BABU SO HAUSA NOVEL

DARAJAR ‘YA’YANA PART 2

Zaharaddeen shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana2-04
Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 29-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
__________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu’alaikum, fatan kuna cikin koshin lafiya… Sagir Ali, Shamsusdden Usman,Fatima Ahsan,Maman Ummi,Shamsiyya,Ummi Amal,Aisha and Aisha Kaka Zanna nagode da kulawarku,sannna inna jin dadin yanda kuke kulawa da shige da ficena,shirun da kukaji yafarune sakamakon ayyuka da sukaimin yawa,fatan zakucikaba da bibiya dakuma hakuri dani. nagode zamu Dora yanzu….. Ruwan wanka sai dai ya diba yaje yayi, wanan rashin dab’ar har ina?tasake yin dariya, to ni in nashiga dakin in ya dawo me zan masa?Na ce, auran kiyayya aka maki?Ta ce, a a ni na kaishi gidan mu, ta ci gaba kin sani ni gaskiya ko ya dawo bana shiga, shi yanzunnan zaice zai rungume ni, niko na tsani haka,ka debo rana ka wani ce zaka rungume ni, salon su Habu su fado dakin?na ce menene dan yaranku sun ganku rungume da juna?Kai ke dai baki da dabi’a,irinku ne ake kwacewa miji cikin sauki,daga baya kizo kina ya ci amanar ki,ni dai in baki canza haliba zan daina zuwa,ta ce;to Hajiya za’a sake, ai ku hajiya cikin daula kuke baku da matsala.Nayi murmushi Tasalla kenan.Shiyasa na ce, kina da hange, ki kalli kasanki mana,Misali waccan Maman Rashidan kuke ce mata ko wa?Tunda nake zuwa gidan nan bai fi so nawa naga ta daura tukunya ba.Kullun in kazo zakaga yaranta suna cin dumame, ko garin rogo amma ban taba ganin mijinta ya dawo ta barshi ya dibi ruwan wanka da kanshi ba, ko ta shareshi taki shiga daki.Sanan sau biyu na taba ganin mijinta nasan yayi sa’ar mata, duk cikinku ‘yan nan sasan da na taba ganin shigowar mazajenku da fitarku ita kadai ke yi wa mijinta sannu da zuwa da yi mashi addu’a in zai fita.Tasalla tayi yar dariya, hajiya kenan, ita waccen ai bata san kimarta ta ya mace ba, in banda haka yaushe zan zauna babu abincin kirki.Amma kina like da mutun kullum sai tayi wankan asuba don jaraba.Na ce, tafi ku godiyar Allah ne da biyayya.Sanan zakuga cigabanta kuna nan, sanan yaranta sunfi naku tarbiya da tsafta.Tasalla ta bata rai,Hajiya mu bar maganar nan, amma ko su maman Auwal zaki tambaya matarnan tana shiryawa yaranta kinaya ne don in mutane sunzo su rinka gaidasu don a ce suna da halin kirki.Na ce, ba wani bayan aike ma ina kallon naku yaran amma baku aikensu don kunsan cewa bazasuba, sai dai ku kira nata.Daga nan Tasalla tayi kus, niko na ce in sha Allahu duk randa zan kuma zuwa sai nayi wa yaranta kwalima tunda naga yaranta basu fi girman su Kausar ba, a raina na raya hakan.Ina Mota na kusa isa gida da motar dama naje gidan kitson da mota ne, sai ga kiran Aisha aminiyata, cikin hanzari na daga ina fadin.Kin haihu kenan? Tayi dariya yau andace kullun na kiraki zancenki daya ne kin haihu?To ga yarki nan a gado.Na ce, Alhamdulillahi ga ni nan.Na kira layin Abban kausar kamar yanda na zata har ta tsinke bai dauka ba, na sake kira.Muryar mace naji cikin harshen turanci tace wakike nema?Sai da sitiyarin ya kusa kufce min, na samu na tsaya tunda cikin unguwa ne, na sake yin sallama cikin rawar murya.Ta ce kina bukatar taimako ne?Na katse layin zufa ta soma tsatstsafo min.Na rude matuka, na kifa kaina a kan sitiyarin ina fadin Allah yasa mafarki nake yi.Na kuma kallon wayar ina shawaran in sake kira ne ko in barshi, sai ga kiranshi ya shigo da sauri na daga amman na kasa magana, Muryarshi ne yanzu ya ce hello!! Dazun bakiyi magana ba sai wata irin muryanake ji.A sanyaye na ce dazun ba kai bane wata ce ta daga.Da sauri ya ce wata wa?A wayata?A’a sai dai in network ne yasa ki kika ji haka.Ya saki zancen da cewa, lfy dai?Na ce e dama ina dawowa daga gidan kitso ne sai Aisha ta kirani ta haihu.Ya ce wace Aishan?Na ce, ta mamana.Ya ce, Allah ya raya, kin cika son yawo.Na ce to yaya in banje yanzun ba dole in sake fitowa don inyi gabadaya.Ya ce to shi kenan ina yaran?Na ce sunje yiwa iya wuni, ya ce ban son fa kina tafiya ke daya fa.Ko mama bakya iya yawo da ita sai ke daya tsura?Na ce, to yaya sun kwana biyu ne basu je sunyi mata yini ba.Ya ce, to shi kenan kardai kiyi dare don na sanku in kuka sami surutu na ce to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan ya kashe wayar ya nufi gurin Mujidat da
ke zaune kan kujera tana dafe da kumatu, inda
Aliyu ya watsa mata mari sakamakon shigowa da
yayi ya ganta ta daga masa waya.Ya kalleta in
kika kara yi min gangancin daga min waya sai na
mugu saba maki, don zaki koma inda kika fito.Ta
mike tsaye kana jin tsoron matarka ne don kar
tasan muna tare ta ce ta fasa aurenka?Cikin
gatse Aliyu ya ce haka ne.Don haka kada ki kara
daga min waya.Ya juya ya shiga dakinsa rai a
bace.Mujidat ta mike tsaye tana kai kawo, wai
mutumin nan yana nufin duk son da nake masa
yafi son matarshi a kaina?In ma yana boye mata
ne sai nayi sanadin da zata sani, in sha Allahu.Sai
dai ta mutu ko ta bar mun shi, don na yi imani
na fita son shi, zanyi komai don naga na rabasu
da makircina kawai,ta hada yatsanta babba da
na tsakiya taja suka yi kara, wanan wata Alama
ce da take yi duk lokacin da ta ma kanta
Alkawarin aikata wani abu cikin izza.Ni kam
kwana nai da motata zuwa gidan Aisha, amma
zuciyata cike take da wasi wasin abin da kunne
na yaji wai netwok ne.Anya kuwa ba binne ni
yaya yayi da rai na ba?Nayi murna da ganin
Aisha cikin koshin lafiya tare da jaririnta.Na dauki
yarainyar ina juyyata, mashaAllahu,Bello ya fiki
karfin jini daga ita har Najib shi suka biyo.Na ce
haka dai su mama suka ce, na ce, ina angon
karnin?Ta ce ya fita na kwantar da yar na kalleta
a Asibiti?A gida kafin ya samo mota har kai ya
fito.Innarsu da mamanmu da ma suka zo sai
kurum suka amshi haihuwar, na ce shi kenan
Allah ya kawo shi cikin sauki.Na nufi wata kula
dake gefe, na ce me suka barararaka miki?Na
bude kular, ta ce tuwo ne, miyar kuka, kinsan
tsaffin nan sai suce wai maijego sai da
tuwo.Muka sa dariya, na ce a ni na horu da tuwo
gurin Iya, haihuwar kausar har wani baki nayi
nayi muni dan uban nan.Muka sa dariya.tace, ai
daga baya Anty Abida ta hada maki sabulu, na ce
ai ta min kokari yanzu ba abin da bana hadawa
da kaina.Ta ce zaki hada min sabulunma nace to,
haka mukai ta fira har shida, sanan mukayi
sallama naje gidan Iya na kwashi yayana muka
tafi gida.
Na kasa bacci cikin dare sai juyyi nake kaso
hamsin da daya na zuciyata, yaya Aley yayi
min.Tabbas zan zama wawiya in ban amince yaya
yana neman mata ba.Yaushe rabon da ya dora
yatsansa kan nawa?Kullun dare ina kwana d
kewa, hawaye na suna kwaranya.Na tashi zaune
in ko haka ne wane mataki zan dauka.Zuciyata ta
dauki zafi ina fidda wani huci, lallai in ya kasance
haka zamuyi rigima ba karama ba, don ba zan
dauki wulakanci a kan matar banza ba.
Washe gari da safe ina ta tunanin yanda zansake
cewa yaya zan sake komawa gidan Aisha, saboda
in na haihu kulun tana hanyar har ayi
suna.Amma ni ko haihuwar Najib dinta banyi
mata wani sintiri ba, yaya hanawa yayi.Kuma
bana son fita batare da izininshi ba.Don nayi
imani shi baya kallona Allah da ya halicceni yana
kallona.Text na tura mashi cewa zanje gidan
Aisha lokacin suna tare da Mujidat suna
karyawa.Ya dauka ya karanta, sai ko ya hade rai
ya soma kiran layi na na daga.Tunkafin in karasa
sallama na ji ya ce, ban amince ba kullum fita,
saboda ki dinga kallon maza ko? Na zaro ido na
mike da sauri na nufi daki dan su Kausar suna
nan gida don anyi musuhutu.Kuma bana so suna
jin matsalar mu.Ya ci gaba da fadan shi, na ce
wacce irin magana kake yi yaya?Don in dinga
kallon mazaje fa ka ce?Kana nufin in na fita haka
nake yi?Ya ce, oho miki, amma ban yafe ba in
kika leko waje, nace naji ai tunda ka hana ba zan
fita ba, amma cewar da kayi wai ina kallon mza
nike son inji hujjar ka.Kana ga don ka shuka
fulawa ta fito kaki kayi mata ban ruwa sai ta
mutu?Na ci gaba, haka ne zata mutu amma
kasani ni nasan DARAJAR YAYA NA.Ko don su zan
kare mutuncina kai shaidane budurwa gar ka
bare ni a leda, ka san haka kuma kullun ina
Adu’a Allah ya kare ni daga sharrin zamani.Ban
jira amsarshi ba na kashe, sanan na fada kan
gado ina kuka.Sai kurum naji hannun kausar a
baya na tana fadin.Momy kiyi hakuri ki kyale
shi.Da sauri na share hawaye na taso kausar
bana ce in ina waya a daki ba ku daina biyo ni?Ta
ce momy ki daina daga wayar Abbanmu, ko ya
kiraki ni bana so yana saki kuka.Na ce naji muje
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwana uku da yin sunan yar gidan Aisha ya ta ci
sunan Fateema, sai ga yaya da rana tsaka ina
mamakin yanda yanzu yake son yimin dirar
mikiya.Ko yana zargin ina fita ne?Oho.Nayi masa
sannu da zuwa ya amsa na ce, baka fada ba
gashi banyi abincin rana ba.Jiya sun bar
shinkafar da na dafa da dare, sai kawai nasa a
firiza yau na duma ma, amma bari in maka ko
macroni ce.Ya ce barshi bani da yunwa, in na fita
zan siyo fura.Sai da yayi bacci sanan ya tashi yayi
wanka ya fita.Duk ina dakina ina karanta littatafi
,tinda nalura bai bukatar ganina kusadashi, nima
hakan yafi min sauki don in yana gari nafi jincewa
nima macece in kwana cikin kewa.Washegari ya
fita zuwa gidan su Iya na dauko jakarshi, don
kwashe kayan wanki wanda ya dawo dasu kamar
yanda na saba.Ina daga suit din shi zan rataye
wata takarda ta fado, na dauka har zan maida
masa cikin Aljihun rigar sai wata zuciyar ta ce
bude mana ki gani, na bude.Yar wasika ce aka
rubuta da harshen turanci, ga abin da yake
rubuce.ZUMA NA KA TAFI DA TUNANINA, HAR
KAJE KADAWO KASANI ZA KA BARNI CIKIN KEWAR
LALLAUSAR FATAR JIKINKA.BA ZAN GUSHE BA HAR
SAI KA DAWO KA SAME NI CIKIN KEWAR LEBUNAN
KA MASU SANTSI TARE DA (YAWUN) KA ME
ZAKI.ALLAH YA DAWO MUN DA KAI
LAFIYA…..Kafin na kai karshe tuni na jike da
zufa, ina gamawa na ga gari yana juya min, ban
an kara ba sai dai naji ni a kasa ribin jikina a
gado rabi a kasa.Kusan minti biyar sanan na tashi
zaune sa sake karanta takardar ina kuka wiwi har
da majina tabbas yaya mata yake bi,domin
takardar ta nuna haka, mata ce kawai ya dace
tayiwa mijinta irin rubutun nan, wata zuciyar ta
tambaye ni ko dai ya sake aure ne?Duk da uban
kishi na sai nasami kaina da cewa inda ma auran
yayi zanfi son haka, da bin matan banza.Na soma
kaikawo cikin gidan ina tunanin matakin da zan
dauka.Shawarar wa zan nema?Na shiga dakina
na fada kan gado na dauki wayata na shiga
kiranshi, amma sai wani tunani ya fado min.Bari
kawai in kira Hajiya Baida’u, marubuciyar littafan
da nake karantawa danneman shawara.Dan ita
bata sanni ba balantana inyi zaton zancen zai iya
yaduwa, sanan tana da basira nasan zata sani a
hanya.Ringing na biyu ta daga, ta daga muka
gaisadama na saba kiranta, na ce Anty ina
nemanshawara ne.Leta na gani a jakar me gida
na wanda ke Alamta cewa yana tarraiya da wata
mace.Ta danyi shiru na dan lokaci.sanan ba yan
wanan letar kina da wata shaidar?Sanan can
dama halinsa ne?Na ce, a to a da can ba na
zarginsa, sai da ga baya na soma zarginsa domin
Anty kwata kwata ya kaura ce min kusan wata
shida zuwa bakwai yanzun,kuma Anty shi mutum
ne mai zurfin sha’awa, ba zai iya daukar ko
kwanaki ba ba tare da mace ba bare watanni.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce kuma ba gudan sa kike ba har hakan ta
faru?Na ce wlh Anty Allah ya sani ban ta ba juya
masa baya ba, har matsalar nan ta shigo.Ta ce,
kuma kina gyara jikinki ba ji yayi kin zama wata
iri ba?Na soma lissafo mata abubuwan da nake
hadawa, ta ce, lallai kina kula da kanki.Na ce,
anty yanzu in yazo in fada mashi takardar don
yasan na sani?Ta ce, a a tunda kinga zarginsa
kike yi kenan baki da tabbas, ki boye takardar
kuma ko a idonki kada yaga damuwa.Ki bishi a
hankali, ki boye sirrin nan tunda uban yayanki
ne.In shaAllahu sai kiga Allah ya dawo maki dashi
kan hanya, na ce,Anty zanyi yadda kika ce, amma
zan ci gaba da bincike.Ta ce, za ki iya amma ki
sani tsananta bincike shima matsala ne, don zaki
iya ganin abinda zai saki hawan jini, na ce anty in
na tabbatar da gaskiyar zan tunkareshi ne in
nuna masa nasani.In ma zai aureta ne gara ya
aureta da zaman banzan nan, ta ce haka ne,
amma kada ki manta da adu’a, na ce insha
Allahu, ina magana cikin kuka.Ta kwantar mun da
hankali da cewa, ki daina kuka, na ce anty me
nene maganin bakin ciki?Ta ce karatun Alkur’ani
zuciyarki zata wanke sarai.Na ce, to anty na
gode.Muka yi sallama na kwanta nayi kuka sama
da minty biyar sanan na tashi na boye takardar
na ci gaba da aikina ina kuma ci gaba da
kuka.Wanan wane bala’ine Abban kausar ke son
jefa ni, ni da ‘YA’YA NA?Ya manta cewa duk abin
da kayi da Dan wani kaima sai anyi da naka?Da
na koma daki sai naji komai nasa kyama yake
bani, shi kansa yanzu kyamarsa nake ji, na
karasa kwashe kayan nasa ina yi musu kallon su
kansu suna dauke da zunubin zinar da yake
yi.Tunda su Kausar suka shigo naga sun tsura
min ido ita da Al’amin shine ya soma
magana.Momy me yasameki a ido?Na ce, ba
komai, ciwo yake min.Sai naga sun kalli juna.Na
tsugunna tsakaninsu menene?Na tambaye su
tare da yin dan guntun murmushi da na kirkiro
ko nace yake.Al’amin ya ce, yaya kausar ce tace
bata so Abba yazo in yazo yayi ta saki kuka, kuma
fa ko an tambayeki sai kice ba komai shi ne nace
ai yanzu ya daina.Amma muna zuwa sai muka
sameki kinyi kuka, ku,ma muka tambayeki sai
kice ba komai.Kausar ta ce, na canka ko Al’amin?
Abban nan ni bana sonshi yanxu.Al’amin ya bata
fuska, nima bana sonshi, bakin ciki ya turnike ni,
bana son kallon da yara suke yiwa
mahaifinsu.Nace kausar ku daina cewa bakwa son
mahaifinku,bana fada muku in kunyi Sallah ku
rinka adu’a Allah ya kawo sauki cikin lamarinba?
Allah yana amsar adu’ar kananan yara, sukace
munayi sosai Momy kullum.
Ko da ya shigo kasa kallonsa nayi, ganinake zan
iya cin kwalarsa, don haka na sa kaina a daki na
rufe tare da sa sabon kuka.Ya kalli su Kausar, ina
mamanku?Al’amin ne ya ce, tana dakinta, yazo
ya buga kofar kamar kada in bude amma sai
nafasa na bude
Ya tsura min ido lafiya?Na kalleshi, me ka gani?
Ya ce, fuskarki na gani a kumbure, na taba baki
sanan na shafa fuskata.Kila baccin da nayi dazun,
ya ce wanan kumburin baiyi kama da bacci ba,
ya fi kamada wanda yayi kuka.Na mai wani irin
kallo.Don yanzu bani wani ganin girman shi, na
ce ai ban san tsawon lokacin da kuka na zai
dauka ba kafin ya tsaya.Ya ce to Allah ya kyauta,
ya juya tare da fadin to a zo a bani abinci.Sai da
na dan bata lokaci sanan naje na shirya komai na
dawo abina.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari ya fita, sai dai duk Aliyu a dame ya
bar garin ya rasa gane kukan da Sadiya take
zabgawa, nashi ganin bai san yayi mata wani abu
ba tun zuwan shi.Rashin kulata ai ba yanzune
farko ba, to kukan na menene?Dole Akwai wani
abu, abin da yasake birkita masa lissafi yanda ko
wayarta yakira sam bata iya dagawa.Rana ta
hudu da komawarshi, ya gaji ya kira kayin Usman
ya fada masa halin da ya bar Sadiya, da kuma
rashin daga wayarsa da take yi.Yamma likis
inayiwa kausar kalaba na wanke mata kai ina
cewa sai gobe zan kaita kitso, sai ga Usman.Muka
gaisa sannan na ce, shigo falo, kausar kuma nace
suyi wasa a nan tsakar gida.Usman ya kalleni,
mijinki ya ce baki daukar wayarshi, kuma ya tafi
ya barki cikin kuka.namike naje na dauko mashi
takardar da na gani cikin kayansa.Shi kanshi
Usman kasa dago kai yayi ya dube ni, can ya ce,
lallai abin da nake zargi ya tabbata, amma don
Allah ki kara hakuri kuma in sha Allahu ko mai zai
wuce. Yanzu bari inje da takardar nan saboda
bincike, na ce yaya kayi hakuri kabar takardar
nan a hannuna saboda ta zama shaida a duk
lokacin da na masa zancen ya musa.Usman ya ce
nima da ma don hakan naso na aje ta guri na,
amma ajeta gunki, na amsa sannan mukayi
sallama.Ya kira Usman dan jin yaya?Usman ya ce
ta ce mun ba komai tana bukatar hutu ne da
dago waya, Aliyu yayi shiru, mamaki yake ji,
kuma yana ganin kamar da wani abu sun hada
bakine ita da usman.Aliyu ya ce, amma bakayi
mata fada ba, in ita ta manta cewa mijinta nake
ya kamata kai ka tuna mata. Usman ya ce, aboki
yanzu kaga aikinike, kasake kirana wani
lokacin.Ya katse wayar ba tare da ya jira amsar
Aliyu ba.Afili ya furta cewa, tabbas akwai wani
abu.
Tabayanshi Mujidat ta rungume shi.Dear wai me
ke faruwa ne?Tunda ka dawo na kasa gane
kanka.Ya kalleta cikin zargi kin sake daga wayar
matata ko?Tayi rau rau, wlh Honey ban daga ba,
ta somayi masa wadan su wassan ni tana rada
mishi a kunci me yasa ba zai mata irin son da
take yi masa ba?Ita fa zata iya mutuwa a kansa,
amma shi yafi son matarsa da ita.Ya hankadeta
tare da fadin dan Allah barni ta yaya ma zaki
hada kanki da matata?Matar sunna wacce ke
zaune don ni kadai, ta soma kuka tunda na hadu
da kai na daina hulda da kowa, nima ina zaune
nan ne dan kai daya.Aliyu ya ce, ban tabbatar da
hakan ba, tunda dana fita zaki iya fita, ta sake
dawowa ta rungume shi, na rantse bana bin
kowa kai daya nake so da kauna.Kuma bazan
daina sonka ba har na mutu.Aliyu ya zauna kan
kujera tare da rike kai, itakuma ta kwanto a
kafadar shi.Tunani take yi a zuciyarta yanda zata
ban bare ma’auratan.
Ina zaune ina danne dannen wayata, nima ina
son bude shafin nan na fcbk don ganin me
duniya take ciki?Aisha kawata da Anty Abida duk
suna ciki har Aisha tana bani labari wai da akwai
malamai sosai.In shiga nan in shiga nan dayake
ina da karanbani sai gani na bude fcbk, banyi
anfani da sunana ba ko adareshi na.Bayan kwana
biyu sai ga Aisha ta zo mun yawon Arba’n, na
nuna mata ta ce, ai na gani kin turo min sako, na
ce yau she?Ta ce duk wadan da kike da numbar
su za su gani, in kin bude, na zaro ido, har da
Abban kausar?Ta ce sosai ma, amma ba lallai ya
lura ba tunda bakiyi anfani da komai naki ba.Ta
nuna min yanda zan dinga komai, bayan tafiyarta
da dare ina kwance, na shiga fcbk nan na shiga
frnds, dinsa, mace daya na gani Mujidat.Na shiga
profile dinta hotunan da tasa nata yana daga
cikin wadan da sukayi like wani gurin ma har
yana cewa kin yi, sanan ga hotunan shi kala kala
cikin photos din ta wasu ta rubuta one an only,
wasu ta rubuta my Husband.(Tofa)
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na tashi xaune wai ya aure ta ne? take kaina ya
sara, duk da ina cewa gara ace auranta yayi fiye
da ya neme ta sai na samu kaina cikin wani
tashin hankali mai tsanani.Na soma kiran layin Ya
Usman ba tare da na damu cewa dare ya dan
soma ba,cikin kuka nike cewa ya Usman ina ganin
fa auranta yayi bai fada mana ba. Yace,Habadai
wacece? Na karanto masa komai yace, kiyi hakuri
ki kwanta zan bincika,kada ki kara hawa fcbk
din,kurum ce masa nayi to amma muna yin
sallama dashina tura mata frnd request, cikin
sa’a ta amshe ni, da yake ita ma na ganta online.
Nace ban ga tasa marriage ba amma naga hoton
mijinta, ta ce eh za dai suyi auren ne, nace ni yar
kano ce ita fa? tace Lagos, amma yanzun tana
Illorin a gidan wanda zata aura.Kuka wiwi na
dinga yi yanzun menene abun yi? na tambayi
kaina, ta tambayeni ina da miji? sai nace mata
bama tare, tace ayya, yakamata mu daidaita.Ita
in sunyi aure bazata taba yarda su rabu da
mijinta ba don tanaji ko uwàr da tahaifeshi bata
kaita sonshi ba,ai ina gama krt na sauka daga nrt
na soma rero kuka tare da yin danasanin wannan
bin diddigin.Alwashi na sha duk randa yazo za’a
yi mai yuwuwa. Ba zan zauna ina wulankanta ba
haka kawai a debo ciwon zamani a kawo min
yarana su zama abun tausayi,na sake zama cool
ko yaushe cikin krt alkurani yana wanke min
zuciya, don haka yanzu bana daga wayarsa sai
dai in yaransa na kusa ya kira na mika ma
Kausar nace ta dauka.Ranar Kausar har tambaya
na take Mommy meyesa ba ka daga wayar Baban
ko yana mki fada ne? Nace a’ah munyi maganar
cewa yake in Kundawo zai kira ku ne,a haka
muka kwashe wata, ranar kwatsam sai gashi,
mamaki da naji banda Mama ko Al’amin bai je ya
masa oyoyo ba?nima batare da na Kalle shi ba
nace sannu da zuwa, yace Yauwa ya dubi yaran
yace Al’amin baku ganin bane, nukamun ganka
Abba sannu da zuwa.Yayi cik ba tare da ya amsa
ba ransa ya baci sosai da wannan ko in kula din
iyalanshi suka mishi,don haka ya dauri aniyar
Cima Sadiya zarafi yau dinnan, nasan dole zai yi
wannan tunanin dan haka na hada ma yara kaya
na kwana daya nace suje gidan Iya su kwana
tunda sati ne gobe, suna fita na kulle gidan na
shiga fall na kulle kaina na cire key din na nufi
daki,ya cire kaya sai gajeren wando zai shiga
wanka,nace toh Abba kausar yau fa zamuyita ta
kare a gidan nan ko ni ko kai?ya juya yana min
kallon mamaki sannan yace ke ina zaton kin soma
shan fakalin ko?nace ‘eh wai don ma ba Zina
nakeyi amma ka bani kunya, ba tsoron Allah ba
kunyarshi baka tunanin darajar yayana ka aje
karuwa a gidanka Kuna fasikanci,saukar Mari naji
tau,sannan yace in ji wane makaryancin, na rike
kuncina ka mareni Akan wata ‘yar iska, toh bazan
iya zama da fasiki ba ka dinga azabtar dani a kan
karuwa na warware gefen zani na ciro yar
takarda na mika mishi, ga aikenta zuwa gareni,
sannan na dauko wayata na same shi yana krt
takarda duk jikinshi yayai sanyi, nayi maza na fito
da pics dinsu da nayi saving, wannan ma karyace
ba hoton ku bane?na soma kuka ka cuce ni ka
cuci yarana haka kake nufin ayi ma Kausar?ya
daka min tsawa kina hauka ne kike ambato sunan
yata cikin wannan maganar?nace ba dadi kake
ma yar wasu?Na sake fashews da sabon kuka ka
bani takarda ta, bazan iyazama da kai ba!kina
haukane zaki ce na sake ki,toh bazan iya ba me
Zancewa Iya?nace in itace matsalar ka bazan fada
mata komai ba in baka sake ni ma zanje yanzu in
fada mata! hanklainshi yatashi ya dauki jallabiya
ya sa nikam ficewa nayi naje dakina na sure hijab
na bude Kofan falon ya rike ni kina hauka ne zaki
je ma Iya da wannan zancen?nace me zai
hana,ya kamoni na kwace nayi waje na bude
kofar gida kafin na bude ya daukoni cak,dakina
ya jefa ni kan Gado yace kina hauka ne?yace nayi
laifi kiyi hkr ki nutsu Muyi magana, nace kai ni fa
na daina Sonka kuma girmanka ya zube a gurina,
ganin zanga-zangar tayi yawa sai ya kulle ni ta
baya ya daga waya ya kira Usman yace don Allah
yana son ganinshi yanzu a gida,ina jinsu a falo
yana fada ma Usman shi bai San ina ji ba wai
duk na daga hankalinta har wai ina kwacewa ni
dole sai naje na fada ma iya.Usman yace aboki
tambaya daya zan maka kayarda kana aikata
laifin nan?yayi shiru ,Usman yace in har ka iya
amsarwa shine zai kawo karshen matsalar, yace
toh ai na fada mata cewa naji na kuma amsa
laifina don haka ta tsaya Muyi magana
taki,Usaman yace a’uzubillah, Aboki me yarude
ka ka fada wannan harka?wlh aboki kurum na
tsinci kaina a wannan halin, ka San zuciyata bata
da Kashi ga kuma sharrin shaidan, Usman yayita
masa nasiha sannan yace a jira ni na fito fuskata
suntum nace Nifa Usman na gaji ba zan zauna
ba,Usman yace yi hakuri nasan kinyi hakuri kuma
inshaAllah bazai kara ba,na kalleshi nasan zai
chigaba kawai ni gara ya aureta in son aure
suke,inkuma matan da yake bi da yawa toh ni
bazan iya zama ba.Usman ya Kalle shi gaskiya ne
Aliyu yace ita kadai ce muke tare wlh kuma itama
tsautsayi ne, Usman yace ko kayi nadama sanin
zaka koma can ku sake haduwa shi yasa ta kawo
shawara cewa taje tayi istibrai in ya so sai Kuyi
aure.Aliyu yace ina bazan auretaba ni nakuma yi
miki alkawarin cewa mun rabu da ita inshaAllah,
a gaban mu yayi waya ya kira maigadinsa yace a
fitar da Mujidat daga gidan kafin ya dawo, itama
ya kirata yace mata ya gode da wasikar da ta sa
mishi a cikin kaya don ta raba shi da matarshi
don haka maza ta bar mishi gidanshi,bai jira
takare kanta ba ya kashe dukkan phones dinsa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ni Sam bai wani Burgeniba,suna cikin gidansuna
ta bani baki har magrib,suna fitowa nayi wanka
na sha magani nayi sallah ina zaune kan
dadduma har sai da nayi sallar Isha dama banyi
girki ba,na hau gado abuna na chigaba da kuka,
na soma barci naji ana shafa ni a wuya abunda
na jima ina kewa amma sai naji tamkar ana
shafa min kaya.Na ture hannunsa a kunne ya
rada mincewa’My choice zan zame miki sweet Aly
dini har abawa ba zan sake chanzawa ba,natashi
zaune muna kallon juna cikin ido nace yaya Sam
yanzu in ka fadi magana bana yarda matsalar
mutum ya kama karya kenan har a gane shi,na
sauka daga kan Gado naje na jingina da bango
ina kallosnshi shima ni yake kallo nace yaya ni fa
nadarmarka bata shige ni ba don nasan dole sai
Kun sake haduwa da yarinyar aurenta kawai shi
ya fi dacewa da kai,ya nufoni amma ina ce an
gama maganar nan,bazan iya auaran ta ba har
ta Haifa min yara na gari Domin ba uwa ta gari
bace,itace tayi ta bibiyata har sai da komai ya
faru kinga kuwa in na aure ta ta kuma ganin wani
shima xata iya cewa tana sonshi,ya kama
hannuna ki yafe min mukoma kamar da, Abban
Kausar na hkr amma sai Kamin rantsuwa cewa
bazaka kara aikata wannan halin ba?
Cikin sauri yace’na rantse ba zan sake ba nayi
alkawarin, nace toh shi kenan na zame hanuna
naje na kwanta sannan nace yawuce, ya Tako ya
zo ya hau gado ya kawo nizuwa jikinshi na tashi
zaune yaya kayi hakuri bazan sake iya hada
shinfida da kai ba har sai kaje kayi gwajin cutar
kanjamau!!!!! Zumbur ya mike tsaya tare da rike
kanshi Sam baiyi tunanin wani HIV ba tunda yake
tarayyada yarinyar, ya fara sintiri a tsabar
dakin,nace da baka yi tunanin haka ba ko?ya
sauke ajiyar zuciya ‘ban yi wannan tunanin ba
wlh Sadiya amma bana zaton tana da shi,tunda
tsawon zamnmu ban taba ganin tayi wani ciwo
ba,nace ba a nan take na, Ance mace tana yin
shekara goma ciwon bai nuna ba,kawai kaje kayi
gwaji in ma tanashan magani a boye wa zai sani?
zufa ta rufeshi sai lumshe ido lallai kamar yana
ganin ta tana shan wasu kwayoyi har ya taba
tamabayar tace na family planning ne,fita yayi da
sauri na tashi na biyo shi ina cewa ina zaka
Abban kausa’r yace’koma asibit zanje yanzu
nan……..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
toh fa sai ku biyo ni cikin Kashi na uku don Jin ya
xata kaya shin Aliyu yana da ciwo?taku Halima K/
Mashi

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button