DARAJAR ‘YA’YANA PART 2

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Darajar Yayana2-02
Posted by ANaM Dorayi on 09:51 PM, 02-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Irin tarbar da kikayimin ta mutunci shi yasana boye kalatata,boye kishinki zaifi alheri, sama da bayyanashi don yanda na yi mani bakikaini son mijinki ba, haka na yi imani na fi ki kishin sa,in kina musu lokaci zai tabbatar miki dahaka. Kije kiyi aikinki sannan ki kunna min T.V Na harareta tare da jan tsaki na nufi dakin yaran. Sun gama cire kayan, Kausar tana linkewa, Al’ameen ya ce,’Mama wace ce wannan??? ….. Na ce ‘Bakuwa ce, Na kunna musu T.V dinsu, na ce kar su fito sai an kira sallah. Nima na shige dakina na fada kan gado. Maganganun yarinyar sun ratsa ni, har na rasa tunanin dayakamata inyi. Ina buqatar shawara, domin na lura da ‘yar iskar matar nan batazo dawasa ba. Wa zan kira don neman shawara? Aisha ko Abida? Aisha ba ta san d wannan zancen ba, bari kawai in kira Anty Abida tunda ta san da matsalar. Ringing na uku ta dauka na ce, ‘Anty Abida ya gida da yara. ‘Ta ce, Lafiya lau. Na kwashe komai na fada mata, ta cika da mamaki, sannan ta ce, ‘Shawarar da zan ba kikar ki bari ta gane lagon ki kar ki nuna fushinki, kuma kar ki kulata kuyi tashin hankali, ballantana ta yi furucin da yaranki za su gane,ki jira zuwan shi muji hukuncin da zai yanke. Na ce, ‘To shi kenan Allah yayi mana jagora.’Ameen, Ta ce. Na kashe wayar ina nazarin maganganunta. Ita ko ‘Yar Gwari, Mujidat tuni ta ciro wayarta ta soma chatting da abokanta. Murfat ke tambayarta wai yanzuntana ina? Mujidat ta ce tana Kaduna. Murfat tace, ‘Ashe muna kusa ni ina Abuja jiya muka zo tare d Alhaji Karimu zai yi meetina na kwana biyu.. Mujidt tace lallai kina cikin kudi, murfat tace sosai ma, abokinshi Alh muslimu ya tambayeki .Mujidat tace yakiranima bandaga wayar ba, kinsan ina ina yanxu? Murfat tace ba kin ce kaduna b? Mujidat tace ina gidan officer Aliyu,Murfat tace kina hauka ne? Zaki je gidansa? sai matar sa ta kasheki a banxa? Mujidat tace ai matar tashi wawiya ce, har ruwa ta bani nasha, bayan na gaya mata cewa mijinta ciki ya min, tace ina baki shawara ki cire cikin nan kixo gurin masu sanki, officer ba sanki yake ba. Mujidat tace , ni inasonshi, zan tsaya nai fada a kanshi, saboda ko nadawo zanta tunanin shine, bazaki fahimta bane saboda bakitaba shiga tarkon So ba, ni kuma na shiga tarkon So mai tsanani.Murfat tace to yaya akayi kika gane gidan?ina kwance Hotel ba lafiya , sai ga wayar direban shi wai Ogafa an canxa shi zuwa Abuja, yanxun haka ya tafi in gaya miki duk sai na rude, take na miqe ina roqon Adewale ya taimakeni , yace sai nabashi kudi, bani da kudi sai dana roki samarina , suma shegu ban samuba sai dana musu alqawarin basu kaina, ina bashi kudin yace naje kaduna zai turo wani dan sanda daga can Headqurter su, yayi Tanbaya kan Aliyu Tukur aka fada masa sunan unguwar su, sannan na nufo Kaduna, nasha wahala kafin na iso, sabida motar dana shiga me arhace, inazuwanan na samu wani dan sanda da Adewale ya hadamu , shima akwai kudin da akayi alqawarin xan bashi, sai daya dafe shi,sannan yayi min jagora zuwa unguwar su Aliyu, nan ya bar ni wai in nemi gidan, wai in mun shig unguwar tare, asirinsa zai tonu, na Adewale ma haka,nadade ina yawo, sannan na samu gidan mamanshi, na shiga bata nan, sai nace a kai ni gidan matarshi, Murfat tace ke yar neman bala’i ce, bari tasa miki guba a abinci kici ki mutu, mujidat tace shi yasa bazan taba cin abincita ba,Murfat tace kidai yi ahankali, garinsu kikazo, tace a garinnasu sai in karbe mijin kuma na zauna lafiya.haka suka yita chat har xwa wani lokaci, Niko munyi sallar magariba har na zubawa yara abinci, 9 da yan mintina yya Aliyu ya iso gida,da ita ya soma cin karo a falo, ckin zafin rai yace me zakiyi agidana?itam cikin daga murya tace goyon cikin dakayi min, abinda naji kenan, na miqe ina kallon yarana,Kausar ce kawai idanta biyu tana yin homework dinta, na miqe na fito da sauri, dai-dai lokacin yana cewa, zan nuna miki kurenki na biyoni gidana yar iska karuwa.nakamashi ina fadin yaya yara fa? itama tace yan iska dai, namijin karuwa. na dafa kaina dan takaici, yar bariki tana zagin mijina da nake girmamawa a gabana, najashi zuwa dakinsa, nace, haba yaya, kamanta cewa kana da yara a gidan nan?dubi yanda yar bariki tazo har cikin gidanka tana zaginka?sabida mutuncinka daka sai da,ai dama haka ne, dukwanda yabar maganar ubangijinsa dole ya fadawa dana sani, da wace rana zaka iya hada yau a gurinka dan bakin ciki? ni dai a gurina babu, ya dago kai ya dubeni, Sadiya nayi nadama sosai wallahi, ba sai ta kanjamau kadai Allah yake kama mazinaciba, in Iya taji batunnan na shiga uku, nasan bazan kara yin daraja ba, kila ma ta cireni daga yayanta, ga wannan matsiyaciyar da alamu fallasa tazi min,nace to yanzu dai nema mata masaukin da zata kwana, in yaso da safe sai mu zauna da ita mu kafa mata sharuda,ya kama hannuna, wadanne irin sharuda za’a kafa mata?kara min haske, sai musa mata sharudan cewa ka yarda zaka amshi dan,amma za’a rufa asirin cewa ba’a son kowa ya ji, dan haka za’a ce mijinta ne ya rasu, iyaynta suka koreta saboda ta musulunta,na tabbata duk wanda yaji haka zai tausaya,to inta haihu sai ta bamu yaron ta tafi abinta,yace wazai rike yaron?nace ni mana, Yya ko ban aure ka ba ai xan rike maka da, bare kuma ina matarka na kasa rike jininka? yadan yi shiru yana nazarin batuna , can yayi dariyar yake yace,Sadiya baki tunanin me mutane zasu ce?in sun gammu da jariri?me zamu fadawa yaran mu? idan sun tambayemu nan gaba? nace ai zamu fada musu dan mu ne, amma bani na haifeshi ba, tunda dama a musulunci bai da gadonka,kaga ba zamu sami matsala ba, ya sake yin shiru, can yace ina ganin fadin gaskiya kawai shine mafita, saboda duk rintsi karya bata kaiwa ko ina baki tunanin cewa nan gaba zata zo nemn danta?kuma asiri zai tonu? nace Allah zai rufa asiri, kai dai da safe mu sameta da batun muji yanda za’ayi.yace shikenan, Allah ya rufa asiri,to yanzu ina zata kwan?ka kaita dakinka,yace a’a, sai dai yara su dawo dakinki, ta kwanta acan , amma bazata kwanar min a daki ba, araina nace yanxun ba, amma da ai tare kuke kwana ma. yace kota kwana a falo? a’a ,bari in kaita dakin yaran.haka kuwa akayi,muka kaita can.Da safe dana kai mata abin kari sai tace a’a, tanada maltina da kuma biredinta, bata cin abincin kowane guri, da kanta takeyi, nace good, sannan na fita.mudai sama-sama mukayi bacci, kuma sama-sama muka karya, duk sai tunani muke, yaya kuwa sai nadama yake, dan dadin da yabi na watanni yaja masa zubewar mutunci na kila tsawon shekaru.misalin sha dayan rana yace in kirata ,muka zauna yara suna makaranta lokacin, ta fito sanye da riga da siket na jeans, kanta babu dankwali, cikinta kuwa har ya turo, ta zauna tana taunar cingam, yaya yace Mujidat dama mun kira kine don mu tattauna dake, shawara ta farko zanbaki dubu dari biyu ki zubar da cikin nan,ta daga masa hannu, ban amince ba ,koda zaka bani duniya da kayan cikinta, inbaka mantaba nafada maka, badan kudi nake tare da kai ba, sonka da kauna ce kawai, kuma cikinnan, (tasa hannunta ta shafa cikin)ribar soyayya ce, taya zan zubar dashi?kawo wata shawarar dai muji,kalamanta sun konan raina tamkar in tashi a gurin,amma sai na shanye.yace to naji, zaki zauna damu ki haihu, amma da sharadin baxaki fadawa kowa komai ba,duk abin dana fadawa mutane zaki tsaya akan haka ne?ta dan yi tsai tana tunani can tace ,zan yarda, amma idan na haihu meye makomata? zan tafi da danne?ko kuwa zan barshi anan?sai lokacin nasa baki , zaki tafi ne kibar yaron a wurina, sai ki tafi abinki,wata ran,xaki iya xuwaki ganshi duk bayn wani lokaci, tayi min wani kallo, tare da yin kwai da cingam dinta kato, sannan ta fasa shi taci gaba da tauna duk muna kallonta, tayi yar dariya, in naki fa? cikin zafin rai Aliyu yace , sai ki tafi da cikinki, danma kin samu zan amsa? nasan uban dayayi miki? tace , ka manta dararen daka yi ta kwana dani?cikin bacin rai yace in baki yarda ba malam kizo ki fice min daga gida kije kiyi duk abunda zaki yi. tace zan fi son haka , dan zama gidan mamanka ze fimin wal-wala, dan haka zan je na fada mata ina dauke da jikanta, ta bani masauki, ni dashi muka kalli juna, yace kije man , zanfi san haka.nace , a’a ,kedai barshi a wancan tsarin,tace in dai har za’a barshi cikin sirri, tonima zan kawo nawa sharadin?Aliyu kam takaici ne ya hana shi daga kai, ban taba ganin shi cikin wannan yanayinba, na takaicida bakin ciki.nace fadi sharadinki muji?tace sharadina sai dai in na haihu zai AURE NI…. kalamanta na karshe suka tafi da numfashina, tsawon kiftawar ido, huhu, nayi nasarar janyo nimfashi na,idanuwana suka futo sukayi jajir, zufa ta ketomin, ta tuntsureda dariya har Aliyu ya dubeta, nima lokacin na dubeta, tace ,ya kika yi saurin firgita?naga keda mijin naki kamar tagwaye, shawarar ku daya, kun burge ni, kuma nasan yana sonki, kuma nima ina san shi dan nasan qualities dinshi, na baku zuwa gobe kuyi shawara. (Uhm!Allah yakayuta,ANaM Dorayi) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu ya harareta, Allah ya kiyaye ni Aliyu na
aureki,ai ko zan yiwa matata kishiya na nemo
mata yar mutunci bake ba karuwar titi,tir Allah
ya tsareni, ya miqe, na baki awa daya kibar
gidana, ko kuma yan sanda su zo su fita dake, da
kyar na miqe kafafuna sunyi sanyi, dakina na
nufa don ko ganin gabana banayi,zuciyata tamkar
ta faso ta fto,rigijif na fadakan gado, inasan yin
kuka amma na kasa, lallai kuka ma rahama ne,
tunda idan kayi shi zaka samu sauki,
Hannuwanshi naji a gadon bayana, ji nake tamkar
ya doramin wuta,zuwa,yanxu nasoma tsanar
yaya Aliyu,gaskiya hakurina yana son ya kare,
danzan iya danne komi, amma banda batun
kishiya ,zan iya hakura ya aureta, amma kuma
zan juri zama da ita?(Mata kenan,da kishiyar
gida!..Allah ka karemu daga bin soye-soyen
zukatanmu…..Ameen.ANaM Dorayi) Birkitonin da
yayi shine ya katse min tunanina yace, haba My
choice, kada wannan ya dameki, zanyi waya
yanxun xa’a turo min yara su tafi da ita, xuwa
ynxun ban damu duk duniya tasan cewa na mata
ciki ba, ai nima dan Adam ne kamar kowa, ban
wuce kuskure ba, nace aika riga ka tafka
kuskure,dole ne ka aureta, kuka ya subucemun,
naci gaba da magana cikin kuka wane hali Iya
xata shiga in taji wannan labarin?ita da ba
cikakkiyar lafiya ba, me zaka cewa y’ay’anka ?
wadanda tun jiya suka damu dasan sanin wacece
wannan bakuwar? y’an ‘uwanka, wane idan kake
dashi da zaka kallesu?su da sukeyimaka kallon
mutunci da kima? ga abokai da sauran mutan
gari?kada ka manta, shi fa mutunci madara ne,
in ya zube sai dai a kwashi kasa,ka riga kayi
abinnan da hausaw ke cewa TSALLE DAYA ME
JEFA MUTUM RIJIYA….ya rike kanshi, sadiya na
yarda duk wanda ya bar layin da aka ja masa a
matsayinsa na musulmi dole yayi nadama mara
amfani,danasan abubuwa zasu zama haka da
banbi san zuciyata ba ,dam malamai suna gaya
mana zuciya wata tsoka ce ajikin dan adam me
hadari in kabi sonta sai ka halaka, ya dube ni,
yanxu kin yarda? kinaga ba wata mafita sai ta
auren ta? nace to inban yadda ba ya xanyi ,nasa
masa kuka ina fadin na amince ka aureta,
,kallona ya dinga yi tamkar na zame masa wata
sabuwa a sanyaye yace”nasan kin hakura ne
saboda ni, amma nasan bakya san kishiya,amma
kina ganin cewa nan gaba bazaki damu ba?na
runtse ido, zuciyata tana wata irin tafasa nace,
batun zan damu ko bazan damu ba a ynzun ba
shine mafita ba,na bude jajayen idanuwana ina
kallonshi, sai dai ina fatan daga baya ba zka
canzamin ba? ya rungume ni, Sadiya kada kiyi
tinanin haka kada kiyi fatan haka, ki tayani
addu’a Allah ya bani ikon yi miki irin halaccin
dakikayi mini,banda kamar ki har abada,kuma ke
kadai nake so ke daya kwal. Haka ya yi ta fada
mini maganganu masu dadi da kwantar da rai,
har zuciyata ta dan sauka. Yaya ya fito ya fita,ni
kuma na kira Anty Abida na fada mata, ta ce
hakan ya yi in ta haihu ya aure tan zai fi sauki a
bakacin ta haihu ta ba ku yaron. Na ce, To ya zan
yi tunda shi ya janyo. Nan dai muka yi sallama
nafito na kuma dora abinci,sai dai ina gamawa
ita ma ta soma dora nata,ban damu ba tunda
neman sulhu muke. Misalin hudu yara suna
Islamiyya suka shigo shi da Usman falo suka
zauna, na kawo ruwa da abinci.Usman ne ya sha
ruwan shi kam gogana har wata ‘yar rama ya yi,
ya kalle ni ya ce, Kira yarinyar nan. Na ce to. Na
daga labulen dakin yara tare da yin sallama, ba
ta amsa ba sai dai ta dago ta dube ni,rufdaciki ta
kwanta kan katifar su Kausar tana chatting, na
ce, Ki zo in ji Mijina. Ta yi min kallon kishi zan ce
ko na tsana, sannan ta ja tsaki. Ni dai na juya na
ce musu tana zuwa. Zan tafi Yaya ya ce in zauna,
na samu guri na zauna. tafi minti shida sannan
ta fito,munyi jugum-jugum kamar masu zaman
makoki, ta tsaya kerere , gani. Ya harareta
.Kizauna mana kin ce wani gaki? Ta zauna tare da
fadin .yau kuma da wacce aka zo? Duk muka yi
shiru, irin zaman nan da ake cewa mutuwa ta
ratsa. Can Aliyu ya ce”Usman wannan ita ce
Mujidat,kuma na maka bayanin komai,dan haka
sai ka dan ce wani abu”.Usman yace”bani da ta
cewa,sai dai ke.ya nuna Mujidat,karkisake kice
zakici zarafin wannan baiwar Allah ko nan gaba
“yakalli Aliyu”ya kamata wannan ya xama cikin
sharudan da zaka gindaya” Aliyu ya kalli
Mujidat”na yarda in kin haihu zan aureki, amma
ki sani so daya tak inayiwa matata ne,dole ki
bata girma da daraja,musamman data soma
bazaman aure ba, sannan zaman haihuwarki ina
gani can wani waje zan nemamiki haya” cikin
sauri na ce ban yar da ba, ai ta zauna anan,
kada a dinga zagayawa “Usman yace “haka ne
kuma,amma kina ga batakura? Na ce “bakomai”
Mujidat dadi ya rufeta ,kuma nan take ta nuna
murnarta, ta kuma sake bayyana tsantsar san
data ce tanawa mijina,dan haka dole tazauna
dani, ban bari ta kai karsheba natashi nayi kicin
abina.tsayawa nayi tsakiyar kicin shuru,anya
kuwa ban yi wautaba?ban zalunci kaina ba?ban
debo rvmuwan dafa kaina ba?amma sai wata
zuciyar tace kedai kada kiyi wannan tnanin, tunda
kin sadaukar da kimai ne dan asirin mjinki y
rufu,Allah ya sani Zuciyarki daya da ita,kuma
Allah zai shige miki gaba. Nasauke ajiyar xuciya
nace Allah gani gareka,sai da suka fito ne naji
muryar Usman na cewa”Madam na tafi”nace “ka
gaida min su Ummulkhairh dasu walida”yace
xasu ji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A ranar Aliyu ya koma Abuja,sabida an dameshi
da kira,gida ya koma sai ni da ita saikuma
yarana,a daren nan naje na fadawa Iya yanda
muka tsara zancen,tayi ta tausaya mata,tare da
shiwa yaya albarka tace ai gara daya taho da
ita,tace in an barta sai ta koma ruwa, tabar
musulinci, nace “ai shine” Iya tace Allah sarki,
naxo in yi mata ta’axiyya,banda abinku, daba
nan kuka kawota ba? Tunda ni kadai ce?nace”Iya
ki barta can kawai,sabida bata jin Hausa sosai”
tace”to shkenan ,kema Allah ya biya ki” na ce
amin.
Daren ranar mun kusa rabashi a waya yaya yana
shimin albarka tare da yi min alkawuruka kala-
kala na riqe ni amana,tare da kyautatamin daji
dani duk wani dadin zaman aure,har sai da aka
kira shi, yace minxai fta gurin aiki1 nce Allah ya
tsare.
Haka muka zauna da Mujidat,bata min
magana,sai dai ni in mata.innayi kamar in
shareta,sai na tuna da haramcin gaba,dan haka
in lokacin sallah yayi tana falo sai in ce
mata”lokacin sallah yayi” wataran
tace”to”wataran tayi min banxa ,sai dai ko ta
amsa ba dole ne ta tashi tayi sallar ba.abinci
kuwa,da kanta take yi,takanyiwa yara
magana,amma ba wai wasaba, sai dai in tana
san abu tace kai bani kaza, ko ke bni kaza. Sun
dameni wai yaushe wannan bakuwar zata tafi?
bata da kirki su suna san ta tafi,nce musu bazata
tafib,Antyn su ce baban su ya kawota ,kuma tana
da kirki,dan dai yanxun bata da lfy ne
shiyasa.suka yi shiru badan sun fahimce ni
ba,intaji fita tana san zaga gari sai dai kawai inga
ta fice bako mayafi. Sai dai nayi masa waya nce
ka fada mata in zata fita ta dinga saka hijabi ko
mayafi, saboda an ce ta musulunta, in tana fta
haka asiri zai tonu.ya ko kirata yace ta
kiyayeshi.kar ta bari tayi abinda zai toxartata,tace
ita bata da hijabi.yayi min waya wai in bata
hijabai guda 2, sannan yace ya hanata fta,kuma
ta sani ya zuba masu sa mata ido a unguwar,
dan kar tai xaton cewa xata fita wani gantalinta
ta dawo masa gida,ko kuma zata yo wani mugun
abun.tace karya damu,dama ita burinta aurenshi,
kuma tunda ta samu bata da matsala da wani
namijin can waje, tana zuwa matsa jikine.
Duk wani zaman kunci na dauka a zaman
Mujidat, sai dai ban damu sosai ba.ganin Aliyu
baya sakar mata fuska sosai.komai tace masa
tana so sai yace ta tambaye ni,bai cika zuwa
gidan bama, sai daiyazo ya debemu da yara mu
tafi can Abujan, akwai lokacin da sai da muka yi
sati uku saboda yara sun samu hutu. Ranar da
muka dawo har da shi ,mun samu ta tana kuka
wiwi, wai bata da lafita,nce masa muje Asibiti,
amota fadi yake Allah yasa ckinnan ya fta, na ce
dan Allah kabari, ka mata addu’ar alkhairi, bayan
dogon bincike likita ya gano tana shan maganin
tari na yara,wanda mata da maza kan sha sabida
su yi maye. Likitan ya ja kunnanta da cewa in ta
ci gaba d sha za ta kashe danta. Muna hanyar
dawowa gidan na ce, Ki daina kada ki je ki yi
sanadin rayuwar danki. Na dube shi. Kayi mata
magana ta daina shan pakalin. Ya ce, ‘Ina
ruwana, ta yi ta sha indazata mutu ma kina
ganin ba zan fi son haka ba? Ta ce, ‘Eh, na san
dama haka za ka ce, kuma sai na haihu lafiya. Na
ce, ‘Inma banda ke mene ne abin sha cikin
maganin mura? Ya ce, ‘Ai ba za ta daina rayuwar
bariki ba. Ta yi shiru tana nazarin dalilinta na
sha,tsabar son shi ne da take yi. Shi kuma ya
kwashe Iyalan shi suka bar mata gidan shi yasa
take sha sabida rage damuwarsa, ga shi ashe za
ta janyo makanta ne, ‘Yar shigarda ta samu a
watse, don ta san in cikin nan ya zube shi kenan
korarta zai yi batada sauran garkuwa za ta jure
ta ci darajar dan da za ta haifa. Ta shiga wata
bakwai lokacind ta cewa Yaya a waya wai tana
son ta fara zuwa awon ciki, ya ce ta fadan in ta
matsu.kin fada min ta yi sai shi ne ya tambaye
ni. ‘Mujidat ta yi miki batun awo? Na ce, ‘A’a,ya
fada min yanda suka yi na ce ‘Ka bari sai ka zo
sai mu yi zancen gani gata, in ya so sai a je
Asibitin a kuma sayi duk wani abu d ake buqata.
Bai amsa min ba ya canza zancen da cewa,
‘Akwai wani bincike dazai kawo ni Kaduna me zan
samu? Na ce, ‘Duk abin da ka ke so. Ya ce,
‘Yanzun ina takura sosai a gidana in na zo zan
dauke ki mu fita a wani masaukin bakin mu dan’
huta. Na ce, ‘Yara fa? Ya ce, ‘Ga gidan Iya. Na
ce, ‘To ma tafi mu bar mai ciki, kar a yi na
wancan karon. ‘A yi ta yi mana, ina ruwana,
daman na san haka za ki ce. Ya ja tsaki tare d
kashe wayar shi. Na sani tabbas rayuwarmu ta
canza yanzun, amma wayaja? Shi ne. Allah yasa
mu dace, ameen. Wata Asabar Aliyu ya nufo gida,
yana karya kwanar unguwar su sai ya ga jama’a
cirko cirko tsaitsaye gungu gungu, wadansu kuma
suna ta maida yanda aka yi,yayin d kunnan shi
ke dauko masa sautin wasu muryoyi suna ihun
neman dauki. Kasancewar shi jami’in dan’ sanda
dole ne ya bincika, don aikin shi ne kare rayukan
al’umma da dukiyoyinsu, ko da ba a unguwarsu
ya ga hakaba, dole ya tsaya.
Don haka ya gangara gefen titi yayi Parking din
Motarsa,yana fitowane wasu matasa sin tsaya
suna dan tattauna batun,Aliyu ya usa gurinsu
fare da yi musu salllama,suka amsa,ya
fambayesu abindake faruwa,daya matshin
yagane Aliyu dan haka yace “yallabai wallahi ‘yan
sara sukane” Aliyi yace ‘yan sara suka kuma?
Yace eh! Wasu matasane ance daga hayi suke
suka fada layinnan suma sara da sukan duk
wansda suka ganiyanunamasa inda
cincirindonbjama’a ke tsaye yace ‘can
meshayinnena Buba suka soka,sannan suka sari
me lemun kysa dashi”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu ya isa gurin daidai ana kokarin sashi amota
yace “bakuyiwa yansada wayaba” ?wabi yace “tin
dazu muka sanar dasu” Aliy yadagawaya yana
sake miran yansanda yana shedamusu cewa a
turomasa mota sabida ‘yan sara suka sun sgigo
ungywarshi ,shine yavasu damar kai masu jikin
Asibiti sannan shikuna yacigaba da gudanar da
bincike jafin isowar yansanda.
Tanbaya yaitayiwa mutaben gari kan yansara
sukan;kasancewar mutanwnmu akwai tsoro da
rashin cikakken wayewa ga wasu sai zuka mi
bashi cikakaken hadinakai.sannanda yanufi
motaesa dan karasa gida,sai yaji wasu matasa
biyu suna magana,dayan yanacewa, “kasan Allah
Aminu su Dawa Adone suka jamana wannan
bala’indashi da Bangis Kauri” Aliyu yace “Kanina
kananyfin Dawa Ado din tsokanarsu yayi?
Duk suja waiwayo suka kalli Aliyu,ganinshu da
nayan Yansanda sai sukace a’a bamusaniba,suka
juya da nufi.n tafiya Aliyu yace tsaya kuji absan
cewa kunsan wani abu,dan Allah kubani
hadinkai.Dayan da akakira Aminu yace,’mufa
zabcenmu daban, ‘yansanda basu da
amana,dazarar kafadi wata magana sai reshe
yajuye da mujiya a kama mutum a tsare”
Aliyu yace ba gaskiya bane,shaci fadine da shrri
irin na wasu mutane suke jifan jami’an tsaro
dashj,mu masu kare rayukan Al’ummane da
dukiyoyinsu bawai masu sharrib,kudinga bamu
hadin kai,tahakane zamu iya gano bara gurbin
al’umma.”
Dayan wanda kebada labarin yace, yallabai
yallabai tsorona kada a kirani shaida,suganeni
insun fito suzo su sassareni”.
Aliyu yace “sam sunanka bazai fitoba, vabu
wanda yasan munyi haka dakai.” Yadafashi.
“Kagama zo nan mushiga daga mota dan kar
wasu sugane kaine kafadamin,kayarda ba
cutardakai zanyiba,taimako zanyi,kaga in ba’a
dauki matakiba zasu iya dawowa.Zaka iya sanin
ko kanwa tsautsayi zai fada?nasan kanada
dangi,da mahaifanka, sannan ga kanka ko
kanada yakinin cewa bazasu dira kankaba?
Saurayin yace “hakane yallabai”
Syka shiga Mota harda saurayin da dayan yace
Aminu.
Aliyu ya kalleshi yace ‘kanina kai ya sunanka?
Nasandai abokinja shine naji ka kira da Aminu”
Yaron yace “Buhari’
Aliyu yace ‘Buhari wane Dawa Ado?’
Buhari yace “Dan dabane,sunada yawa a
ungywarnan,saidai su da bangid sune sukai kauri
suna a ungywarnan”
Aminu yace, “wasuma sunce gudansu Dawa Ado
ana siyar da wiwi,wasu yarsu dake zaman kanata
agubta yake ajiyewa”.
Aliyu yace “to mene labarin wannan fadan?”
Buhari gace,”to nidai mundawo Masallaci jiya da
Magriba dayake layinmu daya da Dawa Ado,sai
naganshi zaune tare da wasu yandaban,
,yaranema wadanda basufi shekara sha shida sha
biyarba,yana fada musu cewa zamu fadawa ‘yan
hayi har naji ya anvaci sunan wani dan daban
hayin yanacewa lallai yanaso ayimasa yankan da
bazai tashiba,ko yatashi kada ya moru.Nidai na
wuce nabarsu,saidai ina zaton kan wiwi ne sjke
fadan, dan naji yanacewa “ankawo mishi kaya
kafin yazo shi wancan ya siye”
Aliyu ya girgiza kai alamun gamsuwa yace, to
yanzu kuyimin kwantabcen gudansi Dawan
dakuma Bangis din, ‘ sukace to.
Nan sukayimasa kwatance yacuro kati mai dauke
da lanbarsa a jiki ya basu,.
“Gashi kusa lanbobina a cikin wayoyinku,sai ku
kirani ko kumin flashing inkira dan insamu taku
lanbara,kunsan dalili?
Sukace a’a. Yace dan kucigaba da bada gudun
mowa cikin hnguwar nan,duk lokacin da kukaga
wabi abu mo kukaji makamancin wannan sai kuyi
maza kukira daya daga cikin wadannana
lanbobin. Ya sanya hannu ta baya yaciru yan
dubu dubu guda biyu ya mika musu tare da
cewa,”Ba cin ganci vane kyauta
nabaku,aikinmuma dazakuyimin ba na kudibane
taimakon kaidakai zakuyi.”
Da murna suka karba, sunyj masa godiya,take
nan suka bashi lanbobinsu,sannan suka gangara
inda suja nunamasa gidansu Dawa Ado da
Bangus Kauri.sanna ya gan ga ra ya ajiyesu ya
wuce hidansa.
Likacin d na ji kwankwasa kofar ina kicin ina
kokarin dafawa yara Indomie, don ni a koshe
nake Iya ta aiko min da dambu, nacishi sosai
bayn La’asar shi yasa. Na nufi kofar cikin raina
ina tunanin ko waye? Ina bude kofa na yi sororo
don bai fada min zai zo ba. Na ce, ‘Oho! Abin
‘Yar haka ne? Ya shigo, sannan ya rufe kofa, ya
kamo ni ya rungume, na karbi jakarsa muka nufi
ciki. Mujidat tana zaune a falo ta ce, Sannu. Ya
ce, ‘Yauwa. ‘Ba tare d ya kalletaba. Muka nufi
dakinsa ina fadin. Kausar, Al’amin ga fa babanku.
Da gudu suka fito dga dakina, muka dunguma
dakinsa mu duka. Na ce daka fada min kana
zuwa Allah d tuni na yi maka abnci na
musamman. Ya ce, ‘Ai rikici na tarar a unguwar
shi yasa da tuni na iso. Na ce, ‘To yanzun me za
ka ci? Ya ce, Me ki ka dafa? Na ce, Ban dafa kmai
ba, yanzu daizan yi wa yara indomie,sai dai
muna da miya a fridge sai na dafa maka farar
shinkafa. Ya ce, ‘A’a ku tashi muje gidan cin
abinci. Na ce, ‘To ka canza kaya mana, ko kuma
ka yi wanka. Ya ce, ‘Duk yanda ki ka ce. Na dubi
Kausar ‘Mu je in ciro muku kaya ki sa musu sai
ke ma ki sa.’Na dube shi. ‘Bari in ba su kaya.
Gira ya daga min na fita. Na dawo na taimaka
masa ya yi wanka. Ya shirya, nima na canza
kaya, duk Mujidat tana zaune a falo tana
kallonmu, sai na ji tausayinta ya tsirga a raina,
na ce, ‘Ki tashi muje cin abinci. Saida ta yi min
wani kallo, sannan ta ce, ‘To. Mun fito sai ya
Aliyu ya ganta, ya ce, ‘Ke fa? Da sauri na ce,
‘Tare za mu je mana. Tsaki ya ja,sannan ya ce,
‘Ni yanzun ba nida damar sakewa kenan? Ban
tanka masa ba, a raina na ce wa yaja? Lokacin
dakuke shanawar ku ai ba ka ce an hana ka
sakewa ba. Da farko yaso mu ci a can,amma
yanzun sai ya ce kawai mu yi take away sabida
bai so zuwanmubada Mujidat. Daga nan sai ya
nausa da mu can gurin kasuwar Bacci, wani katon
shagon saida kayan wuta, na ce me za mu yi
anan? Bai kula ni ba don na lura ya ji zafin
zuwan Mujidat. T.V ya sai mana ta bango
(Plasma),mai kyau sai tsada,sannan ya sayi
resiba,ban san inda zai sa ba. Sannan muka je
wani babban store ya kwasarwa yara kaya har da
keke ya saiwa Al’amin. Yara sunata murna muka
isa gida. Ita dai mujidat duk inda muka je da Ido
take binmu, tare da yatsina fuska,jifa jifa tana
tabe baki tare da tsaki. Ni dai muka yi ciki ta
zauna a falo.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Dakina ya kai T.V, na ce ba na ka ba ne? Ya ce,
‘A’a naku ne,don na lura ke da gidanki,amma kin
bar wa wata falon ki. Na tsura masa ido, ‘Yaya
na gode. Ya harare ni, Lokacin fa dakika samin
suna kin yi alkawarin kirana Sweety Alinki,amma
yanzu sam kin daina na manta rabon da ki kira ni
dawannan sunan. Na ce, Yi hakuri Sweet dina. Sai
na ji su Kausar da Al’amin sun sa dariya.Kausar
ta ce, Momy Abba ne Sweet? Muka kalli juna cikin
dariya na ce, ‘O.K, waton kun tsaya jin mu ne?
Al’amin ya katse zancen da cewa, Abba wai ita
Anty bakuwa sai yaushe za ta tafi? Kausar ta
zabga masa harara, ‘Ina ruwanmuda wata can
Anty Bakuwa. Muka sake kallon juna cikin
mamaki. Na lura fa Kausar ta tsani matar nan.
Nace, Kausar ai ba tafiya za ta yi ba ita ma ta
zama ‘yar nan gidan. Kausar ta zaro ido, ‘Ta
zama ‘yar gidan mu kumma? Ta tura baki,ni dai
Abba ta koma gidansu, kullum sai ta dinga
hararata, ko kuma tayi ta hana mu kallon T.V. Na
ce to ba ga shi Abbanku ya siyo mana wata ba?
Ta yi shiru. Na ce, ‘Kar ki sake yin haka. Ranta a
hade ta ce, to Momy. Mun ci mun sha muna ta
hira har yara suka yi bacci, sannan muka gyara
masu kwanciya, sannan muka nufi dakinshi.Yayo
alwala tare d cewa. Je ki yo alwala muyi Isha’i.
Na yi murmushi , sannan na ce, Wanka zan yi
don ina fashin sallah. Ya runtse ido tare d fadin,
kash! Ga shi gobe zan tafi. Na ce, Kar ka damu
zan yi maka irindabarun da muka sabayi da.
Dariya ya yi, sannan ya ce, shi kenan. Da safe ni
mkadai ce na fito na hada abin kari, sannan yara
suka ci suka fito. Babansu yana kwance na ce
‘Bari in kai su makaranta. Ya mike. ‘Yau ba
Lahadi ba? Na ce, ‘Hadda suke zuwa Asabar da
Lahadi. Ya ce, ‘To ki yi sauri ki zo ki kara yin wata
dabarar. Na yi masa hararar wasa. ‘Bashi yasa na
ce amAuran Mujidat zai taimaka maka ba ya
hade rai, sannan ya koma ya kwanta. Na dauki
makullin motarsa. Bari in ari motar ka. ‘Nan ma
bai tanka ba. Lokacin da muka tafi Mujidat tana
soya kwai a kicin, na cewa Kausar su je su gaida
ta. Kullum dama sai na sa su sun gaishe ta,
kamar kullum sai d ta yatsina fuska sannan ta ce,
Lafiya. ‘Na fita abina. Mujidat tana ganin fitar
Sadiya da yara sai ta maida kofar ta rufe,sannan
ta nufi dakin Aliyu yana kwance sai ya ga mata
tsaye a kanshi tana girgiza. Zumbur ya mike tare
d fito falo, don gudun kar ta kara janyo masa
wani laifin a kan na da. Ita ma ta biyo shi tana yi
masa kallon banza kana tsoro kada matar ka ta
dawo,shiyasa ka fito kar ta same mu tare.ta yi
‘yar dariya. ‘Ai ka gama kuskure tunda har kayi
ajiya a jikina na zo in yi maka gargadi ka rage
nuna tsana da kyama gare ni, in ba haka ba na
rantse maka zan je gidan mahaifiyarka in tona
komai. Aliyu ya ce,’Ai har abada ba zan so ki ba,
kin ci darajar matata data dage sai kin zauna da
mu, banda haka ke din banza. Ta tuntsire da
dariya, ‘Ai ba ka san wani abu ba, ai ita kan ta
matar taka sa’a ta ci d ta kasance mai son
kwatanta adalci, banda haka wallahi da sai ta
raina kanta a wannan zaman da nake yi a gidan
nan, don sai dai inmu dinga kwana da kai gado
daya.ya harare ta, Ni kuma da yake zan tsaya ne
ina kallon ki har ki shigo mini daki,kuma ki sani ni
Allah ya shirye ni. Ta ce, ‘Oho! Yanzun kana
tsammanin cewa kai wani shegen mai imani ne?
Ta yi murmushi mai sauti,sannan ta girgiza kai.
‘Abu daya zan fada maka shi ne ka gode min da
na kawo shawarar auren ka,sannan ka godewa
matarka da ta yarda da in aure ka,ta samawa
kan ta lafiya don wallahi da sai dai ta sallamawa
kan ta domin matsawar ina numfashi duk inda ka
ke sai na bi ka,kuma sai ka yi duk yanda naso. Ya
gyara zaman shi sannan ya ce, ‘Kin yi kadan
shaidaniya. Sannan ya kautar da kai.sam bai
tsammaci zuwan ta ba,sai dai ya ji ta a jikin shi
‘yar barikin ta san lagon shi,wanda baya iya
bijiremata, zuciya muguwar nama har za ta
amince,amma sai Aliyu ya yi ta maza ya hankade
ta duk d tana da ciki, sannan ya ajemata mari a
fuska,ta shafa kumattun tana kallon shi bayan ya
mike yana mata kallon banza,ta yi ‘yar dariya.
‘Dubi yanda idanunka suka canza launi, ban da
cikin jikina da sai na tabbatar maka cewa in ina
nan dole ka rayu da ni,Kasa ba ta amsa ya yi kai
tsaye ya nufi dakinsa ya shiga ya kullo
kofa,sannan ya zauna bakin gado tare da rike
kan shi ya ma rasa wane irin tunani zai yi.Can
kasan makogwaron shi ‘Hasbunallahu Wani’imal
Wakil yake fadi can a hankali ya ji kmai yana
warewa, ya kwanta rigingine ya tabbatar cewa
Mujidat shaidaniya ce, za kuma ta yi duk abin
data fada, auranta kam shine mafita, inbahaka
ba zata jashi zuwa wuta,tunda in tana raye bazai
fasa zinaba.Yadauko wayar shi ya soma kiran
layin matar shi.
Ina daf da gida naji wayata tasoma ruri, nayi
kwana,sannan na daga. ‘Yaya dai Sweety Aly? Ya
ce, ‘Ina kikene? Kin san dai daga ni sai wannan
shaidaniyar a gida. Gabana ya fadi, sam ban tuna
haka ba,nace ‘ga ni nan yaya ina daf da gida. Ita
ce ta bude min gida lokacin da na buga,sai dai
tana bude min ta juya a raina na ce, ‘Hakan ma
nagode. Na aje mota,sannan na nufi ciki. Zaune
na same ta tana sanye da dogon wando na jeans,
sai ‘yar best yanayin shigarta na bata min rai,
musamman in yaya yana gari. Na murda kofar
na ji ta a kulle, na kwankwasa ya bude na bi shi
da kallo, don son in fahimci wani abu, amma ban
gane ba, don haka nace. ‘Lafiya? Ya dube ni, ‘Me
ki ka gani? na ce, ‘a’a bakomai.naga kakirane na
dadene? Ya ce, ‘a’a, kin san ina jiranki ne a sake
yi min irin dabarar jiya.nayi dariya, ‘ai bana
batun dabara barima inyi wanka don ina zaton
anjima zan yi sallah. Damurna yace, ‘Haba? Na
ce, ‘Allah. Ya ce to shiga ina jiran ki. Saidai kuma
ina fitowa na same shi zanzare cikin kakinsa yana
daure takalmi, sororo na tsaya cikin mamaki kafin
nayi magana sai wayarsa ta soma ruri,ya dauka
da sauri. ‘Buhari inajinka. Daga inda nake na jiyo
wanda ya kira da Buhari yana cewa,Yallabai
muna zaune ya wuce kamar yanda nasoma
fadamaka dazun, shi Dawo Ado, malun malun
yasa yana riqe da Adda sannan malun malun din
ta jike sharkaf da jini. Aliyu ya ce, ‘Dan uwanka
Aminu ya kira ni ya fada min wai ‘yan sara sukan
nan sun ce za su sake shigowa anjima, zan fito
yanzu. Yana ‘aje wayar ya dauki dayar ya kira
headquater ya buqaci a turo masa ‘yan sanda
mota biyu. Ina mamakin yanda Yaya keda izza
cikin aikinsa, yanzun nan ya rikide daga soyayya
ya kma zakin maza,ya kama kofa zai bude nace
“Sweet aliy ka manta daniko?” ya waiwayo da
sauri, sannan ya dawo ya rungumeni jikinsa ya
sumbaci kumatuna”ya za’ayi na manta dake?
Ashe zan iya mantawa da kaina kenan?ya dago
fuskata”sai na dawo”na saki murmushi”Allah ya
tsare min kai mai sona”ya sakeni ya fta da sauri.
Sun kama Dawa Ado,Bangis Kauri, sannan suka
dinga fadin sunan yan daban suna kama
su.kazalika sun dire hayi,inda can ma suka
kamasu da yawa,ya mikasu yakuma basu
shawara cewa suyi bincike kan yaran
sosai.sannan su tabbata sun mikasu kotu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Hakanan da dare ina Sallah a dakina,misalin
takwas wanda yanzun yazama na yara,Kausar da
Al’ameen suna kwance ruf da ciki suna
Homework ,Aliyu ya shigo da Sallama,suka amsa
tare dayi masa sannu da zuwa,ya kalli Mama
dake bacci can gefe yace”wai shin mamana tayi
nata Homework din ne? Kausar tace”eh Abba
sunyi tare da mumy”dai-dai lokacin na kammala
addu’a ya tayani shafawa, na kalleshi”sannu da
zuwa” cikin murmushi nayi maganar
yace”yawwa,sannu matata”muka sa dariya, ya
rusuna saitin kunnena yace “kisa yarannan suyi
bacci da wuri” kafin in bshi amsa wayar shi
tasoma ruri.ya daga da sauri,nji yana fadin “Yes
Sir” nace Allah yasa ma zaiyi kwanan gdan yau.
Ilai kuwa, yana gama wayar ya kalleni”
yanzunnan zanwuce Abuja” na zaro ido”Abuja
kuma da daren nan?” yayi dan yake”aikinmu
kenan, ahaka muka yi rantsuwa babu dare ko
rana,duk lokacin da aikin yataso zamu fuskance
shi”na lumshe Ido ahankali nace”yanayin aikinku
yana shafar rayuwarku”ya mike zumbur”muje ki
hada min kayana” Kausar ta tashi zaune”Abba
bari muxo mu rakaka motarka”nace “a’a , ci gaba
da Homework dinki in yashirya zaizo har nan sai
ku raka shi,” tace to. Tara dai-dai ya kammala
komai,dan ban amince ya tafi bai samu nutsuwa
ba, sabida tsoron kada shaidan ya sake ribatarsa
ya kuma kyallo wata,lokacin da muka zo gurin su
Kausar tini duk sunyi bacci. Ya tsuguna duk ya
sumbaci kumatunsu, sannan ya dauki hanya,na
raka shi mota,sai daya tashi sannan na koma
,ban tsaya wani tunani ba na kwanta don Inda
sabo na saba da tafiyar Yaya cikin dare, sai dai
Adduar Allah ya kare min shi.
Kusan sha biyun daramen wata litinin na jiyo ihu
cikin baccina, na tashi da sauri ashe nakuda ce
takama Mujidat. Da gudu na fada cikin dakin tana
zaune dirshan tana juyi da ihu, na ce ta kwanta,
bari na gani ko mota ta da mai. Kafin na dawo
har kan da ya fito sai ihu take har su Kausar sun
tashi nace mota ta ba mai bari in kira Iya. Na
kira ta na fada mata, tacebari ta taho tind dare
bai yi Sosai ba. Kai Mujidat akwai raki, har
nadaina Jin tausayinta, sai dai haushi.Kafin Iya ta
shigo dan ma Ya fito, masha Allah jariri
sambalele, sai dai abin ya yi ta fadar da gaba na
yadda naga yaron tamkar Yaya. Iya ce ta yanke
cibi sannan muka gyara ta tsaf da danta. Kusan 3
dare suka samu bacci, Ni da Iya muka koma
dakina. Ta dubeni. “Sadiya!” na kaleta da
faduwar gaba. Tace, “jaririn nan baki fahimci
komai ba?” Na girgiza kai “A’a iya ban fahimta
ba. Bashi da Lfy ne?” Tace, a’a kama naga yana
yi da mijinki sak, tamkar an tsaga kara, ko
‘ya’yanki basu yi kama da shi ba kamar wannan
yaron, tsorona daya Kar dai ace Gadanga ciki
yayowa wannan yarinyar. “Nayi saurin cewa,
“a’uzu billahi! Iya ba kyau ayiwa mutum
mummunan zato, kin San wannan ba halin Yaya
bane”. Ta ce ‘eh, to haka ne, amman fa mutum
yakan canja daga halinshi da aka San shi dashi.”
na ce, a’a fa iya ita fa wannan da mijinta, kafin
ya mutu mun sha gaisawa da shi. Kuma shi
kamanni hakayake sai kiga baku hada komai ba
amman Kuna kama.” ba don Iya ta gamsu ba
tace to Allah yasa hakanne. Na ce ameen. Nan
mukayi alwala muka kama nafila, addua ta Allah
ya rufawa mijina asiri Kar duniya ta gane wannan
matsalar.
Da safe lokacin da na shiga dakin tana zaune da
danta a hannunta ta tsura masa ido tamkar ba
ita bace tayi ta kurma ihu ba. Na ce ‘kin tashi?”
ta ce, ‘eh mun tashi, kin ga yarona sai kace
Babanshi, naji dadin haka,Dan bazai sake min
musu cewa ba cikinsa bane.” da sauri na ce,
‘kibar maganar nan mana, yanzu bari kuyi wanka
in na kai yara makaranta sai nazo na kai ku
Asibiti.” ta yatsine baki “kin sanar da mjnki?”
nace, a’a kin San Iya tana nan ba dama in masa
zancen ki.’ ta dauko wayarta tana cewa, “ina
ruwana da Mamansa taji. Layinsama a kashe
yake.’ tayi tsaki ta jefar da Wayar, Ni dai na fice
na kama aiki na raina bace, ban cika ganin
laifinta ba Dan shine musabbabin komai.
Da zamu Asibiti na sauke Iya a gida na wuce
dasu. An duba su ance duk suna lfy, muka tsaya
kasuwa na siya abubuwan da basu da shi,sannan
muka nufo gida.
Tsakiyar gado na zauna sannan na soma Kiran
layin mijina, bugu biyu ya daga, nayi Sallama ya
amsa tare da cewa. “Yaya na jiki cool da yawa?”
Na ce, ‘Yaya budurwarka ta haihu.” budurwata
kuma? Ya fada cikin sauri. Na ce, eh Mujidat
danta yana nan namiji……zandakata a anan zuwa
wani lokacin kuma,fatan zaku kara hakuri dani
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347