EL BASHEER 21-25
*EL-BASHEER*
21-24
Alhj usman yace, “kina ganin me gadi zai yadda ya bada ‘yarsa wa mahaukaci?” Haj ta sauke nannauyar
ajiyar zuciya a boye ganin dabarar ta tazo mata da sauki tace, “sosai ma kuwa karka wani damu zan tmbyr maka shi.” Alhj usman ya numfasa yace, “toh shikenan Allah yasa hakan yafi Alkhairi.” “Ameen” haj ta fada tana murmushi dan sosai tayi farinciki komai yazo mata da sauki. A haka dai suka canja wata hirar.
~~~
Da saurin sa ya karasa jikin kofar yana knocking, haj dake zaune tace “waye?” Sabo gateman yace, “nine ranki shi dade kince nazo yanzu sakina ta fadamin da zata wuce” ya fada yana karya murya, haj ta tabe baki tace, “kana iya shigowa,” sabo me gadi ya isa parlon nata ya zube a wajen yana fadin, “hutawar ki lpy hajjaju makkatu ai daga ke ba qari kece kawai Ta Alhji fitilar gidansa.” haj ta lumshe ido tana me jin kanta na kara girma shiyasa takeson harka da sabo dan yana kuranta ta sosai, cike da izza tace, “ina tafe da wata mgn ne sabo saidai ban sani ba ko zaka yadda” sabo yace, “haba wane ni, Nidin banza ai kan kice ma na yadda dari bisa dari.” dan murmushi haj tayi tana me jinjina kwadayi irin na sabo tasan zai yadda ma sbd tsananin kwadayin sa da son abin duniya, tace, “naji kamar kace kana da yara mata ko?” Sabo yace, “kwarai kuwa dayar ma nan da sati za’ayi aurenta sai karamar bata samu miji ba shine muke fata ta samu a hada bikin a huta.” haj tayi murmushi wato komai yana tafiya nrml, tace, “idan ba damuwa so muke ka bamu dayar a hadata aure da yaron Alhj kaga baida lpy kula dashi sai mace kafin ya samu sauki,”
wani irin farinciki ne ya mamaye sabo yana washe jajayen hakoran sa yace, “kai wannan abu da dadi yake yaushe zanki jinin ku haj? Ai kowa baya wuce kaddara fado masa idan wannan ne na yadda dari bisa dari kamar yadda nace tun farko.” haj a ranta tace, _tasan za’a rina._ yyinda kuma a zuciyar sabo yana farinciki zai samu dukiya matukar ya hada ummi da mahaukaci ai ko bata so dole ayi shidai ya samu kudi ko banza za’ace masa surukin Alhj Usman…., haj ta katse shi da fadin, “duk yadda mukayi da Alhj zakaji kana iya tafiya,” sabo baki har kunne yace, “toh..toh..toh.. Madallah a huta lpy.” Nan yabar ta a parlon.
Wayar haj ce tayi ringing dauka tayi tabar wajen tana me shigewa dakinta ta kulle, kafin tace, “Allah ya taimaki manyan gari da fatan kana lpy,” daga dayan bangaren akace, “Gari lpy haj kwana biyu baki leko ba lpy?” Haj tace, “kaidai bari Alhj Rabe megidan ne ya dawo shiyasa ka jini diff,.” Alhj Rabe yace, “ya kamata ki leko fa dan kaya sun iso dakyar ma muka samu suka iso garemu kinsan kasar yanzu an tsananta tsaro,” haj tace, “aiko dole nazo kamar yadda na saba ko yana gari, zan biya ta wajen Na’omi muzo,”
“That’s gud,.” Alhj Rabe ya fada, nan dai suka katse wayar.
*****
“Saude…Saude….” Da hanzarin ta ta fito dankwali a hannu tana kokarin daurawa tace, “lpy sabo naji kana zugamin irin wannan kiran?” Sabo yana kokarin zama kan tabarma yace, “kedai zauna na baki lbrin abinda ke tafe dani,” Inna saude ta zauna tace, “ina jinka,” sabo yace, “Arziki ne ke bibiyarmu saude,” “kai dan Allah?” Inna ta fada tana washe baki, sabo ya girgiza kai yace,
“kinsan yaron nan dan gidan Wanda nakema gadi?” Inna tace, “ni ina zan sanshi? Nasan dai me damara ne,” “Yauwa to shi kinsan yana ciwon hauka ko?” Inna tace, “kwarai kuwa ya warke ne?”
Sabo yace, “inaaaa sai abinda yaci gaba ma, to shine uban yaron daya dawo yaga halin da dan ke ciki ya yanke shawarar yyi masa Aure.”
“A haukan?” Inna ta katse shi da mgn tana zaro ido, sabo yace, “kwarai kuwa a hakan,” Inna tace, “wanne marar hankalin ne zai aurar da ‘yarsa ga mahaukaci?” Sabo yace, “ke dallah ana ga gabas kina ga yamma ki tsaya ki saurara mana,” Inna tace, “toh ai lbrin kane banga inda ya hadu da bayanin farko ba wato arziki na kiranmu,” sabo yace, mutanen gidan suka nemi na basu ‘yata ya aura kafin ya samu sauki,’
“kan ubancan.”
inna ta mike tana rike qugu tace, “bansan cewa ka fara sakin layi ba sabo sai yanzu, kai son duniyar taka har yakai ka bada jamila ga mahaukaci?” Sabo yaja tsaki Mwssstt, yace, ‘dadina dake bakyacin ribar zance iya jamila ce ‘ya a gidan nan?” Sai a lkcin hankalin Inna ya kwanta ta sake zama tana rage murya tace,
‘Ummi zaka basu?” Sabo yace, “toh dawa ta dace idan bashi ba.”
£Ahayye ayyuriyuriiiii….” Inna tasa guda bakinta har kunne tace, “kai shiyasa nake sonka sabo kanada basira ni wlh gaba1 na mance da itan ne kasan sha’anin biki ya matso kusa abubuwa sunyi yawa.” Sabo yana murmushi yace, “toh atakaice dai zuwa wani satin harda ummin za’a yiwa auren da yaron nan mahaukaci,” Inna ta sake yin shewa tace, kai amma baka tabamin Albishir me dadi ba sai yanzu,” dariya sabo yyi yace, “ke kika sani.”
~~~
Wannan shine sumanta na uku tana farfadowa sbd tsananin shiga tashin hankali da firgici, ta kara tabbatarwa lalle bata da wani sauran gata a duniya domin wanda take kallo a matsayin ‘yan uwanta sun koma makiyan ta, yo idan ba makiyi ba waye zai baka mahaukaci kana da lpyr ka? Ina ma aka taba aure da mahaukaci idan ba kaima baka da hankalin ba……”
“Kozaki mutu wlh sai kin aureshi” cewar sabo yana tsaye kan ummi da tunda suka sanar mata ta suma sbd tsananin firgici, wani irin hawaye ne me radadi suka sirnano mata a kumatu, dakyar ta mike zaune daidai lkcin kuma jamila ta kwashe dawata mahaukaciyar dariya harda hawaye tana fadin, “su o’o da angonta mahaukaci tab gsky zanga yadda za’a kaya zama da marar hankali hhhhh…” ta sake kwashewa da dariya inna na taya ta, sidaf ta mike ta shiga daki domin ji take wani quntullun abu me nauyi ya tsaye mata a kirji ta lura matukar taci gaba da zama tare dasu zata gamu da ciwon zuciya.
****
Tunda sabo ya amince sai shirye2 ya kankama, both bangaren Amare da Angwaye, yyinda Ango el-bash besan wainar da ake toyawa ba, saidai frnd dinsa suraj ya shiga lamarin bikin dukda ransa a jagule yake tamkar shi za’ayiwa auren sam baya maraba dashi, yasan yanayin abokin nasa badan halin daya tsinci kansa ba ai mace sai wacce yaso bare ma mata nawa ne suka nuna sonsu gareshi? Shidai da yanada iko tabbas da ya hana Abba bikin nan toh Amma ya zasuyi? Haka Allah ya tsaro abin zai kasance cikin Shirin su.