NOVELSUncategorized

DIYAM 41

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty One: A Stranger in the Dark

Ina jinsu suka fita daga gidan, and some parts of me went with them. 


A juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na koma sama nayi alwala na gabatar da sallar isha sannan na kai kuka na gurin ubangiji na. Bayan na gama nayi shirin bacci na zauna akan gado ina jujjuya waya ta a hannuna, I wish zan iya sanin halin da Sadauki yake ciki, I can’t even begin to imagine in dai har son da yake yi min ya kai wanda nake ji a raina a game dashi to kuma tabbas da nice zuciyata bugawa zata yi in fadi in mutu. It hurts so much to meet him bayan shekaru da yawa and not be able to talk to him, to ina ga shi kuma da yake kallona a matsayin matar wani?

Ina nan zaune naji shigowar Saghir, ya jima a kasa sannan ya hawo sama, nayi tsammanin dakinsa zai wuce kamar kullum amma sai naji ya turo kofar dakina ya shigo da tray a hannunsa ya ajiye akan side table ya zauna a kusa dani yana janyo table din gaban mu. “Sarkin yan tuwo gashi nan na debo miki, ko ba zaki ci ba?” Na zuba a plate ina cewa “Nagode” sai naga ya dauko chokali shima nace “au zakaci ne? Bayan baka cin tuwo?” Yace “albarka ta zan saka miki” murmushi kawai nayi zuciyata tana ayyana min abinda yake ransa. Sai da muka gama ci na kwashe kayan na mayar kasa na taho da ruwa da zuba masa a cup na mika masa ni kuma na zauna ina sha a robar ruwan. Sai dana gama na juya naga ya tsatstsare ni da ido kuma nasan irin wannan kallon but not today, I just can’t.

Sai na mike zan bar gurin yasa hannu da yawo dani kan gadon, ya jawo ni jikinsa yana mammatsa min kafadu na amma sai nayi saurin ture hannunsa dan ji nake kamar wanda yake doramin garwashin wuta a jiki, kafin in matsa ya saka hannunsa biyu ya juyo dani ina facing dinsa ya jawo fuskata dai dai tasa yana kokarin hada bakin mu, nayi saurin juyar da kaina nace “Please stop, bana so” amma yaki hakura, na fara ture shi kuma yana jawo ni kamar dai yadda muka saba yi duk sanda yazo da bukatar sa, ganin yafi karfina yasa na fara kuka shabe shabe da hawaye ina rokonsa akan ya kyaleni amma yaki, can kuma sai ya sake ni da karfi ya hankada ni baya ya mike tsaye yana kallona da idonsa da fuskarsa da duk suka yi ja saboda bacin rai yace “nagaji, nagaji, nagaji Diyam nagaji. Yaushe ne wai zaki daina guduna? Yaushe ne zamu mori auren mu ni da ke? Tunda akayi auren nan shekara bakwai Diyam in na zauna zan iya lissafa miki adadin lokutan da kika bari na kusance ki suma kuma babu wanda kika kawo kanki kuma babu wanda kika karbe ni cikin son ranki. Ni fa mutum ne, inada jini da tsoka a jikina ina bukatar kulawar matata amma ke na fahimci da dutse akayi taki halittar. Kullum ina bawa kaina hakuri ina ganin kamar zaki dawo hayyacinki amma kin ki, ni Saghir ni da mata suke rubibi na a waje har kawo min kansu suke yi amma ni ne matata take guduna. Na gaji wallahi. Hakuri na ya kai bango” na sauko daga gadon ina goge hawaye na nace “then let me go, mu daina daukan alhakin juna haka nan, auren nan tun farko da aka yi shi ni da kai bama so, igiyar nan a hannunka take, ka saki igiyar ni da kai mu huta da kunan zuciya” sai ya tsaya yana kallo na yace “haka kika ce? To tsaya kiji, lokacin da akayi auren nan ni kaina banyi niyyar zama dake ba wallahi, after what happened on our first night I thought in na sake ki ban kyauta miki ba, nayi niyyar in rufa miki asiri in cigaba da zama dake a haka ina tunanin with time zaki soni. Amma har yanzu kinki sona, kina ganin kamar ban isa ba ko something like that, ni kuma nasan babu macen da ta isa tace bata sona, in na sake ki Diyam kamar kinyi winning a kaina kin nuna min ban isa ba, which is something I won’t agree to. Kin san me? Nasan maganin ki. Aure zanyi. I will let you watch as a lady wadda bata kaiki komai ba take away your husband ta marar dani dan lelenta nima in mayar da ita yar lelena a gaban ki, maybe wannan shi zai nuna miki worth dina ki dawo cikin sense dinki” na mike na rike rigarsa cikin rarraunar murya nace “Saghir, ni ban hana ka aure ba, ni ba zan ma damu dan kayi aure ba ka auri duk matar da kake so Saghir but please ni ma ka barni in koma gurin wanda nake so” yace “ohh, wai dama har yanzu baki hakura da yaron nan ba, dama a saboda shi ne kike tayi min wannan wulakancin? Yaron da aka ce min babu wanda yasan inda yake watakila ma ya zama dan shaye shaye ko dan fashi amma ke shi kike so when you already have me?” Nace “so guda daya ne Saghir, kuma Sadauki naje yi wa shi” ya warce rigarsa daga hannuna yace “then you will rot here. Ke da Sadauki sai a mafarki” ya juya ya fita ya barni. Na jingina kaina da jikin bango ina jujjuya kan, sai kuma na zame na kwanta a gurin akan dandaryar tiles. Ina ji hadari ya hado aka fara ruwan sama mai karfi, tiles din dana ke kai ya dauki sanyi amma na kasa tashi ballantana in koma gado in lulluba, ji nake jikin nawa bashi da wani amfani dan haka lullube shima bashi da amfani. Anan assuba ta same ni, sai da akayi assalatu sannan na tashi da jan kafa na shiga toilet na dauro alwala na gabatar da sallah ina kara kai kuka na a gurin ubangiji na dan nasan shi kadai ne zai iya yi min magani, nasan yana gani na yana kuma jina kuma nasan bai manta dani ba dan yafi kowa sona. 

A ranar na tashi da mummunar mura da tari, kuma nasan hakan yana da dangantaka da kwanan da nayi akan tiles. Na shirya Subay’a da kyar, na sha magani na kwanta daga nan kuma sai zazzaɓi ya rufe ni. Daga nan sai ciwo, zazzaɓi ciwon kai mura da tari amma Saghir ko leko inda nake baiyi ba ballantana yaga halin da nake ciki duk kuwa da cewa na tura subay’a ta gaya masa yafi a kirga. A haka nayi ta ciwo na, da kansa yake shirya subay’a ya kaita school kuma ya dauko ta yasiyo musu abinci suci kayansu. Ni kuwa sai naji yunwa tana neman illata ni zan tashi insha tea in koma. Har na kwana biyar a haka.

Ranar Thursday na kira Inna na roke ta ta turo min Asma’u tayi min weekend dan ta dan taya ni wasu abubuwan, na gaya mata bani da lafiya ne. Friday sai gasu sunzo har da Inna, wannan shine zuwan inna gidana na uku tunda nayi aure kuma duk duba ni take zuwa yi in bani da lafiya. A kasa muka zauna dan bata taba hawa sama in tazo, tana tayi min mitar yadda duk nabi na kara ramewa tana cewa me yasa banje asibiti ba? Ni kuma sai nayi shiru kawai dan ina ganin fada mata cewa Saghir ba zai kaini ba bashi da amfani tunda nasan ko tayi masa magana ba zai ji ba sai dai kawai ranta ya baci. Sai kuma nayi tunanin ko ingaya mata zancen Sadauki? Sai dai bani da tabbas din yanzu menene ra’ayinta akan Sadaukin bansan yadda zata dauki kasancewar sa a matsayin ogan Saghir ba. Na dai san tana nemansa akan gadon Ummah na gida dan haka dole zan gaya mata amma ba yanzu ba, sai na samu damar magana dashi tukunna first.

Asma’u ce ta tashi ta gyara min gidana tsaf, har dasu turaren wuta, sannan ta shiga kitchen tayi mana girki muka hadu muka ci tare harda Subay’a. Sai naji dadi sosai, maybe ciwon nawa harda rashin wanda zanyi wa magana da kuma yunwa. Ana yin la’asar Inna tayi sallah sai ta tashi ta fara shirin tafiya. Na fara mita “Inna daga yin la’asar? Ki bari mana sai kamar karfe biyar haka sai ki tafi” tace “uhm uhm, wannan gari na damina yanzu sai kiji ruwa ya sauko. Bana son mijinki yazo ya same ni a gidan nan” muka yi tayi mata dariya ni da Asma’u dan mu a gurin mu kamar babu komai dan sun hadu, ita kuma al kunya ce irin ta fulani. 

Ai kuwa kamar ta fada da bakin mala’iku sai ga ruwan sama ya sauko, da yake muma daki babu wanda yasan ma da hadarin sai kawai zubar ruwa mukaji. Inna ta fara salati mu kuma muna dariya “yau kwana ya kama Inna a gidan Adda” inji Asma’u, Inna tace “kwana bai kama ni ba, ai komai dare ruwan nan in ya dauke sai na tafi gida, balle ma ba lallai ne ya kai daren ba”. Wasa wasa ruwa har magrib, har isha yin sa ake kamar da bakin kwarya, Inna ta shiga dakin kasa inda Asma’u ta gyara dan anan take zama duk sanda tazo gidan saboda basu fiya shiri da Saghir ba, anan tayi sallolinta duk muka zauna muna hira ita dai tana ta bacin rai. Nace “Inna ki bari idan Saghir ya dawo sai ya kai ki a mota tunda ba kya son kwana” ta girgiza kai “ni da bana son ma yasan nazo? Bazan shiga motarsa ba. Allah ya tashe mu lafiya sai in tafi da safen”.

Na dauki Subay’a muka tafi sama saboda naji dadin jikina sosai, na tafi da niyyar inyi mata wanka nima inyi, Asma’u kuma ta tafi kitchen tana gyara abinda muka bata. A lokacin Saghir ya dawo, yaga motsin Asma’u a kitchen sai ya leka, yana ganin ta yace “ke! Yaushe kika zo gidan nan?” Ta dan tsorata saboda bata san shigowar sa ba tunda shi dama ba sallama yake yi ba, ta gaishe shi sannan tace “dazu muka zo duba Adda, ni da Inna” yace “ita Addan taki ce tace muku bata da lafiya? ina gwoggon take?” Ta nuna masa daki a ranta tana tunanin yau Inna zata sha kunya in suka hadu da Saghir.

Ya tura kofar ya shiga, Inna tayi saurin tashi duk ta diririce saboda ganin sa haka a cikin dakin gashi tana kwance dan ma dai ba kaya ta cire ba, ya tsaya a tsaye yace “gwoggo Amina barka da zuwa, ashe waccan makaryaciyar cewa tayi bata da lafiya?” Inna tace “uhm uhm Saghir ba karya tayi ba, kowa yaga Diyam ai yasan bata da lafiya” ya daga kafada yace “to ai sai kuzo ku tafi tun kafin dare ya sake yin nisa kuma” Inna tace “mu tafi kuma?” Asma’u data shigo tace “dare ai ya riga yayi, ballantana daren damina? Anan zamu kwana da safe Inna zata tafi ni kuma zan zauna sai sunday” ya girgiza kansa “no, kuzo ku tafi yanzu. A Kano ai dare baya yi ko sha biyu kuka fita zaku samu abin hawa” ya ciri dari biyar ya ajiye a kusa da Inna “gashi ku hau adaidaita” ya juya ya fita.

Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Asma’u tace “hamma Saghir bashi da mutunci Inna, bara inje in gayawa Adda tayi masa magana, yanzu ina zamu fita a wannan unguwa tasu duk kango? Ga shi har yanzu yayyafi ake yi” Inna ta girgiza kanta, “kar ki gaya mata. Dauko mayafin ki mu tafi. Allah yana nan ai shi zai kaimu gida lafiya” Asma’u bakin ciki ya ishe ta, Inna ma wani irin zafi zuciyarta take yi mata amma bata son gaya wa Diyam, shi da yayi din ai yasan ba dai dai bane kuma Diyam sai dai ta bata ranta kawai amma ba zata hana shi abinda yayi niyya ba, tasan ko bare Diyam ta aura ba zai musu wannan wulakancin ba ballantana ɗan yayanta, ɗan yayan mijinta. Ko Sadauki Diyam ta aura ba zai wulakanta Inna ba.

Mayafan su kawai suka dauka, lokacin karfe goma har ta gota Asma’u dan bakin ciki ko kayanta bata dauka ba suka fita ni ina can ban sani ba, ga duhu ga yayyafi anayi ga uban sanyin da yake kadawa. A bakin gate suka yiwa maigadi sallama, yace “Hajiya tafiya a cikin ruwan nan? Ku bari mana sai da safe ko kuma ayiwa mai gidan magana ya kaiku a mota” Asma’u tace “maigidan ai shi ya kore mu kuma yafi kowa sanin yana da mota”. 

Hanya duk ruwa ya kwanta haka suka ringa haskawa da wayoyinsu suna tafiya karnuka suna tayi musu haushi, babu alamar mutum ballantana abin hawa har suka fita bakin titi. Suka tsaya suna ta karkarwar sanyi amma babu abin hawa babu alamun sa. Asma’u ta fara kuka “Inna mu koma mu gaya masa bamu samu ba. In baya son mu kwana a gidan sa ba sai ya kaimu gida a mota ba? Ai muma muna da gidan ba’a titi muke ba” Inna dai bata ce mata komai ba. Can bayan sun gaji da tsaiwa sai suka fara tafiya a kafa suna saka ran maybe in sunzo round din yan kaba zasu samu adaidaita a can, ko babur ne ma in suka samu hawa zasuyi in dai zai kaisu gida. A lokacin sha daya na dare har ta wuce. Suna cikin tafiya ne wata mota ta tsaya a bayansu, suka juyo suna tunanin ko taimako ne tazo musu amma sai ji suka yi anyi musu fito, daganan suka gane yan iska ne dan haka suka kara sauri. Aka sake biyo su a baya aka ce “yan mata ji mana” Inna ta kankame hannun Asma’u suna sauri kamar zasu tashi sama amma sai motar ta sha gabansu, aka haske musu fuska da fitila sai wani yace “ashe ma tsohuwa ce da yarinya. Kyakykyawar yarinya” Inna ta tura Asma’u bayanta a lokacin da maza biyu suka fito daga motar. “Haba baba, Menene na boye ta? Rage mata hanya kawai zamuyi fa” dayan yace “kema in kina so sai mu rage miki hanyar amma a boot” suka kwashe da dariya sannan suka yo kan su Inna a tare. Da gudu su Inna suka diba, Asma’u tana gaba inna tana binta a baya mazan suna binsu a baya, daya yace “kunga tsohuwa ita ma ta iya gudu? Lallai itama da sauranta ashe”. Basu yi wani nisa ba suka cimmasu suka kama su, Asma’u tana ta ihu, Inna tana ta rokon su su rabu dasu “me muka yi muku yaran nan? Ku sake ta dan Allah marainiya ce” daya yace “nima maraya ne, kinga mun dace kenan”.

Sanda suke tisa keyar Asma’u cikin mota ne wata mota ta hawo ta bayan su a hankali, har ta gibta kuma sai tayi reverse da sauri ta tsaya. Asma’u ta fara kokawa dan ta samu karfin ganin taimako yazo mata wannan ya hana su tayar da motar har na cikin bakuwar motar ya fito da sauri ya taho gurinsu. Wanda yake rike da Asma’u ya fara zarowa daga motar yayi masa naushi biyu take sai ga jini a gaban rigarsa. Ba shiri ya sake ta ya shige motar, wanda yake seat din driver yayi saurin tayar da motar dan yana gudun karbar nasa rabon suka bar gurin a guje. Asma’u ta fadi a gurin tana mayar da numfashi cike da tsoro sannan ta juya tana kallon wanda ya taimaka mata, sai taga Inna ma shi take kallo amma maimakon tsoro mamaki ne kawai a rubuce a fuskarta. “Sadauki?” Ta fada da rawar murya “Sadauki!” Asma’u ma ta fada, tabbas, wannan fuskace da baza ta manta ba duk kuwa da cewa rabon data ganshi tun tana shekara tara a duniya yanzu kuwa shekarar ta goma sha shida. Sai ta mike da gudu ta tafi ta rungume shi. “Yar Asama” ya fada yana rabata da jikinsa, fuskarsa dauke da murmushi.

Ni ina can ina yiwa Subay’a wanka naji shigowar motar Saghir, har na gama yi mata wankan na shirya ta nima na shiga nayi na fito na tarar har ta yi bacci na shimfida sallaya na tayar da sallah, sai dana idar sannan na sauka dan in tabbatar su inna basa bukatar komai kafin in kwanta, amma sai naga dakin ba kowa, kitchen ma haka. Wasa wasa na chaje gidan amma babu su babu alamun su, hankalina ya fara tashi na koma sama na dauko waya da niyyar kiransu amma naji ance min “your account is not sufficient to make this call” bank da kudi, da zan kira Inna jiya ma ranta nayi a network dina. Hankalina in ya kai dubu duk ya tashi a lokacin dole na tafi dakin Saghir da sauri na fara buga masa kofa. Ya bude ya tsaya yana kallona nace “su Inna, ban gansu ba, ka bani aron wayarka dan Allah in kira su” yace “sun tafi gida. Ni nace su tafi. Da iznin waye kika gayyato min mutane zuwa gidana?” Na fara girgiza kai na saboda mamaki nace “mutane? Su Inna da Asma’u ne mutane?” Yace “ohh, aljanu ne ba mutane ba?” Ban jira sauran maganar saba na shiga dakina da sauri na dauko hijab dina, nayi hanyar stairs, nima gidan zan bari tunda har zai iya ya kori uwata daga gidan nan toni zaman me zanyi a cikin sa? Da sauri naga yazo ya wuce ni ya riga ni sauka, ban fahimci me yake yi ba sai dana ganshi a bakin kofar fita daga pallon, ya saka key ya rufe kofar sannan ya juyo ya wuce ni hau stairs yana kallona yace “nasan in na ce miki in kika fita a bakin auren ki da sauri zaki fita tunda abinda kike so kenan”. 

Na bishi a guje ina ihu “ka bude min kofa Saghir, ka bude min kofa nace” sai ma ya shiga dakinsa ya rufe kofa ya rabu dani. Na dawo kasa da sauri ina neman hanyar fita amma babu, duk windows din gidan akwai burglers a jiki, kofar kitchen ta baya kuwa dama tun ina amarya data lalace har yau ba’a gyara taba mun dai a amfani da ita. Sai na kama kuka ni kadai kamar mahaukaciya ina zagaye gidan. Ji nake a raina gwara in kwana a titi a ranar akan in sake kwana a gidan Saghir. A haka har karfina ya kare na zauna na jingina kaina da jikin kujera ina ajjiyar zuciya. A raina ina aiyana abinda zanyi wa Saghir in wani abin ya samu su Inna.

A lokacin ne waya ta tayi kara, nayi saurin dauka na duba naga sunan Inna da sauri na amsa nace “Inna me yasa zaku tafi a cikin daren nan? Kuna ina Inna?” A nutse naji muryar ta, hakan ya kwantar da hankali na sosai tace “ki daina kuka Diyam, muna gida mun iso lafiya” nayi ajjiyar zuciya nace “alhamdulillah. Inna hankali na ya tashi sosai” sayi shiru sai kuma tace “Diyam, Sadauki ne ya kawo mu gida. Ba dan Sadauki ba Diyam yau da bansan me zai same mu ba. Sadauki ne ya taimake ni Diyam a lokacin da Saghir ya wulakanta ni”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button