NOVELSUncategorized

DIYAM 56

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Fifty Six : A Walk To Freedom

“She gave birth to you” 

Maganar ta daki kunnuwana sannan ta wuce har cikin zuciyata, sai naji tamkar ta kunno min emotions din dana ke ta kokarin dannewa a cikin zuciyata, sai hawaye yazo idanuna ya fara zuba kan kuncina a hankali na
fara rera kuka sai ya taho inda nake da sauri yace “Diyam…..” sai kuma ya dakata ya juya ya koma bayan table dinsa ya danna button din bude kofa yace ba tare daya kalleni ba “good bye Halima”.

Na juya nima da sauri na fita ina kokarin goge hawayen fuskata. Na sauka daga stairs din cikin sauri na fita daga building din. So nake kawai in samu seclusion din da zanyi kuka na son raina har in gode Allah. Na tsaya a bakin kenan naga mota tayi packing a gaba na sai driver din ya fito ya zagayo inda nake ya bude min kofar baya yace “oga yace ki shigo a kaiki gida” har nayi tunanin kin shiga sai kuma nayi lissafin gwara inyi kukana a cikin mota ni kadai da ac akan inyi a cikin napep mutane suna kallona.

Na shiga ya rufe kofar ya zagayo gurin driver sannan na masa kwatancen gidan Alhaji Babba muka tafi. Na jawo hijab dina na rufe fuskata nayi kuka na na koshi amma ni kaina bansan kukan menene ba, kukan tausayin kaina ne ko na Sadauki? Kukan abinda ya faru da ne ko kuma wanda zai faru nan gaba? Ko kuma kukan abinda yake faruwa yanzu ne?

Nayi bitar maganganun Sadauki ina son inyi placing dinsa a scale din dai dai da rashin dai dai. A iyakacin fahimta ta tun muna yara nasan kafiya da zuciya sune manyan flaws din Sadauki. And he seemed to be harder yanzu. Ya nutse sosai a cikin kogin revenge yadda har yana kokarin yayi loosing kansa, and I won’t allow that.

Nasan duk abinda yayi akan gaskiyar sa yake, babu inda ya kaushe wa shari’a but still Allah da kansa yace yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina so Sadauki ya kasance a cikin jerin mutanen da Allah yake so. 

Muna zuwa gidan Alhaji Babba na sauka, drivern ya tambayeni in shikenan inda zai kaini na amsa masa da eh. A dakin Alhaji na same sun yi tsuru tsuru har da Fauziyya. Ina shiga Alhaji ya mike yana tambayata “ya kuka yi Diyam?” Na girgiza kaina kawai na zauna a raina ina cewa ‘you are in for a bad news’ duk da daga yanayin su na fahimci sunje gidan Saghir sun tarar da yan haya a ciki. Alhaji ya zauna shima, yanayinsa kawai ya isa ya saka mai raunanniyar zuciya kuka, yana cewa “wannan wacce irin mummunar kaddara ce ta afkawa yaron nan? Wallahi ni ko da wasa bai gaya min ya dauki wadannan kudade ba, ballantana ya gaya min ya karbi wannan ajiya. Ba wanda yake neman shawara a gurinsa shi kadai yake al’amarinsa shida abokansa. Yanzu gashi gidan munje mun tarar da mutane sunce su haya suke yi a hannun wani agent suka karba” sai na basu labarin duk abinda na fahimta da maganar, a lokacin da Saghir yake can yana honeymoon dinsa shi kuma babban abokinsa Kabir ya saka gidan da kuma motar da Saghir din ya siya da sunana a kasuwa, ya karbe kudaden ya hada dana wajensa ya gudu ya bar kasar bayan ya bawa Saghir ajjiyar drugs kuma yayi masa chunen NDLEA.

Kowa yayi shiru a dakin har na gama bayani na, sannan na kara da cewa Sadauki yana kan bakansa na cewa sai an biya shi kudinsa. Har na gama babu wanda ya samu damar bani amsa. Sai dana gama sannan Hajiya Babba tace “Allah, Allah mun tuba. Allah in laifi muka yi maka ka dube mu ka yafe mana ka kawo mana sassaci a lamarin nan. Allah ka dubi yaron nan ka fitar dashi daga wannan matsala” ni dai nace “ameen” amma a raina nasan a inda matsalar take. Alhaji ne yayi deciding cewa zai je yaga Saghir kuma zai gaya masa halin da ake ciki. Sai naji dadi dan ni kam I wasn’t looking forward to breaking the news to Saghir cewa best friend dinsa ne yayi framing dinsa dan ya cinye masa kudi. 

Daga gidan Alhaji gidan Mama na tafi. Ina shiga Subay’a ta taho da gudu ta tarye ni tana cewa “Mommy ina daddy? Kin dauko shi daga gurin yan sandan?” Na jawo ta na rike fuskarta a hannuna nace “Daddy ya sake yin wata tafiyar, amma zai dawo very soon” sai ta saka kuka ita gurin Daddy zata je ita in kira mata shi a waya. Sai da Mama tayi barazanar dukanta sannan na samu tayi shiru. 

Muka zauna na bawa Mama labarin duk abinda ake ciki tace “ki fita cikin maganar nan Diyam. Ki barshi shi da iyayen sa suyi ta fama ai tsuntsun daya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. Duk halin da Saghir yake ciki iyayen sa ne suka jawo masa dan haka ki barsu su girbi abinda suka shuka da hannun su” sai nayi shiru ina kallon Subay’a tana wasa ina tunanin ko zata daina tambayata daddyn ta?

Sai yamma sosai na shirya Subay’a muka koma gida, muna zuwa na tarar Inna itama dawowar ta kenan sai Asma’u take bamu labarin Sadauki yazo yiwa Inna sallama zai tafi ‘business trip’. Na kwanta kawai na rufe idona amma nasan babu wani business guduwa yayi dan kar inyi breaking dinsa. 

An saka ranar shari’a Saghir sati biyu bayan kama shi, na shirya na koma bompai gurinsa amma sai yaki yarda ya ganni, officer din yace “ya zama very emotional kwana biyun nan yace baya son ganin kowa” sai na fahimci cewa Alhaji yazo ya bashi labarin cin amanae da Kabir yayi masa, and it broke him, finally.

Tun da aka saka ranar shari’ar Saghir ban zauna ba, nice gidan Alhaji, nice bompai, nice NDLEA, kuma nice kiran Sadauki. Kullum sai na kira shi da yawar Asma’u amma itama sai ya daina dagawa. Sai in zauna in tsara masa message, duk abinda nasan zai saka ya sauko in tura masa amma ko reply daya ban taba samu ba. 

During one of my visits to NDLEA ne na samu rannan suka saurare ni, nayi musu bayanin abinda ya faru nayi mentioning sunan Kabir and that cought their attention, ashe dama suna suspecting dinsa amma basu da hujjar kama shi dan haka sun yarda zai iya framing Saghir din but still there is a case, kuma dole someone has to take the fall, Saghir kenan, dole zasuyi convicting Saghir suyi sentencing dinsa har sai an kama Kabir ya kuma karbi laifinsa.  I felt relieved, duk da ba wani important improvement bane ba but at least it was a step further.

An siyar da gidan Saghir inda muka zauna, an siyar da tsohuwa da sabuwar motarsa sannan an siyar da motar daya siyawa Fauziyya itama. Sai aka hada da kudaden daya bari account din sa but all that only raised one third of kudin da ake binsa. A lokacin ne na kuma fahimtar cewa Saghir bashi da kowa, bashi da brother dama, cousins din kuma da brother in laws din duk babu wanda yayi zaman arziki dasu ballantana su tsaya masa, uncle din kuma yayi wa yarsa ciki dan haka ko sau daya bai taba shiga maganar ba, daga ni sai Hajiya da Alhaji, ga Alhaji babu isasshiyar lafiya ga kuma tsufa daya kara saukar masa. Yan uwan Hajiya ma duk sun zare hannayensu sunce wannan abin kunyar ba da su ba. 

Nima rannan na dawo gida a gajiye Inna ta kalleni tace “daga yau babu inda zaki kuma fita akan maganar nan. In dake ce wani abu irin wannan ya same ki da daga Saghir din har iyayensa babu wanda zai daga ko dan yatsa ne ya taimaka miki, dariya ma zasu yi miki” na zauna kawai nayi shiru, sai tace “ko kin chanja shawara kuma Saghir din zaki komawa?” Nayi saurin girgiza kaina. Bana son Saghir kuma na gama aurensa, that’s a fact, but still har yanzu mijina ne, nayi kurakurai da dama a rayuwar auren mu bab sani ba ko wannan kokarin da nake masa zai taimaka min wajen goge wadancan laifukan. Sannan kuma, Subay’a, bata da wani uban daya wuce Saghir duk wani wanda zai rike ta sai dai ya zama uban kara amma ba mahaifi ba, and I am not looking forward to telling her that babanta yana prison, what will happen kuma inta fahimci cewa Sadauki yayi playing role a saka babanta a prison din? 

Another dalilina kuma shine Sadauki. Sadauki loves me, for that bani da dobt, wannan kusan shine dalilin da yasa ya gudu saboda kar yaga na damu ya kasa abinda yayi niyya. And I love him, shima bani da dobt a kan wannan dan haka nake so in chanja ra’ayinsa zuwa forgiveness, for his sake, saboda ina gudar masa daukan alhakin wadanda basu da laifi, ina kuma gudar masa dana sani a nan gaba.

Ranar sharia tazo and we all went to the court, na bar Subay’a a gida, wadda a ranar ma sai da tayi min complain din neman daddyn ta. Na samu seat a farko farko na zauna bracing myself for duk outcome din da za’a samu. Muna zaune aka shigo da Saghir, looking very down and defeated, ban taba ganin sa a haka ba. Ya zauna a gurin zaman accused looking down at his fingers. 

Sai aka fara gabatar da kara, aka lissafa all charges against him sai lawyers suka fara maganganun su da ba ganewa ake yi ba, nayi ta stressing ƙwaƙwalwa ta ina so in gane mai suke cewa amma sam bana fahimta sai dai in sunyi magana inga alkali ya gyada kai har suka gama. Sannan ya juyo yana kallon Saghir ya tambaye shi “how do you plead?” Ba tare daya kalle shi ba yace “guilty” and my heart went out to him. 

A take alkali ya yanke masa hukunci, for the crime of kudin Abatcha Motors daya ci, za’a rike shi a prison har sai familyn sa sun biya kudin, for the crime of drugs, shima zai zauna har sai an kama Kabir.

In both cases he is doomed for life.

Aka gama karanta masa sentence dinsa amma bai dago kansa ba, na fara jin koke koke a baya na. Na waiga naga Hajiya tana kuka ita da kanwarta, sai Fauziyya daga can gefe, sai su Murja sun hada kai ita da sauran yan’uwanta suna yin nasu, and then a can karshen room din na hango wadda banyi tunani ba. Suwaiba. Itama tana nata kukan.

Sai aka taho dashi za’a wuce dashi, ya tsaya yana kare mana kallo daya bayan daya, sai muka hada ido and he smiled. Da sauri na mike na tari abin hawa zuwa gida. 

Ranar kwana nayi banyi bacci ba. Washegari Mama tazo suka wuni anan ita dasu Rufaida da Muhsina. Bayan sun tafi da yamma sai naga Subay’a ta shigo da banki irin na kasar nan na yara ta saka a kasan gadon Inna. Nace mata “Subay’a? Banki kika siyo mana?” Tace “eh, kudi zan ringa tarawa a ciki in biya wannan yayan naki kudin sa da yake bin Daddy na” I was stoned, nace “Subay’a? A ina kika ji wannan maganar?” Tace “Mama naji suna hirar da Inna, wai Daddy na yana gurin police sai an biya yayanki kudi sannan za’a fito dashi”.

The next day na tashi da wuri na shirya, Inna ta tambayeni inda zanje sai nace “prison” sai ta shirya min abinci a basket tace “ki kai masa”. 

Da yake anan kano central prison yake, dan haka da kafa na tafi tunda babu nisa da gidan mu. Na jima ma’aikatan prison din suna ta ja min aji kafin su yarda zan ganshi. Sai suka kaini wani guri suka ce in zauna. After waiting for like eternity sai gashi sun fito dashi. He looked very different. Older but calmer. Suka zaunar dashi a kujerar gaban table din da nake sannan wanda ya kawo shi ya matsa baya but yana kallon mu. 

Na sunkuyar da kaina ina lissafa fingers dina shi kuma yana kallona yace “my God, you really are beautiful” na dago na kalle shi and he smiled. Nace “ga abinci nan inji Inna” yace “thank you. Dama kinga azumi nake yi” nayi shiru ina tunanin ban taba ganin Saghir yana azumi ba in ba Ramadan ba. Sai yace “ya kika ga sabon gida na? Yayi kyau?” Na kalli surrounding din gurin nace “nan ba gidan ka bane ba Saghir. I am going to get you out of here” yayi dariya yace “how? Zaki saka ni a jaka ne mu tafi gida tare?” Nayi shiru. Yace “nasan maybe, just maybe, zaki iya convincing your lover boy ya yafe min kudinsa, but zaki iya kamo Kabir ki danka shi a hannun hukuma ki saka yayi confessing cewa shi yayi framing dina?” Nace “maybe, just maybe, zan iya convincing Sadauki ya yafe maka, sannan in saka shi yayi amfani da power dinsa to get you out. Nigeria ce fa, with few phone calls an gama komai”.

Yayi dariya “not even in your dreams. Ba zaiyi ba. Mutumin da yake son ganin baya na ta yaya zai taimaka min?” Nayi shiru, nima kaina bansan ta inda zan bullowa wannan lamari ba but i am going to try.

Yace “I really did mess up ko? Nayi messing up auren mu. It would have been a great one” nace “not ‘you’ but ‘we’. Tare muka hadu muka rusa auren mu. Ina fatan kuma zaka yafe min my part of the mess” yace “oh, you mean the closed doors ko?” Nayi murmushi. Na juya hannunsa yace “na yafe” nace “thank you”.

Sai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardu guda biyu yana kallona sarcastically yace “ya sunan ki ma? Ke ce Halima ko kece Fauziyya?” Bance komai ba sai ya miko min daya, naga sunana baro baro a jiki na bude na karanta

Ni Saghir Muhammad Kollere na saki matata Halima Usman Kollere saki daya, in ta samu miji tayi aure

Na dago ina kallonsa yace “daya ne ba yawa, in kika hada da wancan sun zama biyu kenan. Ni kuma na rike daya a gurina with hope that maybe, just maybe, zaki zauna ki jira ni” nayi murmushi yace “not even in my weirdest dream ko? I will just have to keep hoping”.

Mutumin daya rako shi ya matso yace “time up” na gyada kaina na mike kamar zan tafi sai kuma na dawo na tsaya a gabansa nace 

“For raping me, na yafe maka. For the twins, na yafe maka. For everything, na yafe maka. And I am going to get you out of here” 

Yayi murmushi yace “thank you. Goodbye Halima”. 

Sai na juya da sauri na fita daga gurin, na kuma fita daga cikin prison din, hannuna rike da takarda ta.

Na fara tafiya a kafa ina jin iskar yanayin damina tana ratsani. Wani abu naji ya yaye daga ƙwaƙwalwa ta. I felt a sense of freedom wanda rabon da inji shi tun ranar da aka aura min Saghir. Hatta hanjin cikina ji nayi yana warwarewa tamkar da a nannade yake a guri daya, wani abu daya tokare a makogwarona naji ya sauka at last ina shaƙar numfashi freely. 

And I decided that I am going to do the right thing.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button