NOVELSUncategorized

DIYAM 4

❤️ DIYAM ❤️

Episode Four

Tana saka kaya Murjanatu ta shigo dakin, daga ganin fuskarta Diyam tasan akwai
problem, ta ajiye skirt din hannunta tana bawa Murjanatu data zauna a kan gado dukkan attention dinta. Ta daga gira daya sama tace “me yace kuma?” Murjanatu tace “he asked me about Judith” Diyam ta hade rai tace “what about her” Murjanatu tace “he asked wai bata kawo mana maza gida? Na gaya masa bata kawo wa but he didn’t sound convinced.” Ta sunkuyar da kanta kasa tace “am afraid he is going to send her away” Diyam ta dafe kanta tana zagaye dakin da bacin rai a fuskarta sannan tace “tell him nace Judith is my friend, if he wants to get to her he will have to go through me. Ni na kawo ta gidan nan, in yana son ya kore ta sai ya fara kora ta tukunna” Murjanatu ta saka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tace “ba dani ba, bani Murjanatu ba. Uwata ta daina haihuwa ballantana ta sake haifo ni” Judith ta bude dakin ta leko kanta tace “hey girls, food is ready” sai kuma ta tsaya tana kallon yadda suke kokarin kakaro murmushi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A bayan lecture hall dinsu ta hango Sadiq. Shi kadai kamar kullum, da sigari a hannunsa kamar kullum, tayi saurin dauke kanta ganin yana kokarin juyowa. Amma sai ta tsaya a kofar hall din bata shiga ba tana so taga yau zai shiga ko yauma zamansa zaiyi a waje. Sai da aka kusan fara lecture din sannan ya taho, a gabanta a jefar da sigarin hannunsa ya saka kafa a murje ta, zai wuce Diyam tace ” you know smokers tend to die young ko?” Ya kalleta for some seconds, ya busa mata hayakin bakinsa yace cikin husky voice “says who? I can’t believe malama kamar ki ta yarda da wannan saying din. Kin manta kaddara? Ina islamiyyar taki ta tafi?” Ta sa hannu ta kade hayakin daya huro mata tace “maybe ni da kai munyi understanding kaddara differently. Tell me why do we pray? Why do we struggle? Me yasa muke neman duniya kuma muke neman lahira in dai har an riga an rubuta komai, me yasa ba zamu kwanciyar mu ba mu jira abinda aka rubuta mana yazo ya same mu. Yes kaddara rubuyacciya ce, major abubuwan da zasu faru a rayuwar mu a rubuce suke but what is in between depend on choices din da muke making. Wannan shine fahimtata. Yes, kamar yadda ka fada shekarun da aka rubuta maka ba zasu chanza ba amma how you are going to spend them depend on you, ko dai kayi spending dinsu healthy and happy in ka daina shan sigari ko kuma kayi spending dinsu with lung cancer in ka cigaba da smoking” ya kalle ta daga sama har kasa yace “go to hell, both you and your preaching” ya shige class din ya barta a tsaye. Taji zafin maganar sa amma sai ta hadiye ta bishi a baya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Suna shiga class din wani guy ya kalli Sadiq yace “the Nigerian guy. Why do you skip madam Sally’s class yesterday, don’t you want to depend your country anymore?” Sadiq yayi banza dashi ya shige ya samu guri ya zauna. Sannan yan ajin suka juyo gabaki daya suka zubawa Diyam ido, ta yi gyaran murya tace cikin harshen turanci “abinda na fada rannan gaskiya ne, gaskiya ne based on sani na. Shima kuma musa min din da yayi gaskiya ne based on sanin sa. We may have come from the same country but we live in different worlds. Muna zama cikin different mutane, muna kallon rayuwa from different perspectives. My being right doesn’t makes him wrong. You as potential lawyers should know that” duk yan ajin suka kada mata kai cike da gamsuwa sannan ta wuce ta shige seat din karshe ta zauna.

Madam na shigowa ta fara tambayar Diyam “will you like to continue with that day’s argument?” Diyam ta girgiza kai tace “no ma’am, it’s okay” ta juya gurin Sadiq tace “what about you, are you satisfied as well?” ya gyada kai yace “am okay ma’am. We now understand each other” sai ya juya a hankali ya kalli Diyam, itama ta dago kai suka hada ido and she smiled at him, a take ya fahimci cewa she have the brightest smile he have ever seen.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Bayan sun gama dukkan lectures dinsu, ta fito tana tsaye tana jiran Murjanatu sai gashi ya taho, ya tsaya dan nesa da ita kadan yace “waiting for a friend?” Ta daga murya tace “yeah” sai kuma taga ya zo zai wuce ta, tace “my name is Haleema. Haleema Usman Kollere. But people call me Diyam” ya gyada kai yace “I am Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq. Most people call me Bassam. You can call me that as well”.

Tayi murmushin ta mai kyau tace “nice to meet you Bassam” ya danyi dariya yana jujjuya kai yace “You have a beautiful smile, very beautiful. Ban san me yasa ba kya yawan yinsa ba. Ta daga gira daya sama tace “if it is beautiful than it is precious kenan. Abu mai tsada kuma kasan ba’a ko ina ake ajjiye shi ba” ya sake dariya, his eyes twinkling, amma bai ce komai ba, tace “and you. Ban dauka ka iya dariya ba” ya gyara fuskarsa yace “believe me, I do laugh alot. Yanzu ne dai I am in kind of not laughing situation. But na miki alkawari in na fita daga ciki we will laugh more” daga haka ya juya da sauri ya bar gurin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Yana tafiya Murjanatu tana karasowa. Tana kallon bayansa tace “who is that guy? Amma ya hadu fa” Diyam tayi murmushi bata ce komai ba, Murjanatu ta sake cewa “ko shine rannan kuke maganar sa da Judith?” Suka jera suna tafiya da Diyam tace “yeah shine” Murjanatu ta bata rai tace “then it is official, gaskiya ina taya yayana kishi. Lallai ma Diyam din nan” ta turo baki, Diyam tace “oh ashe baku hadu ba daga ke har yayan naki tunda insecurity yana damunku. Ashe kujerar taku bata kafu ba, ai hausawa sunce fargaba asarar namiji” Murjanatu ta harari bayan Bassam da har yanzu suna iya hango shi tace “ohh dama wancan namiji ne? Ai na dauka macece ta aske kanta ta saka wando. Ai wannan yana ganin yayana zai narke a gurin dan tsoro. Wannan daga ganin sa rainon madara da cerelac ne, yayana kuwa tuwon biski yaci da kunu dan haka ba sa’an sa bane wallahi” Diyam da take ta dariya tace “naga alama kam. Tuwon biskin ne yasa kansa yayi tauri da yawa” ta fada tana lakucewa Murjanatu hanci, Murjanatu tace “ouch, sai kin nane min hancin kinsa na rasa mashinshini?” suka yi dariya baki daya, sannan Murjanatu ta fara rokon Diyam akan ta fita dasu yawo yau da yamma “Please, Please Diyam, this routine is killing me slowly, ai ance taba kida taba karatu ko?” Diyam tace “sai jibi weekend sai muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu a gida”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Washegari Friday, Diyam tana zaune a seat dinta tana rubutu taji ance “hi Diyam” ta dago tana kallonsa bata ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa yace “Assalamu alaikum” tace “ameen wa alaikas salam Bassam” ya kalli seat din kusa da ita yace “can I?” Ta gyada kai ba tare data dago ba. Ya zauna ya fito da book dinsa pretending to be reading amma ita tasan ba karatun yake ba. Can ya ajiye littafin yayi tagumi yana kallonta yace “can I ask you something?” Ba tare da ta kalleshi ba tace “sure” yana taping hannunsa akan desk yace “me yasa ake ce miki Diyam? It means water right? Me yasa ake ce miki water?” Ta daina rubutun ta na kallonsa tace “maybe I am as important as water is to some people” yayi dariya yace “your boyfriend maybe” tayi murmushi kawai. A lokacin lecturer din su ya shigo, ya gyara zamansa yace “boring, boring, boring” ta sake murmushi kawai tana wandering me yake yi a makarantar in bashi da interest a karatun.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button