DIYAM 10
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Ten : The Beginning
Diyam ta dauke kanta tana kallon wani mai yankan fulawa da yake ta
aikin gyara flowers din gurin suna kyau. Amma sam hankalinta ba’a kansa yake ba, hankalinta yana gurin yadda zata fita daga wannan trap din ne, a hankali tace “not again, not now” Bassam yace “what?” Ta juyo tana kallonsa kamar yanzu ta fara ganinsa kafin tace “Bassam. What do you understand by the word Love?” Ya karkata kai yana kallonta sai kuma yayi dan murmushi yace “that is a one million dollars question” tace “just answer it, kai me kake tunanin shine love” yayi shiru tsahon minti biyu yana tunani sannan yace “feelings. Love is a feeling of deepest desire for something. Like kaji kana son kasancewa tare da wanda kake so din” ta gyada kanta tana murmushi tace “yes you are right, love can be that but lust can also be that. Sometimes mutane suna zama confused akan bambancin love the lust. To me zan iya cewa abinda ka fada is just one aspect of love. Ta gyara zama tana kallonsa cikin ido tace “zan baka labari na Bassam, maybe a karshe you will understand the true meaning of love, you will understand kuma abinda yasa nake son yanke alaka ta da kai sannan kuma maybe it will help you find redemption”. Ta koma ta jingina da jikin kujera tana kallon yadda ruwa yake tsiri a wani fountain kusa dasu. A hankali ta fara tariyo rayuwar ta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sunana Haleema Usman Kollere. Wannan shine labari na.
Kamar yadda na gaya maka asalin iyayena yan rugar Kollere ne dake karamar hukumar damagum ta jihar Yobe. Inna ta da baffana ‘yanuwa ne, kakanin su daya. Da kakana na wajen uba da kakata ta wajen uwa uwarsu daya ubansu daya. Innar mu su biyu ne kacal agurin mahaifiyar su daga ita sai kanwarta Yakumbo Hafsatu sai tarin ‘yan uba da suke dasu kasancewar mahaifinsu yayi aure aure da yawa, kusan sa’anni ne su biyun kuma tun suna yara Allah yayi wa mahaifiyarsu rasuwa ta tafi ta barsu a hannun kishiyoyi su kuma sukayi caa a kansu suka mayar dasu bayinsu, ganin ana neman hallakasu yasa kakana na gurin uba, Hardon rugar mu, ya karbo su a gurin ubansu ya kawo su gidansa gurin matarsa Inno wadda itace kakara ta gurin uba kuma ita kadai ce matarsa ta hada su ya yayanta ta rike.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Hardo yana da yaya hudu. Kawu Isa shine babba wanda muke kira da Alhaji Babba, sai kawu Mamman, sai baffana Usumanu, sai kuma autarsu Fatima wadda tsakanin su da baffana akwai nisa sosai dan kusan sa’ar Inna ta ce. Haka suka taso su shida a tare, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce Inno da Hardo basu suka haifi Inna ta da Yakumbo Hafsatu ba. Allah ya yi wa hardo arziki a rugarsu sosai, dan kaf rugar babu wanda yake da garken shanun da yakai nashi cika da manya manyan dabbobi, amma wannan bai saka ya hana yayansa karatu ba duk da dai mazan ne kawai suka yi kuma suma iyakacin su secondary School, duk wanda ya gama a cikinsu sai hardo ya debi shanu ya siyar ya bashi kudi yace “tafi birni ka nemi arzikin ka acan”. Allah Babba ne ya fara shigowa Kano da niyyar neman kudi, aikuwa Allah ya buda masa yana fara juya kudin da aka bashi sai gashi kudi sun ninka kansu, Allah ya bashi baiwar iya kasuwanci dan haka nan take ya kafa kansa a kano, ya gina katon gidansa a sharada ya nemi aure anan rigar mu aka bashi ya tare da iyalinsa. Lokacin da Kawu Mamman ya tashi barin rugar mu sai Alhaji Babba ya nemi ya taho Kano gurinsa dan ya buda masa shima ya samu ya kafa kasuwancin sa, wannan ya saka har yau gidajensu suna nan a jere da juna kowa da iyalinsa kamar gida daya kawai gates ne daban daban.
Baffan mu, tun yana dan ƙaramin sa suka kulla soyayya da wata da ake kira zainabu a cikin rugar. Tun suna yi aboye har abin ya fito fili kuma maganar taje kunnen Inno. Ita Zainabu ta kasance ta fito daga wani family da tun asalinsu tun kaka da kakanni an riga anyi musu tambarin maita a garin wai wani kakan kakansu maye ne, to wannan tambarin shi ya biyo generations har kan mahaifiyar Zainabu da ake kira da yaya Ladi sannan ya sauka akan yarta Zainabu. Amma duk acikin generation din da yake cikin rugar babu wani wanda zai bada labarin sanda akayi waccan maitar ko kuma tabbacin cewa anyi din amma har lokacin tambarin yana nan. Labari yana zuwa gurin Inno wadda kusan ita take juya kowa har shi kansa hardo saboda kafiyarta akan magana, ta kira baffa tace masa “kul, daga yau babu kai babu Zainabu” sai Baffa ya dauke kai kamar ya bar maganar amma ina…. Zainabu ta riga ta kafa rassa a zuciyarsa.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Lokacin daya gama secondary school dinsa sai Hardo ya debi dukiya ya bashi kamar yadda ya bawa yayunsa yace “tafi birni kaje ka nemi arzikin ka” amma sai Baffa ya debi wani abu daga cikin dukiyar ya mayar wa da Hardo yace gashi a je a nemar masa auren Zainabu in yaso sai ya tafi da ita birnin. Ai kuwa nan da nan dangi suka dauki maganar “Manu zai kwaso mana dangin mayu” Zainabu tana dandali akaje har can su Inna ta da gwoggo Fatima da kawayensu suka yi mata atule, tana zuwa gida ta tarar Inno ta saka yara sunje suna ta jifan gidan su wai mayu ne su sun chinye kurwar Manu. Bakin cikin wannan abu ya saka Yaya Ladi ta hada musu kayansu cikin dare suka bar garin ba tare da kowa ya sani ba. Wannan abu ya tayar da hankalin Baffa na, ya shiga damuwa sosai dan ance har rufe kansa yayi ya daina yiwa kowa magana ya daina cin abinci sai sumbatu da kiran sunan Zainabu, daga nan sai magana ta koma cewar tabbas Zainabu mayya ce dan gashi nan ta kama masa kurwa, akayi ta jike jiken magungunan mayu har dai daga baya ya warke. Sai daya warware sosai ya koma kamar babu abinda yake damunsa sannan ya karbi kudin da Hardo ya bashi ya taho kano neman kudi kamar sauran yan uwansa. Amma maimakon yabi sawun Mamman ya tafi gurin Alhaji Babba shima, sai yaki ya tafi cikin garin kano unguwar Yakasai ya sayi gida madaidaici ya boye sauran kudinsa yana kuma fita neman wani kudin. A hankali sai ya fahimci cewar yana da fasaha ta bangaren kanikanci dan sosai yake jin dadin aiki a karkashin wani bakanike, kuma cikin ikon Allah sai ya yi dace mutumin yana kokarin siyar da garejinsa dan haka Baffa ya dauko ajiyar kudinsa suka yiciki ya siyar masa, nan da nan ya fara wannan sana’a, ya debi yara sunayi shima yana yi da kansa kuma Allah ya saka masa albarka nan take guri ya bunkasa. Ya cigaba da tara yan kudadensa ya hada lefensa yayi komai ba tare da kowa ya sani ba sannan ya koma gida yana neman azo a nema masa aure ya samu mata a kano, nan take Hardo ya aiko aka nemi aure anan bayan layin da gidan sa yake, aka bayar akayi komi sannan matan su Alhaji Babba tare da kanwar Inno da sauran yan’uwa da suka taho daga Kollere suka zo kawo kaya amma suna zuwa sai suka tarar da yaya Ladi a matsayin uwar amarya. Ashe bayan tahowar su sai da Baffa ya yi ciku cikun da ya samu labarin inda suka taho kuma ya biyo su ya sayi gida a kusa da inda suke saboda ya zauna kusa da Zainabu sannan kuma ya turo aka nemar masa aurenta a gurin sabon marikin ta wanda aikatau ne yaya Ladi take yi a wajensa shi kuma ya rike Zainabu kamar ya har yake shirin yi mata aure.
Ai kuwa nan take rigima ta balle, mutanen nan da suka zo daga Kollere suka karewa yaya Ladi tas kamar zasu cinyeta danya, ita dai ta zauna tana ta kukan takaici dan sam Zainabu bata gaya mata gaskiyar waye manemin nata ba dan da ta sani da sam ba zata bari ba balle ayi mata wannan cin mutuncin a gaban jama’a. Babu irin sunan da basu kira yaya Ladi dashi ba, wannan ya saka suma mutanen gidan suka tashi suka tare wa yaya Ladi suka yi wa yanuwanmu korar kare aka watso musu kayansu waje. Wannan ya kara tunzura su, suna zuwa Kollere suka bawa Inno da Hardo labarin abinda manu ya jawo musu a take Hardo ya kirawo Liman yace a daura auren Baffa na da Inna ta wadda duk dangi sun san irin kaunar da take gwadawa manu amma ko kallo bata ishe shi ba duk kuwa da irin baiwar kyawu da Allah yayi mata, dan ko kusa ba za’a haɗa inna da Zainabu ba indai ta gurin kyau ne.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A bangaren Zainabu kuwa ana watsewa daga gurin karbar kayan da ba’ayi ba mai rikonta ya kira yaya Ladi ya tambaye ta ita kuma ta bashi labarin duk abinda ya faru wanda yayi sanadin barin su rugar su, a take yayi mata alkawarin zai samo wa zainabu mijin da manu ba zai taba iya zama kamarsa ba. Haka kuwa akayi sati na zagayowa aka daura auren zainabu aka sakata a mota aka tafi da ita gidan mijinta akan idon Manu.
Wannan kenan….
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Tun muna yara labari ya iske mu daga gurin makota na irin wahalar da Inna tasha a hannun Baffa saboda kiyayyar da yake yi mata da kuma bakin cikin raba shi da masoyiyarsa da akayi. Wannan ya saka sana’arsa ma taja baya sosai, yana yin samun kudinsa yaja baya sosai amma sam ba ya taba zuwa gurin Alhaji Babba neman taimako sai dai idan shine yazo gidan yaga halin da suke ciki ya taimaka musu. A haka har shekaru suka ja amma babu haihuwa babu labarin ta, ana cikin haka ne kuma Allah yayi wa Inno rasuwa, wannan yasa Alhaji Babba yaje Kollere ya tattago su Yakumbo Amina da goggo Fatima ya taho dasu gidansa a kano, daga nan kuma duk yayi musu aure anan kanon, a shekarar da Inno ta rasu ne kuma Baffa ya sake sabon aure wanda shi kadai yaje ya nemi abinsa tare da taimakon kanin Hardo da suke dasawa sosai, sai bayan komai ya kankama sannan sauran yanuwa suka sani kuma suka nuna rashin jin dadinsu saboda suna taya Inna ta kishi, amma basu kuma sallama auren ba sai da aka kawo amarya suka bude fuskarta suka ga Zainabu.
Inna ta tayi kukan bakin ciki kamar ranta zai fita, ta hada kayanta tayi yaji zuwa gidan Alhaji Babba shi kuma yazo har gaban Zainabu yace da Baffa “mu yanuwanka kaf babu mu babu wannan matar daka aura, babu mu babu duk wani abinda ya shafe ta” amma Baffa ko a jikinsa. Babban abinda ya kara dagawa yan’uwan Baffa hankali shine dan jaririn da Zainabu tazo dashi a hannunta wanda ko yaye shi bata kai gayi ba. Sunansa Aliyu.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bayan komai ya lafa zama ya cigaba da gudana cikin rashin jin dadi a gidan mu, Baffa yana iyakacin kokarinsa gurin adalci amma Inna gabaki daya ta burkice, ta riga ta sakawa ranta cewa Baffa yafi son Zainabu a kanta dan haka komai sai take ganin kamar zaluntarta yake yi, ko magana sukayi kasa kasa shida Zainabu sai taga kamar gulmarta suke yi, sannan ga rashin haihuwa, dadin dadawa ga dan da Zainabu tazo dashi wanda Baffa ya dauki son duniya ya dora akansa. A bangaren Zainabu kuma, let me tell you about Zainabu, tunda nake a duniya ban taba ganin mutum mai hakuri irin ta ba, irin mutanen nan ne da ko zaka zuba musu kashi aka ba zasu kula kaba sai dai su karkade maka wanda ya taba jikin ka. Dan zan iya cewa idan da akwai hakkin da Inna take dauke dashi a kanta to hakkin Zainabu ne.
Let me tell you about Aliyu. Zuwansu gidan mu Baffa ya chanza masa suna saboda sunan Hardo ne dashi ya ke ce masa Sadauki, Sadauki tun yana jariri kakkarfa ne na gaske dan karfin sa ne ma ya saka Baffa ya saka masa Sadauki. Baki ne, dan kusan kullum ba’ar da Inna take masa kenan “Baƙin munafiki” ko “baƙi mai bakar zuciya”. Yana da godon hanci da nannadadden gashi irin na fulani, bayan wadanda kuma bai dauko komai na Umma (Zainabu) ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Shekaru suka sake turawa, akayi haife haife da yawa, musamman gidan Alhaji Babba wanda yayi ta aure aure on his quest for samun yaya maza amma in banda second born dinsa yaya Kabir bai kuma samun namiji ba. Goggo na da yakumbo na ma da akayi musu aure daga baya duk suma duk sun haihu, wannan ya kara daga hankalin Inna. Cikin ikon Allah Sadauki yana shekara shidda a duniya Inna ta samu cikina, amma hatta shi kansa baffa bata bari yasan da cikin ba saboda tana ganin kamar Ummah zata cinye abinda yake cikin nata. Sai da ciki ya fito sannan aka gani, Baffa kamar zai zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna, yana murna Ummah tana taya shi.
Baffa ya bani labarin cewa ranar haihuwa ta, shi, Ummah da Sadauki ne suka kai Inna asibiti a motar Baffa. Suka zauna suka jira, Ummah tana ta jerawa Inna addu’ar samun saukin nakuda har Allah ya sauke ta lafiya. A lokacin da aka fito dani a zani aka bawa Baffa shi kansa ba zai misalta irin farin cikin da ya samu kansa a ciki ba, ya karbe ni yana nuna wa Ummah wadda take ta goge hawayen taya Baffa murna. Sadauki yazo ya bude fuskata yana kallona, ya shafa fuska ta yana sannan ya gwada hannunsa a jikin fuskar yana ganin banbancin kalar fatar mu, yayi dariya yace “Baffa wannan babyn kyakykyawa ce” Baffa yace “kanwarka ce sadauki. Sunan ta Haleematus Sadiya” Ummah tace “Allah ya raya mana mai sunan Inno” Sadauki yace “to Baffa mai za’ake ce mata?” Baffa ya shafa kansa yace “matarka ce ai, kai Hardo ita Inno, sai ka zaba mata suna da kanka” Sadauki ya yi shiru yana kallon fuska ta yace “Diyam. Diyam zamu ke ce mata Baffa” Ummah tayi dariya tace “to Allah yasa ta zamo mana maganin kishin ruwa” Baffa shima yana dariya yace “ameen”. Ummah ta karbe ni saboda Baffa yaje siyan magungunan da aka rubuta, yana tafiya su goggo Fatima suka zo, da sauri yakumbo ta karbe ni daga hannun Ummah tana tofe ni da adduoi, sannan ta juya gurin Ummah tace “kurwarta kur wallahi. Wannan yarinyar tafi karfinki” daga nan suka juya sunayi wa juna barka tare da yaba kyawuna ba tare da sun lura da Sadauki daya hade rai yana ta zabga musu harara.