Tace to Ni lashe lashen Nan naka ne yake tsuma Ni,Rumaila Tace Wai kace wa Fadila Bata lasar maka kunne? Saddeeq ya dinga dariya kamar me, yace wannan Rumaila kwai Yar tsegumi a Ina taji? Bari kiji me nake nufi,Nan ya fara Wasa da Harshensa a cikin kunnen Rabi salo salo,Rabi Tace wayyo naji hankali na zai gudu wayyoo....kamar ana shawagi Dani a sararin samaniya....Idonta yayi luuuuu ya lumshe Rabi Tace ko Azara'ilu ya Hauro katuwar katangar Nan takane? Saddeeq ko jinta bayayi,Rabi ya zarewa kayanta,Yace duk abinda nake Miki kiyi min kinji? Rabi Tace yo Kai kana da nonon da Zan taba maka  ne? Ni kana ta shashafe Nawa Kai baka da shi wannan ai cin zali ne sabo da Allah fa, Saddeeq ko Bai so Bai San Sanda yake kwasar Dariya ba,yace ae naji kiyi min Haka,Rabi ta kumbura Baki Tace Allah Ni bazan taba fata ba,Ni Nawa ai me laushi ne da girma Kai fa,Kissing din Rabi Yake Yi sosai.

Rabi tun Bata tayashi Tace Kai kaji Abu Ina raina shi Ashe Dadi ake ji,Bata ma San ta fara Taya Angon nata ba,Tace  kace nayi duk abinda kake min na maka Irinsa ko? Muryar Saddeeq na rawa Yace Yeah,Rabi Tace ya naji muryarka Kamar an kunna tsohuwar Radio Tasha tana gocewa? Ni ko baka da lafiya, yace please touch me, Yana nuna Mata abinda zata Masa, tun Ana kunya aka nemeta aka rasa tana Masa duk abinda yace, Saddeeq yaji Amaryarsa ba irin Fadila ba wacce Bata bin Umarninsa ko kadan,shi sai yau ma yasan yayi aure,ji yake Kamar Bai taba saduwa da mace ba sai yau,a ransa yace Wannan itace mace,Yanzu nasan nayi aure dole na faranta Miki Rai Rabi,duk abinda kike so shi za ayi,A fili kuwa kalaman kauna yake furtawa Rabi,Ina sonki matata...ahh....Rabi Ana Nishin Dadi Tace Nima Haka Hubby na,Oh Rabi da Hubby Hh,Sai da yace My princess kin Amince nayi Burin Raina? Rabi Tace a baya na Haram ka  min ta karfi sai yanzu da nake Halak Dinka cika aikinka na huta,Haka Kawai na hanaka gobe ka fara gaba Dani Yi abinka Zan jure.
Murmushi Saddeeq yake Yana ci gaba da Sarrafa Rabi ya shigeta a hankali cikin nutsuwa,a hankali yake binta,Rabi ta Sha wahala kasancewarsa Yana da aure ya Saba baya gajiya da wuri,Rabi taji kukan dadi salo salo,tace Babba da Kai Kayi ta kuka da Nishi Haka? Ni ban taba jin irin wannan ba ko dai Aljanu ne kaima da Kai wannan abin bana lafiya bane, Saddeeq baya hayyacinsa Sai da tayi Hawaye sabo da Bata Saba ba itama duk kuwa da ya taba sau Daya.
Sai da ya samu nutsuwa,sannan da Kansa ya hada ruwan zafi yasa Rabi,Ihu ta saki Tace Wai Ni Haihuwa nayi ne? Sai kace wata mejego,dagewa yayi tare da yiwa Rabi komai har wanka sannan suka kwanta ya makaleta a kirjinsa,Gashi Saddeeq matashi ne kyakyawa Wankan Tarwada gashi Dan kwalisa da daukan wanka kullum cikin kamshi,ga Iya love,ta ko Ina Sadeeq bashi da makusa Rabi anyi Dace,Sai Shagwaba Rabi yakeyi Wai ya Mata da zafi shi Kuma sai lallashi yake faman Yi ji yake kamar ya hadiye Rabi ya Huta,Bai taba son mace kamar Rabi ba a duniya,Rabi a ranta Tace zaka ga daru da rigimata kuwa Nima na samu Rana sai shanya,Fadila Sorrynki Kawai.

Ni kuwa Bayan mun dawo Iya na Kira tare da fesa Mata labari,Iya Tace matsiyata Inshaallah bazai fitar da su ba sai sun ji jiki,Iya Tace ke jibi Zan tafi kauyenmu fa,nace Haba Iya Dan Allah ki zauna Mana sai Nan gaba,Iya Tace a gidan surukai Dan Rashin kunya, Fu'ad ne ya kwace wayar yace Dan Allah Iyanmu karki tafi,Iya Dan Wai ta kawo Hujja a barta ta tafi sai Tace Dan Nan na shanya kubewa da Daddawa a saman Rumfa Kar ayi Ruwan sama su lalace,Dariya Fu'ad ya dinga Yi yace Iya Wannan Hujjar Taki ba Hujja bace kwananki Nawa a Nan idan Ruwa za ayi ai yanzu Kam ya hada harda farantin shanyar Taki ya tafi dasu,Ki Bari gobe zamuzo da Fadila muje yawo,Iya Tace da Jiniya zamuje? Fu'ad yace ae,To yanzu Naga wurin Zama na soke tafiyar sai wani satin me zuwa cewar Iya,Muna ta Dariya,Iya Tace jibi Kuma a gidanka Zan yini Fu'ad ku hada min shayina me kauri komai Rana Ni Kun Gama birgeni,Indai zanzo waje ko da Yamma ko da Rana Ana bani shayi an Gama birgeni, Fu'ad yace Madara Iya Guda za zuba Miki,Iya tace yawwa da Breadi me kwakwa, Fu'ad yace to,Kafin na tafi Kuma kuyi min sakwara me laushi da Miyar agushi (Egusi) naci na koshi, Fu'ad yace karki damu Iya,sai me? Iya Tace ayi min farfesun zabo,Da me? Tace anjima Kuma ka kawo min gasashiyar hantar Nan da ka siyo min Rannan, Fu'ad yace to Iya anjima zanzo na kawo Tace Ina jiranka ka Hado min da Madara L&Z yace to,Muna ta dariyar Iya.

Iyata sabo da samun canji ta Kara haske da kina tayi wani kyau Abinta,A Daren Fu’ad ya kaiwa Iya da Kansa ta dinga godiya,ya kaiwa Umma da Abbi nasu suma,muma ya siyo Mana namu hantar Muka wargaje dadin mu.

 Angon Rabi Kawai Amarci suke kwasa,Rabi Sai abinda take so,da safe ma kanwarsa ce ta kawo musu Breakfast,Rabi ta tsala kwalliya cikin atamfa super ta lefenta,Kanwar Saddeeq ta rike Tace baza ta tafi yanzu ba,Kanwar Saddeeq Zainab Tace Allahu Akbar yanzu muka San Dan Uwan mu ya Kara aure,Fadila ranar Dana kawo Mata abincin farko tsawa ta daka min tare da korata da abincin gida Tace kuje can kuci abincinku Ni ban cin irin wannan ko a gidan Ubana nafi karfinsa,da gani ko Dadi bazai Yi ba,nace Maman Saddeeq fa maman mu ita ta dafa Tace maman fa Taku ai ba Uwata bace ko,Haka na fita na tafi Ina Hawaye,Mama Tace na kyaleta,Rabi Kan Zainab ta dafa,Zainab ta girmi Rabi tayi biyun Rabi a girma Amma Rabi ta dafa kanta Tace na tabaki da Alheria Zainabubu Kanwar mu,Allah ya kawo wacce zata share muku Hawaye wacce zata sharewa Dan Uwanku Hawaye,Ku bini a Sannu Rabi ta furta tare da mikawa Zainab Hannu Suka wani tafa,Zainab sai Dariya takeyi itama,Tace Rabi kinyi a rayuwa Allah ya bada zaman lafiya,Rabi Tace Ameen Zee ta Abuja Birnin tarayya Nima gani nazo zamu Tara tare. 
Sadeeq yazo tare da Zainab suka karya suna ta Hira,Rabi tace Sai Watarana zamuje wajen Kawata Rumaila kiji wacce ta fini abin Dariya sosai,Zainab Tace Allah ya kaimu, kafin ta tafi gida ta bar Rabi da Angonta.

Masu Sharhi Ina godiya,aci gaba da gashi.

AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

       NA KUDI NE

WACCE TA FITAR DA SHI DA WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA BAN YAFE BA.

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.

          101-105

Official

By
AsmaBaffa.

Page naku ne

Aynah
Alhusnah (Mrs Idris)

     Fu'ad sabo da gudun surutun mutane ace Abbinsu ya kulle matansa da yaransa ya tambayeni shawara Bayan mun dawo gida Muna kitchen tare Yana tayani girki yace Baby ya kike gani idan nace a saki su Momy? Rumaila murmushi nayi nace da ka kyauta kuwa Bai kamata a barsu ba ko ba komai akwai yaran Abbi a ciki,Sun bani tausayi wlh Kawai a tura musu aniyarsu a sake su,Murmushi Fu'ad ya saki tare da Jan Hanci na kadan yace Amma dazu kika musu tsiya? Ai Kawai Dan na Dan rama nayi musu Amma sun bani tausayi ko ba komai Iyayen Mijina ne da kannen Mijina Bai Dace na musu hakan ba sai dai zuciya da Bata da Kashi da Kuma irin abinda Suka min na rashin kauna,Basu taba kaunata ba Amma Kawai ka fitar da su Dan Allah suje da Halinsu,Aniyarsu ta bisu Kawai,Murmushi Fu'ad yayi yace to sai gobe Inshaallah sai muje a fitar da su,Allah ya kaimu na furta.

Washe gari misalin Sha Daya na Rana muka dau wanka zuwa police station kudi Fu'ad ya biya aka fitar dasu,kafin a Bari su tafi sai da suka Sha masifa wurin Yan Sanda suka musu kaca kaca,tunda Suka ganni tare da Fu'ad Suka dinga Harara ta suna min kallon banza,ban kulasu Ba Fu'ad ya Kira Driver ya ce ya maida su gida,Momy tazo wucewa ta Bangajeni saura kadan na fada Kan wani table, Fu'ad ya rike Ni da Sauri,su Khaleesat kuwa Tsaki Suka ja min sannan suka Yi gaba, Fu'ad ya kalleni yace ke kika ce a fitar da su,Shuru Kawai nayi ya ja Hannuna Muka nufi gidan Abbi sabo da Fu'ad ya bawa Abbi hakuri a kyalesu Shine Abbi yace duk muzo gida Yana son ganin mu har Rabi da Mijinsu Saddeeq,Mun Iske kowa ya Hallara har su Momy da mazan gidan Baki daya,Yan aiki ne kawai babu,Abbi ransa a bace ya fara magana cikin kakkausar murya yace Momy da Mama ku tashi ku tattara naku ya naku ku bar min gidana,Ko waccenku ta tafi gidan Ubanta sai na neme ku,Ku Kuma duk Yan matan Nan ko wacce na Bata sati Uku wallahi duk wacce Bata fito da Miji ba daga Nan zuwa sati uku to sai na aura Mata duk Wanda Naga dama,ruwanku ne ku kawo Wanda kuke so ruwanku ku barshi Nan da wata daya sai na Daura muku aure,na gaji da Dabbaccin da kuke min a gida,me na rage ku dashi? Ilimi Allah ya gani ba Wanda ban Baku ba Amma kun biyewa Iyayenku Kuna hauka,Ku fada min Iyayenku ba kishiyoyi bane? Har sa Rai kuke Yi Zaku zauna  ku Daya ba kishiya idan kun yi aure,ai ku abin a muku Dariya ne ma,abin kunya ne Kuma ace Wai Kuna gudun kishiya har zaku je ku tayar da tarzoma,abin kunya harda Uwar 'ya Ana kokawa tir da Hali irin na Iyayenku,Rabi Sanda Mijin Fadila ya Mata Fyade Baku damu ba gwara mijinku ya dinga Zina akan yayi auren Sunna ko? Ko Ita Rabi ba 'ya bace? Rabi an samu Baki Tace da Uwata da ubana Kuma suna Raye cikakkiyar 'ya ce ba marainiya ba,Abbi yace rufe min Baki Kema Yar Iskar ce ai,ba tare kuka dinga gulmace gulmace ba? Ko tunanunku ban sani ba? Sai ku Rungumi Kaddara Fadila da ke Ku zauna Yan Uwa abokan gulma,idan kunga dama karku zauna lafiya har Mahdi ya bayyana,Fadila idan Zaki Rungumi kaddara ki zauna da mijinki lafiya kinyiwa kanki gata,idan kin Bari ya sake ki sai dai ki koma Dangin Uwarki ki zauna ba dai gidana ba,Kuma wallahi bazan dauki auren jeka ka dawo ba dukkan ku duk wacce tayi yaji daga gidan Miji to ba gidana ba,Rumaila Kuma matar Dan Uwanku ne ko ku so ta ko ku kita Allah ya rigada ya hada ba yanda zaku yi da ita.

Abbi ne ya Kalli Saddeeq yace Kai Kuma matsalarka Daya da ka Iya yiwa yarinya Fyade baka kyauta ba,wallahi badan ka aureta ba na so na bi Mata hakkinta sai kayi ta Istigifari,Rabi tayi sauri Tace ya Gane gaskiya Abbi Kuma yayi nadama Kuma gashi ya aureni Muna zaman mu lafiya wallahi Dan Allah karka kaishi kotun Musulunci ya Sha Bulala Tamanin wahala ta sameni ta jinyar Miji,Abbi yace ai ba Iya Bulala bace Yana da aure hukuncin kisa za a Masa ta hanyar jefewa,Rabi ta fashe da kuka Tace Dan Allah Abbi karka Bari na dawo bazawara,Abbi yace Kai Saddeeq kaji tsoron Allah kayi kokarin Adalci a tsakaninsu Banda fifiko, Inshaallah Saddeeq ya furta Yana Jin kunyar Kansa abinda ya aikatawa Rabi Yana me Nadama,Tsawa Abbi ya bugawa Momy da Mama yace ku bar min gida na nace muku ko,Suka Mike ba shiri su Islam suna ta bada Hakuri Abbi yace wallahi sai sun tafi,Ana ji ana gani Suka bar gidan da manyan akwatuna sai Hawaye suke zubarwa,Nasiha Abbi yayi sosai Amma su Khaleesat akan an Kori Iyayensu sai fushi sukeyi suna Hararar Rabi,sai Kuma su Harare Ni Nima Ina kallonsu Har Abbi ya sallame mu,Fadila Kamar zata fashe Haka ta fito tare da bangaje Rabi ta fice Kofar gida Wai baza ta Shiga Motar Mijinta ba Matukar Rabi tana ciki,Rabi Baki ta tabe ta shige gidan Gaba suka Yi tafiyarsu da Angonta,Fadila Taxi ta shiga ta koma gidan Saddeeq,Ni da Fu'ad part din Umma muka koma tare da Aunty Samha sai dare muka bar gidan,a wajen Umma muka ci Dinner sannan Muka wuce gida.

Muna Hanya yau ba shi ke Driving ba Driver ne Muna gidan baya tunda Naga Yana ta wani mammane min a jikina Yana faman rirrike min yatsu nasan Abinda ya ke nufi,Yau she Zan koma School kaga fa ka koma Office Nima ya kamata ka mai da ni,ga Islamiyya ma gaba Daya bana zuwa,Yana min wani irin kallo na musamman yace Ina sane Zaki koma Amma Islamiyya kin koma Saturday Sunday 8am to 11am ya Isa,Ba ta Yamma Zan na zuwa ba idan na dawo daga Boko? Kai ya girgiza cike da Izzarsa yace auren naki Kuma fa shike Nan kullum kina school Morning and Evening kin dawo kin gaji ga Assignment da karatu Ni Baki da lokaci na kenan? Zan samu lokacinka Mana dole,a'a Ni ban yarda ba Islamiyyar ma ta kusa da gidan Zan saka ki ta matan Aure Saturday Sunday 8-11am,idan matsalata ta dawo Dani gida nazo na daukeki a makarantar,Dariya ya bani Kawai, yace Zaki Dariya da Hujja ne,Muna komawa gida shigar mu Palo ke da wuya ya daukeni cak muka Haura Sama Bedroom dinsa,A gadon ya kwantar Dani babu Bata lokaci ya Shiga zare min kayan jikina,Nace Wai me zaka Yi ka Bari sai anjima, Hararar Wasa ya watsa min,yace idan Ina Yi ki barni naji Dadi na Ni kadai karki min Ihu,Ina Dariya nace Ni dama ba Wani ihu nakeyi ba,to zamu gani ya furta Yana Mai Shafar Albarkatun Kirjina,Yace Wai me kike Basu ne kullum suke Kara girma? Haka kake cewa kullum Wai sun Kara girma,Wani Abu ya tuna yace au na tuna kitchen ya wuce sai ga shi da wani magani a robar me Kama da faro,yace me kika ga an rubuta? Karantawa nayi Naga an Rubuta...... Charkwai matsagwai Don Jin dadin Jima'i,mace ko Namiji zasu Iya Sha Rabin Robar kafin Saduwa,za aji Dadi na musamman za Kuma a Dade Ana Yi ba tare da an gaji ba.
 Dariya nayi nace waye ya baka? a kunne ya rada min yace a fridge din Abbi na gani na sato,Dariya muka dinga Yi nace ba ruwana wlh,Ke dalla mu shanye muji idan munji yayi sai na siyo Mana,Kinga an Rubuta Ingantaccen maganin gargajiya,ba cuta ba cutarwa,anyi shi da 'yayan zogale da Sinadarin Ayu.
Robar ya Bude ya shanye Rabi,ya bani Nima nayi Bismillah na shanye ragowar Rabin,Yace ance a jira Nan da 10mnt zai fara Aiki,Wanka muka shiga zamuyi kafin magani ya fara Aiki,Ko minti biyar banyi ba Muna Bayi Muna wanka jikinmu duk kumfa,Cinyoyina na fara tsukewa Ina dunkulewa Kamar me Jin sanyi,yace Mene Haka ke ki tashi,Idona ne ya canja ya koma ja,wani sha'awa nakeji ta gaske,Idona ya kalla yace kuka Kuma zakiyi ko Sabulu ne ya Shiga? Nace Ni dai ka karasa min wankan Nan mu tafi Kawai Malam, Fu'ad ya dinga dariya yace a'a mu a hankali zamuyi wankan mu,Shower na Danna da sauri na rike na karasa wanka na tas na Daura Towel nace sai ka fito, Fu'ad Dan mugunta sai yaki Fitowa har nayi Shirin bacci na Shuru,Kofar Toilet din na shiga bugawa,yace Mene Wai? Ka fito Mana Haka kamar me Haihuwa ni zanyi bacci na,Yace kiyi baccinki idan nazo na tashe ki,Toilet din na Bude tare da bankawa ciki,sanye na ganshi da rigar wanka abinsa a jikin mudubi Yana ta kallon fuskarsa Yana wani gyara Dan gemunsa da sajensa,Wani Haushin sa naji Kamar na Naushe shi,Nace kazo mu tafi Dan Darajar Allah Nifa na gaji,Yace Wai na rikeki ne Baby kije Ni Aiki Zan rage Miki Zan wanke Miki Toilet ne, Baki na Bude Ina kallonsa bashi da Niyyar Fitowa harda daukan Blitch Detergent,Da sauri na fisge na mayar na ajiye nace muje kwanciya zamu Yi,bacci zanyi Kuma idan nayi bacci karka tashe Ni,yace na yarda je kiyi baccinki bazan tashe ki ba,Kuka na saki nayi waje Ina Bubbuga kafafu kamar Yarinyar yaye.

 Fitowa yayi yace na fito to,Towel din na fisge na maida shi toilet nace kwanta to,yace Haka Zan kwanta ba kaya? Nace ae  Haka nake nufi,Kin kwanciya yayi,Naja da baya can nesa na taho da gudu Iya karfina na tura shi saman Bed,ai kuwa ya fada Yana ta min dariya,yace kece kullum kike cewa ke babu dadi bakya Jin komai ki ta min Yanga Ashe da ciwo?
Na gane kuskurena dama karya nakeyi tunda na Saba Ina Jin dadi ai kaima ka sani tunda kaga yanda nake Ihun Dadi,to cewa kikeyi Ihun wahala ne,da sauri nace wallahi karya nakeyi na Dadi ne Kuma daga yau na daina pretending.

  Tun kafin ya fara tabani yau nice Ogar aikin Ni nayi komai ya karasa aikinsa,Gaskiya maganin Nan yayi,munji Dadi na musamman gashi Kuma mun Dade sosai sai da Mukayi Style sunfi Uku,gaskiya wannan Rana baza mu mantata ba,Daren kaf sai da muka kare shi a jiyar da juna Dadi.
 Fadila kuwa tunda ta koma gidan Bata kula Mijin nasu ba,Haka ya Kira Rabi tazo part din Fadila tunda itace Babba,Nasiha da fada ya musu sosai,Rabi Tace Inshaallah zanyi Aiki da abinda kace,Ita kuwa Fadila Tsaki ta ja tare da Mikewa ta wuce bedroom dinta,Bayan an Gama yiwa Rabi kwanakinta ya koma bangaren Fadila,tunda ya koma Fadila gaba takeyi da shi ko magana Bata Masa ba,yayi Maganar duniya Taki amsawa,dakinsa dake part dinta Bata je ba,Kuma abinci sai dai ya fita Restaurant ya ci,gaba daya Sadeeq a cikin kunci da tashin hankali yake,ya Matsu kwana biyun Fadila ya Kare ya koma wajen Rabi,Rabi kuwa Sai dai ta gyara sashenta ta dafa abinda take so ta ci ta koshi ta tsala kwalliya,idan Dangin Saddeeq sunzo Wajenta suke zuwa suyi abinda suke so su Kuma Sha Hira da Wasa da dariya ga karramawa.

 A waya Rabi ta kirani ta bani Hakuri Akan duk abinda ta Yi min nace na yafe ba komai,Haka idan Abu ya wuce Mata duhu tana kirana a waya ta tambayeni na Wayar Mata da Kai,Saude ma a waya ta bani Hakuri sannan ta fada min an sa bikinta,Ita kuwa Hajara saura ma sati uku bikinta,a waya ta tura Mana anko,Ina nunawa Fu'ad yace duk abinda nake so ga kudi Nan nasan inda yake ajiyewa na eba nayi,Ni Kuma hakan Daya bani dama Bai sa na dinga Masa barna ba,Kuma bana taba Masa ko sisi sai da saninsa duk da kuwa ya bani damar hakan,Iya kuwa sau Uku Fu'ad ya sake fita da Iya yawo ta zaga gari Ana musu Jiniya,a Nan ya sa aka Mata International passport sabo da tafiyarsu da zasu Yi zuwa kasa me tsarki,Sai da Iya ta damu ita lallai gida zata koma sannan aka Mata Sha Tara ta arziki Driver ya maida ta har kauyenmu gidanta,Iya ta Kara kyau tayi kiba sosai.

 Iya Bata Dade da komawa ba kawarta Wacce ta kaita gidan Sanata suyi aikin share share ta kawo wa Iya Ziyara,Tace Iyan Rumaila naji abin Alherin Daya sameki Kinga yanda kika Kara haske da kiba kuwa gaskiya kinyi auren yarki da kafar dama,Iya Tace Allah ya nufa,gashi Nan da wata Uku zamu keta Hazo zuwa Saudi Allah ya Kira mu mun amsa,Kawar Iya tace Iyye gaskiya Ina murna,Dama akwai abinda ya kawo Ni wajenki Iya,Iya Tace Ina jinki,Dama Baban Sanatan Nan da muke Aiki a gidansa shine matarsa ta Rasu Kuma ita kadai ce matarsa ita ce Uwar yayansa ciki harda me girma Sanata,To kin San mutuncin mutum Aure,In fada Miki tun watan jiya Sanata ya dinga neman Ina za a ganki,nace ai ke kawata ce shine yace nazo na tambayeki idan Zaki Auri Babansa,Iya Tace Tsohon Zan Aura? Haka Kawai Ina zamana lafiya a jawo min takaba da wuri,Kawar Iya Tace ke fa ba tsoho bane,shi kanshi Sanatan yaro ne kwanan Nan ya cika shekaru 40, Kuma irin auren wuri ne,kin San irin auren da Iyayen da keyi da kadan suke girmar yaransu na farko ke kin sani,Wlh Baban Sanata baifi shekara Hamsim da wasu Yan haya haya ba,idan kika ganshi Zaki Rantse yayan Sanata ne, shi yace Kawai Bai son Zama ba mace,Aure shine cikar mutum,Hakan tana faruwa Sanata ya dinga nemanki ko Zaki Auri Babansa,Kuma wallahi Iya Baban me kudi ne na gaske Attajiri ne gadon kudi ne, shi kanshi Sanatan kudinsu ne yasa aka tsaida shi takara,Kuma Baban Sanatan ko yaushe Yana kasar waje idan kika ci sa'a ma da ke zai dinga keta Hazo,Iya kiyi tunani Alheri ke Kwankwasa Miki kofa,Kuma Baban Sanatan zaiyi sa'an Baban Rumaila shekarunsu zai kusa zuwa Daya,Iya Tace Ahhhh wannan Mijin aure ne,wannan abin a aure shi ne,Ya Gama cika sharudan aure,a Ina zamu zauna idan anyi auren? A cikin Kano GRA,Iya Tace na Amince kawai,Kawar Iya ta rangada Guda Tace nasan baza ki ba Dani ba ta wajena sai dai kiyi shawara da danginki da Kuma yaranki,Kar su Rumaila suce Basu yarda ba,Iya Tace sunci Ubansu gaba Dayan su,ko da Basu hanani ba sai yanzu su din banza,Iya Haruna Danuwanki fa zai yarda? Uba na ne shi? Harunan me, Nan take Iya ta jawo waya ta dinga Kiran yaranta ta fada musu,fatan Alheri Suka Mata sun San ko sun hanata baza ta yarda ba ubansu zata ci.
Rumaila ni ta Kira a karshe,Iya Tace ke Rumaila Kafin na tafi kasa me tsarki Inshaallah zanyi aure na samu Mijin Aure,nace Haba Iya Ni Wallahi ban yarda ba,Iya Tace ke din banza Rumaila ke wacece Dan jakar Ubanki? Karki yarda Din,Kuka na saki Fu'ad Yana kwance a cinyata,sai da na Gama Wayar Ina share Hawaye nace Wai kaji Iya ce zata Kara aure, Fu'ad yace to sai me? Ni gaskiya ka buga waya ka Mata nasiha, Fu'ad yace ba ruwana tsakanina da Iya da kunya,surukata ce mene Nawa ciki idan ba so kike Iya taci Ubana ba,kina ji dai Tace kudinta zata Nema na kanta Kar mu dinga taimaka Mata tana Mana biyayyar dole,ai Kai tana Jin maganarka idan ka Mata zata hakura da auren na furta da Shagwaba, Fu'ad yace Sunnar Ma'aiki Zan Hana? Ba ruwana Iya tayi aurenta Allah ya bada lada sannan Addua zamu Yi mata Allah yasa wannan shine auren Iya na karshe har Abada baza ta fito ba,Kansa Dake saman cinyata na goce ya sauka a saman kujera na tashi Fuuuuu Ina kuka nayi cikin Bedroom,Dariya Fu'ad yayi yace Zaki zo ki sameni,Ni kika jefarwa da Kai ko? Ina daga daki nace ae din an jefar.

 Sanata da kawar Iya da wasu Manyan Dattijai su suka Yi bincike akan Iya,Itama Iya da kanta tayi bincike ta hanyar kawarta,Iya Tace farko a fada min cutar da matarsa tayi ta mutu,akace ciwon zuciya Iya Tace Alhmdllh tunda ba kanjamau bace,a hakan ma Iya sai da tayi Test na aure a asibiti shima Tace sai yayi,Sai da ta tabbatar lafiya sannan Tace wani Mummunan halinsa Bai dameni ba Ni Zan gyara Masa Zama idan na Aure shi,Daga Baya yazo zance wajen Iya,shi dai tunda yaga Iya ya Yaba,halin Iya ya birge shi ga sa Nishadi yayi ta cin Dariya,Sanata ma yazo har gidan Iya,yayi mamakin canjawar Iya ya ganta wannan lokacin a nutse,Iya ta kalli Sanata tace Hausawa na cewa dole ace da Mijin Iya Baba yanzu Sanata ka koma dole kace da Matar Baba Iya,Sanata yayi ta Dariya, Iya sai kyauta take Sha,Dake manya ne sati daya sai Iya ce ta bugo waya Tace an daura Aure,Har Abbi ya Mata Murna da su Umma,Ni kuwa bana son zancen,Ranar da Iya zata tare harda Umma aka raka Iya Kano wani katafaren gida na gaske sai Yan aiki ko Ina,Iya ta dinga mamakin lamarin Allah,Haka Muka Bi Flight washe gari zuwa gidan Iya har Fu'ad,su Aunty Rukayya mun Sha mamakin ganin gidan da Mijin Iya ga kudi sai ka ganshi da kuruciya sabo da Naira ta ratsa shi, Ashe Babban Director ne a maaikatar lafiya ta tarayya, Ya dinga Jan mu da Hira da barkwanci kamar dama ya San mu,tun daga wannan Rana na daina Adawa da Auren Iya,Kuma Yana kiran mu a waya mu gaisa,Haka duk Yaran Iya manya marasa karfi sai da ya Basu jari me tsoka,Sanata Kuma Wai duk zai kaisu kasa me tsarki suma.

  Bikin Hajara da yazo munsha wanka da kyar Fu'ad ya Bari nayi kwana daya,Ana Gama biki Iro ya tafi da abarsa Lagos inda yake Aiki,yanzu sai bikin Saude Muka sa a gaba,lokacin Kuma tuni Fu'ad ya maida Ni school Kamar yanda yace Haka, Islamiyyar matan Aure Saturday Sunday,sai ta Boko Kuma kullum,Sannan yanzu Yana ta koya min mota da Kansa,Ita kuwa Rabi an sata Itama a makaranta me hade da Islamiyya idan ta tafi tun safe sai Wurin Magriba take dawowa,Muna zaman mu lafiya hankali kwance cike da so da kaunar juna,Fadila ce dai Taki hakura har yanzu gaba take da mijinta anyi fadan har an gaji an zuba Mata ido Yana ta Amarcinsa da Rabi ko ta kanta baya bi ya gaji da lallashi,Su Khaleesat kuwa sunga Lallai Abbi da gaske auren dole zai musu har Naila dole a cikin masoyansu suka fitar da mazajen aure,Haka mazan ma Islam da Abdulhakeem tare za a hada duk a musu aure dama suna da matansu a Hannu, Fu'ad Kam cikin frnds Dinsa Guda biyu Khaleed da Ahmad sunyi aure ansha Shagali Muna gaisawa da matansu sosai mun Zama kawaye.

Ranar Monday kotu ta Aiko wa da Abbi takadda Akan anyi kararsa kotu yazo kotu da gaggawa Ranar Laraba,Haka Abbi dai ya sanar da Umma da Fu'ad tare da Sauran yaransa Momy da Mama ne suka Kai kararsa kotu,ranar Laraba gaba dayanmu muka Halacci kotu,a can Muka Iske Mama da Momy tare da Baba Jummai tana cikinsu dama abokiyar munafuncinsu ce itama,Baba Jummai Harara ta galla min Dan Kawai tana sha'awar Fu'ad Dina shike Nan ta tsaneni itama sabo da baza ta samu abida take so ba.

Ina matukar Baku Hakuri fans na rashin posting kwana biyu,Abu ne ya taso ba shiri.

Masu Sharhi da nemana don suji ko lafiya Ina godiya Allah ya bar kauna.

AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

      NA KUDI NE 

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

           106-110

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

Hajja Maryam
Aisha
Zainab Sabo
Nafee

      Alkali ne ya karanto Kara,Momy da Mama sune Wanda suka shigar da Kara cewa Kai Mijinsu ka ci zarafinsu ka musu dukan kawo wuka a Gaban yayansu,Alkali ya karanci ma Family Issue ne sai yace Kawai wannan karar a barta ku sameni a Office,Abbi,Momy da Mama da ni, Fu'ad da Fadila mune muka Shiga Office,Alkali yace su Mama kuji tsoran Allah ku Fadi gaskiya,Momy tace ai wallahi a Gaban yaranmu yayi Mana dukan tsiya ko Qur'ani aka kawo Zan dafa,Abbi yayi mamakin karyarsu Wato su babu nadama ma har da tozartashi su kaishi Kara Bayan shi suka yiwa laifi, Alkali ya kalli Abbi yace Alhaji ka dubu Girman Allah ka fada Mana gaskiya,wannan matsalar ba matsala ce wacce za ayi tozarci ba shi yasa nace Kawai kuzo muyi masalaha a Office,Abbi duk abinda ya faru ya kwashe tare da sanarwa Alkali Kuma Alkali ya gamsu,ya kalli Momy yace Amma ku dai mutanen banza ne,maimakon kuyi nadama ku bada Hakuri ku gyara halinku shine ma kuka kawo Kara kotu wannan kauna ce? Ya nuna Mijin naku ma baida daraja a idonku tunda har kuka kasa Hakuri har ya maida ku dakinku shine ma kuka kawo Kara,Wannan har ya Kai a kawo Kara kotu,Nan Alkali ya bude wuta ya dinga cin Uban su Momy karshe ya koma ja musu Aya da Hadisi Yana musu Nasiha,Amma ko a jikinsu sai Ma Momy cewa tayi mu fa Hakkin mu muka zo a bi Mana idan Kuma baza a bi Mana hakkin mu ba zamu daukaka Kara daga Nan har kotun koli.

Alkali yace ke ki Iya bakinki ba a ja da hukuma,Ko dai Yawu ne a kwalkwalwarki ba a sani ba? Sai da Alkali ya Bamu Dariya Wai Yawu ne a kwakwalwar Momy,Baba Jummai tana kusa ta Kwankwasa kofa akace waye? Baba Jummai Tace sheda Zan bayar Nima,Alkali yace shugo ke wace? Tace me Aiki ce a gidan Alhaji,Baba Jummai ta nutsu a Gaban Alkali tace maganar Allah na gaji dama Ni badan Allah nake Aiki a gidan ba,da farkon kawo Ni Aiki gidan dama Muna duba gidan masu kudi ne sai muzo a matsayin Yan aiki,sai Mun kafu mun San sirrin komai na gidan sai muyi cunen Yan fashi suzo su kwashi dukiya a Bamu rabon mu,Kuma dalilin da ya kawo Ni gidan Alhaji kenan, Alhmdllh munyi Nasara Kuma Yan fashi sunzo mun samu sama da milliyan goma a ciki an bani Milliyan Daya,Momy da Mama da su Muka Yi shawarar komai.

Farko naji sun hada Kai suna so su saci kudin Alhaji Wato Abbi su mallaki kadarori da yawa yanda ko ya mutu baza suyi talauci ba,duk da sunfi kowa yawan Yara maza da Mata Amma rashin godiyar Allah tasu ta jawo, Hakan Dana ji yasa na Basu shawara nace Ina da Yan fashi a Hannu idan suna so mu hada Kai zasu samu kudi,Haka Kuma su Momy dukkansu Milliyan Uku Uku Suka samu da aka zo fashi gidan Abbi,Sai Mama Tace a danginsu Kanin babanta me kudin gaske ne a Zamfara Nan ma munyi cunen Yan fashi,na samu Milliyan biyu,Momy da Mama Milliyan biyar biyar Suka sake samu,sai Momy ita Kuma itama Mijin Yayarta me kudi ne a Adamawa Nan mun samu kudi milliyoyi,a kankanin lokaci mun samu kudi kowa sunfi Milliyan ashirin ashirin,Baba Jummai Tace na manta gidan Alhaji Na Allah makwaftan Abbi da aka je Masa fashi sati uku da Suka wuce Momy da Mama da sa Hannunsu Kuma sun samu kudi Nima wacce nake da Yan fashi a Hannu na samu Rabo na,Dama yanzu Abinda akeyi kenan masu Aiki Ana hada Baki da su a cutar da masu gida,ko a turo mace a matsayin Yar Aiki ta sace Yaron gida a samu kudi Kuma a rasa Wanda yayi,a takaice Alkali Ni Baba Jummai a matsayin da naje Aiki kenan Kuma na je gidan masu kudi kala kala a matsayin Yar Aiki na tura musu Yan fashi da Yan kidnapping,gidajen da nayiwa Haka baza su Irgu ba,Kuma Ni tun da kuruciya ta na Sha zaman kurkuku Amma duk hukuncin da aka yanke min bana cikakken sati biyu mutanenmu zasu fitar Dani,Ni yanzu ba tsoron gidan yari nake Yi ba,Kuma wallahi Haka Kawai Shekaran jiya Ina kwance Allah ya saka min Nadama da Dana sanin abinda na aikata da cin Amana,Tausayin Abbi da Kaunar Fu'ad Dansa ita tasa naji Nadama ta kamani,na rasa ta yanda Zan tonawa su Momy Asiri shi yasa nayi amfani da korar da Abbi ya musu na Basu shawara Kan su kaishi Kara kotu.

 Su kuma ta bakinka Alkali kwakwalwarsu Yawu ne a cikinta ba hankali ba tunani Suka yarda,har abinda zasu ce Ni na karanta musu tunaninsu Zan goya musu baya Basu San tona musu asiri zanyi ba,sabo da Haka Ni nayi nadama na Mika wuya ga kotu sannan a shirye nake na nuna duk Yan fashi da sauran Yan ta'adda Dana sani,Ai Momy Faduwa tayi kasa ta sume,Mama kuwa Baba Jummai ta nuna tana Allah ya tsine Miki Azzaluma maciya Amana kinci Amanar yarjejeniyar da Muka kulla munafuka,Baba Jummai Tace Ni dama shekaru na sun ja Nawa Zan Kara Nan gaba ai Kawai a kaini kurkuku na karasa rayuwa ta a can,bani da yaro ko daya bare jika,Mutuwar tsaye Muka Yi Ni da Fu'ad har Alkali,Baba Jummai ta kalleni Tace Rumaila lokacin idan Zaki tuna da yan fashi suka kawo ki part din Fu'ad,me yasa Duk Yan aikin Gidan ba a dakko ko Daya ba sai Ni,Sannan da sukace Fu'ad sai ya Sadu Dani ba Niyyar su bace nice na karanta musu Sabo da a duniya Ina sha'awar Fu'ad, Fu'ad Baki ya bude da sauri tare da rufe fuskarsa da tafin hannunsa Dan wannan abin kunya ne,Baba Jummai taci gaba,Ke Kuma Rumaila sai kika ce kin fanshe Ni kika tausaya min,a lokacin idan na dage sai da Ni za ayi to zaku Iya harbo jirgina musamman idan Yan Sanda Suka zo bincike shi yasa na kyaftawa Dan fashin Ido,nace na nemi afwa a barku kuyi a sirri ko tantama bana Yi Indai an barku Kun lulluba to baza ku aikata komai ba,dalili na shine bakin ciki na Miki tunda ban samu Fu'ad ya sadu Dani ba to kema bazai sadu da ke ba,sabo da nasan Fu'ad akwai tsoron Allah duk Ihun da kikeyi nasan wallahi karya ku keyi,shi yasa na biyewa kowa na dinga Nunawa ban san komai ba,sai gashi cikin hukuncin Allah kin auri Fu'ad,Baba Jummai ta tafa min a Gaban Alkali Tace na yaba Miki kinyi dace Rumaila,Amma su Momy wallahi da su muke komai Muna cutar mutane.

Abbi da dukkan mu mun rasa bakin magana,Momy tayi sumanta ta gaji ta farfado ba Wanda ya kula ta,Alkali yace yanzu za ayi shari’a Kuma wallahi tunda Kun amsa laifinku da kanku Zama daya zuwa biyu Zan yanke Hukunci,ko cikinku akwai me karyata Maganar Jummai? Momy tana Hawaye tace duk abinda ta fada gaskiya ne,Mama ma karya ta kare,Alkali yace ranar Monday a dawo zaman kotu babu Wani zaman sirri a Gaban kowa za ayi,Momy, Mama da Baba Jummai Yan Sanda ne suka tafi dasu za a ci gaba da tsare su har a Gama Kara.

 Da Mamaki Muka dawo gida, jikinmu yayi sanyi,tuni labari ya watsu a dangi,su kansu su Fadila da su Islam kuka Wiwi Suka dinga Yi Basu taba zaton rashin Imanin Iyayensu ya Kai Haka ba,Sai ga Fadila Ana komawa gida ta wuce part din Rabi,Rabi Mamaki ya kamata dama taji komai da ya faru,Rabi da fara'a Tace Sannu da Zuwa Aunty,Fadila da murmushi Tace yawwa Kinga wallahi kwadayin danwake nakeyi Dan Allah kiyi min na ci,Idan nayi da kaina bazan iya ci ba,Rabi Tace Aunty ko dai juna biyu ne?Fadila Tace ban son Iskanci Kawai Ni ki min Ina jira,Rabi ta shiga kitchen sharp sharp tayi Mata,tana ci Saddeeq ya shigo dama kwanan Rabi ne yayi mamaki Amma Kuma yayi farin ciki matuka ganin Matansa suna ta Hira lallai Fadila anji jiki,Zama yayi a cikinsu,su Rabi an samu kishiya harda share Angonta suka ci gaba da hirarsu da Fadila,yace ikon Allah yau baza a kula Ni ba?Fadila Tace Dan Allah Malam tunda ka dawo ka tafi kayi wankanka mu Hirar zumunci mukeyi,Kai Saddeeq ya jinjina yace au abinda zaku Yi min kenan shike Nan sai na rabaku,Fadila ta kalli Rabi Tace je ki kula da mijinki,Rabi ta Mike suka Shiga ciki,Fadila sai da ta cika cikinta sannan ta koma sashenta,Rabi da Saddeeq Kuma da dare a banfaren Fadila Suka raba dare suna Hira.

Ni kuwa da Fu'ad da muka dawo wanka Mukayi Kawai tare da kwanciya Muna tattauna abinda ya faru,Abbi kuwa Bai Yi saurin yanke Hukunci ya saki matansa ba sabo da shi a duniya baya son saki,ace ya auri mace Kuma ya saketa,sai Ranar Laraba da Muka koma kotu,ko da aka zo Shari'a Baba Jummai a waya ta Kira Ogan Yan fashin nasu Tace su hadu a Salama Hotel Dake maitama wata sabuwar harka ta samu,yace sai gobe zai zo,Duk wasu mugaye sai da Baba Jummai ta Basu Venue na wajen haduwa,da Yan Sanda aka kamasu a Hannu Daya Bayan Daya,Ranar Monday aka sake Shiga kotu babu Bata lokaci kowa ya amsa laifinsa,sai lokacin Abbi ya saki Momy da Mama saki dai dai aka yanke musu hukunci,Mama da Momy daurin shekara talatin a gidan Yari Baba Jummai kuwa sabo da ta Dade tana Yi gashi a cikin yan fanshin sun tabbatar da sunyi kisan Kai Alkali ya musu daurin Rai da Rai a gidan Yari har Baba Jummai,Baba Jummai da Yan fashi ko damuwa basuyi sosai ba sabo da dama sun Saba,wannan ne Kawai aka yanke musu Rai da Rai,Momy da Mama su suke ta barka kuka tare da Yaran da suka Haifa,Dukkanmu dasu Umma jikinmu yayi sanyi Kuma mun tausaya musu,Abbi matansa sun koma Biyu Umma ita kadai a gidan Nan sai Yara duk sun koma karkashinta ta Zama Uwar kowa,Aunty Samha da yaranta ita dama gidanta daban Haka Muka ci gaba da Zama cikin kwanciyar hankali da Jin dadi,Har Saude mun Sha biki tana Kano gidan mijinta Haka su Naila Abbi ko Shagali ba ayi ba sabo da abinda ya faru Aure kawai aka daura tare da Kai Amare,Gaba Daya sun sakko wulakanci da Rashin mutunci ya kare,kafin na musu magana ma sun min magana mun gaisa,suna Neman shiri da mu ko yaushe suna zuwa gidana.

Karatuna yayi Nisa Sosai,Bayan wata hudu da auren Rabi ta samu ciki itama ga Fadila nata ya girma,Hajara ma laulayi take fama,nice   dai Kawai har yanzu ba rabo, Fu'ad na sa a gaba Ni Wallahi Nima sai an min ciki,kowa Yana ta samu mun Riga su aure Amma Ni Shuru, Fu'ad muna zaune a Palo Yana Aiki a system dinsa Yana Kora lemon Kwakwa Dana hada Masa,Nace Ni kowa Yana ta samun ciki ban Dani, Fu'ad yayi Dariya yace to me zanyi Aiki na Riga nayi Allah shike ba da Haihuwa ba Ni ba,kici gaba da Hakuri Allah zai bamu ya kike Abu kamar bakya zuwa makaranta Babyna,a kafadarsa na Daura kaina nace Kaine dai baka dagewa sosai idan da kana dagewa ai da tuni na samu ai Allah yace Tashi in taimakeka,Yanzu machine kike so na koma fisabilillahi Abu sau Uku sau hudu har fa cewa kikeyi kin gaji Amma kice bana kokari? Nace Kaine Mana baza ka dinga tuttula madarar taka a ciki ba Taya Receptors zasu sakalo Sperm din su kaishi shi cikin Mahaifa ta su Dora saman kwai, kullum sai saka kwai nakeyi a banza sai Ina Sa Rai sai Naga Kawai Ina period Ina ta saka kwai Haba Dan Allah Dan Annabi,Idan ka kawo ka barshi can ciki jikin Mahaifa sabo da Sinadarin dake Jan sperm ya fisge shi yayi ciki da shi shuuuuuuu ya dasa shi jikin kwai Haba Ni fa Ana mana Genetic a school rashin dagiyarka ce Baby Kawai kayi min ciki yawwa, Fu'ad Dariya yake ta Yi Bai ce komai ba sabo da abin Nawa ya wuce hankalinsa,Aikinsa Kawai ya keyi,System din na rufe nace dare yayi kazo a samo me Sunan Abbi,Ina ta so naji Ana Mama Mama a gidan Nan muje, Fu'ad yace to an gama,dama a ransa yace sai yayi maganina,Ko da muka fara soyewa Fu'ad kin gajiya yayi kamar Engine,sai da ya kure min maleji,Ga mugunta yana ta min kuka na saki tun Ina daurewa,Kuma yaki ya Kyaleni yace yau sai kin samu ciki Baby,nace wallahi Wasa nakeyi nasan Allah ne ke badawa Dan Allah kayi Hakuri,Ba karamar wahala ya bani ba Daren Nan guda,washe gari da safe yace zai sake tashi nayi na gudu dakina na datse da key.

  A shekarar su Iya da Affa,tare da Yan Uwa na kaf suka tafi kasa me tsarki,Rabi da Fadila tare da Saddeeq Suma sai labari naji sun tafi,Saude Ma mijinta ya biya Mata sun tafi tare da Sauran matansa,Kuka na dinga Yi Ni Fu'ad Bai biya min ba,Yana baccin Rana na Shiga na kwanta tare da fashewa da kuka,Yana baccinsa me Dadi ya tashi nace Ni sai kullum ace Ana kauna ta,I love you Taki karewa Amma ga su Rabi can a Makkah da su Iya Ana ta Shagali idan Muka Yi waya suna tare Ana ta Jin dadi Ni kuwa Ina Nan sai dai naci soyayya na koshi cikin ma an kasa Yi min,yanzu Akan wannan kika tashe Ni a bacci? Gasa kikeyi da Mata? Abinda Zaki koya kenan daga Kinga kawa tayi Abu sai kice sai an Miki kema,Fuska ya Bata ya dinga min Masifa Ina kwaikayon wasu,rayuwarsu daban Taki daban Indai Abu ne Zan Miki Amma wlh daga yau idan na sake ji kince kawarki ko wata an Mata Abu ke ba a Miki wlh sai na Bata miki,ku daga Kun samu sake sai iskanci iri iri,wani kawa da Yan Uwa an biya musu ke ba a biya miki ba to wannan Hassada ne Idan Baki sani ba,nayi niyyar Next Year Amma na fasa tunda Tabara ta sa Zaki koyi Hassada,jarabar Su Rabin Nan ma Ni ban San ya akayi suka Yi aure a Nan ba kin wani koma kin jone dasu tashi kiyi waje,Ni fa ba Hassada nake musu ba wlh Kirana sukeyi kullum a waya naji su tare da su Iya Ana ta harka shine naji dama muna tare,shine Zaki zo Ina bacci na ki tashe ni? Kukanki ne zai sa na Miki abinda banyi niya ba? Ki kiyayeni wlh Naga Alama kishiya kike so ayi Miki kema,me yasa Baki Yi koyi da su Rabi ba kice na Miki kishiya kema irin Rabi,Kallonsa Nayi da sauri nace ah dama kace Kawai aure kake Nema,Dama Iya ta fada Baku da tabbas,kwanciya yayi tare da juya min baya Yana dariya a ransa har ya koma baccinsa,Na Gama kulewa dama Dan ya Bata min Rai ya fada,Fita nayi nace ai kuwa yau shima bazai bacci ba,Tsintsiyar shara na dakko na fara shara kuyasss...Kuyasss....Sip na Bude na mayar na zuge da karfi garam,,tsintsiyar na buga a jikin Mirror,juyi ya sakeyi sai Kuma ya Mike gaba Daya ya Shiga Toilet,Kitchen na Shiga na Daura Girkin dare,Yana kallo na Ina ta fushi bana kulashi,da dare ma ko da nayi Shirin bacci a dakina na kwanta,Ina ta juyi na kasa Bacci,sai gashi ya shigo,farin ciki ya kamani a Raina,kwanciya yayi Kawai a bayana tare da daura fuskarsa a dokin wuyana,Kissing bayana yakeyi,ban hanashi ba.

Nace baza kayi fushi da zuciya ba? Dariya yayi yace ai Ni a wannan bana fushi komai fushinki ni ba abinda zanji,wajen wa zanje nayi? Dole sai wajen matata idan kinyi fushi ma kinyi a banza,idan kin hanani ma wlh ta karfi Zan Miki ba ruwana,idan kinyi fushi tunaninki Zan fasa ki daina,Dazu Dan bakin ciki harda hanani bacci Kawai ki fara sharar banza Don kar na huta ko? Dariya nayi nace ai Kaine kace wata kishiya,Shagwabarki ce da neman magana yayi yawa ke baza a zauna lafiya ba sai kinyi Rigima kwana Nan kike wannan Hayyatar,kice wannan kice wancan Allah yasa ma ba ciki kika samu ba kike wannan abin,ba Wani ciki da ciki ne ai Zan Gane,Haka muka Sha soyayyar mu.

Bayan wasu kwanaki na fara zazzabi,Amma Fu'ad Bai sani ba,Sai Dana dawo daga School,ya dawo daga Office da wuri yau har yayi wanka Yana Hutawa na shigo,Yana Jin nice ya Mike ya Rungumeni yaji jikina zafi sosai,Wuyana ya taba da bayan Hannunsa yace Baki da Lfy Baby,tun yaushe kike zazzabi ban sani ba? Hawayen Shagwaba ya ziraro min nace Yau sati daya kenan kullum sai nayi idan naje makaranta,Amma shine baza ki fada min ba? Yace muje asibiti,Ko Uniform Bai Bari na cire ba ya rike Hannu na har cikin mota ya sani muka tafi shike Driving,Muna zuwa wani Hadadden Asibiti ya Bude min file a Private Hospital Likita ce ta min tambayoyi sannan tace na kawo mata fitsari a kwalaba, kwalabar na karba nayi Fitsarin na kawo ta auna,ta turani nayo wasu test din ta tattara bayanai  a Result ta bani ta kalli Fu'ad tace matarka tana da ciki na wata Uku da sati daya,Sai Malaria dake damunta,zata fara zuwa awo duk sati,wasu Magungunan ta rubuta Fu'ad ya karba ya tafi zai siyo,sai murna yake Yi bakinsa yaki rufuwa, Ni Kuma na zauna tare da Likita muna Hira tana ta bani shawarwari da abubuwan da Zan na ci.

Nace Likita Dan Allah ki fada min tsakani da Allah ya zafin nakuda yake?Likita ta dinga dariya tace sai lokaci yayi Zaki ji,Nace Allah yasa kece Zaki karbi haihuwar Nan na yarda da ke Doctor,na damu Likita da surutu nace Oh Allah sarki Dan mijina na dinga Masa masifa naki samun ciki Ashe ma Ina da cikin,Bari na Kira Iya na fada Mata ta fara tanadi.
Lambar Iya ta Makkah na Kira ta daga Tace Dawafi Zan Shiga Rumaila,nace Iya ki min Dawafi Bakwai sau Bakwai sau goma Sha biyu, jikanki ya fito lafiya Iya ciki ne Dani ki siyowa jariri Kaya masu kyau a Nan,idan kin dawo ki fara tanadin yajin jego,Iya kaji Ashirin Zaki soyo min idan na Haihu,Iya Tace gwara da kika fada min kullum a masallacin Kaaba Zan dinga kwana Ina Miki Addua Allah ya saukeki lafiya,Cikin watansa Nawa?nace Iya Ni kunyarki nake ji idan na Haihu Kyaji Kawai,ki lissafa da kanki,Iya Tace anyi shashasha a Nan Amma kin Gama fada min Zaki ce kunya Kuma? Wayata na kashe Dan kar ma na kauce hanya na fadawa Iya, Fu'ad Yana dawowa muka tafi,Zan Dan tsallaka wani tudu na rike Hannun Fu'ad Nace tsallakar Dani Kar cikin Nan ya zube,Dauka na yayi ya ajiye,a hanya ma tafiya ta sadaf Sadaf nake yi Kar ciki ya zube,Girki yanzu kafin na Gama Aiki ne ko cokali Zan dauka a hankali a hankali nake lallabawa,Ko Xxx zamuyi Fu'ad sai dai yayi a hankali idan ba Haka ba bazan yarda ba,tun Yana dariya abin har ya zame masa jiki,Gajiya yayi da Jin yunwa sai na Dade ban Gama abinci ba akan Ina lallaba ciki,shine yaje ya shirya min tsiya da Likita,ranar da ya kaini Awo tace ai me ciki anfi so ta dinga jijjiga jikinta tana yin komai cikin sauri idan ba Haka ba za a haifo jariri nakasashe,Ai tunda Likita ta fada kamar fadar Allah aiki bana gajiya komai na dawo yinsa normal,Haka Kawai ma har wanki nakeyi da Hannu bazanyi a Injin wanki ba, Fu'ad Yana ta kallon ikon Allah ko ya hanani bana yarda.

Yau ma Sai da na Gama komai Amma wata Jallabiya Yana cireta na dakko Ina wankewa yace Wai bakya gajiya ne Baby? Nace baka ji me Likita Tace ba? Ai yanzu kabi doka ka zauna lafiya kawai,Yaron Nan da Alama me Energy Zan haifo, Fu'ad yace ai Haka ake so,yau Baku gaisa ba,ya kamata ka shafa masa Kai ka sa Masa Albarka,Likita Tace idan ana musu magana tun a ciki to da basira ake haifo su ko baka so ya dinga zuwa na Daya a school? Fu'ad yace Ni kuwa nake so,na Mike tsaye Fu'ad Yana shafa cikin Yana kwararawa jariri Addua Ina amsawa da Ameen Ameen,Yace Allah yasa yazama na gari lafiyayye kyakyawa,nace Ameen,yace Allah yasa ya Zama mahadaddacin Alqur'ani,nace Ameen,Allah yasa ya Zama Wanda Musulmai da Musulunci zaiyi Alfahari da shi ko ita, Allah yasa me Biyayyar Iyaye ne,Ameen, Ba mazinaci ba,Ameen,Ba masifaffe ba ko masifaffiya,Ameen, Allah yasa ya Zama nagari mutumin kwarai,Wanda bazai Zama Dan fashi ba,Ameen,ba Dan Kidnapping ba,Ameen,Nace Allah yasa Gomna Zan haifo ko wani minister ko wani Sanata me kishin kasa da Alumma,me kishin Musulunci Fu'ad yace Ameen,Ido Muka hada ya kashe min Ido daya Muka dinga dariya,zai Kuma shafawa na rufe Rigata nace ya Isa Haka Mana Kai baka San kadan ba,sai ka gajiyar da shi Kuma.

Fu’ad Yace to Dinkunan me cikin da kika ce za a miki Baki zabi kayan ba na siyo a Kai dinki,Nace sai ya Dan Kara girma sai Tela ya Dinka min manyan riguna Wanda zasu dinga shanye cikin,Sai Uniform dole a dinka na me ciki,yace an gama Princess,nace sai takalma flat over Size sabo da nasan Nan gaba Zan kumbura,cutar kumburi irin ta me ciki wacce ta kusa Haihuwa zanyi ta,takalma zasu Yi min kadan a siyo Over Size, Fu’ad Dariya ta isheshi ya hadu da me ciki yace to sai me? Nace a cika min Drower da Shaving Stick sabo da idan na kusa Haihuwa kullum Shaving sabo da dubani da Likita zata dinga yi, Fu’ad yace Ni ba nace style Zaki nayin shaving ba Ni bana son kwalkwal,Kai ba Wani style sai an haihu,kullum Kai kace sai an maka me tozon zakara bazan iya ba baza ka jawo Likita ta rainani ba taga sirri na ba, Fu’ad ya dinga dariya kamar me,ko da dare da yaje wajen Umma sai dai taga ya Kama Dariya shi kadai,Umma Tace maza ka Zama kwarkwar Allah ya kawo sauki.

 A makaranta malaman har sun gaji da Halina sai nayi kwanciyata a zaune Ana magana zance bani da lfy,ai Ina da ciki ba abinda ake cewa sai a Kyaleni,ko Assignment Ina sani sai naki Yi Ana tambayata zance bana Jin dadi,Wani malamin Biology ya shigo aji ya tashe Ni yace ke Wai ke kadai ce me ciki a duniya? Nace Malam Kai da kake Biology ai nasan kasan komai da yanayi na me ciki,ya zaka takura min,Ido ya zare min yace ke mu fa Nan karatu akeyi ba ruwanmu da cikin ki,nace lalala Ina matar Aure kake kashe min Ido daya wlh sai na Kai kararka ai Rannan ma Haka kayi min Dan Kira kace kana so na,nace Ina da aure kace baka da matsala akan naki sonka sai kazo kana min Maganar batsa a aji,har kana cewa ta Yaya ciki yake samuwa,Malami ya tsorata yaji sharri na Zan sa a daure shi,dama an tsani malamin Bai da mutunci,ganin Zan tozarta shi ya bani Hakuri yace kwanta kiyi ta baccinki,nace Ni kake kashewa Murya Kamar Mijina? Malam yayi mukus,ai kuwa na kwanta Ina Jinsa Yana ta ciwa student mutunci.

AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

 THE END (KARSHE)








        NA KUDI NE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

         111-115

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

DANGIN RABI FANS

     Yau Fu'ad da Kansa yazo daukana,Ina school an tashi mun fito da Kawayena su Laila muna Hira har mota suka rakani,Laila ta rike min jaka Wai tana tausayin me ciki,Sai da suka gaisar da Fu'ad,ya fito da Kansa tare da Bude min gaba na Shiga ya Rufe sannan ya zaga ya Shiga Muka tafi,Yana tuki yana satar kallo,Baki na turo gaba cike da Shagwaba,Murmushi ya saki tare da Furta Anya kuwa Baby kina karatun Nan? Kafadarsa na dafa tare da Furta sosai ma ai baka ga kokarin da nakeyi ba,kullum sai an tafa min a class duk period,Shawarma joint  muka nufa a can yayi parking Zan bude ya Kai Hannunsa jikin sit Belt zai cire sai Kuma ya kwanta a kirjina,ka zare min Belt pls,Sake kankame Ni yayi yace Dan tsaya na huta,munkai minti 5 a Haka sannan ya tasar min a jiki muka Shiga ciki,mun ci chips da Shawarma tare da Ice cream Dake dama Ina son sanyi abina,sai da muka Gama ya mana take away na wasu kayan tande tande sannan muka koma gida.

Tunda na samu ciki ban damu ba bana Shan wahala har ya cika wata bakwai lokacin yayi girma sosai duk na sake kiba na bude,Sai Kuma yanzu nake wahalar cuta iri iri,daga wannan sai wannan,lokacin tuni Fadila ta Haifo yarta mace katuwa ko suna sai kusan dare Fuad ya kaini,Rabi itama ciki ya girma ita da Hajara,Saude ma haka,Su Naila kuwa dama sun samu Yaron ciki Farida ce Kawai Bata da komai ba a Dade ba Hajara ta Fara Haihuwar Yarta mace, Fu'ad yayi kokari da kyar ya barni nabi Flight zuwa Lagos suna tare da Rabi,Saude ma ta je,ko kwana daya Bai Bari nayi ba na dawo Haka,Kaya manya na masu ciki nake sawa,cikin Yana bani wahala sosai,Yana shiga wata takwas sai kuwa na fara kumbura a kafafuna,sabo da wahala  Fu'ad baya zuwa Aiki sosai sabo da ko aikin Gidan kadan nake Yi,Umma me Aiki ta turo min take tayani wasu abun,Gaba Daya na karaya na koma ga Allah kusan kullum sai nayi kukan wahala,Yau ma da dare nayi Shirin bacci na kwanta da kyar, Fu'ad ya dinga rigima,Ya fara Wasa da sassan jikina Ina nokewa, yace Dan Allah Baby bakya tausayi na? Jiya banyi komai ba Kuma yau ma gashi komai ya Kara sweet,Dan Allah ka dinga barina in hutawa wlh bani da lafiya da me zanji da cikin danka ko da kai,Kullum fa da zazzabi ga ciwon kai Kawai Dan kina da ciki shike Nan Baki da lafiya Dan Allah Sweetheart,Ina ma cikin Nan zai dawo jikinka kaji abinda ake ji,ka tashi kayi Nafeela Allah ya sauke ni lafiya ma Kar nazo na sheka lahira,Ni duk na Mika alamura na ga Allah, Da sauri yace Inshaallah lafiya Zaki Haihu kinji,ganin na damu yace ankon sunan fa da kika ce Zaki fitar? Nace wa yake ta wani anko Ni ta kaina nakeyi ko suna bazan Yi ba Kawai Allah ya sauke ni lafiya,Ameen ya Furta Yana shafa gashi na,yace to Ni ki ji Dani Nima ga Form na kawo a cike min,Dariya nayi Muka Shiga kissing din juna tare da Sarrafa juna Yana abinda yaga dama,a hankali yake komai yanda bazai wahalar Dani ba.

 Washe gari Khaleesat ce tazo sanye cikin Abaya Blue me tsada,Ina kwance a sama na sakko a hankali Ina tafiya da kyar, Khaleesat tana ta kallo na Ina sakkowa a steps Tace Rumaila wallahi ki rage kwailo gaki Nan Ras da ke kinyi wani kyau da kiba kin ganki kuwa? Amma ke kullum ban taba ganinki da lafiya ba sabo da kina da ciki,Dariya nayi Ina Zama kusa da ita sanye nake cikin doguwar Rigar atamfa Dinkin masu ciki,kaina ba dankwali nace ke kike ganin Haka Amma Ina lafiya ga mace me ciki,Gaisawa Mukayi Tace Ina Babyn naki? Allah ya dawo da shi na fada Masa abinda kika ce,tunda Rashin kunya kike Masa,Dariya Khaleesat tayi Tace Kawo min abin ci dama yunwa nake ji idan naje gida sai nayi girki nafi so Kuma Kawai sai abincin dare zanyi,me kika dafa? Nace pounded yam with Egg source Kuma ta Sha nama,Khaleesat Tace wow Abincin da Mijina yafi so kenan Zuba min a flask Kawai na tafi dashi na huta,ki shiga kitchen ki zuba Mana da kanki,Babyn naki fa? Haba ai kin San Flasks dinsa daban ke kin San bazan Baki nasa ba wlh,ai nasan komai nasa na daban ne,nace har spoons Nasa daban ne,babu abinda wani zaiyi amfani da shi sannan na Bawa Babyna shi, Khaleesat Tace Iyayi Kyaji da shi Ni bazan iya wannan abin ba,sai dai idan Kar ya ci,da kanta ta zuba a flasks ta fito ta min Sallama ta wuce.

   Nima fuska ta na gyara na yafa Mayafin na dauki Hand bag Dina nace da me Aikina naje Shopping yanzu Zan dawo,pls kafin na dawo ki Kara gyara kasan,sama na gyara komai yanzu,To a dawo lfy Hajiya,Glass Dina me tsada na maka a fuskata na shiga motar Fu'ad Baka katuwa,Ni ke Driving naje na siyo abinda nake bukata sannan na Kira Fu'ad,Nace ka tashi na biyo na daukeka ko na wuce gida? Yanzu sai da kikai Driving bayan na hanaki nace ki Bari sai kin Haihu,Akwai abinda na damu Zan siya ne shi yasa,zo ki dauke Ni to,Office dinsa na Shiga Ina mota ya fito ya sameni sanye yaje cikin kana Nan Kaya na kirki muka wuce gida,Ina Driving Yana tsokana ta Wai me ciki ko kunya bakya ji kowa yasan ta ya aka same shi,ban kulashi ba sabo da na Saba da tsokanarsa kullum,yace Wai yanzu ya zanyi idan kin Haihu sai anyi 40days zanyi wani Abu? Ae na bashi amsa,yace wlh akwai kura a kasa,ke l bazan iya ba babu ruwana jini na daukewa Zan dawo bakin aiki,nace ai Iya Tace a can Wajenta Zan zauna,tab ki daina ma sa Rai wlh bazan yarda ba muna ta surutu har muka je gida.

 Tafiya na ja rayuwa na gudu ciki na ya cika wata tara, kullum sa rai nakeyi da Haihuwa, Fu'ad ma Bai fita yayi nisa gudun kar a samu matsala,Yau Kuma Saturday Abbi ya tura Fu'ad Lagos zaiyi wani meeting zai wakilce shi,7am ya bi Flight yace da wuri zai dawo,Sai da ya lallabani sabo da na tashi bana Jin dadi,shi Kuma tunaninsa tunda kullum Haka nake cewa Bai kawo komai ba, kuka na sakar Masa da kyar ya lallasheni ya tafi,Ciwon Baya da Mara ne ya takura min naji abin ba sauki Kawai na Kira Umma na fada Mata a waya ai kuwa sai gata ita da Fadila a mota,Fadila ke Driving na hada kayan Dana tanada na Haihuwa a wata jaka katuwa ta Yan gayu me tsada,kana gani kasan Yan gayu ne kudi Kuma ya zauna,Umma ta kalli jakar Tace Haihuwar fari kenan ba a San Kan Nakuda ba har wani kyale kyale akeyi,nace Umma ayi sauri Kar na Haihu a mota Muna Hira da Fadila,Umma Tace ah ba nakuda kike Yi ba,idan tazo wannan Maganar baza ki Iya yinta ba, private Hospital inda nake zuwa Awo can Muka je,Bayan an duba Ni Tace Haihuwa ce Amma ba Yanzu ba sai yamma gado za a baku,Dakina Ni kadai dake na kudi ne ko Ina sai kamshi,Kamar jira ake a bani daki sai ciwo Gadan gadan ya taso,Marata na rike Ina bubbuga kafafu na,Umma ta kalle Ni,Shuru bana iya magana,Fadila tana gefena Tace ciwon ne ya dawo? Ko kulata banyi ba,Dankwalina na zame na mikawa Umma bana magana,na fara wash wash....Umma Tace Sannu Addua zakiyi Nace wacce Zan karanta? Umma Tace ko Mai ma,zamewa nayi na sakko kasan Tiles na zauna Ina cewa Umma Kira min Iya ciwon Nan bana tashi bane dama na fada Masa,Umma Tace ai Rumaila har yanzu Baki fara komai ba tunda kike Iya magana,Nace Nan duk banyi komai ba? Fadila Tace sosai nace to Kawai mutuwa zanyi,Indai ciwo ya fi wannen ai sai na tafiya Kiyama,Umma ce ta Kira Iya ta Mata bayani,Iya hankalinta ya tashi tace bani Rumailan ko Bata Hayyacinta? Umma ta Mika min waya nace Iyata na fashe da kuka,Iya Tace Rumaila ya jikin ba Kuka Zaki ba Addua akeyi,Nace Iya sai dai Allah ya sada mu a darulsalamu,Iya Allah sarki Uwa sai ta goge hawayenta hankalinta ya tashi tace ko nazo ne Rumaila? Nace ae Iya ki taho na ganki,Iya Tace gani Nan Inshaallah,ai Iya mijinta ta sanarwa Kawai ya Mata booking a jirgi tazo sharp sharp,Asibitin ta wuce Direct a Taxi.

 Umma ta Kira Fu'ad Yana Meeting da mutane Yana ganin Kira ya dauki Excuse ya fita ya Kira Umma,Umma Tace muna asibiti fa Rumaila nakuda sunce Haihuwa sai Nan da Magriba ma,Hankalin Fu'ad idan yayi dubu ya tashi,Ina Rumailan? Umma Tace gata yace Bata Wayar ko baza ta Iya ba? Umma Tace ga Fu'ad,Lokacin ciwon ya Murda tun Ina daurewa Ni dai na kasa na fashe da kuka,Yana ji ta waya Ina cewa Zan mutu,dama Ni akwai kwailo,sai birgima nakeyi a saman gadon,idan na gaji na sakko kasa,Sai da ya Dan lafa Sannan Umma ta Kira Fu'ad ta bashi Ni,Sai Kuma ya jini Ras muka gaisa nace naji sauki karka damu yace to,kafin ya rufe Baki ciwon ya dawo nace Iya ya dawo wallahi wayoo Allah marata...wash......... Fu'ad Wayar ya kashe ya koma Meeting,da kyar yake dannewa yayi sauri ya sallami kowa gashi Return ticket dinsa sai 6pm,Gashi zai canja wani babu na time din duk sai yamma,ai kuwa ya dinga tsinewa Nigeria Yana me za ayi da wannan kasar komai nata babu na arziki sai tsiya,ai har abada wannan kasar idan kaga anci gaba a kasar nan to sai dai idan mutanen ciki za a kwashe gaba Daya a kawo sababbi a zuba,Dan ko jariri ne Indai an haife shi a Nigeria to idan ya girma ya Sha nonon zalunci,shi kadai yake ta masifa sai waya yake bugawa Umma ba ji ba gani,Ko minti biyar bayayi zai sake Kira yace Umma ya jikin nata? Taji sauki?har yanzu Bata Haihu ba? Ina asibiti Ina ta gumurzu har Yamma ban Haihu ba sai wurin 5pm da taimakon likitoci na Haifo Dana Namiji katon gaske kyakyawa ajin farko.

 Na Sha wahala,sai bayan na Haihu an gama komai Har jaririn Iya sun Masa wanka Nima nayi na canja kaya,aka hada min tea me kauri Ina Gama shanyewa jini ya Balle min,Hankalin kowa ya tashi jini na tashin hankali ba kadan ba,Nan likitoci Suka fara aikinsu a kaina da kyar aka samu ya tsaya,Wurin Magriba aka Gama min komai na Dan farfado Iya ta sake min wanka na shirya na canja wasu kayan,jiri Yana daukana,dakin Hutu Suka canja min ko Ina Yana kamshi,Bayan sunyi bincike da gwaje gwaje Suka ce dole sai an Kara min jini Leda biyu,Umma ta Yiwa Yan mazan gidan waya duk Suka zo aka dinga gwada su duk babu Wanda yazo Daya da Nawa A+ sai Islam,lafiya Kalau yake Amma Leda Daya Suka ce zasu eba a turo wani shima,lokacin Fu'ad ya dawo dama yasan komai suna waya da Umma,yayi zuru zuru ya fada tunda ya tafi babu abinda ya iya sawa a bakinsa,Direct wurin abinci ya wuce yaci badan Yana so ba sabo da Kawai yaje a gwada shi,Malt ya Sha da Fresh milk, ya wuce wajen aka gwada shi anyi sa'a shima A+ ne irin Nawa Dana Islam,Nan take aka ja nasa,yayi yayi su barshi ya shiga yaga lafiya ta sunki yarda,Zama yayi tare da zuba tagumi,Ya gaji ya koma masallaci yayi Sallah ya zauna Yana ta Addua harda guntun Hawayensa Allah ya bawa Rumailansa lafiya ko ta Jaririn Bai bi ba,Yana masallaci aka Kara min Leda daya,aikuwa Ina Jin jini a jikina naji wani karfi naji ma gaba Daya na warke,Da kaina nayi wanka Amma da ruwa me Dan dumi,sai gashi Dana Yi da towel shima ba duka jiki ba,Har gashi na na wanke sabo da duk kyankyamin kaina nakeyi,Sai Dana Gama na fito na dakko sabon Brush da toothpaste zanyi,Umma Tace Ikon Allah Rumaila da Iya shiri Haka Kamar kin San Haka zata faru komai kinzo da abinki,murmushi nayi nace ai dama dole ka dinga tunani iri iri,Bayan na fito,Suna kallo harda Dan shafa man jariri a kafafunsa da Hannayena,Na dakko turaruka na Ina shafawa sama sama,Har kayan da zansa,Su Iya sai kallon Ikon Allah suke Yi,Iya Tace Dan Ubanki Wai wa kike yiwa kwalliyar ne kina jego,Ni dai banyi magana ba,na saka Bra ta tana kamshi na zura doguwar rigar Atamfa ta sabuwa dal black me digon maroon,Dake akwai ac Nan take gashi na ya Bude na taje sama sama na Dan gyara abina tare da shafa Masa  Dan Mai na tufke,na koma saman gadon Hutu na,Umma sai da suka wanke kayan Dana Bata suka tafi dasu gida,ta sake zuba su a washin machine ta wanke ta shanya,Fadila kuwa lafiyayyen farfesun kaji ta kawo min,su Khaleesat su Rabi duk sun zo,Rabi Tuwon Danyar shinkafa ta kawo Miyar kubewa danya ta Sha kifi Ni Nace shi nake so, nace ta hado da yajin jego,Rabi Tace a jiki yayi kyau Rumaila Harda wannan wanka Haka daga Haihuwa,a kunne ta rada min Karfa ki jawo mutumin ya zauce,Murmushi nayi Kawai na Matsu Naga Fu'ad,Kuma sabo da shi na gyara ban so Mijina yaji wani Abu ba me Dadi ba,ban son ya shaki wani Abu marar Dadi shi yasa na daure,Me wankin toilet tuni ta shigo ta wanke ta sake goge Room din wani kamshi ke tashi,Jariri Yana ta baccinsa cikin kayan sanyi farare masu Matukar kyau da tsada, Fu'ad ne ya siyo tun cikina Yana 7mnths.

 Sai wurin 9pm Kamar yanda Likita Tace zata Bari ya Shiga ya ganni kowa ma zai shiga,Amma Dake Mata ne Basu Hana ba,Daga Ni sai Iya sai Khaleesat,sune zasu kwana tare Dani,Ai Likita Fu'ad ta Kira ya dinga Hararar Likita Yana Tsaki Yana bala'i Kamar zai kashe ta yace Kuma wlh daga wannan bazai sake kawo matarsa wannan Asibitin ba,aka dinga bashi Hakuri,yace ko Asibitin Gomnati ne Idan na nemi Alfarma za a barni ko ta window Naga matata, har Shugaban Asibitin sai da ya bashi Hakuri sannan ya hakura ya ja tsaki ya shiga,shi kuwa me Asibitin ya jawa maaikatansa kunne sosai,Fu'ad kofa ya bude ya shigo da Sallama Yana fargabar halin da zai sameni sai ya ganni a zaune sosai Ina cewa Iya Miko min shi na shafa Masa turare,Iya tace Iyye Rumaila ba kunya,Baki na turo nace Iya ko da ganin kirki ban Masa ba,Iya ta Miko min nayi Bismillah na karbi abina na Bude turare ina shafa Masa a kayansa, Fu'ad yayi Sallama Bamu ji ba ya tsaya Kawai Yana ta kallona da jariri Yana wani murmushi.

Iya Tace Fu'ad Ashe ka shigo,yace Iya Ina ta Sallama Baku ji ba,Dukawa yayi ya Gaida Iya, Khaleesat ta Gaida shi,suka Mike tare da Iya Suka fita,a gefe na ya zauna tare da daura Kansa a kafada ta,a Raina nace da na zauna banyi gyara sosai ba ai sai kaga me gida Yana gudunka,Gashinsa na shafa nace Sannu da Zuwa Daddy, Dariya yayi yace Yawwa Mummy,ya aiki? Alhmdllh,ya bani labarin aikin da zuwansa da hanashi ganina da aka Yi,Yace kinsha wahala ga idonki Nan duk sun kumbura,nace kuka naci,na Sha wahala mutuwa ce Kawai banyi ba,dama Haka Haihuwa take? Kai Allah ya rabamu da Ita, Fu'ad yayi Dariya yace to ai Next year za a Karo Mana mace,da sauri nace wa? Nace wallahi bazan Iya ba,to Bari kaji Likita ma Tace sai nayi shekara bakwai sannan Zan sake Haihuwa mahaifata tana bukatar hutu,Sannu Sarkin karya ance Miki duk abinda ake ciki Likita Bata gaya min ba Tace Kalau kike lafiya sumul,Nace to na Rantse da Allah bazan sake Haihuwa da wuri ba ko kana so ko baka so dole a zabga min Allurar Family planing na Gama magana da Likita, Fu'ad yace Ni ban yarda ba ai sai da amincewar miji,ba sai an Miki ba Ni Zan nayi idan Zan kawo sai zare na kawo a waje na zubar sperm din ba shike Nan ba,nace da wa zaka Yi wannan tangal tangal din? Ni baza ka min Wasa da rayuwa ba Wani Iyawa zaka Yi tun yaushe Dadi zai kwashe ka kayi abinka a ciki Bazai yuwu ba,Nifa baza ka takura min da Haihuwa ba Akan Haka sai nayi yaji wannan Uwar wahala Haka,da nasan Haka abin yake ai da na dauki mataki a kanka tuni, Fu'ad Yana ta kallona Ina ta masifa Ina bala'i,yace Ni dai gaskiya Nan da 2years ki Karo min yarinya,Kuka na saki sosai,yace ke Mene Haka Kuma? Na dago Ina kuka nace ba kace sai na sake Haihuwa ba na karasa da kuka....Fuskata ya leka Dariya na bashi yace to Yi Shuru sai Sanda kike so Zaki Haihu Wasa nake Miki,Lokacin na goge Hawayena na Mika Masa jaririn,Ya karba ya Masa Addua sosai,yace kin Masa Addua? Nace ae,Abinci fa kinci? Nace na Sha Fresh milk,tea ga tuwo na ga Farfesu Fadila ta kawo zanci,sai me kike son ci? Nace Fruits Salat,nace ance na dinga cin gasashiyar Hanta, da Fruits sosai da bargon kifi,Dariya Fu'ad yayi yace kinfi karfin wannan Baby ba sai kin Kara da karya ba a Ina kika taba ganin wani bargon kifi? Jaririn Yana hannunsa na Daura kaina a kafadarsa na lumshe Ido zanyi bacci,Iya da Khaleesat Suka shigo,Iya Tace dare yayi ka tafi gida Kai sarakan Soyayya jegon ma tare zaku Yi,munafuka shi yasa Duk halin da kike ciki sai da kika wani Sha gayu Ni dama na Gama gano ki, Fu'ad yayi Dariya yace Iya ai yau a Nan Zan kwana,Tashi yayi yace zaije ya dawo,Jaririn ya mikawa Khaleesat ya fita Bai Dade ba ya jibgo Mana kayan ci Dana Sha abin ma yayi yawa,Iya ta dinga Masa fada,Gida ya tafi yayi wanka ya kwanta ya huta bacci yayi gaba dashi.

Nima tunda ya tafi bacci nakeyi ban tashi ba sai da Iya ta matsa min na Bawa jariri nono sannan na koma bacci na,sai 11am na tashi,Iya tana ta min fada ban tashi da wuri ba,to ba Sallah zanyi ba,Brush nayi nayi wanka Iya da kanta taje ta min gashin mugunta da towel,Umma ta taho min da wasu kayan Nawa Wanda muka cire da jaririn ta tafi gida ta wanke a washing machine, idan ya bushe masu Aiko su goge su Adana min,Bayan naci na koshi aka sa min Ledar jini na biyu,Yana karewa aka zare,Yan makarantar mu suna ta zuwa dubani da ganin jariri,abokan arzuka,lokacin da Fu'ad yazo Ana Kara min jini ya fita,abokansa Haka Suka dinga cika asibiti suna dubani da ganin jariri na Sha kyautar kudade,Abbi da mazan gidan  suna ta zuwa musamman Islam,Yayan su Fu'ad da matarsa tare da Babar Abbi Duk sun duba Ni a waya.

  Washe gari aka sallame mu Muka tafi Iya ta nace sai dai a maida Ni gidan Umma,nace Iya Fu'ad yace Bai so shi Bai yarda ba,Iya Tace Ubanki Baku Isa ba a barku ku Daya Haihuwar fari kuyi ta shirme,Umma ma Tace Iya tayi gaskiya,Haka Suka tafi Dani,Nace to a kaini na ebo Kaya,Umma Tace mijinki ya kawo Miki muje Driver,Driver ya tuka Muka tafi Part din Umma muka je dakin Dana taba Zama tun kafin aurena da Fu'ad Nan Umma ta shigar Dani ya Sha gyara Bamu dawo da Kaya masu Dirty ba duk an wanke an goge min an shirya a dakin Dama Ashe Umma da Iya sun Gama shawararsu,Sai Fu'ad Kawai Umma ta Kira ta fada Masa,ba yanda zaiyi yace da Ummansa a'a hakura yayi yace ba damuwa,Umma Tace kuyi magana da Rumaila abinda take bukata ka kawo Mata,Okay yace Kawai ransa ya baci kamar yayi kuka,yace Wai mutum da matarsa wannan Hali na Hausawa baza su canja ba.

  Haka ya kirani na karanta Masa duk kayan da zai ebo Amma Wanda yake so sai yaki kwasowa da su ya kwaso Wanda yaga dama,ya biya ya siyo min Abubuwan bukata na amfani,masu Aiki Kawai Naga suna ta shigowa da Kaya,sai da suka Gama ya shigo a karshe,Kayan nake dubawa naji ya kulle kofa ya sa key,Ta baya ya Rungume Ni a jikinsa Yana shakar kamshi na, juyowa nayi nace Su Umma sunce sai dai na zauna a Nan,yace ae ta fada min ya zanyi su ita da Iya,Nace ya Naga banga English Gown din Nan ba? Yace kin San yanda take Miki kyau kuwa? Kika saka ta nazo na ganki ai sai kisa nayi aika aika,Shagwaba na fara nace Ni gaskiya ita nake so tana min dadin sawa,wani kallo ya watsa min nayi Shuru,Jaririn ya dauka Yana ta Kallonsa Yana Jin wani irin Dadi yayi da,Flasks din ya Shiga budaya,Ni Kuma na Bude Kofar daya da key gudun kar ace wani Abun mukeyi,yace Wai kullum sai kinci tuwo ne?nace Iya ce Tace Wai sai na dinga ci anfi karfi ya na Iya,Daya ya Bude yaga faten wake da doya yasha Hanta,yayi Murmushi ya rufe ya Bude wani yaga Farfesun Naman rago yace Iyye kina goge duniya me jego,ya sake Bude daya yaga gasashen nama yace Allah 'yar Nan,Dariya ya bani na dinga kyalkyalewa,yace Ni yanzu an daina kulani,naci abinci ko ban ci ba babu abinda ya dameki sai dai kici ki koshi ki bawa danki Nono Ni ko oho,kirana ma bakya Yi a waya sabo da kin samu da,to ya Zan maka tayi na sani ko kana kyankyanmin me jego,Hararata yayi yace Zan mareki da sigar wasa,Zama nayi na dauki jaririn na juya Masa baya na Bude Zan bashi nono, Fu'ad zai leko na fasa,Yayi Dariya yace kinzo da rainin hankali,mene ban sani ba Ni Zaki boyewa nono? Na fasa bada nonon na jawo flask na zuba Tuwon shinkafa ta miyar Egusi,na sa cokali Ina ci,Spoon ya dauka shima ya fara ci tare Muka ci sai da muka kusa gamawa sannan Umma da Iya Suka shigo Wai za a yiwa jariri wanka,Iya tace yunwa yake ji,Rumaila ba Kya kula da jaririn nan, Dan Rashin Imani Kun wancakalal dashi a Kan gadon can gefe Kuna cika cikin ku shi Kuma ko Oho,Umma Tace ai laifin Fu'ad ne,Iya Tace bashi ya Sha da Allah mu sauri muke Yi,Nace to na sake juya bayana sannan na fara bashi nonon, Fu'ad Yana son ya kalla ga su Umma dole yaci gaba da cin tuwonsa,na bashi Iya ta karba ta tafi Umma kuwa dama kayan ta eba ta tafi,Suna fita yace San min na Sha kinji? Nace bada Ni ba na gyara Rigata daf,a gadon ya kwanta dama ya gaji sai bacci ya tafi da shi.

 Ba wani suna da za ayi sakamakon Babar Abbi tana asibiti Rai a hannun Allah ciwon sugar ya tashi me tsanani,Abbi tafiya yayi can Germany,ranar Suna yaro aka sa Masa sunan Affa na Wato Ahmad,su Fadila Suka ce ai su tunda sunan Affana ne  Fudhal za Ana ce masa,su Suka zaba aka yanka min sa da Raguna biyu,Yan aiki ne Suka soya da komai,dinkuna Fu'ad set Goma Sha ya dinka min na kece Raini ga takalma da jakankuna,har su kayan bacci Inner wears duk sababbi ya Siya min Kamar me hada lefe,kusan abubuwan duk sababbi aka dinga canja min latest,har wayata,na tattara wasu duk na Bawa mabukata.

Muna Haka Allah yayiwa Babar Abbi Rasuwa,kwana biyu aka kawo ta akayi janaza a can garinsu asali aka Yi komai har zaman makoki,sai da akayi bakwai Muka dawo Abuja

 Gidan mu ma Sai da aka canja Masa fasali da kayan ciki kaf sai da ya canja,gidan ya sake tsara shi,sutura shima sai da ya canja fin Rabin nasa dama shi kusan ko yaushe a sa sabon Kaya yake, duk ya bada Wanda ya cire aka gyara Mana gidanmu,Kullum Yana zuwa wajena har na kusa Arba'in Muka tafi da Iya,a can gidan Iya nayi Arba'in,muka zaga dukkan Yan Uwa da abokan arzuka na birni Dana Kauye,Har Dangin Fu'ad Duk na je musu,sannan na dawo duk ya dameni da waya daga Jin nace na Dade da fara Sallah,sai su Iya da Umma Suka sa na Sha gyara sosai sannan na tattara kayana aka fara maida min gidana,Gidan Aunty Samha naje ta min Allurar Planning washe gari Da dare Fu'ad yazo gidan Umma ya dauke ni Muka koma gida,sai zumudi yakeyi duk ya gigice musamman da yaga yanda na canja  nayi wani kyau na musamman,Ni kaina Ina bukatar Mijina,Yace kinje wajen Aunty Samha? Nace No joke naje,inda naji jiki yaushe Zan zauna,Fhudhal ya kalla yace wannan Yaron Dani yayi Kama,Nace ai har gadarar,Ban son sharri yaushe yayi wayon da za Gane wata Gadara,nace gashi Nan Dariya ma Sai yaga dama,ko da Muka Isa gida da me Gadi muka gaisa na bashi 3k kyauta Yana ta godiya,Me Aikina itama Jiya ta dawo daga Kauye,Dattijuwa me hankali da ita ga iya Aiki ga nagarta.

 Gaisawa Mukayi ta koma dakinta, Fu'ad shi ya dakko Jaririn da Hand bag dita dama sanye nake cikin wani lace fari Kar,Shi Kam Danyar Gezna ya Sha wata Grey ya zuba kyau kamar yau aka daura Auren,sai kallon gidan nakeyi da Furniture an canja komai, gida ya Sha gyara Haka,

  Muna Shiga bedroom dinsa na Sha mamakin yanda aka wani shirya Duniyar jariri,da Dan Gadonsa shima fari saman gadon wani Net ne daga ciki kayan Wasa ne suke Lilo a saman Net din iri iri suna kawo wuta kala kala yanda zai daukewa yaro hankali yayi ta Wasa,daga Kan gadon Kuma Teddy ce iri iri gasu nan,Kai Iya Bed din ya ishe ka Bata lokaci wajen kallo.

 Mairo na Bawa shi ta Masa wanka na sa Masa fararen kayan baccinsa masu Dan kauri Yana ta wutsil wutsil da kafafunsa, Fu'ad ya fito a wanka,na bawa Fhudal Nono yayi baccinsa, Fu'ad Yana Gama Shiryawa ya karbe shi yace Jeki Dan Allah kiyi sauri Ni kina Bata min lokaci sabon Ango Ana ta Masa Yanga,Kwantar da shi yayi a Gadonsa ya masa Addua sosai ya kashe abubuwan da suke kawo wuta me kala kala a bed din.

    Daga wanka na fito ko Mai Bai Bari nayi ba ya zare Towel din ya maida shi Bayi ya dauke Ni sai saman Bed dinsa,ya Shiga Lailayani Yana Sarrafa Ni yanda yake so,Albarkatun Kirjina yake Wasa dasu Nima gaba Daya na susuce Masa Ina Masa abububuwan da zasu da shi cikin farin ciki,Yana tsotsar Nipple Dina sai Kawai ya wuce da shanyewa yaro Nononsa,Dagewa nayi na susuta shi Nima ya haukace gaba Daya kamar mayunwacin Zaki Haka ya koma lokacin da ya samu damar Shigata,sabo da an Dan Dade Kuma na Sha gyara na matse sosai har zafi zafi naji Amma Kuma nayi Enjoying fiye da tunani,sai naji Kamar ban taba Jin dadi irin na yau ba shima Haka,Kalaman kauna na Sha su Haka muka kasance cikin farin ciki har karshen Daren,Muna Kwance muna Hira ta soyayya Ahmad Fhudal ya Farka ya fara kuka, Fu'ad ne ya tashi ya kunna Masa Wutar abubuwan wasansa yaga suna Lilo a hankali ga wuta dark blue,green,red suna kawowa,Sai ya daina kukan yayi Shuru Yana ta faman kallonsu Yana ta juya idanuwa,shi kadai sai ya Kama bangale Baki Yana dariya,Na leka nace ya samu abin Yi,Yana ta kusurkusur dinsa Yana kallo har ya koma baccinsa,ya kashe Masa abin Wasan,muma makale juna Mukayi sai bacci ya tafi da mu.

 Haka muka kasance cikin farin ciki Ina zuwa makaranta ta,shekara nayi muka tafi aikin Hajji,daga Nan muka wuce yawo kasashe,sai da hutu na ya Kare Muka dawo Muna ta goge duniyar mu da tsinke love Iya love,kwanci tashi na Gama makaranta saura University Haka su Rabi ma da Hajara da Saude duk Muna zumunci sun waye sun goge,a Scotland ya Nemo min University lafiyayya muka tafi tare shima zaiyi PhD school dinmu Daya,Ga Ahmad yayi wayo sosai na yaye shi,Amma ban samu ciki ba sai da na kusa Gama Degree,Wannan cikin Bai bani wahala ba,ko da nazo Haihuwa ma da sauki a can na Haifi 'yata mace lafiyayya kyakyawa itama kamarsu Daya da Fu'ad sak, yana ta min tsiya bani da karfin jini,Ranar Suna taci sunan Umma Aisha,muna ce Mata Afnan,Muna Gama karatu Muka dawo Nigeria gaba daya,munyi wani uban kyau na Kara gogewa na waye na Zama wata irin Yar gayu ta kirki,ba Wanda zaice Ina da aure ma.

Afnan tayi wayonta muna zaman mu cike da so da kauna.

Yau Weekend muna Fu'ad Yana gida Yana kwance a center carpet,Na kwanta Nima kaina Yana saman kirjinsa a kwance,Fhudal Yana Zaune a saman cikinsa ita Kuma Afnan ta zauna Wai a Kansa ya jawo ta ya maidata kusa da Fhudal yace duk ku karasa Ni ku huta,yanzu Dan Rashin Imani harda ke,Ina chat a waya Ina Masa dariya,Yace Fhudal gidan Umma zai koma can ta can zai na zuwa school,Ya dinga murna Yana tsalle,yace sai anyi Hutu ya dawo Yana ta Murna,sai kuwa ga Islam da gudu Suka tafi Wajensa duk ya kwashe su ya tafi dasu, Fu'ad yace karka dawo dasu Dan Allah daga gidanka ka kaiwa Umma su Zan kawo musu kayan su gobe,Islam yace to Suka tafi.
Daukana yayi yace ke Kuma mu shige daga ciki  Danna Miki na Uku,Dariya nayi nace Haba Ina da Aunty Samha wlh ba Yanzu ba sai Nan da 5yrs yace Ni Kam nayi ta Shan harkata,Bedroom muka Shiga da kafa ya tura kofa ta rufe bam.




  ALHMDLLH

INA MATUKAR GODIYA FANS MUSSAM MASU SHARHI,….

ASMABAFFA
COPY BY ZAINAB BUTALAWA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13

Leave a Reply

Back to top button