BABU SO HAUSA NOVEL

DARAJAR ‘YA’YANA PART 2

Darajar Yayana2-01
Posted by ANaM Dorayi on 09:52 AM, 20-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
__________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu’alaikum, barkanmu da warhaka fatan kuna lafiya,nasan kunjini shiru a cikin wannan littafin,lallai kam kusan incemuku babu wani kwakwkwaran dalili face rashin kulawa daga gareku,saidai dayake ni nayi niyya dole incigaba,da wannan nake bawa masu yawan bibiyata hakuri,In Allah ya yarda da sannu zamu kai har karshen littafin, Na tashi na shiga wanka ina yan kun kunai,ko kallona Iya bata yi ba, sosai nayi gayu atanfa fara da sirkin purple ne. Haka takalmana da mayafina duk purple ne, na fesa turaruka sosai.Iya ta kalleni ta ce, da ma na san kun hada bakine shi ne za a gwada min bariki, in dai namijine kuje Allah ya taimaka. Ni dai nayi sororo raina babu dadi, sannan bani da mifita.Har cikin gida Usman ya shigo suka gaisa da Iya, sanan yace zamuje ne ta gaida Ogansu Aliyu.Iya ta ce, menene na shirya karya Usman ku da matarku.Nina haifeku fa har da kukega zaku yi mun wayo, a gaida Gyambo karshen girma kenanko? Usman ya sunkuyar da kai yana dan murmushi cikin jin kunya, ni dai na ce sai na dawo.Da mota yazo na shiga, gidansa muka fara zuwa ya ce inga Abida matarsa minti biyu. Ina yin sallama ta amsa, sanan ta ce kai Amarya kin tsula kyau sosai, taja hannuna zuwa bedroom din ta. Zo muyi yar shawara,Bakin gado muka zauna.Ta kalleni a da banyi zaton zaki zama mai taurin kai ba.Na zaro ido ina kallonta, ta ce, ranar juma’a da daddare mijiki nan ya ci abinci tare da mijina, ina daga ciki ina juyo su mijinki yana fadawa mijina halin da yake ciki na takura.Gashi kinki ki bashi hadinkai, har yana cewa wani dare da kika ki sauraranshi har ya dagawaya ya kira wata yar sanda dake nacin sonshi ta kuma sadaukar da kanta gareshi.Har ta daga sai kuma tsoron Allah ya shige shi, Allah ya taimaka ya tashi ya shiga yin nafila, daba dan haka ta faru ba, me kike tsammani?Na ce, wai Allah, daga nan sai zina.Tace kina da kwamasho ko baki da shi?Na ce, ina dashi.Madallah.Ta dafani yanxu abinda nakeso dake, kinga ke yar zamani ce, ki rike mijinki, in ba haka ba sai wasu su rike maki shi.Na ce, anty iya ce, Allah ba dan Iya ba zanyi duk abin da yake so.Ta ce, to baga shi yau zaku fita ba, in kin dawo Iya ganewa zatayi?In ba ke kika fada mata ba.Nayi shiru ta ce, to kisani kina cikin tsinuwar ubangiji, in yanxu kika mutu mijinki yana cikin wanan halin sai kin hadu da fushin Allah, ma tsawar ba shi ya yafe maki ba.Gabana ya shiga faduwa, na ce, Allah anty nitsoro nake ji ban san yaya abubuwan suke ba, nima bansan yana fushi dani.Tayi murmushi ba wani wahala.Ta girgiza kafadarta, ki amince da mijinki a duk lokacin da ya bukaci haka na rokeki.Na raunana muryata, in na sa muku aure ba?Na ce eh.Ta ce ki ceci kanki daga halaka fa, kin san komai ke ba jahila bace….Muryar Usman ta katsemu da cewa wai me kike kitsa mata ne?Zo mutafi kinji.Ta ce, jeki kada yajimu basusan naji firarsu ba, dan Allah ki kama mijinki hannu bibbiyu ko bakya son shi?Na sunkuyar da kai ina sonshi mana, bari dai in gani ko zan iya ina tsoro.Na fita muka tafi.,ban san ina muke tafiya ba, don kaina yana sunkuye ne ina wasa da yatsuna.Har zuwa lokacin da motar ta tsaya.Ina daga kaina COMMAND GUEST na gani.Ya ce jirani kadan ina zuwa.Gaba na ya shiga faduwa, koda ban san ko inane nan ba na tabbata Hotel ne tunda naga an rubuta guest.Bayan wasu lokuta ya dawo yana waya, danhaka da hannu ya yafito ni, na fito a baya nabishi yana ci gaba da tafiya tare da tin waya.Kuma na fahimci kamar da ya Aliyu suke magana, dan naji yana fada mai ga mu nan yanxu zamu shiga cikin hotel din.Kuma ni zan wuce ne dan Allah kayi hanzari muka ratsa falon muka nufi jerin dakuna yasa makulli yana bude wani daki.Dai dai lokacin sako ya shigo cikin daki wayata, na ciro na duba.Cewa yayi kishiga kijirani kadan my choice.Na kalli Usman yayi murmushi ba da jimawaba zai zo, yanzu zaki ganshi.Na shiga cikin dakin ina dari dari, tare da yankalle kale, ya tako ya shigo dakin.Kada ki damu ya dauki remote ya kunna TV, kiyi kallo ga tashar India nan abin sonku mata.Ya nuna mata wata takarda.In kina da muradin wani abu ga wanan takardan ga numbe waya ki kira ki zabi dayadaga nau’in abincin da kike so ko na sha, za a kawo miki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo, ya ciro
wallet dinsa ya bude ya ciro katin MTN ya miko
min.Gashi ki loda a wayarki.Ya sake juyawa ya
tafi, tare da cewa ki kulle kofar in yazo zai
kwankwasa sai ki bude, na barki lafiya.A sanyaye
na ce, na gode.Tunda ya fita ta gumi na hada,
tunani da zullumin abu biyu ne na farko in ya zo
mai zai faru?Sanan yaya zan kare da fada iya in
na komagida?Ban ma san takaimaimain lokacin
da zamu bar nan ba.Fim din da ake yine ya dan
shagaltar dani, don haka ban lura da lokaci ba,
sai da na kalli a gogo na rude, shida dai dai na
yamma.A raina na ce tafiya zanyi…..kwankwasa
kofar ya dakatar dani, na bude cike da faduwar
gaba, a zatona shine ashe ma aikacin gurin ne
yake tambayata ko zanci wani abu?Na ce a a yace
kada ki damu Oga ya na nan zuwa, ban tanka shi
ba na maida kofar na rufe.A raina nace wato har
sunsanshi tunda gashi suna cewa yana zuwa.Na
ce wa yasani ma ko yana zuwa da mata…..na
katse zancen da cewa a’u’zubillah, ba kyau
munmunan zato.mikewa nayi ina ta kai komo a
tsakar dakin, tunanina wa zan kira wanda
zaikaiwa iya waya in mata bayanin cewa yaya
nake jira mu dawo.Can na tuno da Bello, na kira
wayarsa dan akwi number shi a wayata, kuma
yana kiran Aisha itama tana kiranshi da layi
na.Muka gaisa, na ce dan Allah Bello in kana
kusa ina son magana da Aisha ne, tayaya zaka
taimaka min?Ya ce bani minti hudu zuwa biyar a
kai mata. Na ce nagode. Sai da na bari kusan
minti shida sanan na kira cikin sa’a kuwa ta
daga.Na ce,Aisha taimako nake nema a wajenki,
don Allah.Ta ce na me?Na ce, kin sani ne?Mun
fita har yanzu bamu dawo ba, shine nakeso kije
kicewa iya don Allah kada taji shiru mun nan
dawowa.Ta ce, keda wa kuka fita?Na turo baki
tamkar ina gabanta, nace da wanan ya Aliyun
mana.Da sauri ta ce, au, ke da mijinki kika fita?
Bata jira amsa ba ta ci gaba da cewa, to ba zan
fada mata ba, na zata ma ke da wata ce, to in
shekara ma zakuyi ina ruwanta?Ta ja tsaki.Dan
Allah malama in zakiba mijinki kulawa ki bashi
kulawa kawai, sai an jima ta kashe batare da
nasake jinta bakina ba, nayi sororo ina kallon
wayar.Shi kuwa ya Aliyu daidai wanan lokacin ya
isa gidansu iya.Tana girki yayi mata sannu da
gida, ta ce yauwa ina yar tawa?Ya ce, yace yanxu
zanje in sameta in nayi wanka daga gidan oga
xuwa gidan sauran Abokai na.Murmushi iya tayi
ta ci gaba da cewa, wai ni za’a yiwa wayo, nifa
na haifesu, ni fa duk abinku kar nake kallonku.
Shiri yayi ango sosai, sai zuba kamshi yake yi, ya
nufi masauki na comman bayan yayi tsarabar kaji
da lemuka da kalolin madara masu tsafta. Ya
gaisa da masu tarbar bakin inda wani daya yake
tabbatar masa da cewa a jiyarsa na nan a ciki,
sun lura da ita yanda ya kamata.Kwankwasa
kofar ta re da muryarsa naji, inda yake cewa
Dear my choice.Jikina ya dauki bari, naje na bude
kofar tare da yi masa sannu da zuwa.Na amshi
ledojin hannunsa, kallo yake tayi tunda ya shigo
har ya maida kofar ya rufe, na ajiye ledar na
zauna kan kujerar dake kusa da gadon.Kai tsaye
yazo ya zauna kan hannun kujerar.Dear my
choice kinjini shiru ko?Yayi maganar cikin wata
laulausar murya
Na kalli a gogo gabana ya ci gaba da faduwa,
nace gashi har magariba ta karato, yanzu iya
tana can aiki yayi mata yawa, tana kuma jira
na.Ya kama hannuna me zakiyi mata da zata
jiraki?Na ce abincin dare mana.Ya hada tafin
hannuna da nashi ya sarke.Sanan ya dan matsa,
in kin tare a gidanki wane zai dinga yi mata aiki?
Cikin raunaniyar murya na ce, zan ke aika mata
duk abin da naci.Idanu na suka kawo ruwa don
tunanin rabuwa da iya.Ya dago fiska menene na
kuka?Na ce, ina tunanin rabuwa da iya ta ne.Ya
kwantoni jikinsa.Yi hakuri kanwata, ai ba wani
nisane tsakanin mu da iya ba, kullum nasan
zatazo ta duba ki, in bata zoba kuma mu
zamuje.Na kalli cikin idanunshi, da gaske zamuje?
Ka min alkawari fa.Ya ce, in sha Allahu.Ya ciro
fari kar din hankici mai kamshi daga aljihunsa ya
soma share min hawaye.Tashi kiyi alwala muyi
sallah sai muci abinci.Gurin da na idar da sallar
ya sameni, ya bajekomai gani da shegen kwadayi,
amma fargaba ya hana ni ci.Duk hankalina tashe
yake, ya lura da haka, sai ya soma lallashi
na.Haba Sadiya my coice, me nene naga duk kin
damu?Nifa mijinkine na sunna.Nace, to ai iya ta
ce kada wani abu ya faru tsakanin mu, har sai
mun tare.Ya ce to zata sani ne, ko ke zaki fada
mata?Na soma kuka, ina kallon fuskarshi.Wlh
yaya zata gane.Zumbur ya mike daga kusa dani
ranshi a bacce, ya soma yin magana cikin daga
murya.Kina fakewa da Iya ne kurum dan kawai ki
cucheni, ba fa haramun zan aikata ba.Kinsan ina
kyalekine ina lallabaki, in nace zan gwada maki
isa ba zaki iya kwatar kankiba ko?Jikina ya soma
bari, yaya don Allah kayi hakuri…..Yi mun
shiru.Ya katsane, sai wahala kike bani kina wani
inyi hakuri, ba zan hakura ba, haka nan ba zan
matsa maki ba, amma ki sani baki ba komawa
gida ko da zamu shekara a nan harsai kin yardar
min a bin da ya halasta min.Na fara kuka wiwi
shi kuma ya fice ya zare makulli ya kulle ni ta
baya.Na fada kan gado ina kuka, wata zuciya ta
ce mun gara fa kiyarda dan sai kin dibi kunyar da
bakiso a hannunki, don dan shi namiji babu
ruwansa.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Dasauri na dauki wayata na soma kiran layin
sa.Tayi ringing kusan sau biyar sanan ya daga,
cikin kuka na ce, yaya dan Allah kazo na
yarda….Da zafin rai ya ce, bana so, ke har kin isa
mzacen da zaki ja raina?Bari kiji wani abu, baki
son ki dade kada iya ta zargeki ko?To ina mai
shaida maki cewa nan zaki kwana, in yaso in kin
koma gida sai inga maizai faru.Ya kashe wayar,
ransa ya baci dani sosai.Daya wayarsa ta soma
ruri da sauri ya cirota don in yaji ringingi din ta
daga office ne, duk da ba ganinsa yake ba sai da
ya nutsu da ya daga ya ji muryar.Cikin sauri
sauri yake magana.ASP kana ina ne?Aliyu ya ce,
ina nan kan titin waff Road.Ya ce, yauwa kana
kusa ma, yi hanzari ka iso nan (headquarter) ka
kwashi yara ku nufiunguwar rimi layin dan marina
gida mai lamba tara, yan fashi sun shiga gidan
sunyi fashi.Sanan sunyi gaba da babban yaron
mai gidan.Ga ni nan zuwa ranka ya dade.Aliyu ya
amsa cikin izza, a duk lokacin da aiki ya taso
Aliyu yakan mance da duk lamarin dake gaban sa
matsawar ba salla ba ce.Sun isa gidan da yan
fashin suka shiga, Aliyu tare da inspector Adamu
da sajan Musa, sai kofur Bala.Cikin natsuwa Aliyu
ke kallon ko ina, kafin ya soma magana.Hajiya
sannunku da juyayi.Ta ce, yauwa.Cikin kuka da
rawar murya ta amsa, ya ce ina mai gidanki?Ta
ce, baya nan, kuma dama sunce shi sukazo
nema.Ya kalli kofur wanda tuni ya soma rubuta
komai, ya sake maida kanshi ga Hajiyar.Ta ina
suka shigo?Ta ja majina, sanan ta ce ta kofa.Ta ci
gaba, sun ga Yusuf ya shigo a cikin motar baban
su to sunyi tsammanin shine tunda gilashin mai
duhu ne.Don haka sai suka biyo shi.Aliyu ya ce,
shi Yusuf din daga ina yake?Ta ce, daga masalaci
ya ke, babansu yayi masa waya, cewa yaje ya
dauko motarsa.Don ni ya soma kira wai in kira
masa Yusuf ya dauki motar, sai na ce ya kira
layin sa ya fita masallaci.Kuma ba lallai bane
daga can ya dawo gida ba, Aliyu ya gyada kai
alamun gamsuwa sanan ya ce, motar ta samu
matsala ne?Ta ce, a a.Sau biyu ana biyo shi ana
kai masa hari a motar da dare shi ne dalilin da
yasa sam bayason karfe tara tayi masa a motar
na dare.Yau ma mitin ne zasuyi da ya taso musu
da gaggawa kuma bai san lokacin da zasu tashi
ba.Aliyu yayi taku zuwa tagar ya daga labulen
windon yana kallon harabar gidan haskenta
kamar duhun magariba baiyi ba.Ya waiwayo ya
dubeta wace mota ce daga cikin wayan nan
motocin guda uku?Ta karaso ta daga dayan
labulen windon wanacan (hondar ce) baka CRV.Ya
saki labulen yanzu mai gidan ya sani?Ta ce, a a
yana kashe duk wayoyin shi ne in zasuyi
mitin.Ina ne gurin aikin nashi?Aliyu ya bukata
cikin rawar murya ta ce, shine manaja a first
bank.
Aliyu yayi shiru kamar mai wani nazari, can ya ce
zaki iya fada mun kamannin yan fashin?Ta ce,
eh, zan iya.Babban su baki ne dogo kuma kamar
yanada yare, don hausarshi bata goge ba.Sai dai
kila muslmi ne, sauran kuma biyu fararene ina
zaton fulanine, biyun dake waje ne ban tantance
su ba.Aliyu ya jefeta da wata tambayar, yaya kika
yi tsammanin musulmine? Ku ziyarci blog dinmu
domin karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce, haka kawai naga kamar musulmine.Aliyu
yayi guntun murmushi.Bari mu barki haka, yanxu
bari muje mu dora bincike.Ta sake fashewa da
kuka.Ran ka ya dade ka taimake ni yanzu yaya
za’ayi mijina ya samu labari dan kada ya fito
sukama shi?Aliyu ya ce, kada ki damu, zamu
bashi kulawa da tsaro, sanan ki saurara sosai
nasan zasu kiraki ina zaton garkuwa zasuyi
dashi.Kiyi mana saving din number, in kuma ba
number ki kiramu ki sanar da mu.Ta ce, to
yallabai na gode.Ya ce ba komai kiyi adu’a.Suna
fita ya kira AC ya koro masa komai, AC ya ce, to
yanxu ku fara ji da maigidan nata, sanan kunsan
yanda zakuyi ko?Aliyu ya ce, yes Sir!Sai dai ina
kake ganin za a bashi mafaka tunda ba dama mu
barshi ya koma gidansa?AC ya ce kuxo nan dashi
daga nan sai a kaishi inda ya dace.Aliyu ya kara
cewa yes sir.Ya dubi yaran kumaje first bank.Sha
biyu da minti ashirin, Alhaji auwal ya fitoa rikice
daga cikin banki, gama mitin dinsu ke da wuya
police commissioner ya kira shi bayan ya kunna
wayarshi.Ya fada mashi cewa ga yarana nan zasu
taho dashi dan kare lafiyarsa.Alhaji auwal ya ce
saboda me ranka ya dade?Commissioner ya ce,
masu bibiyara ne suka shiga gidanka, amma ka
kwantar da hankalinka za a kama su.Suna tafe
cikin mota Alhji sai adu’a yake yi yana tunanin
me ya tarewa wadan nan bayin Allah?Kofur ya
ce, Alh kaji cewa sun tafi da yaronka?Aliyu yayi
mashi tsawa da cewa kofur?Da sauri kofur yace
yes sorry sir.Alhaji Auwal ya ce ranka ya dade
wane dan nawa dauka Yusuf? Aliyu ya ce kada ka
damu, in mun isa can zakaji komai a bakin
yallabai, kuma duk abubuwan zasuxo da sauki.
Alh. Auwal ya ci gaba da adu’a.
Ofishin commissioner yayi tsit tamkar babu
mutane sai karan (ac) da na fanka.CP ya kalli
Aliyu dake kame, ya ce nasan kana da kwazo
Alhamdulillahi,yanzu sashin binciken mu na
takama da kai.Domin aikinka kanayinsa da
karsashi gami da izza.Ya kalli Alh. Auwal kada ka
damu Alh, babu abin da zai samu yaronka.Zamu
baka kula shi kuma zamuyi dauki badadi da
su.Alh, ya ce, kana ganin ba zasu kashe shi ba?
CP ya ce, ai kudi zasu nema munsan irinsu, sai
dai yanda tayi kwatancen shi ina zaton bako ne
kila kuma ya jima yana yi bamu taba arba dasu
ba ne.Amma wanan karon in sha Allah za mu
hadu.Ya kali Aliyu ASP aje ayi shiri yanda ya
kamata.Ina bukatar barayin nan tako wane hali
sai dai banda kisa zan saurari wayarka a ko wane
lokaci kwa iya tafiya
Sai da Aliyu ya tunkari gida sanan ya tuno da
wata Sadiya, amma duk da haka bai wani damu
ba dan yasan zata sami kulawa yan da ya
kamata.Ya sake ciro waya ya kira, jim kadan aka
daga, ya ce Ibrahim dan Allah ajiyata na nan?Aiki
ya rike ni da safe zan turo aboki na ya tafi da
ita.Ibrahim ya ce ba ko mai yalla bai.Sun saba da
Ibrahim ne sakamakon wata matsala da ta taba
tasowa a Hotel din su Aliyu suka bincika case
din.Ibrahim shine me kula da dakunan kwana na
cikin Hotel din.Motar yansanda tayi faking a kofar
gidansu Aliyu ya shiga gidan da hanzari.Sai da ya
gama shirinsa sosai sanan ya nufi dakin iya.Tana
kokarin fitowa suka ci karo, yace iya na kama
hanya zantafi wajenta aiki ya taso.Usman zai tafi
ya daukota ko da gobe ne.Kar ki damu canma
gida ne gidan Oga ne.Haushi ya hanata magana,
Aliyu ya dafa kafarta, ki min adu’a iya da yan
fashi zamuyi arta bu, kin san aikin mu bakin rai
muke yin shi.Ta ce Allah ya baku sa’a.Gudu gudu
ya fito.Da kallo ta bishi har ga Allah bana son
aikin dan sanda amma bata so ta bata rai a kan
haka, dan kada ta tauye shi.Ta tabbata adu’ar ta
ita ce daukakarshi, fushinta zai iya tauye shi a fili
ta furta, Allah ka yi wa yaran nan Albarka
dukansu, ka dorasu a kan hanya ma daidaiciya
amin.Nikam a a lokacin ina can tsoro, fargaba da
bakin ciki sun isheni.Kai har da nadama.Naji
haushin kaina da naki bin umurnin mijina, gashi
yanzu ya tafi yana fushi dani.Nasan mala’iku ma
ba zasu raga min ba, kuma iyar da nake cewa
zata yi mun fada in taga na dade, to sai dai ta
kashe ni.Dan ina ganin tabbas nan zan kwana.Da
na bi umurninsa kila da yanxu mun tafi gida cikin
jin dadi.Kila ma yayi ta shi min albarka, mala’ku
suna amsawa.Naja tsaki tare da cewa, kash!
Nima ban yi ba wlh.Haka nayi kwanan zaune,
danma na rage daren da yin nafilfili, sai da nayi
sallar asubahi sanan na kwanta.Bacci ya tafi dani,
ban farka ba sai kusan sha daya.Kwankwasa kofa
ne ya tasheni, nazo na ce wanene?Ya ce, Ibrahim
ne.Na ce, ai ya rufe dakin ya tafi da makullin.Ya
ce, ba ko mai ga wani makullin, me kike bukata?
Nace ba ko mai, akwai abinci a nan dakin dayazo
dashi jiya.Ibrahim ya ce, to shi kenan.Ina jin
takun tafiyar sa, na zauna a gurin dantsabar
takaici, bani da ma ranar tafiya gida ke nan.Shi
kam dai dai wanan lokacin yana gidan Alhaji
Auwal cikin falonsu inda yake sauraron bayani
daga bakin Hajiya.Yanda sukayi da yan fashin da
suka kirata.Ta ce, kamar yanda kayi zaton zasu
kira sunkira ni yau ya da safe.Aliyu ya ce, karfe
nawa?Ta ce takwas da rabi dai dai suka ce kudi
suke so naira miliyan uku da rabi.Sun ce in har
ba a sami kudin ba zuwa jibi zasu kashe shi,
kuma sun ce basa son jami’an tsaro su shigo ciki,
kuma basa so a nemi ragi.Me kika ce musu?Ta
ce, ni kuma duk abin da suka ce da to nake ta
amsa musu. Ya gyara zama ya ce, ina suka ce a
kai musu kudin?Wai filin golf.Ina number da suka
kiraki?Ta dauko wayar ta fito da namber ga ta
nan.
Ya amsa ya dauki number sanan ya fita harabar
gidan yana sanar da CP halin da ake ciki.CP ya
ce, ka tafi da layin kamfanin su, wane layi ne?
Aliyu ya ce (MTN) ne.CP ya ce, maza ka tafi dashi
ka tambatar kayi abin da ya dace da wuri, dan
kila cire layin zasuyi ko kuma anjima su kira da
wani layin da ban.Aliyu ya ce, an gama sir.Sai da
yaje office din Usman sanan ya tuna da
Sadiya.Bayan sun gama magana akan abin da ya
kai shi, dama usman MTN yake aiki, sanan ya ce,
wanan yarinyar mai shegen tsoron tsiya, kuka
tayi ta min na barta na tafi abina.Idan ka tashi
dan Allah katafi ka taho da ita don ni ko ganinta
bana son yi.Usman yayi murmushi, sanan ya ce,
kayi mata uzuri, kasan yarinya ce sai a
hankali.Usman ba da bata lokaci ba ya sanar da
manajan su, nan take aka soma gudanar da
bincike a kan lambar.Sun gano layin a yanzu baya
kan waya, amma sun hada komai yadda da an
dora shikan waya zasu gano inda mai layin
yake.Nan take kuma ya kira CP yayi masa
bayani.CP ya ce, good! Kara zage damtse in kuma
kana bukatar yara duk sanar dani.Yes sir!Inji
Aliyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na idar da sallah azahar ke nan sai naji alamun
ana bude kofa, fatana Allah yasa yaya Aliyu ne,
in sha Allahu yanzu nan zan bashi mamaki
Sai dai kashi!Ya na budewa sai naga yaya Usman,
ya ce tattaro kayanki muje gida.Na dauki jakata
da mayafi, sanan na gaishe shi, ya amsa tare da
cewa ki kwaso lemukanmana.Na ce, na kishi da
su. Ya ce, ai kya kai wa iya tsara ba ko kina nufin
gidan Oga ba a baki ko mai ba duk da cewa kin
kwana?
Yayi tambayar cikin zolaya, na dawo na dauka,
har ya taya ni sai lokacin naga Ibrahim din da
suke nagana, gajere ne baki.Sai da muka tsaya
Marhaba Store ya kara min tsaraba wai harda
turmin zani matar Oga ta ce a ba Iya.Da zan fita
nace masa nagode, ya gai da anty Abida, ya ce
zata ji.Sanan ya ce, ki saki jikinki don kada ta
gane ba can kika je ba.Ina yin sallama iya tana
zaune, cikin faduwar gaba na isa gurinta ina yi
mata sannu, ta amsa fiska daure.Jikina yayi
sanyi, nayi karfin halin cewa.Iya kin ganni sai
yanzun?Tun da yaya ya kaini ya Aliyu bai zo ba
har sai da na kwana, wai suna aikin wani case ne
a hannun sa.Iya ta ce, kai ma dallah da jin haka
sai nayi shiru, don na san zance na bai shiga Iya
ba, na mika mata leda.Gashi inji matar ogan yaya
din wai in baki tana gaida ke.Sai naga iya tayi
murmushi ta girgiza kai, sanan ta ce an gode.Tun
lokacin ban sami bakin magana ba sai daki da na
shige na kwanta.Har yanzu haushin kaina nake ji,
da na sani nabi umirnin miji na, gashi wanda
naki don ita bata yarda ba, kuma nayi imani ko
da mezan ran tse ba zata yarda da ni ba.Aliyu
yayi nasarar kama dan fashin nan tare da
taimakon masu layikan wato network na
waya.Don yan fashin sunyi anfani da layika
dabandaban, ya kama oga tare da wani yaronsa
guda daya, jim kadan bayan an basu kudi sun
saki yaron.Sun dauki hanyar kawo da a lamun
zasu bar Kaduna ne, ya harbi tayarsu sanan ya
harbi ogan a kafa.Sauran sun gudu shi kuma
dayan tsayawar da yayi zai dauki kudin daga but
din motar shi ya kawo Aliyu yayi nasarar kama
shi.Wanan gaggarumar nasarar ta sa an karawa
Aliyu girma daga ASP zuwa DSP, inda aka tara yan
jaridu suka watsawa duniya.
Duk kwanakin nan da aka dauka sam Aliyu baya
shiga harka ta, in na gaida shi zai amsa amma ko
kallo ban isheshi ba.Haka nan har daki na same
shi don inyi masa murna kan karin girman da ya
samu, amma sai ya ce dan Allah in fitar masa
daga daki.Har Iya ta na ce mun Allah ya kara,
tun da na ba da kaina ba loka cin da ya da ce ba
ai yazama dole in jure wulakanci, bani da hujjar
yin musu dole in yi shiru.Gadan gadan ya tada
aikin gidan sa, da alamu ya sami kudi, ranar
wata a Abar bai fita da wuri ba.Sai da suka shirya
sanan sun fita hanya sanan ta soma yi masa fada
me yasa yake yiwa marainiyar haka?Ya ce, bata
jin magana ne, gara ma ki mata fada tun yanxun
don ba zan dauki gaddama ba.Sunje iya nata
santin gidan, ta ce gobe kawo kayanta ko?Aliyu
ya ce, amma na dakin anjima zan kwasosu har
da TV da su Radiyo, kema na sai miki TV.Ta rinka
godiya.Washegari makota da yan uwa tare da
matan yayan mu sukazo suka yi mun jere, da
dddare kuma aka yi mun rakiya.Iya tayi mun
fada sosai, kuma ta kara nanata mun cewa tunda
ni na dage da son ya Aliyu lallai in lallaba
halayanshi.Don bata so in kawo mata wani kara’i
sananta sa mana Albarka tare da yi mana adu’a
tagari.Kowa ya tafi sai ni daya, nayi sallar isha’i
da shafa’i da wutiri, sanan nayi wanka, kwalliya
sosai nayi duk da cewa ina cike da fargaba zai
kalleni ko ba zai kalle ni ba.In ma ya kalleni ni
me zai faru?Goma da wani abu naji ana
kwankwasa kofar gidanmu.Da sauri naje na bude,
shi daya ne kuma sanye da kakinsa na dan
sanda, ke nan shi Abokanai ba zasu rakosa ba
kamar kowane ango.Na amshi kayan hannunsa,
jakace da leda tare da yi masa sannu da zuwa,
ban zaci zai amsa ba, amma ga mamakina najini
a jikinshi ya rumgumeni tsam.Sanan ya amsa da
yauwa sannu.Ina makale a kafadar shi ya kulle
gidan mu.Ina mamakin halin yayan mu sosai,
tamkar bashine yake gaba dni ba.Abaki yayi ta
bani kazar da ya shigo da ita tare da madarar
holandia.Duk fargaba ya cika ni, amma haka
naita sha har sai da yaga kamar zanyi amai, ya
ce, kin koshi?Na ce eh.Munyi Sallah inda ya dafa
kaina yayi mun addu’a.Bai bata lokaci ba gurin
ibadar aure, wasanninsa sunyi mun nauyi.Don
haka na soma rokonsa yayi hakuri, mai makon
haka sai yaji kamar wata sarewa nake busa
mashi.Nasha wahala a wanan daren nawa na
farko, domin duk wani haushinsa sai da ya huce
shi, sanan ya dawo yana tausaya min.Don shi da
kanshi bai sai saita kanshi ba.Shi ya taima ka min
na gyara kaina.Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ba mu jima da kwanciya ba aka kira sallah, ya
tafi masallaci nima nayi tawa sallar.Naso
kwanciya amma sanin cewa zai fita da wuri yasa
ni shiga kincin don hada abin kari.Lokacin da ya
dawo zatonsa zai sameni a kwance, sai ya ganni
kicin.Ji kawai nayi an rumgumeni ta baya.Na
gaida shi ya amsa ya ce, naje nayi bacci don
yasan ina jin bacci, na ce ba komai inya fita zan
kwanta.Tare muka karya, sanan ya ce, inzo in
cuda masa bayan sa tun ina jin kunya har na
gyare don kuma yariga ya tsomani cikin
ruwan.Tundaga ranar komai tare muke yi, wata
masifafiyar soyaya yake nuna min har na dinga
mamaki, sai dai ina gyaruwa wajen kwanciya.Don
ya Aliyu mabukaci ne fiye da zatona, rana, safe,
dare office ma sai ya dawo, haka nayi ta jurewa,
saboda yana ririta ni kamar ya hadiye ni.Satin
mu biyu nayi fari fiye da da, fatata ta goge,
amma na rame.Dan Almajirin da ya so min shine
ke min aike, kullun sai na saka mai abinda muka
ci ya kai ma iya.Ranar da nacika sati biyu ranar
iya tazo, dukinda nayi iya tana da ido, bayan na
bata ruwa da abin tabawa sai na zauna kusa da
ita ina cewa iya nayi kewarki sosai ke fa?Ta ce,
Sadiya kewa ai ba a magana.Amman kuna zaune
lafiya?Na ce lafiya lau, Iya.Yaya na ji dani, baki
gani ba.Tace Sadiya ni sai naga kin rame, kina cin
abinci kuwa?Na ce, ina ci mana.Aka kwankwasa
gidan, na ce gashi nan ma.Da sauri naje na
bude, ya manneni a jikin sa na ce iya tazo.Ya ce
tana nan?Na ce eh.A zatona zai sake ni amma
har fallon mu saida ya zauna sanan na zame na
barsu suna gaisawa da Iya.Na kawo masa ruwa
da abinci, yace my choice ba zan ci abinci ba,
dama nazo ne in dubaki kawai don na kira
wayarki a kashe.Nace yanzu aka kawo wuta, ka
kuma san batir din baya rike chaji.Ya ce, haka
ne.Zan chanja maki wayar ma, Iya ma in sai
mata.Tace ni yanzu gadanga in ka hada ni da
waya ban san yaya zanyi da ita ba.Na ce, zaki iya
mana, mun gode yaya.Yayi murmushi tunkafin a
siyo?Ta ce, ai nasan tunda ka furta zaka
aikata.Iya ta ce, gadanga kai naga kayi bul ka
kara kiba ita ko yar tawa duk ta rame.Ya kalleni,
ashe bani kadai nake ganin wanan ramar ba, to
ko Asibiti zamuje?Na ce, yaya babu inda yake
min ciwo sai muje Asibiti?Yace rama ciwo ne My
choice, zasu baki magani.Iya ta ce, ni da na zaci
ko rigima kuke.Ya ce, haba dai, ai yar taki tana
da biyayya.Iya tayi murmushi sanan ta ce, haka
nike so,Allah yayi muku albarka, ya baku yaya na
gari.Yaya ne, ya amsa da amin.Tare da dago
haba ta.Iya ta ce bari na tafi.Naje daki na dauko
dubu daya na ce, iya gashi, ta ce ina kika sami
kudi?Na ce, in abokan yaya suka zo suka bani, ko
na bashi sai ya ce in ajiye abina.Kuma ni ko katin
waya shi ke loda min.Ta amsa tare da ce min
Allah ya anfana.Na ce, Iya da kin dan bari sai
anjima.Yaya ya harareni ke zakiyi mata aikinta a
gida?Na ce, (cikin shagwaba) ba ina kai mata
kullum ba, ia yana isarki ko?Ta ce har ma in rage
in ba wani.Sai dai duk da haka ina yin girkin
saboda almajirai ko yan ciranin nan na
mokatanmu.Na ce, har yanzu iya kina ci dasu?Iya
ta ce, wanda ka bada shine naka.Nace to ki tsaya
zanyi da yawa sai in sa miki.Aliyu ya kawo hannu
ya dan mintsineni gefen ciki na, tare da cewa
sauran aikin ke zakiyi mata?Iya ta nufi hanyar
fita tana fadin Sadiyayyena kina in zauna shiko
gadanga korata ma yake.Da sauri kuma cikin
dariya ya ce, lah, iya bankoreki ba, nima yanxu
zanfita nazo duba ta ne kawai, kuyi zamanku ni
bari na tafi. Duk muka sa dariya, Iya ta ce a a
yayan nan ni dai naji dadin yanda na sameku
haka, fatana Allah ya kauda shedan tsakanin
ku.Ta bude kofar gidan ta fita, ya bita nikuma
nayi mata alkawarin xuwa inyini in an
kwanabiyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan ya dawo daga yi mata rakiya ya sameni
ina gyara gurin, ya makaloni jikinsa ya dago
fiskata.Sarai kinsan abinda ya kawoni, shine kike
rokon iya ta zauna ko?Gaba na ya fadi, amma sai
nayi yake tare dafadin ba haka bane.Muka nufi
dakinsa.Na rasa duk lokacin da yaya zai zo mun
da wanan batun gabana ya dinga faduwa
kenan.Na kasa sabawa.Ko shi ke sani rama?
Oho.Kawaye na duk wace tazo sai tayi zancen
ramata, haka Aisha, ta damu da son jin dalili
Na dage kan cewa ba ko mai, tunda bai kyautu in
fada mata yanayin mijina ba.Munje Asibiti likita
shima ya sha mamakin jin banda matsala kuma
ba inda yake min ciwo, amma na rame.Sai dai ya
ruvuta mana magunguna masu sa cin abinci,
amma duk da haka sai a hankali.Wani dare anty
Abida ita da Usman sun kawo mana ziyara
munata hira, sai Aliyu ya kawo batun ramata, aka
danyi zancen har Usman yana tsokanata da cewa
ina tsoron kishiya ne ki daina tunani, aboki na
naki ne ke daya.Nayi dariya sanan na ce, nasan
haka shima yasan haka.Yaya Aliyu yayi dariya.My
choice ban maki alkawari ba fa.Na ce, yaya kaima
kasan ko bakai min alkawari ba kai nawa ne ni
daya.Abida taja ni bed Room dina muka zauna
bakin gado, ta kalleni wai me yake damunki? Na
ce, ba ko mai wlh.Ta ce, ki fada mun ban sani ba
ko zan iya taimakonki.Nayi shiru ina nazari, can
nace anty ba ko mai, Allah sai dai ina zaton ko
dan yaya yana da yawan buka ta ne?Kin san
Allah anty na yaya bashi da hakuri hatta kai da
na ganshi ya dawo gaba na ya dinga faduwa ke
nan.Ta kada kai zancen ke nan, amma wanan ba
abin damuwa bane, da farko ki daina tsorata har
gabanki ya dinga faduwa.Kisa haka aikin da ya
zaman maki dole, aure bauta ne, in zakiyi sallah
gabanki na faduwa?Na ce, a a.Ta ce aikin gida fa?
Na ce, a a.Ta ce, wanan ma kisashi cikin dolenki,
tunda zama ne ba na kare ba.Gashi baki son
kishiya.Tayi dariya sai dai zan fada maki wasu
abubuwa da zasu taimakeki, dauko biro da
takarda.Na ce, to.Na tashi na dauko memo, ta
soma bayani kamar haka:
ki samo Dabino,Zuma,Aya, da Cukui zaki maidasu
gari ne, sanan ki dinga zuba madara peak da
zuma kina sha kullum safe da yamma.Kinji daya?
Na ce eh, na rubuta.Ta ci gaba, ki samu,kankana
ki dinga yawan shanta har kwallon,na ce gashi
kankana bata dame ni ba, ta zaro ido to kuwa ta
dame ki, kuma kya iya yanyankata ki zuba mata
madara peak ki dinga sha shima har
kwallo.Sanan a kai na kan Akuya, ki dafa shi da
romo, sai dai bazaki zuba mashi mai ba,
maimakon mai ridi zaki zuba da yawa ki cinye ke
daya.Haka kuma zaki sami garin dabino ki fasa
kwai da madara peak ki juya ki shanye.Nace wai
zan iya duk wanan?Ta ce, ki gwada tun gobe zaki
sanya ya nemo maki amma karki fada masa
dalilinki na son kayan, kawai kice zakiyi anfani da
su ne.
Kan batun ramarki kuwa, ki canza abin kari, da
me kike karyawa?Na ce,Tea ne sai Bread da Kwai,
watarana inyi kunu da kosai, ko indomie da
kwai.Ta ce ki koma cin dankalin turawa da
agada,ko doya da kuma kwai, in da hali harda
farfesu.Shayinki kuma ya zama yaji sugar da
bota, milo da madara.Ki zuba sosai yayi kauri
kisha.Sanan kirinka baccin rana shima baccin
yana sa kiba, sanan da daddare kici abinci
sosai.Na ce, to anty na gode.Ta ce, ba komai, ke
dai kada kiyi wasa, in kinyi su da kyau na tabbata
sai kin dawo neman wasu.Ko da yake ban fada
maki na tafin hannu ba,kin san hannu yana daya
daga cikin mai aikawa da sakonni.In mijinki mai
yawan kama maki hannu ne, ki samu zautun ki
kwaba da suga ta narke, kullun in zaki kwanta ki
rinka shafe hannunki.Sanan ki rinka shafawa a
lebunanki, nace to na gode anty sosai.Sallamar
yaya ce ta katse mu, ya ce, me ta baki kike ta
godiya?Nace abubuwan karin kiba ne wanda zan
rinka karin kumallo da su.Ya kalli Abida dama
zaki iya wanan taimakon amma kika share mu?
Muka sa dariya harda shi.Ya ce, mun gode.Ta ce,
ba wani abu bane wanan har da za ayi mun
godiya.Kai dai ka dage da siyo wa.Ya ce, in sha
Allahu ko su ke nan kudin za a siya, me nene da
me nene za a siya?Na ce, na rubuta zan nuna
maka.Yayi murmushi, to da kyau, yace kizo, abiki
yace zaku biya ta gidan yar uwarki ko?Ta ce, eh,
tare da mikewa na shiga dube duben me zan
bata, turare na bata mai kyaunace ta kaiwa
Ummulkhairi.Ka fin ya dawo da ga rakasu, har na
gama rubuta abinda ta ce na rinka karyawa da
shi,ya ce agada da dankali sai da safe, nayi
godiya da cewa Allah ya kaimu.Cikin satyn na
hada duk wani abu da anty Abida ta fada mun,
na shiga anfani da su.Kafin wata daya naga canji
sosai, yanzu bana wahala da duk dawainiyar da
miji na yazo mun da ita.Sanan nasoma cika ina
cika kayana gwanin sha’awa.Shi kanshi yaya wani
sabon ji dani ya sake ko mai tare muke yi in har
yana gida ni dashi mun zama abu daya.Ko tari
nayi sai ya tabbatar ba na cutarwa bane, haka
nima ina binshi sau da kafa, da ya nuna ra’ayin
abu zan masa balle ya ce my choice ina son
kaza.Ai in na soma sai ya gundire shi, duk abinda
bai so na kiyayeshi har abada.Shinfidar da muka
yiwa rayuwar mu ba zan iya bada labarinta ba,
kowa yana mamakin mu tamkar mun shafe
shekaru goma muna soyayya kafin muyi
aure.Muna cikin wata na uku iya ta matsa masa
wai sai ya maidani makaranta, form din (N.C.E)
ya sai min bada bata lokaci ba na zama daliba a
makarantar horas da malamai dake riga
cikun.Aliyu ya ce, ya zama dole in nemi avin
hawa ko don ke.Na ce Allah ya bada iko.Ba da
jimawa ba kuwa ya ,mallaki motarsa dai dai ta
talaka.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Don haka bani da matsala sai dai yanayin aikin sa
ya ce in ya sami lokaci zai rinka koya mun, na ce
to.Ban jima ba na iya mota, sau da yawa ni ke
kaishi gurin aiki in dawo, sanan in tafi
makaranta.Kai yaya ya nuna mun dukkan gata, a
lokacin jini ke babu matar da ta kaini sa’ar zuwa
duniya a zamaninnmu. Wata safiya na farka da
zazzabi, mura, ciwon kai da sauran su, gashi
ranar yaya ba gida ya kwana ba, saboda wani
case da ke hannunsa.Bana kiranshi in dai yana
wurin aiki, amma shi in ya sami lokaci yana kira
na.Ina kudindine a kan gado naji ringing waya ta,
da kyar na lallaba na dauko, na daga.Ya ce, my
choice kin wuni lafiya?Cikin wata murya na ce,
lafiya lau.Ya ce, me ya same ki naji ki haka?Wani
dan kukan shagwaba ya subuce mun na ce,
zazzabi.Nanfa ya rikice sai gashi a gida bayan
minti ashirin.Banyi ko wanka ba ya sani a mota
sai asibiti, gwajin farko ciki ya bayyana, murnar
da ya Aliyu ya dinga yi ta rinka bani mamaki.Kula
da tarairaya ina ganinsu gurin sweet Aly na da
iya, cikin ya sa ni yin kyau, duk da na sha wahala
kafin yayi kwari.Sanan na bude nayi kiba gwanin
sha’Awa.Lokacin da cikin ya tsufa sai kuma na
kumbura abin da yayi matukar daga hankalin
yaya.Duk da cewa likitan ya ce babu
matsala.Cikin haka aka chanja yaya zuwa kogi,
ranarda ya zo mun da maganar na sha kuka.Duk
da ya zaci dama zanyi rigima bai tsammaci har
haka ba.Yayi ta lallashina da cewa, sadiya my
choice,ki kwantar da hankalinki.Ai duk matar mai
kaki San sanda ko Soja da sauransu, dole ta
kwana da sanin akwai yawon zaga duniya.Banzaci
zan dade haka ba tare da an canzani wani gari
ba.Na shafa cikina yanzu baka nan zan haihu?In
katafi yanzu sai yaushe zan sake ganinka?Ya ce
da na sami sarari zanzo, na kwanta a jikinshi.Ni
dai zanbika sweey Ali kaji yaya na?Ganin yanda
na rikice sai ya ce, to shi ke nanmu tafi tare ko?
Na ce, to sanan nayi shiru.Ana gobe zai tafi yaje
suka hada baki da iya,na zage ina ta hada kaya
har yana taya ni, sai ga iya tayi sallama.Na ce,
sweet yaya na dubi iya tazo kamar tasan zamuje
sallama.Iya ta shigo har cikin daki na, ta kalli
kayan da akwatinan ta ce, wanan fa, kwalima ce?
Na ce iya kin manta gobe ne fa zamu tafi can
jihar kogi inda aka tura yaya.Iya ta ce, zakutafi ko
zai tafi?Ina zaki tafi da wanan katon cikin ga
kumburi?Na kalli yaya na wanda ke ta aikin jera
min kaya na a cikin a kwati.Ni ina kwasowa daga
cikin sif.Kin kallona yayi, sai da na ce yaya!Ya
kalleni na ce, kaji kuma wai ba tare zamuba, inji
iya?Ya ce, eh, a a ai kinji ta ce saboda cikinki na
ce, tabdi jan!Ni kam ba zan zauna ba.Iya ta ce,
lallai Sadiya ba inda zakije yar dadi muji, ni yanzu
ma zuwa nayi in tafi dake.Na saka kuka, iya
sororo tayi tana kallona, shi kuma sai ya tashi
tsam ya dawo kusa dani.Iya kije gida zan kawo
ta.Iya ta mike ai ba wani lallashi ba in zata zo
dan ma kada ka sake yi mata karya.Ke ko yanxu
ance ki bishi kya je?Na ci gaba da kuka na iya dai
ta tafi tana cewa sai kiyi ta yi.Tana fita ya
rungumeni, haba my choice ni na lura iya tafimu
gaskiya.Ki bari in kin haihu sai muje, ina zo zan
tafi dake.Yanzu kinga dole inje in ga yanayin
garin.Na ce, yaya dama na san cewa baka damu
dani ba, can na san baka sona.Ya manneni a
jikinsa, inji wa yace bani sonki?A zaman da
mukayi baki fahimci matsanancin son da nake
maki ba?Na ce, to me yasa zaka tafi ka barni?Ya
ce, ina canne amma na rantse maki zuciyata tana
tare dake.Yanxu ni dake bamu san haihuwa ba,
gashi yanayin aikina ba na za,ma bane bugu da
kari ba mu san kowa ba in haihuwa ta zo maki
bana kusa yaya ke nan?Nayi shiru a raina na
tabbata haka ne, amma damuwa ta daya, yaya
na nasan ba zaka jure zama ba mace ba, don
nasan yanayin ka.Ina tsoron matan zamani.Ya ce,
au, dama dan wanan ne?Nayi maki alkawarin ba
zan kalli wata ya mace da sunan so ko wani abu
ba, baki tunabaya ba?Na tsare kaina kuma Allah
ya tsareni, ba wanan a raina, nace to ya ya
zakayi?Ya ce, azumi mana, ko can shi na tayi ta
irin na annabi dauda.Inyi yau gobe in huta, kada
ki damu ki kyautata min zato, bani da sha’awar
aikata kazamin laifi irin su zina da
makamantansu. Na kalleshi na yarda da kai
mijina, kuma ni da kai mutuwa ce zata raba
mu.Zan jira dawowarka, amma za ka dinga
yawan kirana?Yace, kema na yarda ki kirani duk
lokacin dakike so, nace to amma dai mu kwana
abinmu a nan da safe in katafi sai na tafi nima.Ya
ce, sammako zanyi, na ce, eh, duk da haka, ya
ce shi kenan, sai muje da daddare mu kai
kayanki ko?Na ce, eh.
Hakika yaya na sweet Ali ya tafi ya barni da
tsananin kewarsa. Kafin ya kai munyi waya yafi
sau goma.Haka nan na hakura na saba da kwana
ni daya, daran wata lahadi na farka da wani
matsanancin ciwon ciki da baya.Kafin in tashi iya
yaya na soma kira, ya daga a rude na ce yaya
zan mutu ka yafe mun, nayarda wayar saboda
ciwon mara da ya murdo min.Kalamaina suka
farkar da iya, tazo tana cewa haihuwar ce Sadiya?
Yaya ya kashe ya sake kira a rude, iya ta daga ya
ce Iya don Allah…………Kuyimin hakuri indakata
anan zuwa lokaci nagaba sai mudira daga inda
muka tsaya,fatan zanga comment dinku
rututu,kafin nan nake cewa zaku iya ziyartar blog
dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button