NOVELSUncategorized

DIYAM 21

❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episode Twenty One : The Two Corpses 2

Na dauke idona daga fuskarsa na mayar kan daya gadon da yake gaba na, sannan a hankali na taka na isa gaban gadon na saka hannu biyu na yaye sheet din da aka rufe mutumin.
Idona ya sauka akan Baffa, kamar Sadauki shima gashinsa a jike da jini amma fuskarsa tas da ita babu emotions kamar mai bacci, na jima ina kallon sa dan ina jin ban taba yi masa cikakken kallo irin na yau ba. Kofa aka bude daga bayana wata nurse ta shigo da sauri tace “what .. ?” Sai kuma tayi shiru, ta karbe sheet din daga hannuna ta mayar ta rufe shi sannan ta kama hannuna ta jani kamar wata robot ta fita dani. Gurin su Inna ta kaini, wadda har yanzu take jikin Mama tana ta kuka, hannun ta daya rike da Asma’u. Nurse din tace “tare kuke da wannan yarinyar?” Inna ta kalle ni, da alama sai yanzu ta lura da zuwa na asibitin, tayi sauri ta jawo ni tana gyada wa nurse din kai tace “yata ce, yata ce” cikin kuka. Sai kuma ta rungume ni tana kara sautin kukanta.

Mama tace “haba addah, ya zaki saka yara a gaba kiyi ta wannan kukan haka? Da wanne zasu ji. Dan Allah ki rage wannan kukan inba so kike kema ki yanke jiki ki fadi ba” ta jawo ni daga jikin Inna ta zaunar dani a kan benchi ta rike fuskata tace “kai kiyi kuka kinji Diyam? Kiyi ta karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun” na gyada mata kai ina kallonta. To ni kukan me zanyi ne bayan nasan mafarki nake yi? Yanzu zan farka amma bana so in farka din sai Baffa da Sadauki sun tashi. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wata nurse naga ta fito daga wani daki da sauri ta kira doctor sun koma tare, sai na samu kaina da mikewa na bisu amma ban shiga ba sai na tsaya a bakin kofar ina kallon ciki ta glass din jikin kofar. Ummah na hango akan gado, nurses biyu da likita daya a kanta suna ta kokarin bata taimako. Sai kuma ta fara convulsing, idanunta suka kakkafe doctor din yana ta kokarin reviving dinta amma sai jikinta ya saki. Ina kallo suka yi ta aaunata sannan doctor din ya kalli nurse din data dauko takarda da biro yace “time od death: 4:35” sannan ya bude kofa ya wuce ni jikinsa duk a sanyaye.

 “Death” na maimaita. “Ummah, Baffa, Sadauki” na fada a hankali ina jin kaina yana juyawa. Na bi bayansa a hankali naga ya tafi gurin su Inna yayi musu wata magana, sai naga Inna ta saki hannun Asma’u da sauri ta rufe bakinta ta durkushe a gurin, Mama tana ta salati ita ma su Aunty Fatima suna tayata. Da sauri Inna tazo ta wuce ni ta shiga dakin da Ummah take sai kuma ta sake fitowa da sauri ta hada kanta da bakin kofar tana kuka kamar ranta zai fita. Tunda nake a lokacin ban taba ganin Inna cikin tashin hankali irin na yau ba.

Muryar yaya ladi na jiyo ta shigo gurin. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. La haula wala quwata illah billah. Wayyo Usumanu wayyo Aliyu, yanzu aka kira ni akace sunyi hatsari an kawo su nan. Ya jikin nasu? Ya kuke ta kuka haka?” Kowa ya kalleta sai dai ya kara kukansa, ta rike kafada ta “Halima? Ina marasa lafiyan suke? Ina Zainabu kuma? Ya banganta anan ba?”

Nurses ne su biyu suka zo suka kamata suka jata gefe, duk suma a diririce suke suna yi mata magana, bana jin me suke cewa amma can naji ta saka wani kuka mai ban tausayi sannan ta wuce mu da sauri ta shiga dakin da Ummah take. Alhaji Babba ne da kawu Isa suka shigo gurin, Alhaji Babba yana fada 

“menene hakan duk kun cika asibiti da koke koke? Kukan zai dawo dasu ne? Kun kuma san babu kyau yiwa mamaci kuka ko? Fatima ki riko yaran ke kuma Hafsa ki kamo Amina mu zamu taho da gawawwakin ayi musu wanka ayi musu suttura tun kafin magrib tayi”. 

Wannan maganar tasa ita ta dawo dani cikin hayyacina, lokaci daya naji reality din mutuwar ya doke ni. Na juya da sauri ina kallon kofar dakunan da gawawwakin suke. “Baffa!!” Na fada da iyakacin karfina “Sadauki!! Ummah” Aunty Fatima tayi saurin rufe min baki na da hannunta tace “kul Diyam, ba’a yiwa mamaci ihu”. Sai na mayar da kaina jikinta na kwanta na rufe ido ba tare da na sake cewa komai ba. Nasan dai mun shiga mota sannan mun fita, sai kuma naji mun shiga gida mun shiga daki an zaunar dani akan kujera. Sannan ne na bude ido ana ganni a palon Inna, Asma’u tana zaune kusa dani tasha kuka ta koshi, ina jiyo tashin sautin kukan Ummah sama sama amma ban juya ba ballantana in kalli inda take. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Muryar Alhaji Babba naji ya shigo gidan, ya daga labilen palon Inna yace “a dauke carpet din palonsa sai muyi masa wanka a can” na runtse idona ina so hawaye ya fito min amma babu. Muna nan zaune sai muka ji hayaniya kuma, muryar Alhaji Babba “ku fita da ita daga gidan nan, ai tun sanda ya aure ta mun gaya masa babu mu babu ita, dan haka yanzu ma babu mu babu ita” sai muryar yaya ladi tana kuka. Ji nayi kamar in tashi in shake shi, how dare he said that a ranar da Baffa ya bar duniya? A ranar da Ummah ta bar duniya?” Rigima sosai har makota suka fara taruwa, sai ga dattijon mutumin da har yau yaya ladi take gidan sa yazo yace “a gidan aurenta za’ayi mata suttura kamar kowacce matar aure, kai kuma baka isa ka hana ba in kuma zaka iya to ka dauko yan sanda” ganin mutane suna ta kallonsa accusingly ya saka Alhaji Babba ya ja baya ya bari aka shigo da gawar Ummah. Na tambayi kaina to ina Sadauki kuma? 

Tare akayi musu suttura, shi a palonsa ita a nata, sannan aka zo aka fita dasu ta gabanmu a tare. Na bi su a baya nayi musu rakiya har bakin gate sannan na tsaya ina kallo aja jera gawawwakin su akayi musu sallah a tare aka dauke su zuwa gidan su na karshe.

Na koma gida ina tafi ina hada hanya. A tsakar gida na durkusa a cure a guri daya ina kara tambayar kaina ina Sadauki? Ji nake nima inama dai mala’ikan mutuwar zai zo ya hada dani. Mama ce tafito ta ganni a gurin, sai ta dauko tabarma ta shimfida mana muka zauna ta jani zuwa cinyarta na kwanta. Anan mukayi sallar magrib, sai ga yaya ladi ta fito tazo inda nake ta shafa kaina tace “sannu Halima, Allah yaji kansu yayi musu rahama, shi kuma Aliyu Allah ya bashi lafiya” na dago kai da sauri na ina kallonta sai naji tace wa Mama “zan koma asibiti inga halin da yake ciki” Mama tace “to Allah ya jishe mu alkhairi” nace da Mama “waye a abibitin?” Tace “Sadauki mana” naji wani abu mai nauyi daya tokare tun daga zuciyata zuwa makogwarona ya janye, numfashi na ya fara fita da sauri nace “Sadauki? Ba tare suka mutu ba? Na dauka ko an kai gawarsa wani gurin” ta rike hannuna tace “Sadauki bai mutu ba ya samu buguwa ne a kansa shi yasa doctors sukayi sedating dinsa. Baffanku kuma tun kafin a kawo su asibiti ya cika, Ummah kuma tashin hankali ne ya saka ta yanke jiki ta fadi, jininta yayi mugun hawan da cikin yan mintina ta mutu” naji wani abu yana sauka daga kai na zuwa kafafuwana. Sadauki is alive. Then there is hope for me.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A daren ranar banyi bacci ba, muna kwance ina rungume da Asma’u da take ta jera ajjiyar zuciya saboda kukan da tasha, sai da naga ta samu bacci mai nauyi sannan na zame jikina na fita palo, Inna na gani zaune akan sallaya ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka a hankali, sai na wuce ta na shiga toilet nayo alwala nafito nima na tayar da Sallah, yau shine daren Baffa da Ummah na farko a kabarinsu kuma nasan suna bukatar adduoin mu sosai. Har na idar da sallolina Inna tana kuka, sai na kwanta akan sallayar na dora kaina akan cinyoyinta sannan nima na samu kuka yazo min. 

Washegari yan Kollere suka zo, gida ya cika taf ana ta karbar yan gaisuwa amma babu wanda naji ya kuma maganar halin da Sadauki yake ciki, yaya ladi ma kuma ban kuma ganinta ba duk kuwa da cewa jama’ar Ummah suna ta zuwa gaisuwa suma. Inna dai kam tayi kuka kamar idonta zai fita kowa yashigo gidan sai ya tausaya “uwargidan sace kuma uwar yayansa”. Sai dare na ajiye tsorona na tambayi Inna “Inna ya jikin Sadauki kuwa?” Ta kalle ni ta dauke kai, “ban sani ba” ta fada tare da cigaba da jan carbin ta. 

Ranar da akayi sadakar uku ranar munga mutane, dan ko ranar mutuwar gidan baiyi wannan cikar ba, ranar yaya ladi tazo akayi adduoi da ita, sai da aka gama ta tashi zata tafi na bita a baya nace “yaya ladi ya jikin Sadauki?” Ta juyo ta kalleni tace “da sauki Halima, jikinsa da sauki” sai ta juya tayi tafiyarta. Alhaji Babba ya shigo bayan an gaishe shi yace “Amina zamu saka a gyara muku guri a can gidana, idan anyi bakwai sai ku koma can ku zauna ke da yara saboda nan din ba zaku ji dadin zama ba ku kadai. Allah ya ji kansa” akace ameen sannan akayi masa godiya ya tashi ya tafi.
Zuwa yamma I have taken all I can, ji nake nima kamar nawa jinin zai hau irin na ummah nima in mutu, an gama adduoin kuma an mayar da gidan kamar gidan biki sai ciye ciye ake da hira da dariya. Na shiga dakin inna na bude jakar ta na dauki kudi na saka hijab dina na fixe ba tare da kowa ya lura ba. Adaidai na hau direct na tafi asibitin malam, naje har emergency room nayi sa’a kuma visiting hours ne dan haka na tambayi nurses Aliyu Usman Kollere nake nema sai suka ce inje aminity room 3. Da sauri na na tafi, zuciya ta tana jin kamar zata kara sauri tayi gaba ta riga ni shiga dakin.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A kwance na same shi da drip a hannunsa daga alamar har yanzu allurar baccin akeyi masa, fuskarsa da dan fada kuma tayi haske, kansa a nade da bandage. Babu kowa a dakin sai shi kadai. Na karasa ciki inajin wani irin tausayinsa yana saukar min, na zauna a gefen gadon na kamo hannunsa nayi intertwining fingers din mu. Ya dan bata rai sai kuma yayi blinking ya bude jajayen idonsa yana kallona, ya kakalo murmushi mai nuna yana jin ciwon yinsa yace “you are here” na gyada kai nace “am here” yace “waye ya dauko ki daga school?” nace “Abban su Rumaisa” yace “good” mukayi shiru kuma can sai yace “ya jikin Baffa?” Gabana naji ya fadi na zuba masa ido, wato bai ma san abinda yake faruwa ba? Ya sake cewa “yaya ladi tace min ya samu karaya ne shine aka kai shi asibitin kashi. Shine kuma duk kuka tafi gurinsa ko?” Ya sake kirkiro murmushi “dama nasan Ummah tafi son Baffa akaina shine ta tafi jinyarsa ta barni, in kin koma ki gaya mata nayi fushi, nima tawa matar tazo ta ganni” na cije lebena ina danne kukan da yake so ya kwace min, sai yace “don’t cry please, everything will be alright” 

Na gyada kaina nace “yes Sadauki, everything will be alright. Ka koma kayi baccinka” ya lumshe ido yana kara rike fingers dina a cikin nasa. Mun jima a haka ina kallon fuskarsa ina jin wani irin yanayi yana kara shiga ta a kansa, nayi kokarin zare hannuna daga nasa sai ya kara rikewa a hankali cikin bacci yace “don’t leave me please, stay with me please” sai ya dora hannayenmu akan kirjinsa sannan ya dora daya hannun ya sake rike wa. 

A haka yaya ladi ta shigo ta same mu, ta tsaya tana kallon mu sannan ta girgiza kanta tace “an mutu an bar muku gadon wahala”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button