NOVELSUncategorized

DIYAM 3

❤️ DIYAM ❤️
Episode Three

Bayan tafiyar su Diyam, ya jima zaune shi kadai, yana ta sakawa yana kwancewa yana kuma zukar hayaki zuwa hunhun sa.
Sai da ya ga kwalin ya kare sannan ya jefar da shi ya duba agogon hannunsa yayi tsaki ya mike. Cab ya tare zuwa hotel din da ya ke. Yana shiga dakin ya zauna akan gado yana kare wa dakin kallo kamar yau ya fara ganinsa, idonsa ya sauka akan hoton wata yar kyakkyawar budurwa akan study table dinsa tana murmushi. Ya lumshe idonsa ya bude. She have been the reason for everything daya ke ciki a yanzu, for all his pain and his agony. Ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta for the hundredth time amma yanzu ma kamar ko yaushe bata dauka ba. He wandered me yasa ba tayi blocking dinsa ba dan gwara ya kira bata shiga ba akan ya kira ba’a dauka ba, meaning ta gani kenan, meaning tasan all what he is going through but she just doesn’t care.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Fatima sunanta, Khausar suke kiranta, he had been in love with her for as long as he can remember, maybe tun da yasan menene love din but he failed to tell her. Daga baya kawai sai yaji labarin wai zata auri brother dinsa, that has been the beginning of his agony, wannan ne asalin dalilin fara shan sigarin sa. Yayi iyakacin kokarinsa tun a lokacin dan ganin cewa ya cire ta a ransa and he succeeded a little, but then sai auren baiyi da brother din nasa ba and his brother ended up marrying another. Wannan turn of events din ba karamin faranta masa rai yayi ba, he saw it as another chance na auren wadda yake so.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Shekara guda kenan da faruwar hakan. A cikin shekarar ne kuma yayi failing terribly in his course of study a Abuja, amma sai ya alakanta hakan da cewa dan baya son course din ne, yace yafi son yabi footprints din maternal grandmother dinsa wadda ta kasance lawyer, da kyar yayi iyakacin kokarinsa har ya samu aka barshi ya taho UK karatu duk da cewa iyayensa basu so hakan ba sunfi son ya zauna tare dasu amma saida ya taho tare da daurin gindin kakar tasa, yayi hakane saboda ita, saboda Khausar, for she now lives in UK tare da auntyn su. But sai me kuma? He realized bayan zuwansa cewa ai she is already dating his cousin kuma, wannan yasa ya daura damarar ganin ko sama da kasa zasu hadu sai ya raba wannan relationship din, wannan ya jawo rigima ba yar kadan ba tsakanin sa da cousin dinsa Ayan and he failed miserably. A karshe Khausar looked into his eyes and said “I will never marry you ko mazan duniya sun kare”, and that made him mad, so mad that when his aunty tries to resolve the issue he looked into her eyes and said “go to hell”.

Sati biyu kenan da faruwar hakan. Tun daga ranar ya hado kayansa ya dawo wannan hotel din da zama shi kadai. Kuma tun daga ranar babu wanda ya neme shi kaf family dinsu not even his Mami.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); But wannan duk ba shine babban problem dinsa ba. Problem dinsa shine satin sa daya da barin gidan auntyn sa parents dinsa sukayi blocking dinsa out of their family bank account. Tun tashinsa da wannan account din suke amfani gaba daya gidan, kowa yana da access da shi sai dai kawai a karshen wata kayi bayanin abinda kayi da kudin daka dauka, yanzu babu. Shi kuma ba aikin yi ba, dan haka blocking dinsa daga family account ya mayar dashi almost koboless. Bashi da komai, hatta kayan abinci bashi dasu kuma kudin siyan abincin nasa has almost run out, zuwa karshen satin nan yasan ko na abinci bashi dashi.

Yasan wannan duk hikimar Mami ce, they want to fish him out ya kawo kansa ya karbi laifinsa, shi kuma yana jin tsoron yadda hukuncin sa zai zama, ba zaiji da dadi a gurin daddyn sa ba. Kuma yasan he have lost Khausar for good. Yayi biyu babu. Abinda yake bukata a yanzu shine karfin gwuiwar facing family dinsa, accepting mistake dinsa da kuma repenting, but to do that yana bukatar courage, yana bukatar wani yayi masa magana at least ko fada ne ayi masa a gaya masa yayi ba dai dai ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Bai san mai yasa yarinyar dazu ta fado masa a rai ba, Diyam. Ya kwanta ya rufe ido yana tunano fuskarta, tabbas tana da courage. From her looks, yadda take ware kanta daga cikin mutane zuwa yadda turancinta bai gama nuna ba yasan cewa she is from a poor background, maybe irin yayan talakawan nan ne da gwamnati take dauka take basu scholarship suke tahowa kasashen waje suyi karatu. But she really does have courage, daga yadda tayi magana rannan a class da kuma yadda tayi facing dinsa straight in the eyes ta gaya masa maganganu. Har dare yarinyar tana cikin ransa, amma kuma ya kasa yanke mata hukunci a ransa.

Washegari kamar kullum Diyam ta riga kowa tashi. Tayi wanka tayi alwala tazo ta bude al’qurani tana bita har akayi assalatu sannan ta je dakin Murjanatu ta tashe ta tazo ta tayar da sallah. By seven har ta gama komai, ta dumama sauran tuwon jiya ta zauna tana ci Judith ta fito tayi joining dinta sannan Murjanatu ta fito itama, but sai taki cin tuwon ta hada tea da bread ta sha. Suna yi suna hirar abubuwan da suka shafi karatun su, Murjanatu tana ta mitar takura musu da Diyam take yi suke zuwa school a kafa bayan ga mota an ajiye musu musamman saboda zirga zirgar su.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Suna shiga makaranta Murjanatu tana haki ta kalli Diyam tace “you and yaya na deserve each other. Kafiya ce daku da naci akan abinda kuka sa kanku. At the end kuma ku wahalar da wanda yake tare daku. Ni dai daga yau na daina turturing kaina wallahi, motar zanke shigowa koda ni kadai ce” Diyam ta daga gira daya tace “ba sai ki shiga ba, in kin iya driving din” suka yi dariya tare da Judith, ita kuma Murjanatu ta tura baki tayi gaba tana kunkuni ta barsu tunda ba department dinsu daya ba, suna dan yin gaba kadan suka rabu da Judith itama sannan Diyam ta karasa department dinsu ita kadai.

Tun daga nesa ta gane shi. Yana tsaye kamar kullum da headphone a kunnensa da kuma sigari a hannunsa. Ta duba agogon hannun ta taga it is not 8:00 yet amma har ya fara zuke zuke, maybe ko breakfast baiyi ba. Ta dauke kai ganin cewa bai ganta ba dan kamar yayi zurfi cikin tunani.

Har suka yi nisa da lecture din tana ta saka ran ganin ya shigo amma shiru bai shigo ba, sai da aka fara concluding sannan ya shigo dan haka ko zama bai gama ba malamin ya fita, and she felt sorry for him. Suna nan wani malamin ya sake shiga ya gama ya fita daga nan kuma zasuyi one hour break sai su sake wata shikenan. Ta fita ta nemi coffee shop ta zauna aka kawo mata coffee da cake taci duk da dai ba yunwa take ji ba but she just need to eat something saboda suna da wata two hours lecture din, Madam Sally. Tana zaune ta hango wucewarsa yayi hanyar gate. She wonders ina zaije tunda suna da wata lecture din? Sai kuma ta daga kafada tana mamakin me yasa ta damu da business dinsa.

Har suka tashi a ranar bata kara ganin sa ba. Da daddare suna cin abinci ta bawa su Murjanatu labarin encounter dinta da guy din tace “I am just feeling sorry for him. He obviously is distracted, confused maybe” Murjanatu ta harare ta tace “ni dai babu ruwana. Daga tausayi kuma sai muji wata magana ta daban. Kinsan in yaya yaji wannan maganar zai iya harbo nuclear bomb ya tarwatsa Oxford gaba-daya” Diyam ta daga kafada tace “Allah yasa uranium zai harbo ba nuclear bomb ba. I will talk to whoever I want to talk to” Murjanatu tace “you are not going to give my brother a break are you?” Diyam ta mike tsaye tace “no i am not, har sai yayi abinda nace masa” Murjanatu tayi murmushi tace “maybe baki san shi ba kamar yadda kike tunani” Diyam ta  wuce daki da sauri tana jin zafi yana taso wa a zuciyarta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Da safe basu da lecture da wuri dan haka suka yi baccin su sosai. Sai after ten Diyam ta tashi ta fita parlor ta tarar Judith tana kitchen tana hada musu breakfast. Ta dawo dakin ta ta shiga wanka. Tana fitowa wayar ta tana ringing amma ko kallonta bata yi ba ta dauke kanta ta cigaba da shiryawa amma a zuciyarta tana mamakin yadda yake keeping track din komai nata, yasan sanda take da lectures yasan kuma sanda take free. Wayar tana katsewa taji text ya shigo, ta dauka takaranta, sakon barka da safiya ne mai hade da tsadaddun kalaman da sai da suka huda zuciyarta amma sai kawai ta tabe baki ta ajiye wayar. Ita dashi a ga wanda yafi taurin kai.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button