NOVELSUncategorized

DIYAM 5

❤️ Diyam ❤️

By

Maman Maama

Episode fiveh

Yana tashi da safe kamar kullum abinda ya fara yi shine duba wayarsa, hopping to see
ko dan text message ne ko da kuwa daga brother dinsa ne amma kamar kullum nothing, ya runtse idonsa ya bude, haushin su yake ji gabaki dayansu, wato suna nufin zasu iya cire shi daga rayuwarsu ko? Suna nufin zasu iya shafe babinsa su manta dashi, wato suna nufin koma me zai same shi basu da problem ko?


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ya sake duba account balance dinsa yaga kudin ciki ko ticket ba zai siya masa ba in ma yace gidan zai koma. Jin dadinsa daya ya biya kudin hotel room dinsa in advance tun kafin suyi blocking dinsa daga family account. Ya jima yana tunanin abinyi sannan yayi scrolling through contact dinsa ya nemo number din brother n sa ya tura masa text message. Ya duba wallet dinsa ya ga cash din daya rage masa, yayi tsaki tare da komawa ya kwanta a ransa yace “makarantar ma ba za’a je din ba”. Ya jima a kwance sannan kuma ya mike da sauri ya shiga toilet, ya yanke shawarar abinda zaiyi. Idan ba zasu turo masa kudi ba to shi zai nemi kudi da kansa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Yana gama shiryawa ya tafi wani sabon mall da aka bude nan kusa da hotel ɗin sa, tunda sabon guri ne yasan suna bukatar ma’aikata dan haka yaje ya nemi aikin salesman, bai sha wahala ba saboda yadda suka ganshi fes fes dashi dan gayu suka bashi aikin, zasu ke biyansa daily kuma pay din babu laifi, at least ya samu kudin abinci kafin komai ya warware masa.

A bangaren Diyam kuwa yau Saturday tun da suka tashi suke aikin sanitation din gidan kamar yadda suka saba yi duk sati. Sai da suka share ko’ina suka goge sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror tana kallon reflection dinta. She have come a long way. Last year kamar yanzu in aka ce mata zata zo inda take a yanzu she won’t believe it, her life have been so fast, so dramatic and so challenging kuma she have succeeded all those challenges har ta kawo inda take a yanzu. Ta dauki mai tana shafawa a hankali tana noticing irin laushi da santsin da fatar ta take kara yi kullum, tabbas weather din London ta karbe ta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Sai kuma taji tana kewar gida, ta gama shiryawa ta fita parlor ta zauna jiran su gama su fito su tafi shopping kamar yadda suka shirya. Anan ta dauko wayarta tana noticing time sannan ta kira Inna. Bugu daya ta dauka daga dukkan alamu tayi missing dinta itama. Ta gaishe ta, Inna tana ta tambayarta lafiyar ta data Murjanatu, sannan Diyam tace “ya naji ki shiru? Ina rigimammiyar taki ne?” Inna tace “babanta yazo ya dauke ta sun fita” Diyam ta lumshe idonta ta bude tace “ya zo garin kenan?” Inna tace “eh dazu da safe yazo, shine ya dauketa suka fita wai za’a siya mata keke, ko me zatayi da keke tana mace? Yace min ai zuwa nan da wani satin zai samu yazo ya ganku” Diyam ta kawar da maganar ta hanyar cewa “sun shirya kenan, shi da yar tasa” Inna tace “ina fa? Ta dai bishi da kyar. Daga gani ba da son ranta ba dan dai babu yadda zatayi” Diyam ta kwantar da kanta a jikin kujera tana jin duk tension din data bari a Nijeriya yana dawo mata. A hankali tace “ki gaishe ta inta dawo, a gaishe min da Asma’u” suka yi sallama lokacin da Judith da Murjanatu suka fito kusan a tare.

Duk su ukun suka tafi shopping din a tare, Diyam tana driving, Judith a side dinta Murjanatu kuma a baya. Annashuwa suke ji suna ta wake waken su da dararrakinsu. Murjanatu ce tace su je sabon mall din da wata kawarta tagaya mata an bude, nan take suka karbi address din suka saka a GPS ya kaisu har kofar mall din. Suka fito suka yi locking motar suka shiga suna yaba kyau da haduwar gurin. Suna shiga suka ji ance “welcome, what do you want to buy today” suka juya gaba dayansu a tare, idon Diyam ya sauka a kan Bassam da yake kallonsu da murmushi a fuskarsa, for the first time ta ganshi babu cigarette amma headphone din yana nan sai dai ya sauko dashi wuyansa, three-quarters wando da farar riga mai tambarin mall din wadanda suka kama shi suka fitar da ainahin cikar zatin sa. Cikakkiyar sumar kansa a taje a gyare tas. He looks so handsome and matured. Nan take murmushin nasa ya bace, ita kuma ta fara yi tace “Bassam?” Ya shafa kansa ya juya baya yace “damn it” Diyam tayi dariya tana zagayo wa gabansa tace “wow. This is no nice of you Bassam. Mutum mai dogaro da kansa ba sai ya jira an yi masa ba, ka burge ni sosai. And you look good” ta fada tana kallonsa daga sama har kasa. Ya kalle ta shima yace “you don’t look bad yourself” tace “thanks” sannan ta gabatar dashi a gurin su Murjanatu wadda tunda ta ganshi ta gane shi ta kuma bata rai take ta zabga masa harara. Amma ba karya, ita kanta tasan kyakykyawa ne.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Shi ya zagaya dasu zuwa gurin duk abinda suke son siya, in sun je kuma zaiyi musu bayanin different brands na abinda zasu siya da kuma banbancinsu. A haka suka yi ta lodar kaya kamar Allah ya aiko su, kayan abinci kayan kwalliya kayan sawa, kayan ciye ciye da kayan shiririta, har sai da Bassam da kansa ya tsorata da siyayyar tasu yana gudun kar su je biya kudin su ya gaza suzo suji kunya kuma shi gashi bashi da kudin da zai biya musu amma dai sai yayi shiru. Amma suna zuwa gurin biya sai yaga ta basu credit card, ya dauke numfashin sa yana jiran yaji ance insufficient fund amma sai yaga an ciri kudin an miko mata card dinta. Nan aka loda musu kayan a manyan ledoji aka bawa labourers su kai musu mota, shi kuma ya bisu da niyyar ya tare musu cab amma sai yaga sun doshi wata lafiyayyar mota sun bude an saka musu kayan a ciki. Ya tsaya yana mamaki, a car? Student? In UK? Who is she? She definitely is not on scholarship kamar yadda ya dauka daga farko. Ya zagaya side dinta ya dafa windown yace “so, this is your car?” Tayi dariya tace “not mine, ara nayi from a friend of mine” tana jin Murjanatu tayi gyaran murya amma bata kula ta ba. Tace “to naga gurin aikin ka, zanke kawo maka ziyara” ya daga kafada yace “it is just a temporary part time job, kafin inyi clearing some situation” ta gyada kai tace “the not laughing situation?” Yayi dariya yace “yeah, one and the same” tace “da fatan ba zai ke hana ka zuwa school ba kamar yadda ya hana ka zuwa ranar Friday” ya kalle ta cikin ido yace “I will come, ko dan in ganki ma” tayi saurin fitar da idonta daga cikin nasa tace “see you on Monday then” suna jan motar daga gurin Murjanatu tace “you really are playing with fire” babu wanda ya bata amsa a cikin su. Daga nan basu koma gida ba sai suka shiga gari yawo, shiga can fita can suna ta bin GPS, suka tsaya wani restaurant suka ci abinci, suka je gidan wata kawar Murjanatu suka yi sallah, basu suka dawo gida ba sai yamma likis.

Da dare Diyam na kwance a kan gadon ta, jikinta likis saboda gajiyar zirga-zirga da sukayi tayi duk da cewa a mota suke. Ita kanta taji dadin fitar duk da dai bata nuna wa Murjanatu a fuska ba, she maintained her serious face. Ta tashi ta dauki ledar sweets da biscuits din da ta siyo da yawa kamar wata yarinya, ta jera su a bedside drawers dinta sannan ta dauko ledar m and m’s ta kwanta ta na jefa wa a baki tana duba lecture note dinta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Wayarta dake gefenta ce tayi kara, tana dubawa taga alert na kudin daya haura wadanda ta kashe musu, ko bata tambaya ba tasan daga inda kudin suka taho. Ta danyi tsaki ta ajiye wayar dai dai shigowar wani text message din. Ta sake dauka ta karanta kamar haka:

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button