AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 23-24

??23 and 24??

A hankali take typing, ba ‘ason rantaba harta karasa rubuta masa” ina son sosae, har cikin zuciyata”

Hmm Yace “Amma naji dadi sosae Ameelanah??”

Suna cikin fira Afham yahau, yaga taga text dinshi harta karanta amma babu amsa,
gabanshi ya fadi a ranshi Yace “Ya Allah ka taimakeni akan soyayyatah! Ganinta online yasa ya shiga rubuta mata wani text din..

Afham “Sunana Afham, ina zaune a garin gombe, na ansa numbrki ne a wurin qanwatah Aneesha, Ameelah kinyi matuqar burgeni ne, saboda irin kyaun da Allah yamiki, lokaci daya naji zuciyatah ta kamu da sonki, ina fatan babu wanda ya rigani!”

Ameelah ta jima tana tunani akan text din kafin ta bashi amsa, kalamansa masu dadi sun ratsa zuciyarta,

Ameelah “gsky ngde sosae??”

Afham Yace “hka kawai zakice, kinko san yadda zuciyata ta kamu da sonki, dan Allah kibani cikankiyar amsa wadda zata gamsar da zuciyata”

Ameelah taja nunfashi tana nazarin kalamansa masu sanya zuciya shaukin so da kauna, sannan tayi murmushi,

Ameelah “??hmm tohm mezance??

Afham yace “inaso ne ki bani amsa, wlhy Ameelah daga jiya zuwa yanzu zuciyatah qara cika take da zazzafar qaunarki, idanuwana basa muradin kallon komai bayan kyankyawar fuskarki, ki aminta dani namiki Alkawarin bazan barkiba”

Murmushi take tana kara maimaita kalaman a kwakwalwarta, kanta yadau zafi, tana zaune ta kurawa text din ido,
TaRasa abinyi gashi bangare guda HMM text dinshi sai shigowa suke shima da irin nashi rigimar, ga messages na Facebook sai shigowa suke,
rufe datar kawai tayi ta zauna ta dafe kai tana tunanin Afham,
( Ameelah tabani tausayi, irin zaman danaga tayi saikace shege agurin rabon gado, saikuma wata zuciyar tace meye abin tausayi a tattare da wannan bayan nema take taci AMANAR AURE, ai Allah bazai taba barinta tasamu kwanciyar hankali ba)
*** ***
Batasan iyakar mintocin data bata tana tunani ba sai dai qarar wayarta ne daya katseta, number Aneesah ne da tayi saving da ‘qawah’ sai data kusan katsewa kafin ta dauka ta sanya a kunne cikin rashin kuzari.

Tun kafin tayi magana Aneesah cikin barkwanci ta fara cewa “haba qawah, gsky banji dadiba yanda kika saka yayanah cikin damuwah, Allah yana sonki da yawah ba yabon kai ba yen mata da yawa na sonshi amma ban taba ganin wadda yakeso kamanki ba! Don Allah ki amince mishi, kinji qawata”

Ajiyar zuciyah Ameelah tayi kafin tace “bazaki gane bane qawah matsalan kawai itace inada….”
katseta Aneesah tayi dacewa “kina dame nidai karkicemun kinada saurayi, kuma basaina gane ba kawai ki fitar da yayana dga cikin damuwah, kinga yadda yashigo dakina kuwa, a gigice wai ameelah taki aminta dashi”

Murmushi ameelah tayi sannan tace “shikanan zamuyi magana dashi anjima”

Dariyar jin dadi Aneesah tayi kafin tace “ngde sosae qawah bari na mishi Albishir”

Ameelah tayi saurin cewa “kenifa bacewa nayi na amint…. kafin Ameelah tayi magana aneesah ta kashe wayan, Shirun da ameela taji yasa tarinka fadan Hello, hello, a lokacin tafahimci cewa takashe wayar, tayi ajiyar zuciya, zuciyarta cike da tunani kala kala..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button