NOVELSUncategorized

DIYAM 2

 ❤️DIYAM  ❤️
                                                 
  Page two

Washegari basu da madam Sally, malamar da tayi musu lecture din jiya, a takaice ma lecture din safe kawai suke da ita shikenan
sun gama. Wannan yasa suna fitowa kowa ya fara kokarin tafiya gida dan gabatar da al’amuran sa na yau da kullum. Yarinyar jiya ce ta fito a karshe, tana rungume takardu a kirjinta da hannu daya daya hannun kuma tana rike da wayarta, tana ta waige waige kamar me neman wani sai kuma ta fara tafiya a hankali tamkar mai jin tsoron taka kasa.

Daga inda yake tsaye yana hango yadda daliban suke fitowa daya bayan daya. Ya dauko pack din cigarette a aljihunsa da lighter ya kunna yayi mata dogon zuka ya lumshe ido. Deliberately ya riga kowa fitowa saboda yana son ya ga fitowarta, yana son su cigaba da maganar jiya, yana so kuma ya ja mata kunne akan tasan maganar da zata fada tasan kuma a inda zata fada. Ya danyi karamin tsaki. Haka kawai tana neman ta zubar masa da class a cikin mutane dan duk friends dinsa sunsan shi ɗan Nigeria ne kuma zasu dauka abinda ta fada gaskiya ne.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Yana kallonta ta fito, ta danyi dube dube sannan ta taho direct zuwa side din da yake, tana tafiya a hankali tamkar mai kirga takunta wanda hakan ya bashi damar karewa siffarta kallo, ‘too beautiful’ yayi deciding, ‘too beautiful for my taste’. Har tazo ta wuce shi bata ko lura dashi a gurin ba, ya bata dama ta danyi nisa sannan ya yar da cigarette din hannunsa ya bita da dan sauri yace “hey” ta dan tsorata kadan sannan kuma ta kalle shi ta dauke kai ta cigaba da tafiya, ya daidaita takun shi da nata ya sake cewa “hi” ta dakata tana kwallonsa cikin ido ba tare da ko alamar tsoro ba tace masa “Assalamu alaikum” ya dan shafa kansa yana jin duk confidence din da ya ke dashi yana draining. Her eyes makes him uncomfortable. Jin bai amsa ba yasa ta sauke idonta kasa ta cigaba da tafiya. Ya bita a baya yana cewa “my name is Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq” ya sake shafa kansa yace “my God, this is so awkward, I always feel like this duk sanda nake introducing kaina. I hate my name. Na rasa dalilin da yasa iyayen mu suke son lallai sai sun saka wa yayansu sunan iyayen su. I mean, it make the name only circles and remains in the family. I always wish I can change my name” ta daka ta ta tsare shi da ido, ya dauko handkerchief a aljihunsa ya goge fuskarsa duk kuwa da cewa ba gumi yake ba, he obviously looked nervous, duk planning din da yayi na irin maganganun da zai gaya mata ya gudu ya barshi. A zuciyarsa ya gode wa Allah da ya zamanto su kadai ne a gurin. Yayi ajjiyar zuciya yace “I am talking too much, aren’t I?” Ta girgiza kai kawai sannan a nutse tace “in my religion, Islam, an bawa mutum damar chanza sunansa in baya so, what you only need to do is ka sayi rago ka yanka da niyyar ka chanza suna, sai ka kira mutane su shaida, shikenan. But I don’t know ko naka addinin ya yarda da haka” he was stunned, wato kallon wanda ba musulmi ba take masa, how can she even think that? Ya bude baki zaiyi magana amma ya kasa cewa komai, sai daya hadiye wani abu mai daci a makogwaronsa sannan a karshe yace “I am a Muslim also” ta dauke kanta tace “sorry, my bad” cikin jin zafin maganar ta yace “me yasa kika yi tunanin ni ba musulmi ba ne ba?”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ta kalle shi tun daga kan brown wind tossed hair dinsa, his cigarette stained lips, katuwar head phone din dake kunnuwansa, shirt dinsa da take dauke da katoton hoton Lady Gaga, wandon sa da yake tsatstsage daga guiwa, zuwa takalminsa da yafi kama dana sojoji, sannan ta daga gira daya sama tace “na farko you don’t dress like a Muslim, na biyu nayi maka sallama baka amsa ba, na uku muslims don’t complain about their parent’s choice of name, Abubakar Sadiq suna ne mai dadi kuma mai daraja” he was speechless, tunda yake ba’a taba yaga shi irin yau ba, me wannan yarinyar take tunani? Wacece ita? Babu abinda yake so a lokacin irin ya hada wa kyakkyawar fuskanta jini da majina. Ya dunkule hannu amma sai jikinsa yayi betraying dinsa har ta juya ta barshi a tsaye, instead, sai yaji bakinsa yana furta “baki gaya min sunanki ba” ta juyo tace “why?” Ya maimaita “why? I just told you my name that’s why” tace “I didn’t ask you for it” daga haka bata kuma cewa komai ba sai ma kara sauri da tayi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ya dunkule hannunsa ya naushi iska, ya rankwashi kansa yana jin haushin kansa sai kuma ya shafa gurin daya rankwasa alamar yaji zafi, gaskiya ya fara sanyi da yawa, har shi mace zata yiwa haka? Who is she?

Daga bayanshi yaga wata yarinya tazo ta wuce shi da sauri tana kira “Diyam!! Wait for me” yaga ta tsaya ta jirata ta karaso sannan suka cigaba da tafiya tare. “Diyam” ya maimaita, how can someone name his child water? Me parents dinta suke tunani? sai kuma ya koma gefe ya samu guri ya zauna, ya dauko sigari ya kunna, ya gyara zaman headphone dinsa ya zuki tabarsa ya lumshe ido yana lissafa hanyoyin da zai rama abinda Diyam tayi masa.

      *****.             *****.         *****

Diyam taji kiran da akayi mata, ta juya suka hada ido da kawarta Judith, kawarta ce tun a Nigeria suka hadu lokacin suna shirye shiryen tahowa UK, a lokacin da suka yi registration ne Diyam ta fahimci cewa Judith tana neman gidan zama sai kawai ta jata suka zauna tare a nata gidan, tare da Murjanatu. Tayi mata murmushi lokacin da Judith ta karaso suka jera suka cigaba da tafiya a tare. Judith tace “if you don’t mind me asking, were you talking to that guy?” Diyam tace “yes I was, what about it?” Judith ta danyi dariya tace “it is just that you never talk to anybody” Diyam ma tayi dariya tace “believe me, it wasn’t such a good talk. Am sure that guy is never going to talk to me again” suka yi dariya baki daya, Diyam ta dafa goshin ta tace “God, am so boring, how do you guys manage living with me?” Judith tace “it is never easy” haka suka cigaba da tafiya suna hira akan halayen Diyam.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A kafa suka tafi estate ɗin da gidan su yake, suka je block E suka hau lift zuwa fifth floor inda apartment dinsu yake. Judith ta fito da key din hannunta ta bude kofa. Suna shiga a parlor duk suka zube a kasa saboda gajiya. Murjanatu ta fito daga kitchen da spatula a hannunta tana kallonsu, black beauty ce, mai dan karamin jiki, manyan idanuwa da cikar gashin gira. Kana ganinta zata yi maka kama da irin shagwababbun yaran nan wadanda suka taso cikin naira, tace “shi yasa naki zuwa yau. Haka kawai akan lecture daya bazan sha wannan wahalar ba” diyam ta kalleta tace “kinyi missing, alot” Murjanatu ta karkata kai gefe tace “at least ai nayi muku girki ko? So what you should be saying is ‘thank you'” Judith ta mike tayi pecking Murjanatu a cheek dinta tace “thank you”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Suna cikin cin abincin, wanda Diyam chakula kawai take kamar mai cin magani tana ta complain din how much she misses abincin gida. Tace “I can give anything, I mean anything, dan in samu tuwo in ci” Murjanatu ta tabe baki tace “niko ko missing tuwo banyi ba, sam dama ni ba sonshi nake yi ba” Wayar Diyam tayi kara ta kalleta kawai ta dauke kai. Judith ta dauka tana kallon sunan mai kiran har ta katse sannan ta ajiye tace “ban taba ganin marar zuciya irin mutumin nan ba, wulakancin da kike masa Diyam ya isa haka” Murjanatu ta daga hannu tace “hey, yayan nawa kike cewa marar zuciya?” Tana yin shiru wayar ta tana yin kara, ta langwabar da kai tace “Please Diyam, kinga ya kira a wayata. Please just for today” Diyam ta harare ta bata ce komai ba, Murjanatu ta daga wayar ta gaishe da wanda ya kira tana kallon Diyam tace “lfy lau take, yanzu muka dawo daga lecture wallahi duk mun gaji yaya. Eh bata zuwa da motar wai exercise ne zuwa school din. Eh shikenan for today. Gata nan tana cin abinci. Bata ci da yawa wallahi yaya, wai tuwo take so. Ah ah ni ban sani ba wallahi. Yaya ni Wallahi ban iya tuwo ba. Okay, sai anjima” ta ajiye wayar tana turo baki fuskarta kamar zata yi kuka tace “wai inyi miki tuwo yau da daddare ince with love from him” duk suka yi dariya, Diyam ta tashi tana rawa tana yiwa Murjanatu gwalo ita kuma ta dauki pillow ta bita da gudu suka shige corridorn da bedrooms dinsu suke.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button