NOVELSUncategorized

DIYAM 13

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirteen: My Saviour

Ranar da mukayi hutu a ranar Mama ta aiko babban danta yaya Mukhtar wanda kusan sa’an Sadauki ne yazo tare da drivern su ya dauke mu.
Lokacin Sadauki bayanan sun tafi gidan yaya Ladi shida Ummah, haka na shirya raina duk babu dadi ga yaya Mukhtar yana tayi min jaraba wai in yi sauri ina bata masa lokaci ni kuma Allah Allah nake su Sadauki su dawo kafin mu tafi dan muyi sallama amma ina, haka ya tasa keyar mu yana ta rankwashi na muka shiga mota ina ta waigen ta inda Sadauki zai billo amma har muka sha kwana babu shi babu alamar sa.

Tun daga nan fa shikenan na turbune fuska kamar an aiko min da mutuwa. Da muka je gidan ma da kyar na gaishe da Mama, ta harare ni tace “ke kuma me akayi miki kike wannan bacin ran?” Nan take hawaye ya fara zubo min, na saka bayan hannu na ina gogewa nace “ni gidan mu zan koma” yaya Mukhtar ya dungure min kai yace “yi mana shiru anan, shagwababbiya kawai” ai kuwa nan take na bare baki “wayyo Allah na wayyo Sadauki” Mama ta tafa hannu tana salati “wayyo Sadauki? Dama abinda duk Adda take fada gaskiya ne? To zaki ci ubanki ne ke da sadaukin, babu inda zaki je muna nan dake a gidan nan”.

Mama yayanta biyar, yaya Mukhtar ne babba sai yaya Abdullahi sannan Rumaisa wadda take sa’a ta kuma a lokacin kusan itace best friend dina bayan Sadauki sannan Muhsina sai Rufaida yar auta kuma sa’ar Asma’u. 

Tunda muka je gidan, ga dai kayan wasa nan iri iri saboda babansu mai budi ne amma ni sam basa gabana, sai in ringa tunanin ina ma tare da Sadauki muka zo, nasan da zai so video game din su Abdullahi. Mama tayi fadan har ta gaji ta rabu dani tace “shegen taurin kai irin na uba” ni dai nayi tagumi ina kallonta. Da Rumaisa kadai muke dan yin hira, shima kuma duk kusan hirar sa ce dan ita din ma mutuniyarsa ce saboda ni, duk sanda taje gidan mu yana yi mata wasa sosai. Ranar nan muna backyard,su yaya Mukhtar suna ball mu kuma muna kallon su. Nayi tagumi sam hankali na baya tare dasu ban sani ba ashe hawaye ne suke bin kumatu na, kawai sai jin saukar ball nayi a goshina, na hantsila na fada bayan bench din da muke zaune, nan take sai ga jini yana zuba daga hancina. Rumaisa ta zagayo tana yi min sannu, na mike ina kallon yaya Mukhtar da yake yi min dariyar mugunta alamar shine ya buga min ball din yace “yanzu sai kiyi kukan mai dalili ai” murya can kasa nace “Allah ya isa na kuma sai na gayawa Sadauki” ai kuwa a guje ya bini har bayan Mama, ta rike shi tana tambayar abinda ya hada mu ga hancina da jini, ni dai ban tsaya bin ta kansu ba na shige daki na rufe kofa.

A daddafe mukayi sati biyu, a ranar da muka cika sati biyu kuwa sai ga Baffa ya sako Sadauki a gaban mota sunzo daukar mu. Ina fita maimakon in tafi gurin Baffa sai na wuce shi na tafi gurin sadauki. Mama ta fito ta gaishe da Baffa tana mita “hutun nasu fa bai kare ba, ni ai ba’a gaya min yau za’azo daukar su ba gashi ko dinkunan su ba’a karbo a gurin tailor ba” Baffa ya daga Asma’u da tazo gurinsa da gudu yace “in an gama dinkin a aika musu dashi gida”.

Tun a mota na fara zayyanawa Sadauki duk irin cin zalin da yaya Mukhtar yayi min, tun daga dungemin kan da yayi har zuwa doka min ball da yayi a ka. Baice komai ba sai ya mulmula min goshin kamar yanzu akayi dukan. Bamu kuma tayar da maganar ba ni har na manta ma sai kawai rannan Mama ta aiko yaya Mukhtar ya kawo mana dunkunan da tayi mana ni da Asma’u. Sai da muka gama gwaggadawa muna ta murna ya fito Inna ta biyo bayansa tana bashi sakon godiya zuwa ga Mama, bai yi aune ba sai jin saukar ball yayi a goshinsa, ya hantsila ya fadi a gaban Inna jini yana bin hancinsa. Muka daga kai cike da mamaki sai ga Sadauki yana saukowa daga stairs din saman dakin Baffa, ya tsaya a gaban Mukhtar yace “gobe ma in Diyam ta kara zuwa gidan ku ka sake buga mata ball aka”.

Inna tayi kukan kura ta riko shi, amma sai nayi sauri na rike hannunta har ya samu ya zame ya fice da gudu, ai kuwa sai tayo kaina, na ruga sai dakin Baffa na rufe kofa ina leken ta taga. Tayi ta banbamin fada tana debe wa Sadauki albarka “bakin mugu mai bakar zuciya. Allah ya isan sa, idan ya dake ta ina ruwanka? Dan uwanta ne, kai kuma fa? Marar asali” tayi tayi dai babu wanda ya kula ta, ta tashi Mukhtar ta bashi ruwa ya wanke fuskarsa amma sai ya kasa fita wai tsoro yake kar Sadauki ya kuma kamashi a waje. Haka ya koma daki har sai da na fito nace “kayi tafiyarka, babu abinda zaiyi maka ai ya ramamin”. Kuma haka ya fita a tsorace amma Sadauki yana kan mota ko kallonsa baiyi ba. Tun daga ranar ko kallon banza yaya Mukhtar bai kara yi min ba.

Yana daga al’adata kullum da daddare dakin Ummah nake zuwa inyi kallo. Inna ta hana amma sai Baffa ya daure min gindi yace “ai homework Sadauki yake koya mata a can din. In kuma kin iya sai ke kike yi mata a daki” Inna bata yi makaranta ba dan haka dole ta hakura. Yes, muna yin homework din in mun gama kuma muyi kallo muyi hira ko Ummah tayi mana tatsuniya. Inna dai ba’a san ranta ba. Wannan yasa ta dage sai data samo mana islamiyyar dare duk kuwa da cewa muna yin ta assuba sannan muyi ta yamma. Baffa yayi magana tace “ai ilimi baya yawa” haka ina ji ina gani kullum nake tafiya islamiyya da daddare. Ni raina baya son islamiyyar nan musamman saboda malaman akwai cin zali kullum zaka gansu suna yawo da doguwar bulala ni kuma babu abinda bana so irin a taba lafiya ta. Ga prefects suma da shegiyar mugunta. Kullum sai Sadauki ya tabbatar naje da wuri saboda kar a dake ni, in lokacin tashi yayi kuma shi zaije ya taho dani saboda kar wani ya tare ni a hanya yaci zalina. 

Ranar nan sai na kasa bada hadda. Yasaiyadi ya ware mu ya kira monitan aji uku yace ya zane mu. Haka aka zazzabga min dorina a baya na, gurin ya tashi yayi rudu rudu. Tun da aka dake ni nake kuka har aka tashi Sadauki yazo tafiya dani. Ina fita kuwa na gaya masa duk abinda ya faru, yace in nuna masa wanda ya dake nin a nuna masa muka taho gida. Dama ranar laraba ne, ban san yadda akayi ba sai ranar assabar na tafi makaranta wata yar ajinmu ta tare ni a hanya tace “Diyam, wallahi kar ki je makaranta yau, ana nan an ciro bulalai ance yau sai an zane ki, wai yayanki Sadauki ya tare monitan daya dake ki rannan ya zane shi shida kaninsa. Wallahi yasaiyadi uku ne suke jiranki a makaranta” nan take cikina ya duri ruwa, na juya da sauri sai gida, ina shiga na lallaba na wuce dakin Inna na shige dakin Ummah, nayi sa’a itama bata nan tana dakin Baffa sai Sadauki yana kallo. Na dora hannu aka ina kuka na gaya masa abinda ya faru, yace “zauna. Kin daina zuwa islamiyyar daga yau. Ai ba jakarsu bace ke da zasu saka ki a gaba suna duka kamar ganga. Ina nan zaune a kusa dashi har Ummah ta dawo, ita ta dauka har na taso daga islamiyyar ne dan haka tace “Diyam ki tafi gurin innar ki kar tazo tana nemanki”. 

Washegari ina kallon Sadauki yana ta yan aiyukansa a saman rufin dakin Baffa, da Baffa yayi masa magana sai yace “Baffa zafi ake yi, hawa zanke yi sama ina shan iska da daddare” yana gama wa sai ya kira ni gefe yace min “idan Inna tace ki tafi islamiyya da daddare ki hau sama kiyi kwanciyarki” shikenan nayi graduating daga islamiyyar dare. Kullum da dare in lokacin islamiyya yayi sai in lallaba in hayewa ta sama inyi kwanciya ta akan katifar da Sadauki ya shimfida min. Daga baya sai Sadauki shima ya fara biyo ni, yazo muyi ta hirar mu muna dariya, ko kuma yazo mana da games din Chess, Watt ko ludo muyi tayin kayanmu. Amma duk kanin mu munsan cewa duk wanda ya juri zuwa rafi to kuwa tabbas watarana zai fasa tulunsa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button