NOVELSUncategorized

DIYAM 6

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Six: The Lucky Ones

Ta kalli jakar alawar kusa da ita ta sake karanta text din sai kawai tayi murmushi, sai kuma ta bata rai ta mike da sauri ta tafi dakin Murjanatu. Ta tarar da ita tana arranging kayan kwalliyar data siyo tace “ke kika gaya masa munje shopping?” Ba tare data kalleta ba tace “sure. Wani abu ne” Diyam tayi tsaki tace “Will you please stop telling him duk abinda nake yi? I need some privacy and some space” Murjanatu dai bata ce mata komai ba har ta yi mata banging kofar ta tafi, sai kuma tayi murmushi a hankali tace “hypocrite”. Sai da Diyam ta gama duk abinda zata yi ta yi shirin bacci sannan ta dauko wayarta ta tura masa reply

Thanks

Ta jima tana kallon kalmar, tana so ta kara rubuta wasu kalaman no matter how small wadanda zasu nuna masa irin yadda take ji a zuciyarta a game dashi amma ta kasa. Bata so tayi giving up, not now, not ever. Haka ta tura masa kalmar guda daya ta koma ta kwanta tana jin ranta babu dadi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bassam kuma ranar kasa bacci yayi, yayi ta tossing akan gadonsa. Abu na farko daya ke ransa shine sabon aikin daya samarwa kansa, yaji dadin aikin nasa sosai dan shi tunda yake bai taba aikin neman kudi ba, komai yi masa ake yi. Yanzu yasan at least bashi da fargabar running out of money. Abu na biyu kuma da yake ransa shine Diyam, ya rasa dalilin da yasa yarinyar ta tsaya masa a ransa tun encounter dinsu ta farko, he just can’t stop thinking about her. A haka har bacci ya dauke shi. Cikin dare ya farka idonsa ya sauka akan hoton Khausar dake kan bedside dinsa, ya saka hannu ya kife hoton ya juya ya cigaba da baccin sa.

Ranar Monday ya rigata zuwa hall dinsu. Sai ya zauna akan kujerar da take kusa da wadda take zama koda yaushe ya dauko littafi yana bubbudawa kamar mai karanta wa amma sam hankalinsa baya kai, hankalin sa yafi karkata zuwa ga kofar da students suke shigowa zuciyarsa tana kara dokanta da son ganinta. Can ya ganta ta shigo, suna hada ido tayi masa murmushi and all his problems melted away. Tun kafin ta zauna lecturer dinsu ya shigo dan haka basu yi magana ba suka mayar da hankalinsu kan lecture. Amma Diyam tana lura dashi yafi mayar da hankalinsa gurin kallonta maimakon gurin lecture, and her heart sank.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Lecturer yana fita ya juyo gaba-daya gurinta yace “so, miss Nigeria, you are from Yobe state, right?” Ta dan bata rai tana kallonsa tace “Yobe kuma?” Yace “eh, rannan kince min sunan ki Haleema Usman Kollere, and I know Kollere is in damagum local government, yobe state” tayi dariya tana rike baki tace “you are amazing” yayi murmushi proudly yace “I know my geography” ta mike tsaye tana zuba kayanta a jaka, shima ya mike, tace “You surely do, but I am not from Yobe. Kamar yadda na fada ranar nan ni yar kano ce, yes, my grandparents na uwa da uba duk fulanin Kollere ne amma ni a kano aka haifeni, kano ne a birth certificate dina dan haka kano nake amfani dashi” suka jera suna fita daga ajin tace “so you are from Abuja, where in Abuja are you from?” Yace “somewhere” ta tsaya a waje tana kallonsa tace “wayo ko? Wato ni na bude baki na gaya maka daga inda nake shine kai kuma zaka wani ce min somewhere ko?” Yace “a,a ke fa kawai kince min ke yar kano ce, kano ai tana da girma” direct tace masa “Municipal. Yakasai. Kai fa?” Ya sosa kai yana kallonta, taga bashi da niyyar fada tayi gaba tace “ohhh, I hate stingy people” ya biyo ta da sauri yace “I don’t want to lie to you, kinfi karfin haka. And I also don’t want to tell you yet” tace “saboda me?” Ya sake yin shiru. Ta karkata kai tana kallonsa tace “someone as shiny as you must have come from the Villa, not less” yayi dariya yace “You are wrong, ko kusa da Villa ban kai ba” tace “where then?” Ya kalli surrounding din gurin yace “ina zamuje ne naga mun fito waje” ta gane so yake ya chanja maganar tace “cafeteria, yunwa nake ji, I over slept har na makara kuma munyi fada da Murjanatu taki tashina” yayi dariya yace “me ya hadaku?” Tace “girl’s stuff, you won’t understand” ya rungume hannunsa a kirji yana kallonta yace “stingy, are we?” Tayi dariya tace “ba zaka gane ba fa” yace “okay, let’s go. Nima banyi breakfast ba”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Shi yayi musu order abinci, bacon and eggs, da coffee. Suka fara ci sannan yace “so, how did a Fulani girl daga rugar Kollere ta samu kanta a Oxford?” Ba tare data kalleshi ba tace “luck”  yace “hmmm?” ta ajiye chokalin hannunta tana kallonsa tace “you talk about kaddara ranar nan ko? To ita ta kawo ni nan, I was destined to be here and here I am. How about you? How did a guy from somewhere in Abuja find himself here” shima yace “luck” ta daga gira daya sama tana kallonsa sannan yace “okay, I was lucky to be born into a wealthy family” tayi murmushi tace “Villa?” Yace “definitely not” sukayi dariya baki daya.

Ranar kusan tare sukayi komai, har suka tashi daga school suka kuma tafi tare, sai daya rakata har bakin block dinsu sannan yayi mata sallama ya tare cab zuwa gurin aikinsa. Yana jin zuciyarsa fari kal kamar takarda, duk wani bacin rai da stress duk ya gushe daga ransa. He is finally finding happiness.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Diyam kuma tana shiga parlon su ta yarda jakarta ta kwanta ta lumshe ido, tana jin Judith ta shigo parlon tana yi mata magana amma sai tayi pretending kamar bacci take yi nan kuwa idonta biyu, lissafi kawai take yi a ranta. Most of the time shi yasa tafi son zaman makaranta saboda in tana can tana mantawa ne da duk wasu problems dinta amma tana zuwa gida sai taji kamar damuwowinta jiranta suke yi a bakin kofa. Jiya da daddare sukayi rigima da Murjanatu, kuma ita tasan Murjanatu gaskiya take gaya mata, tasan yaudarar kanta kawai take yi taki admitting hakan. Ta dauko wayarta tana kallon hoton dake kan screen din tana murmushi, sai kuma ta shiga cikin ta fara kallon pictures tana ta dariya ita kadai. She missed Nigeria sosai, but wannan zaman da take, wannan karatun da take, shine kadai solution dinta a yanzu. Me yasa mutane including Murjanatu suka kasa fahimtar hakan?

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Sai bayan la’asar Murjanatu ta dawo. Kafin nan Diyam ta shirya musu pasta saboda tasan Murjanatu tana so duk dan su shirya. Tana shigowa kallo daya tayi wa Diyam ta kara tura baki gaba ta wuce daki, sai da tayi wanka ta shirya cikin riga da wando budaddu kalar ruwan toka da suka kara wa bakar fatar ta kyau sannan ta dawo parlon ta tsaya ta rike kugu tace “shine kika taho kika barni ko? Kuma na tambaya ance min tare da wannan tsinannen Bassam din kuka taho” Diyam ta mike zaune tace “ayyah Fanna, karki tsine masa, kinsan bakin ku dafi ne dashi, kar kisa ya tambade shi da baiyi miki komai ba” Murjanatu ta zauna ta dora daya kan daya tace “tunda yake kula matar yayana ai yayi min laifi, kuma wallahi daga ke har shi ku shiga hankalinku idan ba haka ba yana zuwa next week sai na gaya masa, kuma kunsan sauran” Diyam tace “oh oh, to gaya masan mana, an gaya miki kowama tsoronsa yakeji kamar ke, ni kinsan daga ke harshi dai dai nake daku. Naci nasha tsumin fulani barebari sai dai su ganni su barni” nan kuma suka koma wasan fulani da barebari, sannan suka ci abincinsu tamkar ba sune jiya suka yi fada ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button