NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 9

 *WA ZAI FURTA?*????
              0⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*Wallahi tallahi inajin dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty Rabi dayi Mata addu’a da masu yiwa mahaifina addu’a na gode Allah yabar kauna my fans my pride ana mugun tare irin sosai dinnan*????????????.
*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda zaka ba kowa ba arziki irin nasu o’e ba daga mu sai ‘ya’yanmu???? Wanda ya tsargu dashi nake*????????????????????????‍♀

_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*

???????? *Unex*????( Babu kamar ki ).

*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon munafukai*????

???????? *AUREN FARI FANS*????????????????one love well.

*INA CIGIYAR MZ*????????????????

        ***************
*KADUNA RIGASA*
Tabbas Ummi Taji uwar bari,
Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in kwatar ma kaina yanci. Mutane dake cewar duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.
  Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba sai da nazo, Bata laifi, bata gundurar sa. Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don mallakarsa.
Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).
  Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.
Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.
Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban iya ba.
Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa nayi abinda yake so. Idan Kuma na sameshi daki………..ohhhhh na fahimci zancen ki. Ta katseta tana Yar dariya.
Baya Miki korafin Baki da kula?
Wallahi yanayi Aunty.
Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.
Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare, ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kibar wurin…..ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.
Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda Shi mutum ne Mai tsananin son kula.
Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaaa Nan da Nan sai ya harzuka…….gabanta ya Fadi…tohhh wannan dalilin ke sawa kullum sai sunyi rigima?
Ikon Allah.
Ta yi shiru dai, taji Amira ta shiga ranta sosai ganin ba bakin ciki ba Jin zafi ta zauna tana Mata irin wannan bayani Mai tsada Wanda ta tabbatar idan ita ce bazatayi hakan ba.
Kunya ta kamata sai kawai ta sauko bisa kujera…..Dan Allah Aunty Amira kiyi hakuri abubuwan da nayi a baya wallahi hada zuga irin ta mutane Amma Yanzu na gane……..Dan Allah tashi ki zauna ba komai. Shawarar da Zan baki shine ki kuji fitar da sirrin auren ki ga ko wanene wasu ba shawarar kwarai zasu Baki ba, ko meye kiyi keda mijinki ba Wanda yaji ya gani ko wace Kika gani gidan aurenta wallahi hakuri takeyi. Shi Aure 90% hakuri ke raya Shi sauran 10%din ne ilimi da soyayya. Saboda haka Dan Allah ki zauna mu fahimci juna tunda kaddara ta hada mu ba kanmu aka Fara ba iyayenmu da kakanni duk haka muka gansu Kuma zamansu lafiya ba don Babu kishi ba sai don hakuri da hangen nesa.
In shaa Allah Aunty Zan kiyaye Allah yayi Mana jagora……….
Tirkashi, competition zai tashi muje zuwa muga cikin Amarya da uwar gida wacece zata amshi first position????????
        **************
*Federal University dutsinma*

Yana son buga tsalle ya kasa , kanshi ya kumbura jinshi yake Babu kamar sa, ya gyara kwalar rigarsa sannan ya kalleta sama da kasa I warned you several times but u refused to listen to me, idan takamar ki *Hauka* ki sani Nan school din akwai *iyayenki*………Shima yasa Kai yabi bayan Bilkisu. Wuri ya dauki ihu…….mufeeda tayi tsaye ta kasa motsi tana sonyin kuka Amma ta daure kada ta Kara zubda ma kanta abin magana……
Yasan wata sabuwar rigimar ce, tana niyyar Zama Aisha tace me Kuma ya faru naji ana ihu?
Ni da waccen sakaran fa, ta tareni jiya suna mun wani kuri na banza akan Anwar shine na kaita gabansa nayi Mata nawa gargadin ta gane cewa ni ba tashi nake ba……..wa?
Aisha ta bukata tana zaro ido…..dai dai lokacin da ya karaso tayi kamar Bata ganshi ba tace *Anwar* Mana.
Me nayi? Ya bukata tare da tsareta da ido,
Wai ke me yasa bakya Sona da kwanciyar hankali?
Ta kalli Aisha tana Yar dariya kinji fa?
Sannan ta kalleshi, Da sunyi mun tsinannen duka jiya ai Ni Dana shiga tashin hankali ko? Ya zaro ido, duka?
Ta balla mishi harara wallahi tallahi duk ranar da ka janyo mun duka wajen ajabon Yan matanka a school dinnan har Kai sai sunja maka bala’i don security office zanje nayi reporting……ya kyalkyace da dariya Yan matan nawa ne ajebo?
Ke meye naki da zasu dake ki?
Ban sani ba kaje su baka amsa……..ya Kara dariya matsa in zauna…..da sauri ta matsa ganin Yana kokarin Haye Mata kafa…….kana da hankali Anwar?
Wani lokacin Ina taba hauka,, ya fada Yana dariya.
Aisha Mike Kai wallahi bazan biye muku ba Bari in koma baya inyi karatu.
Ita da yunkura zata tashi yayi saurin rike habar hijab dinta ya mayar da ita ta zauna……. Ba inda zakije wallahi.
Wai ke me yasa kin rainani?
Idan kina son abu gardama banayi sai nine Zaki ……….zaniyi me?
Mutane fa na kallon mu ya sunan abinda kayi?
Aisha ta girgiza Kai ta wuce tana murmushi.
Tasha mur, karatu zanyi ko ka tashi ko Kuma Ni na tashi…….babu daya ciki. Kiyi abinki bazan dameki ba.
 Gobe ne birthday dina me Zaki bani gift?
Tayi murmushi kai dai ka cika roko wlhi. Zan siyi ledojin pure water na ba Yan class suyi maka wanka,
Tabbb, ai bazan zo class ba gobe saboda hakan.
Wasa kakeyi ……
Allah kuwa.
To shikenan ka huta.
To meye Zaki bani?
Ta kalleshi cike da kosawa to meye Zan baka ne?
Gift!, Yace Yana Yar dariya.
Ta Sha mur, ka Fadi abinda kakeso Zan baka.
Zakiyi mun special girki, sannan ki kaini shopping………. Ta kyalkyace da dariya.
Yabi kumatun ta da kallo Yana son dimple dinta ainun.
 Shikenan Zan maka what next?
Karfe nawa zanzo?
Da safe kafin na tafi class kaga gobe har 6 Ina school…..no is too early. Bayan magrib dai……… Bana fitar dare sai dai kazo 2 kafin muyi lecture 4…….. Hmmm shikenan ya fada ba don ransa yaso ba sai don gudun kada tace duka ta fasa.
  Tare suka shiga test din ka kujerarta ga tashi. Ta kanga mishi fuskar computer din Yana tashi yanayin nata.
Sai gashi suna gamawa taci 20/20 Shi Kuma Yana da 18/20.
Tayi ta tsalle tana Murna.
Sun jero sai dariya takeyi tana Jin dadi, ta kalleshi yau wace rana naci CBT 20 last session wallahi naci da yawa 11 ko 12.
Murmushi kawai yayi.
Ta hango su Aisha shikenan bye bye wanna go thank you till tomorrow.
Ya juyo zai magana tuni ta tsallaka tana sauri so takeyi kawai ta Basu labari.
Ya danyi tsoki kawai ya wuce.
Nawa kuka samu?
Aisha ta yatsine fuska 13, khausar tayi tsoki Ni 10……. Wallahi saura kadan na shiga cikin department dinku Kinga ruwan Yan 7,8 da 9?
Ta zaro ido wallahi Anwar yayi mun duka na cinye……..duk suka zaburo 20?.
Cike da Murna tace wallahi kuwa.
Ohhh Allah ya kashe ya Baki inji Aisha.
Ai yau nayi sa’a Kuma wallahi ba layi daya muka hau ba.
   Yana tsaye shagon Abdul ya hangosu.
Kamar ya kwada musu Kira kwatsam sai ga Dr Dan Musa ya tari gabansu.
Bilkisu see me by 2 in ma office……..okay sir. Ta ce kawai suka wuce.
Wahalalle naga ubanda zai gani.
Baki zuwa? Inji khausar,
Eh, kullum aikin kenan kuma ba wat maganar arziki ba kame kame.
  Anwar ya bishi da harara lokacin da yazo zai gitta.
  Bayan sallar la’asar ta tafi dakin su Jennifer sukayi mata kwatancen gidan zainab wowo wacce keyi wa Yan makarantar cake. Ta iya cake sosai na biki da birthday ga sauki.
Aisha ta rakata. Mata Mai fara’a ta amshe su hannu biyu biyu.
Sannan suka ce cake sukeso na birthday Amma na maza.
Tace ba matsala.
Ko na nawa kike so Zaki samu. Kuma karfe nawa? Akwai Wanda Zaki ba yakai man goben wajen 1:30 haka?
In shaa Allah bani number da za a nemeki da ita.
Sukayi musayar number ta biya kudin babban cake na gani na fada.
Bayan sun fito ta kalli Aisha Zan surprising din sa ne.
Suka biya super market ta siyo manya manyan lemuka carton daya *na grapes* 
  Hmm kawai Aisha ta ce tana murmushi.
Ta harareta, Fadi ta cikinki Mana, *there’s nothing ooo just wanna surprise him and show my gratitude on what he has done for me Sha*
I knew, inji Aisha tana Yar dariya.
  Karfe shidda na safe ta tura mishi text “`Happy birthday Anwar wishing you more dollars in your account, you are an amazing person stay blessed“`
   KO minti daya ba’ayi ba yayi reply
“` Thank you my personal person“`
 Murmushi kawai tayi.
Shi kuwa ya karanta text din yafi sau dari.
Ko wa ka gani a class da ledar pure water saboda Shima haka yakeyi wa mutane Amma ba Anwar ba alamar sa, ko su sadeeq Basu San cewar baya zuwa class ba.
Bilkisu kadai tasan haka.
Sadeeq ya karaso kusa da ita hajia Kira Mana Anwar please…
Tayi murmushi yace yau bazai shigo school ba.
Aji ya dau surutu suka ce ko hostel ne yau sai sun bishi.
Kamar yanda sukayi alkawari da zainab sai ga cake…… Cake abinda ka cake sky blue yayi kyau karshe an nado Shi a leda cikin kwali. Sai kamshi ke tashi. Flowers din sunyi kyau Mai Rose ne da wasu design cake din ya tsaru.
    Tana kwance daki ya kirata.
Yana jiranta bakin hanya.
Ta ce toh, sanye yake da round neck shirt orange Mai ratsin fari a jikinta an rubuta *You are mine only* a gaban rigar. Dark blue jeans ne wandon da facing cap Fara anyi rubutu orange *Mine for ever* daga sama.
Kunnensa like da ear piece. Kanta a kasa tana tafiya a hankali.
Ya saki ajiyar zuciya kadan idonsa na kanta har ta karaso…..
Murmushi ta sakar mishi kafin tace happy birthday once again.
Godiya! Ya fada Yana latsa waya Shi adole ba kallonta yake ba.
Ta harareshi dai dai ya Dan dago.
Yayi murmushi ko amsar Bata Miki ba?
Yayi kyau karshe….ta fada a zuci a zahiri Kuma tayi shiru kawai.
Muje…….tace tare da yin gaba kadan.
Ki jira muyi hoto Mana….. Da wa? Tabb 
Ya Dan Sha mur, dake ko bazakiyi ba?
Eh, tace tana Kara ci gaba da tafiya.
Yaji haushi sosai.
Are you serious? Ya biyota.
Ta Dan waigo *did I look like a joker?*
Dan Allah kizo muyi pic Bilkisu…….. Ta zaro ido Wai da gaske kakeyi?
Sai ta danyi dariya kawai ta sunne Kai….
Ya ja tsoki, don ya karanci kunya takeji.
  Suna Isa shagon ta ce me kake so?
Ya Sha mur Yana fushi duk abinda ya Miki.
Tayi kamar Bata lura ba ta amso meat pie da soya milk drink na cikin kwalba Mai tsadar guda goma.
  Ta fito, gashi sai me?
Ya karba da hannu daya dayan Kuma Yana latsa waya. Yace shikenan thanks.
     Duk taji ba dadi kamar tace suje to suyi hoton Amma gaskiya Bata iyawa.
 Suka jera zuwa bakin hanya sai fushi yakeyi.
Zaka koma hostel ne?
Akwai abinda Zan Miki ne idan na tsaya?
Zan baka sako ne muje da mashin din a bakin gidan mu ka karba……. Ki je ki kawon Ina Nan.
Har lokacin fuskarsa ba fara’a.
Ta langabe Kai Wai Anwar fushin na menene?
Mtsew kawai yaja guntun tsoki.
Kaji?
Oh my God , me kike so Yanzu Wai?
Muje ka karbi sakon.
Jeki gani Nan zuwa.
Har zata Kara magana sai Kuma ta fasa ta wuce don itama ta Fara kulewa.
 Tana niyyar shiga gida taji tsayuwar mashin, da sauri ta waiga sai kawai tayi murmushi ganin shine ya Dan harareta.
Tayi ciki tana dariya.
Kwalin lemun ta Fara fitowa dashi tasa agaban mashin din sannan tace Ina zuwa ku jira.
 Ta dawo da cake din ta Mika mishi ga cake kaci sosai…….. Da sauri ya kalleta.
Tayi murmushi.
Kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yace da Dan mashin din muje………
Kamar tace dawo muyi hoton Amma bakinta yayi nauyi.
 Haka ta shiga gida sukuku…………
A hostel party sosai akayi yaji dadi abinda tayi mishi Yana son Allah ya kawo ranar da Shima zai Bata mamaki. Amma rashin yin hoton nan ya Bata Masa rai matuka, ya Fara gajiya da halin ko’inkula da ta keyi mishi, yanda Yan Mata ke rokonsa akan suyi hoton dashi Amma shi yau yabroki mace suyi taki amincewa *dame Bilkisu ke takama?*
     Wajen Sha biyu ya tura Mata text *Thanks for the cake* sai da safe ta gani. 
Bata Sami halin reply ba.
 Yana zaune ta shiga class din Koda suka hada ido tayi murmushi Shi Kuma ya daure fuska ya kawar da Kai.
Gabanta ya fadi, ranta ya Fara baci menene abin Jin haushi daga tace bazatayi hoto dashi ba? Ya taba ganin tayi hoto da wani ko wata?
Ta ajiye books dinta ta Isa wurin sa.
Ina kwana?
Ya dago Kai tare da cire ear piece. Ya kalleta Yaya? Fuskar sa ba yabo ba fallasa,
Zamuyi macro after this lecture please if you are free…….. It’s alright. Ya fada a takaice.
Ta juya ranta ba dadi.
Yan aji sai zolayar sukeyi jiya yaji tsoro baizo class ba kada a mishi wanka yana ta dariya da yazo zasu hada ido sai ya kawar.
Duk taji babu dadi.
Ana Gama lecture wasu suka shigo alamar venue din su ne.
Fitowa sukayi, ajin dake hade dashi ba mutane sosai Yana tsaye bakin taga tace Anwar muje Nan naga ba kowa……… Anwar let’s snap please Helen ta karaso tare da dafa kafadarsa…….
Wani dadi ya ziyarce Shi yace anzo wurin.
Ya kalli Bilkisu okay jirani Ina zuwa.
Kawai suka Fara hotuna. Kamar jira akeyi sai ko wace ta taso wasu ma wucewa zasuyi ga Anwar da farin jini
 Nan da Nan hankalin Bilkisu ya tashi ta kasa daurewa ganin yanda suke faman rikeshi wasu na kwanciya kafadar sa.
Ta shiga ajin idanun ta duk sunyi ja…..
Yafi mintuna talatin tana zaune ta ma kasa tashi suk tana hangensu ta taga.
Sadeeq ya karaso maigadon ya naga kinyi zaune baku Fara ba?
Eh, hotuna yakeyi yabar Ni Nan kamar sakarai, ta fada a wahale kamar zata kurma ihu.
Malami ya shigo yace ku fita zamuyi darasi……
Haka suka fito tare da jingina jikin icce ita da sadeeq har lokacin hotuna sukeyi ko kallon inda take baiyi ba.
Sadeeq ko zamu je ka nuna mun Dan Allah? Ta fada Rai bace…….. A ‘a ki jira ya Gama kinsan halin mutumin….wallahi yau Kam bana so ko da kuwa yazo.
Tohhhh….. sadeeq yace kafin ya Kara magana sai ga Anwar din.
  Bilkisu muje.
Ta kalleshi kallon da ya gwammace bugu dashi sannan tace bana so kaje kawai…….
Duk akayo musu ratai da ido.
Nan da Nan ya hasala don yasan a rina iyakar rainin wayo yarinyar nan ta daukeshi sakarai, 
Saboda me Baki so? Ya bukata a hasale….
Ina ce hoto ne a gabanka, ko? Ina jiranka mintuna kusan talatin…..Kai ma abokina meye haka.
Zanci ubanka sadeeq…ya daka mishi tsawa.
Kada Allah yasa taso waya rasa?
Don kinga Ina lallabaki naje nayi hoton me ya hana kizo ayi dake?
Ko Zaki hanani ne?
Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya maka kaima……duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake. Sannan ya kalleta kada Allah yasa kiso ke Kika rasa…….. Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka idanun sa sunyi jawur.
Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina?
Hakan take ta nanatawa cikin zuciya.
Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse……. Ta zaro ido fada?
Hmmmmm Baki San halin Anwar ba….. Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya shiga….
Yana zaune ya hade Kai da table. Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa,
Anwar!.. 
Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa.
Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba abokai . Ta Fara magana a hankali…..
Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi …….bazanyi hakurin ba. Ya fada kamar zai mareta.
Duk ajin akayi shiru ana kallonsu,
Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki? Ni idan naje wurin malamai su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci cikin jama’a?…… Naji kayi hakuri,……
Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri…..gabanta ya Fadi. 
Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi……. Bazanyi hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi…..kawai yabarta wurin.
 Na shiga uku ni Bilkisu ta fada.
Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa.
Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin? Ni Anwar zai dizga?
Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu?
Me yasa tun farko na bashi fuska?
Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har abada. Biji biji take ganin hanya….ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba…..ta bude daki ta fada bisa katifa sai kuka………
Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa Anas na shiga uku nayiwa  Bilkisu wulakanci.
Ya zaro ido me ya faru.?
Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata…..naji me ya faru.
Ya Mike kamar mahaukaci…….laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri. Zamu shirya …..ya fice dakin.
Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take.
Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa.
Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no. Sa cikin wayarta.
    Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi.
Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za’ayi C.A Kuma course din da tafi tsoro.
Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi.
Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though Shima ya Dan fada.
Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali….. Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong.
Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu….. Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya Mata hauka. Mtsew ya buga tsoki.
 Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din.
Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo.
Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi……. Alhamdulillah dama Ina ta addu’ar kada a riga ni.
Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai haukace.
Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara hasala……. Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya zauna tare da Bilkisu test…….???????????????????????? Tirkashi.

Ayi hakuri da kadan…✍????. Zainab wowo ce????????
Juma@ mubarak don’t forget to receive suratul kahfi????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button