DANGIN RABI HAUSA NOVEL

DANGIN RABI HAUSA NOVEL

Dari biyar na dakko wacce ita ce gareni kacal na mikawa Umma nace gashi Umma idan Allah ya sauke ku lafiya ki Bawa Abbi gudunmuwa ayi hakuri ba yawa,Mamaki da alajabi ya daurewa su Umma Kai  ganin ko a dangi idan suna biki ba Wanda ya taba Basu gudunmuwa sabo da ana ganin suna da kudi me zasu Yi da ita Amma sai ga Rumaila ta bada dari biyar iya karfinta abin Nan har Fu'ad ya Basu mamaki,Umma Tace Haba baza mu karba ba,kawai na saki kuka nace Ni ba ku na bawa ba Abbi zaku bawa gudun muwa da Ina da abinda yafi Haka shi Zan bayar.

Shuru sukayi daga Bisani suka bani kudi naki karba,har Fu'ad ya bani da yawa naki karba Dole suka kyaleni Nene tana ta rokata nazo fa bikin Nan Lallai nace indai Ina da Lafiya zanzo.
Har zasu tafi Umma Tace Rumaila Wai da gaske ne ciki gareki na shege? Ba musu nace a ae,waye ya Miki? Nace Nima ban sani ba, Fu'ad yace tanan kin Bata wayonki wlh ,Shuru nayi na tsaya Kamar gunki Hawaye na sharara Kamar ruwa ganin shi Fu'ad ma Kamar da gaske Bai San komai ba Akan cikin dake jikina,cikin Maganar Kurame na nuna wa Fu'ad da Hannu irin cikin ka ne,Bai Gane ba sai Baki ma ya tabe sai Sallama suka min Suka tafi abinsu.

Jikina a sanyaye na koma gida na kwanta Hawaye Yana zubo min Ina tambaya Ina uban Dana yake ne? Nifa na kasa Gane wannan lamari Amma ai Uban sa ba kowa bane face Fu’ad,a fili nace Zan haufo me Kama da Kai wlh har gida Zan Kai maka danka.

  Waye Fu'ad?

AsmaBaffa.
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.

       NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD, GTBANK.

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

           16-20

Official

By
AsmaBaffa

PAGE NAKU NE

BESTIN BEELAT
HAFSATOU
KHADIJA A HAMZA
MATAR MALAM
MUM NAWAZ
SARAUNIYA

    Fu'ad Suffiyan Jawa 

Alhaji Suffiyan Jawa Dan Asalin Adamawa State ne Fulanin Asali ne,asalinsu dama su Sunyi gadon Dukiya masu Arziki ne, family dinsu Gasu kyawawan gaske farare Kamar larabawa shi yasa ake Kiran Family dinsu da Jawa means Jajaye,Alhaji Suffiyan Dane ga Alhaji Sulaiman da Hajiya Fanna,Su Biyu Suka Haifa a duniya,Alhaji Suffiyan sai Hajiya Rahina har Alhaji Sulaiman Yana da kani Alhaji Sunusi Wanda shima me kudi ne sosai yaransa takwas,Sai Alhaji Usman shima me kudi ne a Germany yake zaune da yayansa biyar, har Allah yayi wa Sulaiman rasuwa Basu sake Haihuwa ba,Fanna kuwa tana raye ta tsufa sosai Basu fiye barinta a Nigeria ba sai dai tazo da yawo tana Germany tare dasu Alhaji Sunusi Ana duba lafiyarta, ta Bangaren Fanna uwa kuwa tana da kanne itace Hajiya Saratu Wato Nenen kauye,Sai Hajiya Hauwau itace a Kano tana auren wani Babban Alkali da Yaransu biyar, sai sauran dangi sosai suna da su talakawa da masu kudi Amma talakawan ba wani zumunci ake yi da su ba.

Alhaji Suffiyan Shi yayi gadon Dukiya ta gaske Kuma Allah yayi Mata albarka yaci gaba da kula da komai Tunda ya Fara Business komai yaci gaba da bunkusa sabo da Yana da nasibi,Yana yawon fita kasashe har Allah ya kaishi Sudan can yankin North a anan ya Hadu da Hajiya Maryam kyakyawar gaske Yana dawowa aka shirya biki da komai a can Sudan aka Daura Aure ya dakko Matarsa Suka dawo Nigeria Birnin tarayya Abuja.

Tunda ya Auri Hajiya Maryam wato Umma Bata Haihu ba ko Bari Bata taba Yi ba,ganin Haka Su Fanna Suka Nemo Masa Hajiya Amina Wato Momy Yar Zamfara ce ya Aure ta,Yana Aurenta cikin Ikon Allah Shekara Daya ta Haifo Danta Kyakyawa wankan tarwada sabo da ita ba Fara ba ce,Ranar suna yaro yaci sunan Baban Suffiyan wato Sulaiman Ana ce Masa Karamin Alhaji, Sai Kuma bayan Shekara Uku Hajiya Amina wacce ake cewa Momy ta sake Haifo Yarta mace taci suna Haneefa,Lokacin Kuma Maryam itama Allah ya Bata ciki sai Murna takeyi,Momy ma ta tayata murna suna zaman lafiya abinsu,Maryam wato Umma ta haifo danta Namiji Kyakyawa fari tas Kamar Bature ranar suna yaci suna Fu'ad Sunan Baban Umma kenan a can Sudan Wanda shima ya rasu tuni sai Mamanta ta rage da Yan Uwa,Bayan Shekara biyu Hajiya Amina da Hajiya Maryam Suka sake haifuwa kusan a tare tsiransu kwana Uku Amina ta Haifo Namiji Umma ta haifo mace Kyakyawa itama Rana Daya aka musu suna Islam,macen Kuma Naila,Tunda Fu'ad ya taso a wajen Momy ya girma Kamar ita ta Haife shi shi yasa ake ce Masa Dan Momy wasu suce Abban Momy tunda Sunan Baban kishiyar ta ne suna zaman lafiya suna yiwa junansu Kara,Bayan wani lokaci Abba ya Nemo wata Matar ya aura Hajiya Rakiya Yar Kano, itama tazo ta Fara haifo mazanta sai da ta Haifo maza Uku a jere,Affan,Hunaif da Hafeez, Momy ta sake Haifo Fadila,Mubeena Hajiya Rakiya Ana ce Mata Mama itace ta Haifo Khaleesat,Safna da  Sakna,Momy ma ta Karo Danta Abdulhakeem Sai Kuma Suka hakura da Haihuwa gaba daya,Ita kuwa Umman Fu'ad dama bata sake Haihuwa ba Daga Fu'ad sai Naila ta Haifa.

Yara sun taso cikin gata, Alhajin Karami shima a turai yake zama da matarsa Da yaransa biyu,sabo da baya zama a gidan shi yasa Sam ba a wani San da shi ba,Naira ta ratsa su, yanzu haka shi yasa Basu San Talauci ba suna Jin sunfi kowa a duniya abinda suke so suke yi,an Basu Ilmin Addini Dana zamani Babu abinda Suka nema Suka Rasa,Abbi Kam yayi iya yinsa sabo da shi mutumin arziki ne me karamci da mutunta Dan Adam dukkan danginsa Haka suke sai dai matansa Umma ce kadai ta daban da yaranta ba laifi suna kamantawa Naila ita ma tabi sauran Yan Matan Bata da wata tarbiyya,me Dan saukin Hali Khaleesat ce kawai,Shi kuwa Fu'ad Allah ne ya bashi Kwarjini da farin jini,duk gidan da kowa nasu sunfi son sa shine Dan gaban goshi,gashi Ana Jin tsoronsa komai sai anyi Shawara da shi,sai da amincewarsa ake komai,har kishiyoyin komai Fu'ad ake fadawa,shi yasa Wanda Bai sani ba sai yace shine Babba a gidan,Sulaiman tunda yaje karatu Uk ya Hadu da wata Yar Ghana musulma Aisha ya Aure ta yanzu Haka da Yaransu biyu Na'im da Ni'ima, har ya Gama masters Bai dawo da Zama Nigeria ba Yana can Uk a can ya samu babban aiki can sai dai yazo da yawo ko idan za ayi family Meeting, Haneefa ta Auri wani Dan Gomnan Adamawa tana Nan Abuja a katafaren gidanta da yaranta Uku.

 Bayan Fu'ad ya Gama Degree dinsa a Harkar Business Abbinsu yaga wata Takari Yar Kano ce yarinya danya budurwa a kasa Mai tsarki Samha yarinya ce karama baza ta wuce 28 years ba ya Aure ta itama,yaransa da Danginsa sunji Haushin auren yarinyar da yayi Yar cikinsa Suka ce wannan ai sai dai yaransa su aura ba shi ba,Amma Abbi tunda Yana son Abarsa ko a jikinsa,ita Kam gidanta daban a Abuja ya kera Mata kyakyawace chocolate Yar gayu da ita, yanda take daukan wanka tana Gadara kace matar Shugaban kasa ce, to ta samu daula iya Daula kaf kasar ba Wanda Bai San Jawa family ba masu kudin Allah Tsine uwar me karya,Samha ta Haifo Danta Namiji Suhail,mace Kuma Suhaila da Farhan yaran kullum suna Babban Family House wajen Umma Kamar ita ta Haife su Basu fiye Zama gidan mamansu ba,yanzu Haka suna Primary school, Ana ta Shirin bikin Fadila da Angonta Usman Dan wani Ambassador, to Abbi matansa dai Hudu cif ba space ya Gama cike ko Ina.

 Fu'ad Kamar yanda kuka sani Fari tas ne Kyakyawa me dogon Hanci,Yana da tsayi ba da yawa ba,me kyau da Dan jikinsa ba Mai kiba ba sannan ba ramamme ba normal,Yana da yalwar gashi Baki wuluk me yawa da laushi ga santsi,tare da sajensa da gemunsa Dan chakwas ya Masa mugun kyau,Bakinsa Karami me dauke da jajayen lips,gashin idonsa da girarsa masu yawa Baki wuluk,Haka jikinsa kana ganinsa kasan Namiji ne me kyau Wanda ya Gama gajiya da Haduwa,skin dinsa har sheki takeyi sabo da Bai Saba da wahala ba,Naira da Hutu sun zauna Masa,yatsunsa da Kafafunsa abin kallo ne sun gaji da kyau,Haka idan Yana magana ko Murmushi Dole ya tafi da imanin mutum,gashi da farin jini da Kwarjini ba komai zaka iya fada Masa a gaban sa ba,ga iya wanka,ko wanne Kaya yasa kyau yake masa,Ga Ilmin Addini Dana zamani,sanin ya kamata a nutse yake,so Gentle kullum cikin Tsafta da kamshi yake,Baya kula Mata duk kyan budurwa karya take ya kalleta bare ta birge shi,shi Bakar mace ma tafi birge shi iyayinsa yace ya gaji da kallon farare a turai gashi fari,gidan su farare shi sai baka Fara taje da farinta da kyanta nasa ya ishe shi kallo,Wannan kenan, zaku ci gaba da Jin wasu abin Nan gaba.

 Ci gaban labari

Iya ce ta samu Mijinta da dare suna kwance,shugowarsa kenan Iya Tace Malam nifa ban Gane ba anyi Yamma da Kare? Me shayi yace Kamar ya?ke Ni fa Allah ya gani Iyan Rumaila kin isheni kullum da miji yazo Yana so yayi kwanciyar Aure dake kin fara mita kenan, me kike so Wanda bana Miki? Nasan Wani Abu kike so Dan maganarki Indai kinyi ta a irin wannan lokacin to nasan kudi kike so,to Bari kiji karya jari bazan iya Baki ko kwandala ba,idan Zaki bani hakki na Dan Allah ki bani idan baza ki iya ba ki fada min,Iya tace nice ma karya jari? Me shayi yace ae mana karya jari,malama Ni bude min Raftar Nononki na tatsi sauran ragowar yara da suka Gama la’anta shi,abinda ma yara sun Gama takaleshi Dan ma kinci sa’a Ina da Adalci,ki kula Dani bani da Imani kika sake wukar yanka Bredi na zan sa na yanki kudina da kika ci,Nonon naki kamar kunnen Balamar tinkiya Zaki dameni a kansu, kaddara tasa nake iya kokarin maleji da su,ga Yan Mata Nan lafiyayyu Neman Irina sukeyi naki Amincewa nace sai ke,Ba kunya Iya Tace wallahi sai ka bani dubu daya zan yarda sabo da gobe so nake naci kaza ko jini na ya farfado wani Duk ranar girkin mutum ba hutawa mutum kamar tsohon maye,Me shayi Haka suka dinga fada Amma iya bala’i sai da ya Bawa Iya dari biyar sannan ta yarda da shi,a ranta Tace wlh bazan iya zama ba Bari Nan da sati biyu ko uku sai ya sake Ni wlh babu kudi bazai yuwu ayi ta Shan banza ba,bauta nazo Yi ko aikina kenan dafawa yara abinci da kwanciya da miji,sai dai Ni ayi ta morar lafiya ta a banza,haka Iya ta dinga mita har a fili ma Yana jinta.

Sai Yamma Lis su Umma Suka koma gida Abuja Bayan sun bar kauyen mu,Fu'ad part dinsa ya wuce yayi wanka tare da Shiryawa cikin black Jean 3quatr yayi Ass down Rabin Duwawunsa a waje sai Boxers dinsa Designer me kyau ake gani ko Riga Bai saka ba sai kamshi yake zubawa,fatarsa sumul sumul luwai luwai sai sheki yake yi kamar me,a Dining ya zauna yaga Umma har tasa an shirya Masa Abinci,Pounded yam ce da miyar cabbage Tasha Kifi,sai Farfesun kaji ga lemuka da Fruits salat,a nutse yake yin komai nasa yaci abincinsa yazo cin farfesun ya Tuno da kazar Daya ci a wajena,tsaki yaja a Ransa yace me ya kaini naci girkin ma wannan kazamar me cikin shege,rufe Farfesun yayi Yana tsaki yasha fruits salat dinsa ya wuce palonsa Wanda ya gaji da hadewa,Tv ya kunna Yana kallon Ball.

Umma kuwa bayan tayi wanka taci Abinci bangaren Abbi ta wuce ta Iske ya dawo shima Yana kwance a Sofa,kusa da shi ta zauna tace Sannu da Hutawa,Da fara'a yace gimbiyar Mata an dawo lafiya? Dariya Umma keyi Sabo da tasan wasan Abbi,yace ya yaran da dangi Umma ta bashi labarin komai har cikin Rumaila,Abbi Yana mamaki cike da takaici yace Anya kuwa yarinyar zata aikata Haka sai Idan ko Fyade akayi Mata akwai ayar tambaya,Umma tace wlh Ina mamaki,kasan ita kadai take rayuwa a wani lalataccen gida Wai ance gona take zuwa tana samo itace da ciyawa tana siyarwa ta ci da kanta iyayenta sun koreta Haka Babanta wani mugun Dan Daudu ne kai wannan yarinya abar tausayi ce gata kyakyawar gaske,yaran Gari da manya ta Zama abin tsokana a Kauyen,kawayenta su Rabi ma baka ga wulakancin da suke Mata ba Kuma Bata fushi Bata ramawa banza take musu,Abbi yace ai su Rabi na karance su Basu da hankali ko kadan,Umma Tace to kasan duk da halin da take ciki Muka isketa Shar da ita tayi girkinta me Dadi harda Naman kaza ta sauke mu Fu'ad yaci ya koshi harda guzuri a Leda,Abbi yace Lallai ta Ciri tuta Dan Iyayi yaci abinta tab,Umma ta Mika Masa Dari biyar gashi gudunmuwa,Abbi yace wacce gudun Muwa Kuma Ni duk dangi na ba Wanda ke bani gudunmuwa ko kwandala sabo da Ina da kudi,Amma duk Arzikin mutum idan aka Masa Alheri sai ya ji Dadi,Umma Tace Rumaila ce Tace a baka gudunmuwa Bata da abinda yafi wannan Tace a karba da hakuri, Kuma Muka Bata kudi yarinyar Nan juyin duniya Taki karba Rabi kuwa garin karbar kudi Kamar zata cire min yatsa har da fisgewa,Abbi yace Kinga abinda nake fada Miki Kai wannan yarinya Ubangiji ya Sa Mata Albarka Allah ya fitar da ita daga halin da take ciki, Allah ya kawo ta bikin Nan Ni Kuma Zan Zama gatan ta cewar Abbi,Umma Tace gaskiya abin a taimaka Mata ne gata yarinyar kirki,Abbi ya karbi dari biyar Yana ta murna.

Ni Rumaila kuwa bayan Su Umma sun tafi ranar kwana nayi Ina farin ciki na dauki aniyar zuwa Birnin Abuja biki ko Zan samu saukin Abinda ke damuna idan Ina Ganin Fu'ad kyawunsa zai na debe min kewa,tunda Suka tafi Kullum neman kudin mota nake Yi sosai ba ji ba gani Kullum Ina gona Ina samo itace,su Kuwa su Fadila sai shiri akeyi Amarya Tasha gyara,Hankalina Bai kwanta ba sai da na hada kudin zuwa Dana dawowa,Dukkan Yan Uwa na Wanda muke Uwa daya da sauransu sun samu labarin Abinda ya faru Dani Amma Babu Wanda yaji tausayi na sai ma cewa Suka Yi Iskanci nane kawai,Su Rabi ma suna ta Shirin tafiya basa kulani Biki ya rage Saura kwana Hudu Suka shirya Hajara,Saude,Rabi,Sai babar Rabi Baba Uwale,da Yayar Baban Rabi Goggo Hanne,sai Kanin Baban Rabi Malam Hamisu karamar mota Suka dauka shata har Abuja ta Kai su,Suna zuwa Nene da Umma tare da Abbi sai tambaya suke Ina Rumaila fa? Uwale tace baza tazo ba Kuma Kun sani da cikin shege ai akwai kunya ta shiga jama'a,Umma da sauri tace dan Allah ku rufa Mata asiri kaf gidan Nan Babu Wanda Muka fadawa sai Abbi mun boye Mata sirri karku fada,Kamar gaske Suka amsa da to ai baza mu fada ba, Amma munafukai Babar Rabi Tace wajen Momy suna tare da Mama da wasu Yaran gida.

 Momy tana yatsina fuska kamar taga Kashi Tace Ina wannan Yarinyar me shishigin tsiya da suka zo tare da su Rabi wata ko Rumaila take ko wa? Babar Rabi Tace Ai tana gida tayi cikin shege,dawowarsu da wata uku ta samu ciki,Amai yawu Baki gani ba,iyayenta ma sun koreta gaba daya tana can wani rubabben gidansu na da ita kadai tana ci da kanta,Mama ta saki Salati shegiya Uwar shishigin dama da gani zata aikata annamimiya,To waye ya dirka Mata?Babar Rabi Tace cikin rada rada kar ku fada a gidan Nan ance Wai Fu'ad Dan Umma shine ya mata,Kowa ya zaro ido,Momy Tace Fu'ad Dina dai? Babar Rabi Tace ae shi ne,Mama Tace yanzu naji gaskiya Haba shi yasa Ashe munafunci ne Suka kwashi kafa Suka je kauyen a girman kan Fu'ad yaje Kauye ai sai dole,abinka da duk inda kishiyoyi Suka Kai dole akwai Abu tsakani,Momy Tace biri yayi Kama da mutum lallai shi yasa na taba kamata a bangarensa,dama ance a kiyayi mutum shuru shuru, Fu'ad Yana Iyayi Haka Ashe ta Gina Bata Shiga bane,Yaran su Fadila da su Islam Suka cika da mamaki,su ma su Rabi har Yan aiki da masu gadi sun fesa musu Kuma Suka ce Fu'ad ne Wai,ba a Dade ba zance yaje kunnen kowa a gidan,Naila,Umma, Fu'ad,Nene da Abbi sune Kawai basu San gulmar ba,Momy Tace Allah ya kawo ta bikin Nan duk sai Mun sa musu Ido daga ita har Fu'ad sai Mun gano gaskiya Mun Kama su hannu dumu dumu sannan mu dauki mataki,Fadila Tace Kuna kamasu Momy ku kirani a waya Bayan biki Nima zanzo na fayyace wani sirri me girma Dana sani akan Rumaila daga Nan nasan sai gidan yari shegiya na tsaneta,Mama Tace kin tsaneta ko na tsaneta,Sam Ni Bata min ba cewa Momy itama,Haka Suka dinga kus kus Ana ta yada zance, duk sun batawa Fu'ad suna tunda har dangi Dana waje duk Wanda ya shafe su sun fada Masa,Ana ta kallon Fu'ad a banza Ana gulma ,shi Bai sani ba ma Sam.

 Su Rabi Kam Fu'ad ma ya gansu a part din Nene aka sauke su Amma Bai ga Rumaila ba,Har biki ya rage Saura kwana Daya a Fara shagali,Lokacin Ina mota Babu Wanda na fadawa zanje sai Affa na duk da baya kulani na sanar Masa.

Ina mota da Goba a Jakata Ina ta ci sabo da Gudun Amai ko zubar da yawu, motar mu a Hanya ta samu matsala shi yasa ban samu Isa da wuri ba sai gab da Sallar Isha,Ina fita a taxi a kofar gidan ga haske Kamar Rana Nan na hango Yan mazan gidan da wasu bakin ma a kofar gida suna ta hada Hada,Dake doguwar Riga Na saka baka na yafa mayafinta Sam baza ka Gane daga kauye nake ba,Fu’ad na Fara hangowa da kana Nan Kaya suna zaune a saman wani carpet me kyau da tsada da wasu maza da Alama abokansa ne sai Tafawa sukeyi,Jakata na rataya ga Leda katuwa a Hannu na da kyar nake iya dauka,idan na dauka nayi tafiya Daya biyu Sai na ajiye na huta Ina ta faman yarfe Hannu,Cikin abokan su Islam wani yace Kunga wata Lange Lange ai da ganinta kasan baza tayi karfi ba yanda take Fara Haka,duk Wanda ya Auri wannan ya Auri Asabiti kullum, Asibiti salamu’alaykum ce kalar cuta ce gaba dayanta,Islam yace Amma fa ta hadu duka mazan har abokan Fu’ad suna ta kallo na Kamar zasu cinye Ni,Ni kuwa ko kulasu banyi ba,Nazo gab da Islam Zan wuce ya leka fuska ta yace Iyyee Ashe kece dama Rumaila kike ko? Murmushi nayi ba shiri nace nice Mana Ina wuni lafiya Alhmdllh kinzo bikin kenan,ke Baki Zo da wuri ba Ina ta tambayar su Rabi Ina me Iya Awara Suka ce baza ki Zo ba,wannan kayan fa a Leda Haka kike dauka da kyar? Nace Bari na fada maka a sirri gefe muka koma Ina magana kasa kasa mun tsaya gaf da juna nace Albasar Abbi ce na kawo Ina laifi idan aka muku girki? Islam ya dinga dariya yace Lallai kina son Abbi kinfi mu ma mu yaransa,Nace ae tayani dauka Dan Allah Hannu na zafi,Islam yace angama ai ko Dan Iya awararki Zan dauka,Hannu yasa ya daukar min cak,yace kawo Hand bag din Taki itama na Mika Masa kuwa Ina Furta na gode Muka jera har cikin katafaren Gidan,Islam sarkin surutu Yana ta labari.

 Nace a Ina su Rabi suke? Yace part din Nene  nace to muje bangaren Umma a Raina gudun wulakancinsu nake yi shi yasa na canja wajen Zama,Umma tana Sallah na tura me aiki ta Kira min ita,Ina Palo ta Idar da Sallah ta sakko kasa tana ganina Fara'arta ta Karu Tace nayi zaton baza kizo ba,Haba Umma ai nayi Alkawari Gashi nazo har kasa na durkusa na gaida ta sannan na Bata Albasar tana ta godiya nace Taki ce Umma da Abbi zan bawa na tuna ai baya girki, hhh Umma tayi Dariya tana godiya.

Umma Tace part din Nene ya cika da mutane ki zauna a Nan ga Daki Nan ki zaba,Godiya nayi tace kici Abinci kiyi wanka ki huta kafin gobe me lalle zata Zo da safe da wuri idan tayi min sai tayi Miki,nace na gode Umma,Abinci naci me Rai da lafiya sannan nayi wanka na saka kayan Bacci na tare da zurma katon Hijab na wuce wajen Nene,Can Muka hadu muna Hira da ita,Haka bakin Dake part din Muka gaisa,su Rabi sai kallon banza suke min,Saude Tace mayyar sai da tazo Kamar Yan Uwanta,Ni Kam tafiyata nayi wajen Umma na shige dakina na kwanta bayan nayi Sallar Isha,Islamiyyar Dana Yi a gidan Nan farkon da Fu’ad yake Kora mu ba a banza ba harda Adduar bacci nayi baccin gajiya yayi gaba da Ni.

9pm Ina cikin bacci Hayaniyar Yan Matan gidan da samari ta tashe Ni a bacci,na sake fitowa Palo San kallu Yan gayu Yan Mata, Naji Naila da Khaleesat suna cewa Umma bamu samu kitson attach din ba dare yayi kin San Yaya Fu'ad sai ya Zane mu shi yasa Muka dawo Haka sai lalle kawai Muka Yi mu Kuma da su Suhaila yaran Nan gaskiya kitson Attach zamuyi yafi kyau,Umma tace an muku fada Babu kyau Amma kunki yarda sai ku tambaya cikin kawayenku ko akwai Wanda Suka iya suyi muku a yau gobe Baku da time din Yi Kun Sani ku ma,na Iya kitso sosai ni har na Attachment na iya sanda nayi agolanci a gidan tsohon Mijin Iya na Rigim na koya a wajen Wasu Igbo sunzo Bautar kasa suna Zama kusa da gidan mu a wajensu na kware sosai Ina zuwa shagon Saloon din da suka Bude Ina yiwa mutane suna biya na wani Abu sabo da Haka fit nayo waje da Goba ta da yawa a leda,Naila da Khaleesat Suka kalle Ni tare da tabe Baki Naila tace mutan kauye anzo kenan? Nace ae munzo,Naji Kuna Neman me kitson Attach na iya sosai ku kawo na gwada Yi mu gani.

 Shekeke Suka kalleni Umma ta Gasa musu Harara tace idan basa so je kiyi baccinki Rumaila,Khaleesat tana turo Baki tace gashi gwada wallahi idan Kika Bata min gashi sai na mareki,Nace ae naji na karbi gashin da za a Kara ta zauna a kasan Center carpet na zauna a kujera,Tace cire Hijab din Nan naki ban yarda da shi ba ko wari yake Yi,Na cire na ajiye shi gefe sanye da Silk kayan Bacci na cikin Wanda aka siya Mana farkon zuwan mu gidan,duk Surata a waje Umma Tace yafa mayafi Kar maza su shugo,Hijab din na yafa a saman kafada ta ya rufe min har kirji na,sai kuwa ga Fu'ad ya shigo Yana wani takama ya kwanta a kusa da Umma tare da Dora kansa a Cinyarta.

Ina Yini na gaida shi lfy yace kawai da kyar,Khaleesat Tace kiyi sauri malama,a Dora ruwan zafi kusa sabo da za'a Masa steme (steaming)ake cewa cewar Naila tana dariya nace to,Kitso na Fara zubawa style me Arnen kyau Wanda Basu taba gani ba Allah ya bani  basira da kaina nake kirkira,Ai kuwa Suka gigice ganin yanda yake zuba kyau,Naila Tace da an sani Ni aka Fara yiwa,Duk Wanda ya shigo ko mace ko Namiji sai ya yaba,Islam Yana zuwa Yace ah bayan Awarar a kitso ma an kware,Murmushi nayi me kyau fararen hakora na Suka bayyana kanana, Fu'ad kuwa sai Bata Rai yake Yi, Khaleesat tana ta faman kallo a karamin mudubin Dake hannunta,Gani da saurin kitso Haka na yarfa mata shi,da kanta tayi Steaming nasa,Naila ma kalar nata daban Ina Yi Ina ballar Goba ta,gani da saurin Jin yunwa tunda na Fara laulayi,Suhaila Yarinyar Anty Samha Amaryar Abbi na kalla nace ebo min Abinci a kitchen,Da Gudu taje ta ciko min plate da Fried rice harda kaza Ina kitso Ina ci sai gashi na cinye,nace kawo min ruwa taje ta kawo min na Sha sannan naci gaba da cin Goba ta, Fu'ad Yana ta mamakin ci irin nawa,a Haka na gamawa Naila,Ina gamawa na samo kunun gyada na shanye tas, nayi wa Suhaila style na Yara me kyau,tunda wasu kawayensu Suka gani Suka Fara zuwa suna cewa Dan Allah Zaki min Nima ko gobe ne? Nace baza ku samu ba yanzu Haka bayana ciwo yake Yi 12 pm ma tayi,gobe fa? Nace Ina da aiki Mijina zaizo Zan kula da shi,Da sauri Fu'ad ya kalleni irin karyar Dana Yi,Tace laaa kina da aure Yar karama da ke?, Nace Wasa kike a Haka din kuw...kafin na rufe Baki sai wayata tayi kara Ina dubawa Naga Jauro, Jauro Ana Kudu Bai San me ya faru da Ni ba,Wayar na daga tare da kashe murya nace Jauros Wai Ni irin soyayyar Nan, Fu'ad bakinsa ya Danne kar Dariya ta fito ya jawo Laptop dinsa Yana dannawa.

Shagwaba da kukan soyayya na saki Ina buga kafa ni…ni….Allah yaushe zaka dawo Habibi na….ka barni na gaji da jira….Allah zanyi maka kuka na fara wani irin kuka me tafiya da Imanin Wanda ake wa, Fu’ad tsigar jikinsa ce ta tashi Yarrrrrr…..wani Yanayin ya shige shi,Wanda ake wa shagwabar daban me ji a jikinsa daban,Ban dade ba Muka Gama Wayar, Fu’ad a aransa yace na kama Wanda yayi ciki Kawai Jauro ne, Allah yasa tsautsayi ya kawo ka zance live in prison zansa a daure shi daurin Rai da Rai,barin irin wannan a duniya hatsari ne,ban San me yake sakawa ba, Umma tuni ta tafi bacci shima Fu’ad tashi yayi ya wuce,sai wurin 1am na Gama na tafi na wanke Hannu na da sabulu na kwanta sai bacci.
Su Khaleesat da Ya Fu’ad Bai Kore su ba basa Zama idan Yana waje yanzun Nan zai ta masifa Amma yau ya kyalesu har aka musu kitso.

Da Sassafe a daki nayi Iksasaye (Exercise) kadan na koma Bacci sai 10pm yunwa ta tashe Ni ko wanka banyi ba naje kitchen na ebo abin Kari naci na koshi sannan nayi wanka tare da wanke Toilet din na fito na gyara dakin neat na saka skert din Atamfa Wanda shima a gidan aka dinka Mana zuwan farko Bra na saka purple sannan nasa Vest a sama itama Purple nayi kyau shape komai ya fito,ban Saba daura dankwali ba,gashi na na tafke jelar ta wuce tsakiyar baya na Haka na fita Palo na Iske har an gamawa Umma Lalle suna zaune tare da Fu'ad ya Sha wata sabuwar Gezna Light blue ya gaji da Haduwa sai kamshi yake zubawa,Umma na gaisar da shi Ogan ko kulani baiyi ba sai dai ya kallen sau daya,Goba ta na dakko a Leda na zauna gaban me lalle ta Fara tsara min ita abinka da Fara sai na dauki haske,Hannaye da kafafu aka zana min Baki da ja,tana gamawa na mike tsaye tare da kwaye Yar lukutar Cinyata sumul sumul nace zana min Fuskar Iyata a cinya ta Kamar yanda ake Yi a turai tattoo, me lalle da Umma Suka dinga dariya Banda Fu'ad dake aikin lissafinsa na kudade,Umma Tace in Banda shirmenki Ina tasan Iyan Taki da zata zana Miki ita,nace au sai sunga mutum ma? To wlh anyi asarar Basira a Nan Baki iya komai ba,me lalle tace zancen kike so,Nace to zana min flower me kyau a cinyar Nan tawa na dinga kallonta Ina Jin Dadi,Me lalle ta zage ta Zane min cinya ta Kuma tayi kyau sosai.


Ina sauraron Lissafin da sukeyi na kudi da Baki,idan Sunyi Lissafin abinda aka siya sai ya buga a waya,Ni kuwa sabo da na Saba da Talla munyi mugun iya Lissafin kudi kafin ya Danna a wayarsa na Fadi adadin kudin nace kudi sun Kama kaza mun iya buga Lissafin kudi,idan yayi a waya sai yaga dai dai da abinda nace Amma share Ni sukeyi ko na fada basa yarda har aka Gama min lalle ne ya bushe naje na wanke a toilet lokacin tuni me lalle ta tafi Umma ta fita Itama, Fu'ad ma haka,Yan Matan gidan sai shige da fice suke Yi,wannan ta figi mota ta fita kaga ta dawo wata tayi gaba itama,Hayaniya da Kade Kade a manyan speakers sun dameni Yan Mata ne Suka kunna mayafi na yafa saman vest din na fuce daga part din na koma Garden na Samu bishiya me sanyi na zauna a kasanta Ina zaune Ina cin soyayyar gyada me gishiri. 

AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: ????????????????
DANGIN RABI
????????????????

FREE PAGE

DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM

         NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

             21-25

Official

By
AsmaBaffa

Page naku be

Maman Dee
Minerh
Aunty Nurse Zaria
Maryam Barau
Umma Khursum
Fulani Gal Bing
Lawee warra
Mariya Abubakar Gml
Maman Humaira
Azrahh
BB
Matar mijinta
Alhusnah (Mrs Idris)
Mmn Aliyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Back to top button