NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 1

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahrulkhair)*


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


*1*

Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi.  

Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala.  daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad’i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min.

Cike da takama da kasaita ta matso daf da ni janyo wuyana tayi tare da ɗauke ni da marin da sai da network din kaina ya dauke gaba daya.
“Munafuka annamimiya irin mugun hali, wato ragowar tuwon da na bari zamu dumama da safe shi ne kika biyo dare zaki cinye shi ko? Dama na dade da fadawa Malam kin fara sata amma ya nuna min kamar nayi miki kaxafi” kafin kace wani abu tuni jama’ar gidan mu sun taru kasancewar gidanmu gidan yawa ne, shi yasa duk motsin da zaka yi a kunnen mutane zaka yi shi, tofa albarkacin bakinsu suka shiga yi dukkan su babu wanda ya tsawatar a kan abinda aka yi min sai ma zuga inna salamatu da suke yi, babu wata kalma da ke fitowa daga bakinsu banda ta aibatawa da muzantawa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Dakin babana inna salamatu ta shiga, tarar da shi tayi yana bacci abinsa, sababin da ta rika yi masa a kansa ne ya farkar da shi, tashi yayi ya biyota suka taho wajena, tsaye na ganshi a kaina, wani irin kallo yake min mai cike da tsana, babu abinda ya fito daga bakinsa sai “tabbas abinda ake zargin ki da shi ya tabbata Sa’adatu, wannan shi ne sakamakon tarbiyyar da nayi miki, sakayyar da xaki min kenan a ajiye abu ki sata ko? abin boye ya fito sarari abinda ake zargin ki da shi ya tabbata yau na gani da idona, da a zatona sharri ake miki amma yau naga zahiri” baƙin ciki ne ya tokare min xuciyata naji kukan ya tafi gaba ɗaya saboda ba wannan ne karo na farko da na fara gamuwa da irin wannan kalubalen ba idan da sabo na saba, indai wannan rayuwar ce mun saba da ita ni da mahaifiyata, an mayar da mu tamkar gumaka marasa amfani a cikin gidan.

Maganar baba ce ta katse min tunanina “Sa’adatu ba ki da labarin na hana a rika baki abincina ne, ba ki da labari nace? amsa min!!!
Kaina a kasa na amsa masa da
“Eh”
“To daga yau na haramta miki abincina ke da uwarki don baxan zauna ina ciyar da ƙatuwar banxa mara amfani ba, shekara sha tara babu abokin tashi duk yan uwanki an gabatar da su ke kadai kika rage, mugun halin uwarki ya hana ki samun miji, to ki sani baxan  cigaba da ciyar da ke ba, saboda duk abinda ke faruwa uwarki tana sane ta kyaleki kara zube ta saka miki ido kiyi abinda kika ga dama to sai dai kuwa ta ɗauki nauyin ki, hidimar ma da nayi a baya ta isa Allah ya bada lada”
Wucewa yayi dakinsa yana huci.
Tuntsurewa Inna salamatu tayi da dariya. 

“Oh Allah ya taimake mu yayanmu suna da farin jini, tun suna yan sha shida ake kwashe mana su, to kin ji dai abinda tsohonki yace da kansa ba sako ba, sai a yi kokari a fito da miji ko kuma a tsufa a gida”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Haka ragowar matan gidan da yayansu suka rika min dariya gami da goranta min a kan rashin samun mijin aure, jikina babu wani karfi kamar an xare min laka na kasa tashi daga wajen da nake sbd takaici nafi minti goma ina xubar da hawayen bakin ciki, yanxu idan Baba ya hana mu abinci wane hali yake so na tsinci kaina.

Tabbas idan rayuwata ta cigaba da kasancewa a haka ban san ina xan sa kaina ba.

Ya Salim na hango daga kofar ɓangaren su yana dago min hannu, alamar na biyo shi. salim dan kanin mahaifina ne kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda basa goyon bayan abinda ake yi mana ni da mahaifiyata, har wasu daga ya’yan gidanmu suna tunanin ko sona yake yi, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa take ta fadi tashi dan ganin ta raba ni da shi. Bin bayan shi nayi muka fito soro, cikin nutsuwa ya kira sunana “Sa’ar mata!!” Da yake da wannan sunan yake kiran a.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Dago fuskata nayi tare da share kwallar da ta cika idona na amsa masa da na’am ya salim.

“Kiyi hakuri a kan abubuwan da suke faruwa a gidan nan, ina daki ina jin irin abinda suke miki kasa jurewa nayi na fita, saboda xuciyata baxa ta jure jin mugwayen kalaman da suke fada miki ba, ki daurewa zuciyarki ki rika kulawa da dukkan abinda xai sa a rika yi miki irin wannan cin mutuncin, indai matsalar abinci ce tasa aka yi miki insha Allah na ɗauki nauyi kullum zan rika kawo muku abincin da xaku ci ke da innah. Ki kara hakuri komai na Allah yana da iyaka kuma dukkan tsananin yana tare da sauki, wannan rashin auren ki ɗauke shi a matsayin jarrabawa, duk wadannan abubuwan da suke faruwa wata rana sai sun zama tarihi a gareku ke da innah, kiyi hakuri ki jure a kan dukkan kalubalen da xaki fuskanta a gidan nan, lokacin ki na yi xaki tashi, da aure da mutuwa duk lokaci ne da su kuma mijinki na nan xuwa ya ɗauke ki, ya samar miki kyakkyawar rayuwa.

Wadannan kalaman na ya salim ba karamin kwantar min da hankali suka yi ba, sai naji dukkan damuwata tayi sauki, farin ciki ya saukar min.

Leda ya miki min, karbi wannan sa’ar mata. Girgiza kai nayi ka bar shi yaya wannan kyautar sai ta jawo maka matsala.
Bata rai yayi ki karba kowace irin matsala xata jawo ba ruwanki.
Tsugunnawa nayi na karba tare da yi masa godiya, wucewa daki nayi na barshi tsaye yana min kallo mai cike da tausayawa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button