DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

Ban San me ya faru da Ni ba Amma sai nayi murmushin karfin Hali nace jinin Haila na fara jiya da wajen Asuba,Amma sai ki Bari ki Bata musu gado baza ki fada ba a Baki kunzugu ba,Bayi na fada dake Iya ta koya min tsarki da ruwan zafi ko shiga ciki a zauna sai kuwa na hada na Shiga da kyar Ina kuka na dinga gasa kaina sai da naji sauki da dadin jikina sannan nayi wankan tsarki nayi brush da wankan sabulu na fito na Iske su Rabi sun wanke Bedsheet a Injin wanki sun shanya,A boye nayi Sallah Kuma Allah ya taimake Ni jini ya dauke,tunda abin ya faru walwalata tayi baya Umma da Nene suyi ta tambaya ta ko ba lafiya ba,nace lafiya nake har na manta na hakura na saki raina,ban sake sanya Fu’ad a Ido na ba har kwana uku naji dai Nene tace yaje Kano wajen Hajiyan kano,Ana jibi zamu tafi Kauye ya dawo na dinga murna ban San dalili ba sabo da tun daga ranar Da Yan fashi suka hada mu nake Jinsa har Raina,ta wani bangaren Kuma Ina Jin haushin abinda ya faru tsakanina da shi Kuma na kulle a Raina sai na nuna Masa naji haushi bazan ga kwarjininsa ba,fata nake Allah ya hada Ni daga Ni sai shi na cashe Masa nayi Masa tas.

Inda ake ajiye motoci na dinga zuwa ko zamu hadu idan zai Shiga mota Bamu hadu ba sai da Yamma lis na ganshi ya fito cikin wasu kananan Kaya sun Masa kyau karshe sai faman kallonsa nake Yi, Driver ya Bude Masa gidan baya ya kame tare da Bude Jarida zai karanta da Sauri na zaga ta inda yake ta Glass na Shiga Yi Masa zancen kurame Ina nuna Masa da Hannu,kasa fahimta yayi me nake nufi ya sauke Glass kadan yace mene? Nace au nufinka ka manta? Ka manta abinda ka Yi min? Sabo da kar Driver ya gane me nake nufi na furta Ka Gama facakarka kayi watanda ka balangwaje kace baka tuna ba?Baki ya tabe tare da furta bana gane hausarki ta Yan kauye,Na nuna kaina da yatsa nace Ni,na nuna shi nace Kai na sake nuna cinyoyina nace zafi wannan,abinda ke tsakiya jini,zafi masifa zugi da da balbalin bala'i,Ni kin fadawa kowa,boye sirri Wai Nan fada nake yanda Driver bazai gane ba,Kuma Fu'ad har shi Basu fuskanci kan zancen ba,ya daga Glass dinsa sama yace driver muje,Ina kallo ya tafi na saka kuka ganin Sam Bai gane ba to ko Aljani ne ban sani ba.

Da dare Ina part din  Umma Na tayata girki muna Palo Fu'ad ya shigo su Rabi ma suka shigo muna zaune Yana ta Jan Tsaki shi a dole sai Umma ta Kore mu sabo da shi ko kannensa basa zama Inda yake zaune,Ina Zaune Wayata tayi kara,da Sauri na duba ganin Hajara ce kawar mu na daga,Ina cewa Shalo.... Hajara, Fu'ad ya kusa Dariya sabo da shi dai Shalo din Nan tawa tana bashi Dariya,Nace Shalo....Shalo...Hajara...Shaloooo... kina jina? Hajara tace ke shegiya Rumaila Affanki ya zama Dan Daudu wallahi yanzu doya da kaji yake soyawa a Tasha,Kuma Yana Nan Yana daura zani Yana rataya jaka,sunansa Yar Shila,nace Allah Hajara? Hajara tace Alqur'an ki tambaya kiji,tunda naji a bakin Hajara magana ta tabbata,Nace to Allah ya shirye shi na kashe waya jiki a sanyaye na kalli Rabi nace Affa ne ya koma mace,shi yace lallai sai ya koma mace sabo da Haka ya zama Dan Daudu,su Rabi suna tafa Hannaye suka ce Sallallahu sanyi Kalau yanzu Affan naki? Nace sunansa Yar Shila ma,da ace Ina biyewa bacin Rai da tuni na Dade da yin mushe a daki, Ni dai Kwana Nan masifa ce take ta samu na zanje na bawa Fadila Hakuri na Bata dubu biyunta ko hakkinta ne yake tambaya ta, Fu'ad Yana ta kallon kauyencinmu ya gaji yayi fushi ya fita akan Umma Taki korar mu Yana zaune a dakin.

Ai kuwa har Dakin
Fadila naje domin na Bata Hakuri,na sameta a saman gadonta har kasa na durkusa, lokacin Fu’ad yazo zai tambayi Fadila wanne Kalar kayan daki take so sai yaji Ina magana sai ya tsaya a jikin Kofar Yana saurara,nace Anty Fadila Dan Allah kiyi Hakuri ki yafe min abinda na Miki Uwata kika zaga shi yasa nayi Miki Haka Nima sabo da na rama kiji haushi kema Kamar yanda naji,kin San Uwa mahaifiya ba Wasa bace,Babu Wanda za a zagi Uwarsa a zauna lafiya, Mari ta zabga min har biyu Tace ke kin Isa ai Allah ya Toni asirinki kika ce ke Yarinyar Yan fashi ce shi yasa harda fyalle wuka wlh sai an dau mataki a kanki jaka Kawai Yar fashi Yar kidnapping,Wallahi Tallahi Billahillazi la ila ha Illahuwa ko Qur’ani aka bani zan dafa ban taba fashi ba yanda akeyi ban sani ba,Kawai dai Baki shi ke yanka wuya barazana nayi miki kiyi Hakuri….Hannu ta daga zata dukeni Fu’ad ya shigo yace ke mene Haka? Baki da hankali Fadila,Ya….hannu ya daga Mata ban son Jin komai naji komai,ke wacce mahaukaciya ce Fadila? Baki da fahimta ne? Wannan yarinyar ce zata Yi wani fashi,hankali ne da ita? Ki kalle ta shekarunta Nawa? Yarki ce da Zaki dake ta? Wlh kar naji Maganar Nan ta fita sai kin Gane kurenki,Tsawa ya daka min tashi kifita da shegen surutun ku kuke furta Maganar da za a kashe ku, da sauri na Mike na fita ko Maular da Muka ce zamu je tsoron Yan fashi ya jawo mun fasa,Saude ce Tace Wai baza muje Maular ba? Nace ke bala’i Yana ta samu na zanje na karowa kaina masifa gaskiya mu tafi gida na gaji.

Naila ce da Khaleesat suka Tara Mana kwancen Kaya Kudade da Alheri Muka samu iri iri,Ana gobe zamu tafi Naila tazo wajen Nene muma muna palon na Mike nace Bari na tashi naje fatata ta gane kurenta,Nene Tace au wankan ma shine fata zata Gane kurenta? Dariya Muka Yi gaba daya har Naila,Na Mike na tafi abina.

 Washe gari da sassafe Muka yiwa Wanda muka samu Sallama Abbi yasa Driver ya kaimu Tasha ya biya Mana kudin mota aka Bamu dubu goma goma ga kayan sawa Dana shafawa da sauran abubuwan mun samo Sha Tara ta arziki,Zamu shiga mota kenan sai ga Fu'ad ansha fited suits Ruwan Toka yayi kyau da alama fita zaiyi,Saude ta rera Wakar Kauye Tace.... munai maka sallama Dan Uwa Dan Uwa a cikin wannan Rana...... .. Ashe Fu'ad a wani Kauye yayi Service yaji Yan matan kauyen suna wannan wakar,hannu muke daga Masa Muna Bye bye da Waka muke hada Baki.... Assalamualaikum Dan Uwa Dan a cikin wannan Rana.....Shima ya dago Mana hannu Yana bye bye yace da wakar.... kar ku barta da yunwa da yunwa a cikin wannan Rana..... Mamaki ya kama mu Yan aiki sai Dariya sukeyi abin mamaki,Rabi Tace da Waka ....mu gidan mu ba yunwa sai Bredi sai shayi sai abincin turawa.....tafiya yayi abinsa ya barmu karshe muma Muka shiga mota Driver ya kaimu tasha ya biya kudin mota lafiyya Inji Abbi.

Sai Da Rana sannan Muka Isa kauyenmu,dama mun sanar da gida zamu dawo,Direct gidan Affa na wuce na ganshi daure da zanin Shadda dark Blue Yana ta karairaya a Kofar gida,a Haka na gaida shi da Maganar matansa yace Oh gantali dadi an dawo Ashe? sai ki koma wajen Uwarki inda kuka Saba yawo,nace dama gaidaka zanyi,yace na gode sai ayi gaba Umma ta gaida Aysha ya furta Yana shanye hannu daya shi a dole mace,tafiyata nayi gidan Iyata,Da murna ta tarbe Ni har kishiyarta da mijinta tare da yaransa suna zamansu lafiya gwanin sha'awa,Bayan na huta na bawa iya kudin tare da nuna Mata kayan da muka samu tana ta godiya,nace Iya kyau dai kiyi zamanki a Nan karki Bari a sakeki kinga Ana zaune lafiya,Baki Iya ta tabe tace wlh sai idan banga harka ba dole na barshi bana son tsimulmula sai dai a baka ci Kawai da Yar sutura Sallah ko anko baza a baka kudi a hannu ba ka fantama bashi da maraba da mazajen Dana aura,Haba Iya Dan Allah ki dinga godewa Allah,da Ubanki nake godewa ke kin Isa kice Zaki min nasiha,Shuru nayi Kawai na kyale Iya.

Yanga Muka dinga Yi a kauyen Muna saka kayan da muka samo na birni,mun zama wasu abin kallo sai kallon mu akeyi kullum muyi ta bawa kawayenmu labarin birni,wani farin jini na Kara samari sai binmu sukeyi,Ina Zaune kusa da Iya da dare Bayan Mun Gama cin tuwonmu yaro yayi sallama,Muka amsa yace Wai Rumaila tazo Inji Jauro,Jauro saurayi nane tin farko ya Dade Yana so na ganin naje birni na Kara gogewa shike Nan ya sake haukacewa a kaina Kuma Jauro kyakyawa ne sannan cirani yake zuwa Ibadan ya waye kamar ba Dan Kauye ba Haka yake,Sai Dana Gama Yanga ta sannan na fita wajensa ya siyo Mana rake muna Sha muna hira,santin rake yasa nace a.a..a Birni ba a shansa Haka sai an yanka da wuka kanana na,Yan gayu ma da cokali me yatsu suke cokala suna sawa a Baki,Jauro yace Gashi rake shi wanke Hanta yake tas Yana Kara karfin gani,Na karasa Masa da karfin ji ma,Wai ya soyayya ta ne?tana Nan kuwa?a wanne mataki Nake? Dake Ina Jin radio idan Ana fadar Yanayin weather kullum da safe,Nan take na bawa Jauro amsa da cewa kana matakin 40°c Selshiyus na furta wani iri sabo da ba Ilimi,Jauro yace gaskiya tayi kadan ko dari ban Kai ba? Nace ae Ina laifi ma kayi Hakuri Haka sabo da akwai samari da yawa Suma Kuma dukan su akwai matakin da suke shine a cikin 100° na Raba muku ka samu 40 ai kafi kowa soyayyarka ai tafi raken Nan Zaki.

Mun Dade muna hira da Jauro sannan ya tafi gida Bayan ya bani dari biyu.

 Tunda na dawo bani da Aiki sai tunani da ya zan koma can naji dadi Amma ba dama,Haka idan Ina tuna Fu'ad sai farin ciki ya kamani Ni kadai nake zancen zuci Ina murna cike da farin ciki, lokacin Kuma Fu'ad shi ya Gama Shirin tafiya Germany wata uku zaiyi ya dawo Abbi ne ya tura shi sabo da Haka kwanan mu biyu da tafiya shima ya tafi turai.

Tunda na dawo lafiya Muke zaman mu a gidan Mijin Iya Yana so na sosai,aikin gida Kuma Ina tayasu sosai har wanki da guga nake wa Mijin Iya,na dauke shi kamar Uba na,watan mu Uku da dawowa daga Birni katsam na fara zazzabi Amai tashin zuciya inyi ta zubar da yawu,Kirjina ya sake cikowa nayi mugun haske nayi kiba da kyau,gaba daya kalar me ciki ta bayyana a jikina anyi maganin malaria har an gaji,Iya takan ce Ni dai na gaji da wannan Amai da zubar da yawu gaskiya Rumaila Ina da ja a kanki ,Iya me kike tunani? Dan Allah Iya ki daina zargina Haka nake furtawa Iya kullum, Watarana wata kurma Bata jin magana tazo gidanmu ta shigo da Sauri Ina yiwa iya dakan daddawa naji Kurman Nan ta cikwikwiye Ni tana zancen kurame tana masifa tana Nunawa mutanen gidan Iya da kishiyarta cewa ciki ne dani,duk Basu gane ba sai da me shayi Mijin Iya ya shugo Kurma ta Masa nuni ya fahimta tare da sanarwa Iyata,Iya ta rufe Ni da duka ta ko Ina ta Jani dakinta tana kuka tace fada min waye ya Miki ciki? nace Ni fa Iya bani da ciki ki kaini asibiti ma a gwada ni.
 Yamma ta Riga da tayi ba damar zuwa asibiti dole sai gobe da safe,da sassafe Iya ta shirya Nima na shirya har da saka Hijab Kato Muka fita da Iya zuwa Asibiti.

AsmaBaffa
????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.

     NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861, ASMAU GARBA MUHAMMAD,GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39.

             11-15

Official

By
AsmaBaffa

PAGE NAKU NE

REAL MAMAN WALEEDA
SAMEERAN GAYA
SADEEYAN GAYA

   Ina ta kuka har Muka je asibiti Karami Dake kauyen Iya bako sallama ta fada ciki Tace Likita so nake ki gwada min yarinyar Nan ko ta samu ciki,Likita ta Mika musu Kwalaba Tace tayi fitsari a Nan Hajiya,Iya ta Jani inda aka tanada sabo da hakan a gaban Iya nayi Fitsarin a cikin Kwalaba aka bawa Likita,Nan take ta gwada Tace Alhmdllh Baba kiyi murna yarki tana da ciki na wata Biyu da sati Uku,Nan take na hau kuka Ina rantsuwa Ina karya ne Iyata wlh Karya ne aje asibitin birni a gani,Iya ta fashe da kuka ta fisgi Hannuna muka koma gida,Shima Mijin Iya jikinsa yayi sanyi,washe Gari da Sassafe Iya ta daukeni Muka tafi asibitin cikin garin Jigawa ba Bata lokaci Iya ta bada kudi aka Yi sau uku a asibiti daban daban aka tabbar Ina da cikin Nan,Har scanning aka yi,Iya Bata sake kulani ba har Muka koma gida,da dare nace Iya yunwa nake ji,Iya Tace kije Wanda ya Miki ciki ya Baki mana Yar iska, shegiya,gantalalliya,dama abinda Kika je Yi kenan,duk Tarbiyyar Dana Baki Rumaila,hakazaki min? Yanzu kowa zaice Ni na na lalataki,ga Babanki baya kaunarki bazai iya rike ki ba,Rumaila kin cuce Ni Rumaila Iya ta fashe da kuka Nima na rushe da kuka.

 Iya tana kuka Tace fada min waye ya lalata min ke Rumaila? Nace Iya Dan gidan me Gidan da muka je gidansa a birni Fu'ad shine Iya ya sace Ni Ina bacci ban sani ba Nima farkawa nayi na ganni a dakinsa sannan ban sake sanin Ina nake ba sai na sake farkawa na ganni a dakin da aka sauke mu Iya,da zamu taho na Masa magana ya nuna Bai sani ba Sam,Iya Tace Ina zai nuna ya sani tunda ya cuce mu ya Shaka Miki hodar Iblis,nace Iya duk abinda na sani shi na fada Miki wallahi abinda ya faru kenan Dani Iya,Amma Iya abin Haushin idan na tuna shi sai naji Wani sanyi da farin ciki,Iya Masifar sonsa nakeyi Ni abinda ya min ma bana Jin Haushinsa idan naji Haushinsa Ina tuna fuskarsa kyawunsa da dadin muryarsa sai naji farin ciki,Iya Ina sonsa....Mari iya ta dinga watsa min tana kuka sannan ta rufe Ni da duka sai da Kishiyarta da mijinta tare da yaran gida Suka CeCe Ni da kyar,Iya tana Huci Tace gobe da Sassafe idan na ganki a gidan Nan Allah ya Isa ban yafe Miki ba Rumaila,bana kaunar ganinki kusa Dani kiyi nesa Dani tun kafin na Tsine Miki Albarka.

Ina ta kuka duk gidan ba Wanda ya Goya min baya,shima Mijin Iya yace da Baki Kore ta ba ma Wlh sakinki zanyi bazan rike Yar iska ta gurbata min tarbiyar yarana ba,Kishiyar Iya tace wallahi kuwa taje can wajen Ubanta ko ta koma duniya can bariki inda ta kwaso abinta.
Kuka nayi shi har na gaji Haka na kwana a zauren gidan ban iya ko rumtsawa ba,Gari na wayewa na silale da kayana kaf Iya ta Watso min na kwasa, idanuna a kumbure da kyar nake gani na nufi gidan Affa Ashe zance ma tuni ya watsu a Gari Rumaila tayi cikin shege a Birni har Affa yaji labari Yana kofar gida Yana sharewa daure da Zanin Atamfa saman wata jallabiyarsa Yana ta rera wakokinsa Yana hango Ni yace karki karaso kina zuwa Zan karya ki,nasan Halinsa sai na nufi wajen kawuna yayan Iya shima ya Koro ni har gidan su Rabi da Saude naje Suka ce su sun daina kula Yar iska Kar na Jaja musu a Gari a dinga zaginsu,Nace Rabi Dan uwanki ne fa ya min ciki Rabi tayi shewa Tace wannan yan gayun ne zasu rike ko yatsanki Rumaila,kazama talaka irinki me zasu ci da ke,Haka Suka fada min maganganu masu zafi,Manyan mutane sai Tsine min akeyi har a masallatai na Gari sabo da jahilci .

Duk Sallah idan an Idar sai dai kaji liman yace wannan yarinya Rumaila da tayi abin fada a garin Nan ta kwaso cikin shege a birni Allah ya tsine mata Albarka Ana amsawa da Ameen.
Gidan Iya da Muka Bari Wanda ba kowa ciki sai tsofaffin kayan kitchen na iya sune kawai a gidan ga gidan ya kusa rushewa na tabbata da kyar zai tsallake damunar da zata sauka,Haka na Samu na tura yaro ya kwaso min ragowar kayana tas a wajen iya na share gidan fes na gyara komai na samo wata tsohuwar tabarma na Shimfida a kasan dakin a Nan na kwanta,tun daga wannan Rana na tsaida Sallah naji masifa da jarabta Iriri ai dole na tsaida Sallah ,Addua nake kullum Ina kaiwa Allah kuka na,Abinci ma Sai dai naje nayi bara a makwafta,Haka a zageni a bani na karba na cinye,kudin sabulu Kuma gona nake zuwa nayo ciyawa na siyarwa masu dabbobi Naira Ishirin talatin a Haka nake rayuwa na fita a hayyaci na gaba Daya,Ko Iya ko Affa Babu Wanda ya tausaya min bare Yan Uwa ba Wanda ke kulani har Yara ma jifa na sukeyi suna tsokanata da wakar tayi cikin shege a Abuja,sai gaba Daya sunana ya canja daga Rumaila sai dai tayi cikin shege a Abuja.

Ruwa na fita Ebowa da Botiki na Ina tafiya Ina tofar da yawu,zuwana bakin Rijiyar wani Amai ya taso min na koma gefe na shiga sheka Amai ba ji ba gani,Mutane da Yara suka taru a kaina Ana min ihu tayi cikin shege,na rigada na Saba sannan Ni ba komai ke bata min Rai ba sabo da Haka na share su na ebi ruwa na nayi tafiya ta abina,Su Rabi ma Gaba dayansu sun guje Ni ko a Hanya basa min magana su ma har Tsokana ta sukeyi suna cewa Ashe Yar iska ce Ni Basu sani ba abin da ya kona min Rai kenan Amma bani da bakin magana Babu abinda zan Kare kaina da shi Kuma kowa idan Haka ta faru da shi dole a guje shi banga laifinsu ba,Hajara ce ke Dan sassauta min Watarana har abinci take kawo min daga gidan su.

 Bayan Tafiyar Fu'ad Germany Bai dawo Gari ba sai after 3months lokacin bikin Fadila saura 3weeks,ya Kara wani uban kyau yayi fresh,Shima Abbinsu yayi tafiya zuwa Dubai Yana dawowa yace ya kamata mutum ko uku ne a gidan Nan su shirya suje Kauyen Yan uwan mu wato gidan su Rabi,duk sha'ani ko abin bakin ciki suna zuwa Amma su ko mutum Daya Bai taba zuwa ba,Sannan Ina son yarinyar Rumaila mutuniyar kirki me tarbiyya a je a gaisar da iyayenta,Tunda Abbi ke magana ba Wanda ya amsa sai ma kowa cewa yayi bazai iya zuwa kauye ba,yasan dama baza su je ba,Sabo da Haka kawai yace Bari na zabi Wanda zasu je a bisa Umarni na,Yana furta Haka Fu'ad Dake kusa da Abbi ya mike tsam da niyyar barin Palon sabo da Kar ma ace da shi,sai kuwa ya tsinci Muryar Abba yace ka yiwa kanka Dan Momy  harda Kai za aje, wani yaji ya sha... shiiiiii Yana tsuke Dan Bakinsa me dauke da jajayen lips masu taushi,Sai Nene,Nene Tace Alherin Allah ya Kai maka Abbin Yara sai tafiya ko da kafar katako,Umma kuwa da kanta tace zanje Abbin Islam mu ukun ma mun Isa,Sai mubi flight Abbi yace akwai Wanda zasu dauke ku da securities har kauyen.

Haka kuwa akayi Bayan An bugo Iv na bikin Fadila da kwana biyu  Umma,Nene da Fu'ad Suka Shirya Ranar Saturday da safe suke wuce a flight,Ko da Suka sauka a Jigawa state Already Motoci Uku masu tsadar gaske Sunyi parking Daya motar Fu'ad  ne shi kadai ya shiga sai faman fushi yake Yi an Masa Dole, Umma Tace mota daya ta ishe mu bana son kallon Nan na mutanen Kauye,ai kuwa mota daya suka shiga.

 Har cikin kauyen motocinsu Suka gangara a hankali,suna ta kallon kauyen Fu'ad a ransa yace Dole yaran Nan suyi jahilci no wonder dama akwai kauye Haka a kasar Nan Allah sarki na tausaya musu suna rayuwa cikin kunci Allah mun gode maka, Ni kuwa Rumaila yau naje gona nayi ciyawa da yawa na siyar na samo itace da yawa na siyar har dubu Daya da dari biyar na Samu yau bazan je makwafta neman Abinci ba sai farin ciki nakeyi,Wata Kazata Dana ke kiwo Wanda Kawu ne ya bani ita gashi Bata yin Yaya juya ce,sabo da Haka kwadayin me ciki yasa na Samu na yanka kazar katuwa da ita na gyara ta a gidana Ni Daya na soya ta Tasha Maggi tayi Dadi sosai na zuba a kwano na rufe abata a dakina.

 Taliya na dafa da miyar jajjage Lallai yau Dadi zanci,sabo da Haka na Kara gyara gidan fes da shi kana gani kasan akwai Tsafta a gidan Nan ko Ina fes Kal Kal,wanka nayi tare da wanke gashin kaina na shafa Dan Vaseline Dina sama Sama sabo da ana zafi,Vest Fara tas na saka tare da jean skert Wanda a gidan Su Fu'ad Khaleesat ta bani,Tabarma na Shimfida a jikin bishiyar tsakar gidan na kunna wayata Ina Jin gidan Radio Kamar yanda na Saba,gefe Kuma ga Guava manya manya a plate guda biyar Ina yankawa da wuka Ina ci,idan Ina cinta bana tashin zuciya bare Amai.

Su kuwa Su Umma kwatancen da aka musu Suka bi aka nuna musu har gidan su Rabi,ai Saude Hajara da Rabi suna Jin labarin mota a kofar gidan su Rabi Yan Abuja sun Zo da gudu Suka dawo gidan su Uku,Hajara Bata San su ba Tace Na Shiga Uku Kunga Bature da Shadda yayi shigar Hausawa,Rabi Tace banza shine Yaya Fu'ad din ai ga Umma ga Nene,Hajara Tace Yasin Nan gaba ko da tsiya sai Baba ya barni na biku Nima ko Dan wannan baturen ai naje inyi ta kallonsa,Rabi tace to shine fa Rumaila take wa karya Tace shine ya Mata ciki,Allah ya tsinewa me karya Kamar wannan me zaiyi da ita cewar Hajara,Saude ta tabe Baki tace Wai Dan taga a Kauyen Nan ana cewa tafi kowa kyau gata Fara shine take hada kanta da wannan,a can fa Baki ga shishigin data dinga Yi ba tana ta cusa Kai Rabi Tace Kuma ba kwar jini ba ita tasan inda ta kwaso cikinta yanzu haka ma Is Ilu me gadi ne yayi Mata.

 Sai da Suka Gama zagin Rumaila tas sannan Suka fada gidan Suna washe Baki lokacin tuni su Umma sun shiga gidan,an sauke su ana rawar jiki,bayan sun gaisa da masu gidan sannan su Rabi,Umma Tace Rabi Ina kawar taku fa? Baki Rabi ta tabe tace ai tayi cikin shege mun daina kulata tana Nan da katon cikinta,Salati Umma da Nene Suka saki tare da furta Rumailan? Saude Tace ita fa Dawowar mu da wata uku ta Fara laulayi,Fu'ad Dake zaune gefen Momy ya Bude manyan idanunsa da mamaki Yana ganinta Saliha Amma ta aikata Haka Amma sai yace Jahilci ne yasa Bata San Mene Zina ba shi yasa Bari yayi Mata Uzuri,duk abincin da aka kawo musu Fu'ad Bai ko kalle shi ba,dama Umma tasan bazai ci ba sarkin Iyayi su dai furar su lafiyayya Suka Sha har pure water sun Sha,Nene taci shinkafa da miyar da aka kawo musu,Umma Tace Ga Iv dama Muka kawo na bikin Fadila Kuma bamu taba zuwa ba sai yanzu Abbi yace ya kamata a kawo muku ziyara,Baban Rabi da Mamanta tare da wasu Dangin su biyu Suka dinga godiya da cewa Inshaallah zasu Zo,Fu'ad ya zaro kudi Yan Dubu dubu Yana bawa kowa har su Rabi sun samu Dubu biyar biyar.

Umma tace ku rakamu Inda Rumaila take mu gaisa da ita da Iyayenta,Rabi tace Yasin ko mun raka ku baza mu Dade a wajenta ba Kar ace muma mun Zama Yan iska,Uwaku ku Baku San Kaddara ba cewar Umma.

Har gida na Rumaila suka raka su Rabi suka shiga Suka Iske Ni na tasa goba a gaba Ina ta ci gidana fes Haka Babu alamar ciki a jikina Kuma nayi wani haske nayi kyau,Dariya Suka dinga Yi min ban kulasu ba Suka ce to masu gashi har gadon baya sai a rufe ga Umma da Nene Nan sun Zo zasu ganki,Haka kawai naji wani farin ciki ya lullube Ni na washe Baki nace Dan Allah? Tunda Mata ne ai ba sai na lullube kaina ba zafi ne ya dameni kice kawai su shugo,ai kuwa su Rabi suka juya tare da cewa Umma Ku shugo tace anyi sa'a Bata tafi Gona ba Wai Dan su Bata Ni a wajen su Umma ai kuwa Har Fu'ad aka shigo da Sallama mamakin ganinsa ya kamani yayi wani uban kyau komai fari ya saka Shaddar ta Masa kyau,kwarjininsa yasa naji wani Iri na manta ma ba dankwali a kaina dama bamu Saba daura dankwali ba,gashi na ya zubo har tsakiyar bayana Baki wuluk da shi,Surata ya karewa kallo a boye Kamar waya yake dannawa,tabarmar na gyarawa su Umma shi Kuma na kawo Masa kujera ta zaman gindin Murhu,a Nan yayi magana Yana tsaye yace Miya zanyi ko tuwo da Zaki bani kujerar Mata na zauna,kaji yaro da Iyayi Umma ta furta,na kalle shi ya galla min Harara na dauke kaina cike da kunya nace Nan kauye ne irin wannan gare mu,Su Rabi Suka Fara Dariya harda cewa gare ki dai ai ke da wa? Share su nayi na durkusa na gaida su Umma Ina ta cin goba Dan Kar na tsaya na Fara tofar da yawu ko Amai,shima na juya na gaida shi da kyar yace lfy,su Rabi suna ta gulma ta,Allah ya rufa min asiri na shiga dakina Na ciko wani katon Tire na zubo musu taliya da miyata tana ta kamshi,kazar Nan gaba Daya Na zubo a plate me Dan kyau na kawo na ajiye gabansu,dama watarana indai Ina da kudi pure water nake sha,saura guda hudu na kawo musu shima.

Mamaki ya Kama su Rabi Ina na Samu kayan Dadi Haka? Umma Tace Inye Ashe Yar tawa Dadi kawai take ci,dariya nayi kadan Nace Kawu nane yake bani Ina kiwatawa shine ita Kuma wannan juya ce Bata Haihuwa na gaji da asarar Abinci na na yanka ta na huta,Umma tace baza muci ba Alhmdllh,rokonsu na Fara Dan Allah Umma kuci nasan kunfi karfinta indai Baku ci ba kawai Ni Baku Zo min ba,dariya Suka Yi Suka dauki cokali suka Fara ci Suka ji girki me shegen Dadi dama na gidan su Rabi Babu Dadi shi yasa Suka kasa ci,Fu’ad ya kalli su Umma sun wani zage sai ci suke Yi,Umma ta Mika Masa spoon Tace kaci Mana,Su Rabi suna ta dariya a gefe Wai sun San ma bazai ci ba,Da mamakinsu sai Suka ga ya karbi spoon ya Fara ci shima yaji Dadi sai ma ya wuce su Umma dama ya fisu Jin yunwa,baici komai ba,Nene Tace Ina Iyayin? Sake Bata fuska yayi Yana cin abincinsa,Har Naman kazar yake ci iya cinsa Haka su Umma ma Nene sai Santi take Yi,Tace ke Kam Yar Nan Wanda ya Aure ki yayi dacen me iya girki,a Ina Kika koya ne Haka Kamar wata me dafa Abinci a restaurant ko gidan Sarkin garin Nan?Dariya akayi har Fu’ad sai da ya murmusa,Nace ai Nene dagewa nayi na koya wajen Iyata,kin kyauta cewar Umma,na kalli su Rabi na tabe Baki nace wasu kuwa sai shegen gishiri a Miya.

Hand bag dinta me tsada ta Bude ta Mika min IV tace gashi bikin Fadila kizo Mana fa,nace to Allah ya kaimu,kazar Nan duk Fu’ad ya kusa cinyewa ko Ni banci ko dandane ba,Ina ta kallo Ina hadiyar yawu Ina sa Rai ko zai rage min Amma ganin Kamar Ina yawan kallon ragowar kazar Dan mugunta sai yace Umma Miko min ledar nan,Bata kawo komai ba ta zaro Leda baka sabuwa ta bashi ya juye kazar tas a ledar ya mike tsaye yace muje mu gaisa da Iyayenta sauri muke,Umma Tace wannan wanne Iskanci ne Dan Momy? Kamar Bai ji ba,Ni kuwa hankali na ya tashi sabo da Iya Tace idan na sake zuwa inda take sai ta Tsine min,ga Affa na ya Zama Dan Daudu yanzu a kasuwa ma yake soya kaji da Doya da kwai harda waina Masa da Miya.

Ya zanyi Dole na shiga daki na zura katon Hijab na fito Muka tafi Su Rabi suna binmu a baya sai gulma ta sukeyi suna dariya,Gidan Affa Muka je munci sa'a kuwa dawowarsa daga kasuwa kenan Yana tafe yana karairaya Kugunsa daure da zanin Shadda ga Kuma singlet ya saka,Yana tafiya Yana wulwula ludayin Miya Kamar mace harda Rike kugu,Nace to gashi Affa na Kira shi,ganina da Baki Bai koreni ba ko ya zageni Wanda nayi mamakin hakan,Kallon bakin yayi yace Marabanku dai bayin Allah kune tafe Haka cikin Rana tafatsar fatsar,Habarsa ya rike Yace ikon Allah Ashe tare kuke da Yan maza ke Rumaila shigo da su,Su Umma suka tsaya suna kallon ikon Allah,kunya ta lullube Ni Raina ya baci idona ya cika da kwalla ta da kyar nake dannewa,Su Rabi kuwa sabo da Rashin mutunci sai ma cewa sukayi 'yar Shila ya doyar da wainar?yace Tana can na barwa yarana kafin anjima na koma garin Rana zamanin Nan wa zai Bari Rana ta dinga dukan fatar mutum tana Masa Illa wannan sai maza.

Umma tace Rabi Baku da kirki wlh Rumaila kawarku Amma kuke Mata Haka?Mahaifinta ne fa,Mahaifi ai Mahaifi ne wlh Sam Baku birge ba Kun Bata wayonku,Ana Haka sai ga Baban Rabi Dana Hajara zasu je wani wajen Ni kuwa dama Ina mutunta su na dauke su Kamar su Suka Haife Ni sabo da kawayena,Har kasa na Duka na gaida su,karshe Nima Direct nace Zubairu Shugaban kwarata a dawo lafiya,dake Baban Rabi an Sha kamashi a dakin Mata Yana kwartanci,mugun kwarto ne shi yasa Nima na rama tunda kowa Yana da abin fada, Nene Tace Kun gani Rumaila ta fiku hankali da komai wlh,Amma gaskiya ku gyara ku daina Zagin iyayenku,ke Rumaila ko sun Miki ki barsu da Halinsu Allah Yana gani karki sake fada wani kwarto karki Kara,Hawaye ya shiga sintiri a kumatuna nace Ni na gaji da abinda suke min ko abinda Yan gari ke min ban damu ba Amma ace su kawaye na ai da ciwo,Ni Dan sun min ban damu ba Amma wallahi duk Wanda ya zagi Iyayena sai na zagi nasa, Fu'ad ya kalleni sau daya daya ji tausayi na a duniya yace kizo mu tafi dake can is Better,Na makale kafada Ina shesheka nace Ya...yasin....Ni bazan bi ku ba...sauran Yan gidanku su min wulakanci,Nene Tace da wulakancin Kauye gwara na birni,nace Yan birnin da sukayi Degree a iya wulakanci.

Zan saki a makaranta Fu'ad ya furta,nace Ni bazan biku ba,kyale Ni suka Yi Muka shiga dakin Affa a tsaitsaye Suka gaisa da Affa na da Matarsa Suka Basu kudi,Gidan da Iyata ke Aure Muka nufa,tunawa nayi na fada Mata Fu'ad ya min ciki yanzu idan ta ganshi ya kenan,Allah yasa su Rabi sunyi fushi sun tafi, sabo da Haka na canja Shawara nace na tuna Iya Bata Nan yau tana Can Kano taje wani biki,Umma Tace eyya to idan ta dawo ki gaishe ta nace to Muka juya na tafi rakasu.

Sauri nayi na koma kusa da Fu’ad ledar Kazata ragowa da take hannunsa na rike kadan da sauri ya juyo Dan bai san nazo ba,a hankali nace Dan Allah kawo na rike maka Bako Bai kamata a barshi da Kaya ba,Dariya ce ta kwace Masa ya Gama gano wayo na Dama ya gane son Naman nake Yi shi yasa ya min Haka,ai kuwa yace bana Jin nauyi bar min abata Zan rike na gode,a boye na Harare shi Ashe ya gani sai ya Bata Rai,nace Ni bana so na bar bakinmu da wahala Dan Allah ka kawo har mota Zan saka maka,Kafada kawai ya makale Kamar yaron yaye sai ya bani dariya na manta ma da cikin Dake jiki na Sam,Gaf da motar su ya bani ledar yace ga abinki nan,da sauri na karba tare da cewa na gode Na Gode.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button