DIYAM 15
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifteen: Baffa
Cikin hanzari Inna ta juya ta koma daki, baya yi second uku ba sai gata ta fito da sharfadediyar dorinar da ta siyo ta ajiye danyi min barazana a duk lokacin dana ki jin maganarta. Da sauri na zagaya na koma bayan
Sadauki, na kusa fuskata a bayansa zuciya ta tana aiyana min cewa yau kwanana ya kare, na tabbatar da cewa yana iya jin bugun zuciya ta a bayansa. Cikin tsananin zafin rai Inna ta karaso inda muke tsaye amma sai Sadauki ya sake tura ni baya ya hadani da jikin bango shi kuma ya tokare ni da jikinsa. Nan Inna ta fara dukansa da iyakacin karfinta da wannan dorinar ta hannunta amma ko gezau baiyi ba, shi kawai kokarinsa shine ya kare duk dukan kar wani ya sameni.
Sai da dorinar hannunta ta kakkarye sannan ta yar da ita ta shiga kitchen ta dauko muciyar tuwo, a lokacin ne Baffa yayi sauri ya rike hannunta, sai kuma ta saka kuka tadora fuskarta a kafadar Baffa. Sai kuma yaja hannunta a hankali ya shige da ita zuwa dakinta. Umma ce ta taho itama zuwa inda muke tsaye ta sauke kyakykyawan mari a kuncin Sadauki, kafin ya dago kai ta kuma marin daya side din sannan kuma cikin sassarfa ta wuce dakinta, Sadauki ya bita da sauri yana kiran sunanta “Ummah ta, Ummah ta. Ummah dan Allah kiyi hakuri”. Sai ya kasance an barni ni kadai a tsakar gidan. Na durkushe a gurin ina jin kafafuwana suna rawa, sai kuma na dafa bango na mike da niyyar komawa sama in dauko kayana, a lokacin Baffa ya fito daga dakin Inna, nayi saurin komawa na dunkule a guri daya ina cewa “wayyo Allah Baffa kayi hakuri. Na tuba, bazan sake kin zuwa islamiyya ba” yazo ya tsaya a gaba na ya miko min hannunsa yace “zo uwata” na sake ja da baya, ya kama hannuna yace “zo Diyam, ba dukan ki zanyi ba, magana zamuyi kawai” na mike a darare amma sai naga yayi min murmushi.
Dakin sa ya jani muka tafi, ya zaunar dani akan kujera sannan shima ya zauna a kusa dani yana kallon yadda jikina yake karkarwa yace “share hawayenki ki daina kuka, ni ba dukanki zanyi ba kuma bazan bari innar ki ta dake ki ba in dai har kika gaya min gaskiya. In kuwa kika yi min karya, zan zaneki sannan bazan hana innar ki dukan ki ba kuma sauran ke da Allah, kinsan baya son mai karya ballantana mai yiwa iyayensa karya” na gyada kai ina jin dadi a raina tunda yace ba za’a dake ni ba sai in nayi karya, ni kuwa yadda nake ji da jikin nan nawa me zai saka inyi karya? Yace “me yasa innarki ta tura ki islamiyya kika ki zuwa kika buya?” Na share hawayen tunowa da laifi na na islamiyya sannan nace “dukana za’ayi in naje” yace “me kika yi zasu dake ki?” Na bashi labarin abinda Sadauki yayiwa monitan aji uku. Ya jinjina kai yace “to me yasa da akayi haka baki zo kin gaya min ko kumako gayawa innarki ta gaya min in yaso ni sai inje makarantar in basu hakuri shi kuma Sadauki inyi masa fada ba?” Na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna ina tambayar kaina me yasa? Ni da abin ya faru ma it never occurred to me cewa in gaya wa inna, in na gaya mata gani nake fada zata yi min ko kuma ma ta dake ni, besides, bana so ayi wa Sadauki fada akan me yasa ya daki wancan yaron.
Yace “to Sadauki ne yace kike buya a sama?” Na gyada kaina, yace “kuma sai shima yake zuwa kuke zama tare a saman?” Na kuma cewa “eh” yace “to me kuke yi a saman?” Nace “games muke yi” yace “wanne irin game?” Nace “ko chess ko lido ko whot ko kuma….” Sai kuma nayi shiru, Yace “ko kuma me? Kinsan dai kinyi min alkawarin zaki gaya min gaskiya ko?” Nace “ko kuma muyi ta labari” yace “wanne irin labari?” Nace “ko ya bani labarin gareji ko makarantar su nima sai in bashi labarin makarantar mu da kawayena” yayi shiru yana jinjina kai sannan yace “to yanzu ina dankalinki da hijab dinki?” Na nuna sama da hannuna, yace “ya akayi kika cire su?” Nace “hijabin cirewa nayi dan kar yayi squeezing, dankwalin kuma bansan ya zame ba” yace “to me yasa kika sauko da gudu dazu, fada kukayi?” Na girgiza kaina sai kuma nayi murmushi ina tuno kalaman sadauki, Baffa ya sake maimaita tambayarsa yana nazarina, nace “na fada mukayi ba, kunyarsa nake ji shine na rufe idona shi kuma yace sai na bude masa yagani” Baffa ya dan bata fuska yace “me yasa kike jin kunyarsa?” Na dan rufe fuskata alamar kunya Nace “cewa yayi I am the only star in his sky” Baffa ya bude baki da mamaki yace “shi Sadaukin?” Na gyada kaina ina murmushi. Ya jima yana kallona sannan yace “to sai wanne wasan kuma kukeyi a saman?” Innocently na daga hannuna nace “shikenan” ya kuma yin shiru yana kallon na, sai kuma ya gyada kai yace “to yanzu kingakinyi wa innarki dani baffan ki laifi, an tura ki islamiyya kinki zuwa, me zaki ce mana?” Na durkusa a gabansa nace “Baffa kayi hakuri” ya kama hannuna yace “na hakura, saura Inna”.
A zaune muka sameta, idonta akan tv amma daga gani ba kallon take yi ba, hallonta daya akan Asma’u tana shafa kanta a hankali ita kuma tana bacci. Na rakube daga bakin kofa ina kallonta, Baffa yaje ya zauna akan kujerar da take kusa da ita sannan ya kirawo ni da hannu yace “me kika cewa innarki?” Na durkusa nace “Inna kiyi hakuri, na tuba, bazan kara buya ba inkin kuma tura ni islamiyya” ta watsa min harara tace “kuma ba zaki kara kula Sadauki ba?” Na sunkuyar da kaina nayi shiru. Baffa yace “tashi ki tafi dakin ku ki kwanta” na tashi babu musu na shiga na kwanta, sai kawai naji ina tunanin koya Sadauki yake ji a jikinsa? Dan nasan ba karamin dokuwa yayi a gurin Inna ba.
A palo bayan na wuce Inna tace “shikenan? Shikenan maganar nan ta wuce? Shikenan ba zaka dauki mataki akan yaron nan da yake neman ya lalata maka yarinya ba?” Baffa yace “nayi magana da Diyam, abinda kike tunani ba haka bane ba. Tabbas shi ya hanata zuwa makaranta saboda wai ance za’a dake ta in taje akan laifin da shine ya aikata ba ita ba. Tabbas Sadauki yayi laifi kuma zan zauna inyi magana dashi kamar yadda nayi da Diyam. Zan fahimci inda yake da kuskure in nusar dashi, inda kuma yayi laifi inyi masa fada” hawaye ya zubo daga idon inna tace “shikenan abinda zakayi masa?” Yace “to gaya min me kike so inyi masa?” Tace “ka mayar dashi gidan ubansa tun kafin yalalata mana yarinya ya cuce mu” ya girgiza kansa yace “Sadauki ba zai lalata Diyam ba, in ma hakan ta faru to mune zamu kasance masu laifi fiye dashi. Yanzu in tambayeki? Me yasa da Diyam ta gudo daga makaranta batazo gurinki a matsayin ki na mahaifiyarta ba sai ta tafi gurin Sadauki?” Da sauri inna tace”saboda ya cinye kurwarta bata ganin kan kowa da gashi sai nashi” Baffa ya girgiza kai yace “saboda a gurinsa take ganin zata samu maslaha in ta zo gurinki problem zata karawa kanta. Yarinyar nan dududu shekarunta goma da watanni a duniya, yanzu ne ya kamata ace kin kara jawo ta jikin ki kin koyar da ita lamurran duniya, amma me? Diyam tsoron ki take ji, komai tayi gani takeyi kamar laifi zatayi a gurinki. Yanzu da ace ma lalata tan yakeyi kamar yadda kika yi tunani ta yaya zaki sani? Kince ba kya son taje dakin Zainab, amma ke kin gaza yi mata abinda Zainab din take yi mata har take nacin zuwa dakin nata, wasa da dariya, kulawa, nuna soyayya, wannan shine kadai abinda Diyam take bukata daga gurinki a wannan lokacin. Ke kika haife ta, dan haka in kika sakar mata fuska zakiyi mamakin yadda zata sake dake itama”.
Inna ta kalleshi tace “dama na sani, nasan duk yadda zakayi ka juya maganar nan ta koma kamar laifina ce sai kayi, ni kumana riga na sani, nasan cewa kafi son Sadauki akan Diyam, kafi son agola akan yar data fito daga jikin ka, kamar yadda ka fi son zainabu akai na ni uwargidan ka kuma yar uwarka ta jin, kuma uwar yayanka na gaskiyai” Baffa ya mike tsaye yana girgiza kai yace “Diyam ni na haifeta, Sadauki kuma nina rike shi tun yana cikin tsumman sa dan haka dukkan su yaya nane, babu banbanci. Maganar tsakanin ki da Zainab kuma ke kike ganin haka, ke kika saka haka a ranki. Amma ina son ki bude idonki ki kalli gabanki sosai zaki fahimci ke kadai kike fadanki babu wanda yake amsa miki”
Har ya kai bakin kofa tace “ina neman alfarma guda daya a gurinka” ya juyo amma bai ce komai ba, tace “ina son idan har Diyam ta kammala primary a kaita boarding school” yace “Allah ya nuna mana lokacin”.
Writing……