NOVELSUncategorized

DIYAM 22

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Two : Birthday Gift

Abinda na tarar a gidan mu dana koma banji dadinsa ba, harkoki kawai ake yi ana wadaka da abinci, wato shi wanda akayiwa mutuwa shi kadai ta
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); shafa ko? Shi kadai yasan me yake ji? Wato mutuwa ba zata zamo izna ga sauran mutane su nutsu su daina biyewa duniya ba? An bubbude koina har palon Baffa mutane ne a ciki, bedroom dinsa ne kawai a rufe.

Dakin mu na wuce da niyyar in kwanta inji da abinda yake damuna amma sai na tarar da yammata ne fal a dakin, suna ta dauke dauken hotuna da kallon videos a waya suna kyalkyatar dariya. Ko magana banyi musu ba na fito da shiga part din Ummah, babu kowa anan kofar palon ma a saye take dan haka na tura na shiga na mayar na rufe. Direct dakin Sadauki na tafi na bude na shiga. Dan karami ne dai dai size din dakin mu ni da Asma’u, katifa ce kawai a dakin sai wardrobe, standing fan, sai kuma tarkacen takardu a gefe. Sai hoto guda daya a jikin bango. Na tsaya a gaban hoton ina kallonsa kamar yau na fara ganinsa, Ummah ce da Baffa a zaune akan kujera, sai Sadauki a durkushe a gaban baffa sai ni kuma akan cinyar Ummah da shubeya a hannu na. 

Na tuna sanda aka dauki hoton da wata sallah ne lokacin Inna tana da cikin Asma’u, babu yadda Baffa baiyi ba ita ba akan tazo ayi hoton taki tace sai dai yaje mu dauka daga ita sai shi sai ni. Shi kuma yaki. Na zauna a gaban hoton ina jin kewarsu tana kara mamaye ni, ina jin kamar inyi rewinding din rayuwar mu ta dawo baya in cigaba da ganin su, in cigaba da ganin Sadauki a gidan mu. Inna tuna cewa Sadauki bai san anyi mutuwar nan ba sai inji zuciya ta duk ta narke, bansan yadda zai dauke ta ba, ina gudun kar wani abun ya same shi shima. In na tuna yanzu bashi da kowa a duniya sai inji kamar in tashi in koma asibitin in zauna a wurinsa. Hope dina daya shine na yaya ladi zata kaishi gurin mahaifinsa tunda nasan dole zata san waye shi, in ma bata sani ba shi wanda ya hada auren ai zai sani. Amma kuma in nayi wannan lissafin sai inji zuciya ta ta kara tsinkewa saboda tunanin rabuwa da Sadauki. Kuma what if shi uban baya bukatarsa? What if shine yakori Ummah da jariri yace baya so?
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Anan dakin bacci mai nauyi ya dauke ni saboda kwana ukun nan duk bana samun bacci mai nauyi. Na jima ina yin baccin sai naji magana kamar a tsakiyar kaina ance “Diyam? Uban me kike yi anan?” Na tashi zaune ina mitstsika ido amma na kasa bude idona saboda fitilar da aka haske ni da ita. Aunty Fatima tazo ta kama ni muka mike “tun dazu ake ta neman ki, babu inda ba muje ba duk hankali ya tashi mun dauka an sace ki ne” nace “kuyi hakuri, bansan bacci ya dauke ni ba, hayaniya ce ta yi yawa acan ni kuma ina so in zauna ni kadai” sai kuma sukaji tausayina, amma inna sai da tace “kuma ki rasa inda zaki je ki kwanta sai nan dakin? Ba gwara ki tafi makota ba?”.

Sai da aka sake kwana biyu sannan na kuma samun dama na tafi dubo Sadauki, wannan karon tare da Rumaisa muka tafi kuma sai da na saka tayi min alƙawarin ba zata gaya wa kowa ba. A zaune muka tarar dashi yaya ladi tana ta fama dashi akan yaci abinci. Tun a fuskarsa na gane yaji dadin zuwana sosai. Yace “kun taho da waya? Ina son in kira Ummah, ina so kuma inji ya jikin Baffa” na girgiza masa kai nace “bani da waya ai ka sani, kuma bansan zaka bukata ba shi yasa ban karbo wata na taho da ita ba” ya jingina kansa a jikin gado yana runtse idonsa yace “a gurin da muka yi accident aka dauke min waya ta, ita kuma wannan tsohuwar wai tata ta lalace” na jawo kujera na zauna ina karbar kwanon abincin daga hannun yaya ladi nace “duk suna lfy Sadauki, ummah cema tace inzo in duba mata kai. Kasan ba zata iya barin Baffa ba Musamman yanzu da bashi da lfy” ya gyada kai yana murmushi yace “ji nake yi kawai ina so in ganta” ina kallon Rumaisa ta tashi ta fice daga dakin. Na zuba masa tuwon alkama miyar danyar kubewar da yaya ladi tayo masa na zauna ina bashi a baki, ba musu yake karba idanuwansa a kaina ko kiftawa baya yi har sai da ya cinye wanda na zuba masa tas, yaya ladi tace “oh, tun safe nake fama da shi akan yaci abinci yaki ci, shifa yace inyi masa tuwon amma shima ya bar ni da abina, amma da yake ke kece gashi nan ai ya cinye tas” ya juya yana kallonta yace “baki iya tarairayar miji ba ne shi yasa” da alama so yake suyi wasa irin yadda suka saba amma sai ta kasa mayar masa, sai ta hau tattara kayan gurin ta fita dasu.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na saka tissue ina goge masa bakinsa sai ya rike hannun yana kallona cikin ido yace “kin rame, kinyi duhu, idonki sun kumbura” na kirkiro murmushi nace “ka manta daga makaranta na dawo, kuma exams muka gama bama samun isashshen bacci” ya saki hannuna yace “fada min gaskiya, ya jikin Baffa, is it bad? A ina ya karye?” Na kasa kallon idonsa nace “a hannu ne kuma da sauki” yace “hannu kuma? I thought kafa ce ma saboda shi yake driving” na dago ina kallonsa da mamaki dan nasan Baffa hardly drives in dai da Sadauki a motar. Nace “me ya faru?” Ya sunkuyar da kai yace “rami muka daka sai taya ta fashe, daga nan motar ta fara a dungure akan titi, sai data daki wata bishiya sannan ta tsaya” na gyada kaina ina rike hawaye na.

Muna komawa gida muka tarar da inna a tsakar gida tana alwalar magrib tace “daga ina kuke?” Rumaisa tace “makota muka shiga”. Shikenan bata kara ce mana komai ba.

Washegari bayan nayi sallah na kwanta akan kujera amma ba bacci nake yi ba, na rufe idona ne kawai saboda bana son kowa yayi min magana a lokacin. Ina ji akayi ta hidimar abinci sannan aka fito palo aka baje kowa yana ci ana ta hira, cikin hirar naji Inna tana bawa yan uwanta da suka zo daga Kollere labari:

“Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari’a tsakani na da zainabu sai a lahira za’a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum ‘sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza’ nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace “Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam’ to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira” naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wata ta tambayeta “to ina yaron yake yanzu?” Tace “yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba” sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can’t take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe.

Washegari akayi sadakar bakwai. Jama’a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita. 

A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba’a gaya min ba nasan ya sani. “Ina Ummah?” Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace “sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za’ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida” ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya “yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?” Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama. 

Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace “Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu’a kuma sai kuma a lahira in munje muma” 

Baice min komai ba bai kuma yi  magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya “in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki” ta harari waje “muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura”. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya  taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma’u da take makale dani tana taya ni kukan itama. 

Can naji Inna tana cewa “su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa” Mama tazo ta tashe mu ni da Asma’u “ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba” na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan. 

Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button