NOVELSUncategorized

EL BASHEER 25-28

*EL-BASHEER*

25-28

Sale qanin haj ne zaune a parlon hajiyar suna mgn yace, “gsky haj na gaji da gafara sa banga qaho ba, koyaushe kice baki samu dama bane yaushe kikeso damar ta zo ne? Nifa
wlh idan bazan samu kudin nan ba sai na tura abokai na su kashe mijin naki idan ya mutu ai dole a baki gado mu tattara dana dan nasa tunda ba hankali ne dashi ba muyi gaba” haj tace, “kaifa sale azarbabin ka ya cika yawa ance maka haka kawai ake kashe babban mutum batare da an shirya ba?” Sale yaja tsaki “to ke yaya ai naga abin naki ne kina sanyi-sanyi ni kuma komai da zafi-zafi nakeso,’ haj tace, “so nake wannan bikin daya baro mana na samu ayishi, kaga ko a harkar bikin nan ya sakar min bakin aljihu komai nace bani yake ko ita yarinyar akwati uku nasa akai mata sauran kudin 12 da yace ayi na makale ga sauran wasu hidimar dukfa ana samu.”  sale yace,  “nidai kin sanni bani da kyau, ana gama bikin mu aika shi.” haj tace, “ina tunanin wata shawarar idan nayanke zan gaya maka,” Sale yace, “yanzu naji mgn, ina ganalalliyar yarinyar nan ta tafi ne?” Haj ta hade rai tace, “nifa matsalata dakai kenan kushe min ‘ya, yanzu kuma me tayi?” Sale yace, “koma dai menene ki tmbyeta matsalar ku ce kinga tafiya ta saidai kafin na wuce miko min wasu kudin na samu na sigari.”        
haj ta bude pos dinta ta cillo masa kudi tace, “aikin kenan mtwss” dariya sale yyi yace, “kardai ki zafafa akwai yarinya akasa,” haj ba tare data fahimci me yake nufi ba tace, “kaga ni jeka sai na kira ka,” sale yace, “ko bakice bama tafiya zanyi.” nan yyi ficewar sa.***
Alhj Rabe ne ya kira haj daidai lkcn ta fito mota ta dawo daga unguwa, “Hello ina jinka Manyan gari” Alhj rabe yace, “karki manta akwai meeting da za’ayi nan da two weeks” daidai lkcin da zata gifta ta gefen part din El-bash tace, 
   “oh har ansa ranar meeting din?” Alhj rabe yace, 
   “eh akwai sabbin mutane ma da muka samu wanda suka kware wajen satar yara musamman en makaranta da ‘yan mata”  Haj tayi murmushi tace,
   “kai kace wannan karon Oga kwata-kwata zai halacci wajen…..” Diff…tayi shiru sbd hada ido da tayi da el-bash dake jikin window parlon sa ya nade hanayen sa a qirji fuskar nan babu alamar Annuri.
A tsorace ta saukar da wayar hannunta, saurin karasawa tayi jikin windon sai taga still direction din data bari yake kallo tana waigawa kuwa taga wata tsuntsuwa ce ta sauka tana dan yawonta a hankali kamar yadda tsuntsaye keyi idan sun sakko kasa, wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki tana jan tsaki  
   “ashe ma bani yake kallo ba,” tayi mgnr a fili, saidai wata zuciyar tata tace,
   _”kamar fa itan yake kallo tun farko da alama, sai kace me hankali yana sauraron ta_ 
   “Kai Amma kuwa dana shiga uku dan babu wanda yasan ina suke haduwa da kuma asalin waye ogansu na kungiya, kungiyar da jami’an tsaro sukayi mata caa suna neman ta ruwa a jallo sbd illar da sukema kasa da kuma mutanen cikinta…,          
   a razane ta sake juyowa tana kallon sa sbd tabar inda yake, sai kuma still taga direction din dazu yake kallo dan tabe baki tayi toh ni meyasa zan damu mutumin ma da bashi da hankali? Ko yaji ma yasan me nakeyi?     
   __Kinsan kuwa da da Hankalin nasa da kin muku babbar barna dan nemanku ake wanted wani irin bugawa qirjinta yyi sbd tunowa da wanene *EL-BASHEER* Jami’in Sirri na kasa, badan ta masa aiki ya haukace ba da tuni ya kamasu.
    Da wannan tunanin ta karasa parlon ta.

    Tana shiga ta tarar sakina a kwance kan kujera tana kallo, haj har ta zauna sakna batace mata komi ba, haj tace, “ke bakiga shigowa na bane?” Sakina ta da gyara kwanciyar ta tace,
    “toh ni momy me zance?”  Haj suwaiba tace, “ke kul baki kiyayeni ba wlh, ke banda rashin sanin ciwon kai me zakiyi da mahaukaci?” Na lura tunda kikaji lbrn auren sa kike ta kunci toh gwara ma tun wuri ki cireshi a rai ko kitattara ki koma gidan ubanki can kauye.”
  Sakina ta mike zaune tana tura baki tace, 
  “nifa bawai ina sonsa bane kawai dai zan zauna dashi ne har na tayaku neman dukiyar sa,” 
   haj suwaiba tace, “dallah rufemin baki wawiyar banza, ai ko a wasa bana fatan kiyi aure d mahaukaci bare kuma dgske, dukiyar sa kuma ke zaki ce mana ga yadda zamuyi? Kul baki kiyayen ba.” 
   sakina ta mike tsaye tana dira kafa irin na tabararrun yara tace, “ai shikenan momy ni na hakura dashi tayi mgnr tana wucewa dakinta. 

Haj suwaiba ta dafe kanta daya sara mata tace, “haba yarinya daya kina neman jazamin bala’i Mtwss tayi tsaki tana gyara zaman ta.


~~~~~
Ummi har wata irin rama tayi sbd tashin hankali, lkcn da aka kawo akwatin ummi guda uku taga en habaici da tashin hankali, kowa saida ya fadi ta bakinsa ana wannan akwati ko bazawara iyakaci kenan, abin nema ya samu gun jamila da qawayenta, nan suka saka ummi gaba da dariya kowa yazo za’a jawo akwati a nuna masa ana shewa, kowa yaga alamar inda ummin zataje ma ba zaman jin dadi zatayi ba, toh zama da mahaukaci ma ina yaga dadi? Kowa da abinda yake fada, unguwa kowa ya dauka ummi mahaukaci zata aura, mutane sai dariya ake mata musamman wasu da suke kallon ta a matsayin me girman kai sbd ba kula kowa take ba daga mazan har matan shiyasa abin yai mata yawa, kadan ne tsirarai masu tausaya mata. En Mata dayawa sunci burin rakiyar ummi dandai kawai suje su gano Ango mahaukaci, dan tabbas sunsan yana cikin qazanta da wari, ita kanta jamila amarya cewa tayi sai taje rakiyar ummi ta gano Ango mahaukaci, Ummi banda kuka ba abinda take, gaba1 ta zuqe ta lalace.


****
Yau ta kasance juma’a Rana me Albarka ranar da ake daurin auren ummi da el-bash, karfe 2pm za’a daura, dake a yanayin rashin lpy yake Ango sai Abba be wani yi taro dayawa ba.
     Tun karfe daya Suraj ya kawo wa el-bash sabon dinkin sa daya sha aiki, tunda ya aje kayan el-bash be kalli inda suke ba, Suraj ya masa kwatance da hannu Alamar ya saka, el-bash yyi banza dashi, Abinka daya saba koyaushe kananun kaya zaka ganshi dashi, dakyar Suraj ya sashi dole ya canja kaya, qasumbar ma ba’a rage ba dan ki yyi, kamo hannunsa suraj yyi da nufin su fita suna zuwa daidai kofa ya tukare, Suraj yace,
 “muje,” 
el-bash ya hade fuska sosai yaki fita, Suraj ya dafe kansa ya tuna tabbas tunda el-bash ya fara hauka be kara fitowa waje ba, Dabara suraj ya sake masa akan ya fita nan ma yaki, saida Abba zai wuce ya hango su, nan yazo da saurin sa yace, 
  “lpy suraj baku fita ba?” Suraj yace, 
   “wlh Abba tun dazu nake fama ya fito yaki,” Abba ya kamo hannun El-bash yace, 
   “muje,” sai a lkcn ya fito, har bakin mota Abba ya rakasu sannan ya tabbatar ya shiga mota kafin ya barsu, suraj ne ya zaga dayan gefen ya shiga, sai security abokin aikinsu me suna Musa yaja motar, sauran frnds dinsu suka biyosu a baya. 


Koda akaje wajen daurin Auren ma kin fitowa yyi, bare yaga jama’a sosai sai ya makale a mota, duk yadda akaso ya fito ki yyi sai hakura akayi, sauran mazan unguwar su Ummi ba haka suka so ba, gsky sunso suga mahaukacin ummi Amman yaki fitowa ga motar baqin glass ne bare a hango shi, dayawa abinda ya kawo su kenan sai basu samu yadda suke so ba.


Gyaran murya me sanarwa yyi, kafin ya fara cewa A wannan rana ta juma’a Ana daura Auren Asma’u Ahmad (ummi) da Angon ta El-Basheer Usman Tafida akan sadaki dubu Dari. Nan aka fara kabbara Ana murna aure ya dauru, dayawa wanda suka zo gulma sun cika da mmikin jin kudin da aka biya sadakin ummi, yyinda jamila da Angon ta Haruna akan sadaki dubu talatin. Kowa ya rude da zance sai kace nace ake. 


Ummi dake jiyowa ta sake fashewa da kuka, yanzu kuma ta fahimci ma sayar ta akayi tunda aka biya wannan uban kudin, Allah sarki ita kuma haka tata kaddarar rayuwar tazo kenan sayar da ita za’ayi.

Sauran mutanen gida sai maida zancen sadaki ake, ba haka jamila taso ji ba, taso ace a sadakin ma tafi ummi, saidai bata sani ba ko a lefen ma ummi ta fita nesa ba kusa ba dandai haj suwaiba ta rage ne.

Haka dai akaci gaba da shagalin biki, Abba yace yanaso a kawo Amaryar a ranar, hakan kuwa akayi bayan sallar Isha aka fara shirye2 kai Amarya ummi wacce ta hade cikin lace dinta daya daga cikin na akwatin ta, dinkin dai gashi nan dai, sai gyale da aka yafa mata,  zugar mutanen da suka shirya dan zuwa kai Amarya Allah yai yawa dasu, kowa so yake yaje yaga dakin ummi da mijin nata,  ummi dai takaici ma ya hanata cewa komi haka dai take binsu kamar jela. 

Motocin da akazo daukar amarya ma Abin ba’ace komi dan kuwa Abba mota ya bayar aka tafi kwaso masu kawo amarya, besan meyasa ba haka kurum yaji 100% auren ya kwanta masa. Masu niyyar zuwa kuwa sunyi murna dan kuwa an samu abin hawa. Yyinda a bangaren su Suraj abin ba’ace komi harka ce ta iyaye babu yadda zasuyi auren ma ba farinciki suke dashi ba bare kuma a tura zugar motoci kamar za’a dauko Sarauniya, Tabbas da El-bash a yadda yake ne da bazai taba auren ‘yar me gadin gidansu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button