NOVELSUncategorized

DIYAM 26

9

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty Six : Forever and Ever

Alherin Allah ya kai gun masoya na a duk inda kuke. Ina gani, ina karantawa kuma ina godiya da duk comments dinku, it kept me going.


This page is dedicated to duk wadda za’ayiwa ko kuma aka taba yiwa auren dole.
This page is dedicated to duk saurayin da aka raba shi da budurwarsa ba tare da wani cikakken dalili ba.
This page is dedicated to duk iyayen da suke da ra’ayin yiwa yayansu auren dole. Ina fatan wannan labarin zai saka ku chanza ra’ayin ku.
Ku fahimce ni sosai, auren dole nake nufi bawai auren haɗi ba, akwai banbanci tsakanin arranged marriage da kuma forced marriage.
Mama ta shigo ta karbi wayar daga hannuna tayi cutting kiran. Bata ce min komai ba ta saka wayar a jakarta ta harhada sauran kayanta ta rataya jakarta. Inna tace “ba dai tafiya zaki yi ba” Mama tace “tafiya zanyi, ni ba zan iya kallon wannan kayan takaicin ba, Allah ya bamu alkhairi”. Ta juya da sauri ta bar dakin. Inna tayi ajjiyar zuciya dan ta fahimci Mama fushi tayi akan magana ta, tazo ta zauna a bakin gado daga gefena tace “shi kika kira ko? Diyam taurin kanki ne yake jawo miki koma menene akeyi miki. Ke ba kya jin magana ta, da ace tun farko da na hanaki kulashi kin daina ai da bata kai ga haka ba” tayi shiru tana sauraron kuka na, sannan tayi tsaki tace “nima zuciyata ba son hadin nan naki da saghir tace ba kawai dai dan babu yadda zanyi ne, ba wai saghir din ne bana so ba a’a auren ki ne yanzu bana so, duk da dai kamar yadda Alhaji ya fada ana yiwa wadanda basu kaiki bana aure kuma su zauna amma nasan da babanki yana nan da bazai miki aure yanzu ba. To ni wannan shine damuwata. Amma in kika duba ta wani bangaren fa zaki ga gata akayi miki, Saghir yafi wancan yaron da kike ta naci komai, yafishi kudi ya fishi kyau ya fishi asali ya fishi shekaru ya fishi hankali ya fishi wayewa sannan uwa uba gashi dan uwanki. To me kike nema kuma bayan duk wannan” a hankali cikin dasashshiyar murya nace mata “bana son shi Inna. Bana son Saghir Sadauki nake so, bana son aure yanzu karatu nake so. Inna ki taimaka min kar kuyi min auren dole” sai na dora kaina akan cinyarta na cigaba da rera kuka, ta dora hannunta a kaina tana shafawa, a hankali tace “gata akeyi miki Diyam, yanzu ba zaki gane ba sai nan gaba”.

Kafin azahar zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, ko palo ban kuma lekawa ba ina kwance daki a kudundune ina karkarwa. Ina jin yan gidan suna ta zuwa dubani kuma nasan da yawa daga cikinsu tsegumi ne yake kawo su. Ina jin Hajiya Yalwati ta shigo itama suna ta magana da Inna “amma dai Amina in kika yarda da wannan hadin kun zalinci yarinyar nan wallahi. Saghir in ana so ya shiryu ai gagarumar mace wadda taga jiya taga yau za’a samo a hada shi da ita ba yar mitsitsiyar Diyam din nan ba, ya zata yi dashi?” Inna tace “to wai Yalwati ya kuke so inyi ne da raina ne? Nima fa ba son abin nan nake yi ba amma ya zanyi? Yanzu zan iya cewa da Alhaji Babba ba zai aurawa Diyam Saghir ba? Duk duniya tana da wadanda suka fisu ne ko kuma ni duk duniya ina da wadanda suka fisu ne? Hakuri kawai zatayi nima kuma inyi hakurin sai mu hadu muyi tayi musu addu’a. Duk wannan koke koken nata daga anyi auren fa shikenan. Yara nawa ne akayi musu auren irin haka kuma gasu nan har sun hayayyafa sunyi zaman su” Hajiya Yalwati tace “to ba dole suyi zamansu ba tunda sun hayayyafa? Amma kije ki tambayesu kiji idan har yau abin baya musu ciwo a ransu. Kije ki tambayesu kiji irin wahalar da suka sha kafin su hakura din. To wannan fa wai ina yi miki magana ne akan in mace bata son miji aka aura mata shi to ina ga in shi din ma baya sonta? Kar ki manta Saghir fa bashi yace yana son Diyam ba. Kinsan kuwa ciwon auren wanda baya sonka? Kinsan kuwa irin bakin cikin da zai ta kunsa maka?” 

Inna ta dauke kanta gefe tana jin kamar bakar magana ce Hajiya Yalwati take gaya mata. Ita kuwa ita tasan bakin cikin auren wanda baya sonka don har yau tana iya tuno farkon aurenta da Baffa ko kallo bata ishe shi ba, sai gabanta ya fadi data tuno Saghir, idan har Baffa daya tashi ya kuma yi karatu a kauye yayi mata wulakanci saboda baya sonta to ina kuma ga Saghir din da ya gama bude idonsa a kasashen turawa?

Da yamma Aunty Fatima autar su Baffa tazo, ita ta tashe ni zaune tana taba jikina tace “Amina anya kuwa wannan yarinyar ba za’a kaita asibiti ba, jikin ta yayi zafi da yawa fa?” Hmmm shine kawai abinda inna tace tana jan charbi, Aunty Fatima ta bani magani na sha na koma na kwanta tana cewa “wallahi baki ji irin dadin da naji ba dazu da Alhaji Babba ya kira ni take gaya min wannan labarin, kai amma Allah ya sanya alkhairi shi kenan munyi abinmu tuwo na maina. Dama tunda Hamma Manu ya rasu yaran nan Diyam da Asma’u suke raina ina ta tunanin su kinga yanzu shikenan, in akayi auren dai ta dauki kanwarta suje can suyi zamansu kema kin huta, duk inda zai tafi yawon nasa ba sai ya saka matarsa a gaba su tafi tare ba? Itama ma a hakan zata waye din ai” a raina nace kaji wata kuma, ita wayewa ce damuwarta.

Washegari da safe jikina ya danyi sauki sai wani matsanancin ciwon kai da nake ji. Inna ta saka na tashi da kyar ina shan kunun gyadar da Hajiya Babba ta aiko min dashi wai taji ance naki cin abinci. Ina cikin sha aka budo kofar dakin kamar za’a balla ta, duk muka tsorata muka daga kai sai idona ya sauka akan Hamma Saghir da yake haki kamar wanda yayi tseren gudu, Inna tana yake tace “a’a Saghir saukar yaushe?” Ya dauke idonshi daga kanta ba tare daya amsa mata ba ya kalle ni cikin ido yace “dan ubanki, tun wuri kije ki gaya musu cewa ba kya sona tun kafin a makala min ke ki zokina nadama” ban dauke idona daga kansa ba har ya juya ya fice ya bar mana kofa a bude, na sauke kaina kasa na ajiye kunun hannuna, ina jin Inna ta tashi da sauri ta fita tana salati. A hankali naji wata irin tsana, tsanar da ban taba tunanin it is possible ba tana shiga zuciyata a game da Saghir, abinda ya fada bashi yafi bata min raiba akan ambaton ubana da yayi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na jawo pillow na kwanta sama sama ina jiyo hayaniya a palo, naji Inna tana tsara musu abinda Saghir yace, muryarta har kakkaryewa takeyi kamar zata yi kuka, sai kuma naji Alhaji Babba yana magana shima amma bana fahimtar me yake cewa sai can naji yace “kai ka haife mu ko mu muka haife ka? To sai an aura maka ita din in yaso in an kaita gidan naka ka kasheta kakawo mana gawarta”.

Na runtse idona na jawo wani pillown na dora a kaina na toshe kunnuwana.

Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace “to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki” Inna ta fara girgiza kai “na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa” Mama ta fara daukan zafi “Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?” Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.

Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba. 

Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace “sun zo, bara inje” amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa “ba za’a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda” Alhaji Bukar yace “shikenan dai? Shikenan maganar ‘yan sanda dai?” Alhaji Babba yace “ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan” Alhaji Bukar yace “ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai” Alhaji Babba yace “anji din, aure dai ba za’a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani” Alhaji Bukar yace “tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba”. Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma? 

Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace “Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta” Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa “in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan” ya fada yana nuna Mama, “ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir”.

Alhaji Babba ya mike “kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za’a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na fito palo sai naga Inna da amaryar Alhaji Babba a can gefe suna magana kasa kasa amma basu ganni ba, sai na wuce su na bude kofar palon na fita waje ina karewa compound din kallo, haka kawai naji zuciyata tana gaya min in tsaya anan wajen. Ban jima ba kuwa sai na hango su sun fito daga part din Alhaji Babba su hudu, manyan maza guda biyu da Mama sai kuma mutumin da ko cikin duhu na hango shi zan gane shi. Sadauki. Su biyun sauri suke yi shi kuma a hankali yake tafiya yana ta waige waige, sai kawai na sati handle din kofar na fita da gudu na tafi inda yake, tun daga nesa ya hango ni sai ya juyo ya bude min hannayensa ni kuma na wuce direct zuwa kirjinsa ya mayar da hannayen ya rufe. Na fashe da kuka ina kankame shi. 

A hankali yace “shshshsh, ya isa haka kukan, stop crying please. Wai litre hawaye nawa zaki zubar ne a cikin wata daya?” Sama sama naki hayaniya a compound din amma sai nake ji (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); kamar wani background noice ne akan maganar da Sadauki yake gaya min. “Be strong Diyam, you are stronger than this. Ki zama jaruma ki bude hannayenki ki karbi duk wata kaddara da Allah zai dora miki ki dauke ta a matsayin jarabawa, ki dauka cewa Allah yana jaraba ki ne dan yaga how strong are you for the blessings He plans a head for you. Ki sani cewa Allah yana tare dake a ko da yaushe, kuma ki saka a ranki cewa ni Sadauki zan kasance tare da ke a koda yaushe, this is my promise to you, I will be with you forever and ever, I will love you forever and ever. Always ki saka a ranki cewa an angle is watching over you. Always. No matter what happens and no matter how long”

Hayaniya ake yi sosai yayinda ni kuma nayi luf a kirjinsa ina jin kamar anan aka halicceni, ina jin muryar Inna “ba zaka shika ta ba? Maye” Alhaji Babba “kuyi ta dukansa har sai ya sakar mana ‘yarmu” dan uwan baban Sadauki “kar wanda ya taba shi, wallahi duk wanda ya taba shi sai yayi nadama”. 

Lokaci daya kuma sai Sadauki ya sake ni, ya rike fuskata yana kallona idonsa cike da wani yanayin da ban taba gani ba and then without another word ya kama hanyar waje da sauri, ina jin Alhaji Babba yana bawa yaran gidan umarnin su dake shi amma sai naga kawai kaucewa suke suna bashi guri har ya fita. Ni nasan a wannan yanayin da yake ciki da wani ya taba shi da tabbas in bai kaishi lahira ba to kuwa zai kaishi asibiti. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Yana fita daga gidan naji wani nauyi a zuciyata, wani duhu ya mamaye idanuwana, sai kuma kafafuwana suka lankwashe na zube a gurin unconscious.

Hope ba kuyi kuka sosai ba. Lol.
Love you all.
Chears

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button