NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 26

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣6⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.

        **************
*Federal University dutsinma*

     …….Ta shako wuyanta ta buga da table, gyalen ta ya fadi hular gashin da ke kanta itama tayo kasa, wani chukuikuyon kitso ya bayyana ba ‘a ko ganin tsagar ga kegen can manne a wuya…..kaiii Bilkisu kina hauka…mAnwar ya fada a firgice….. Ta nuna Shi da hannu daya korar mun wadannan kattin ta kallesu tana zare ido…. *What the hell are you doing here*?????…. Wata Kara mufeeda ta saki ta dago ta da karfi goshinta ya Kara tsawo kamar wani bread da ake Kira danbisije na funtua…
Ya yunkura zai riketa ta Kara buga kanta a table….Zan nakasa ta Anwar wallahi…… Ya daga hannuwa sama okay ..okay… Ya kallesu kuje waje… Kofar class din da bakin tagogi students ne makil …… Idanun ta sun kada sunyi jawur tana magana tana zare mishi ido…… Kai bazaka iya maganin ta ba ko? Zan ci ubanta yau saboda duk makarantar nan yarinyar nan ta tsone man ido….. Zan yi..wallahi zanyi maganin ta please kada ki janyo mun bala’i kada kiyi kisan Kai Bilkisu…. wannan cin fuskane ki barshi ta mayar da gyalenta please….Ta ingizata da karfi tayi baya ta fada cikin sit bayanta ya daki kujera da karfi ta saki wata Kara…. Yayi wurinta da gudu a firgice…… Tayi tsalle ta dira gabansa kana tabata Ina karairayata……. Chief security suka gani da wasu securities subhanallah meke faruwa anan…. Yana ganin Anwar yace ranka ya dade da kanka???
Dan Allah ku fita da mufeeda kuje da ita…. Magana yakeyi a harmutse duk ya rikice, Bilkisu kuwa ya dake ta Sha mur Kai baka taba cewa ita ce tayi wannan tashin hankalin ba……. Ya kalli security daya je da ita clinic…. Yallabai kuyi hakuri muje office… Ita ce tayi gaba…… Zuciyar ki tayi yawa Bilkisu wannan yarinyar ta wahala me yasa Zaki…. Ta dalla mishi harara , ka Sanya a daureni na daki sahibar ka kasa a kaini prison….. Ohh my God,
Da gudu sadeeq ya dawo cikin makaranta jin wannan mummunan labari,
Abin mamaki Bilkisu ta Sami shaidar lallai mufeeda ce ta Fara tsokanar ta….. Anwar ya shiga ya fita case ya mutu. Suka fito duk ta chukuikuye fuska… Sadeeq yarinyar kaga zata yi kisan Kai ko?
Bilkisu me…… Na rantse da Allah idan ka Kara mun maganar waccen Yar iskar Zan sameta har dakinta na Mata tsinannen duka Wai Anwar kasan Hali na kuwa?
Na sani a yau, na sani wallahi Dan Allah kada ki Kara kula ta zan kawo karshen matsalar….. Kada ma ka kawo zata ci ubanta…. Ya kalli sadeeq duk sukayi murmushi.
  Kawo key din na dauko Miki motar sadeeq ku jira anan….. Ya wuce da sauri, sadeeq ya danyi dariya, duk kin hargitsa mun Anwar kin San Shi baya son tashin hankali….. Tunda takai fagen mufeeda ko? Ai Dole ya hargitse, wace irin masifa ce Suleiman ke bai gani ba?
Kasan Allah ka gaya mishi idan bai nesa da mufeeda ba sai na halaka ta…… Itama daga yau Dole ta shiga taitayinta kuma Zan fada mishi.
    Ya iso, ganin baida niyyar fitowa yasa ta fada baya ta zauna Dole sadeeq ya shiga gaba…. Suna fita yayi hanyar gidan sa Yana fadin Bari ki Fara ajiye mu tukun ta mishi banza kawai.
  Har ciki ya shiga da motar suna tsayawa ta fito ya dan koma gefe ta shiga wani mugun ribos da tayi sai da ta birge duk Wanda ke shiyyar…. Ya bita da murmushi kaiii sadeeq yarinyar can karshe ce….. Suka kyalkyace da dariya Ina so na ce ta dafan abinci amma duk na tsorata da ita…. Sadeeq ya kwashe da dariya Bilkisun kake tsoro????
…. wallahi tsoronta nake sadeeq, ya fada Yana dariya.
Kaga tsawar da ta daka mun Wai na ce su mustapha su fita???
Duk suka Kara kyalkyace da dariya…. sadeeq ya ce ko baba da babansa.
  Mufeeda kuka kawai takeyi, ba dukan ya Mata zafi ba, irin yanda ta cire Mata hular gashi ta tozarta ta gaban jama’a….. Ta kasa daina kuka, kunya ta hanata fitowa daga clinic din ta tafi daki.
Hakuri kawai kawayenta ke bata, Asma’u ta ce Ina ga mufeeda ki shafawa kanki lafiya ki kyale Anwar… Wallahi ko Zan rasa rayuwata bazan hakura dashi ba….. Duk suka zaro ido.
   Amina ta ce wallahi matar sa da gaske sunyi Aure mufeeda ki fita batun Anwar ki tsira da mutuncin ki nifa nake gane Miki Yanzu irin wannan cin mutuncin keda dadi?
 Ta goge kwallan da suka zubo ko Zan kyale Anwar sai na Rama wulakancin da ta mun wallahi bata Sha lale ba….. Ai kuwa next ba ita ce zata nada Miki duka ba wadannan kattin da ke gadin ta….. Ku duk baku San abinda naji ba, wallahi Anwar fa shine *Hamza bushara* …… Duk suka kwalalo idanu suna kallonta. Da gaske Asma’u?
Tayi murmushi wallahi kuwa, aini tuni na Fara sensing Anwar wani shege ne ko Kuma baban sa ne wani don gadarar gayen tayi yawa ko lecturers Kuna ganin shakkar sa sukeyi….. Mufeeda ta saki wani irin kuka irin shikenan ta shiga uku kawai…..  Amina ta dafa kafadarta kiyi hakuri ba class din ki bane Anwar maganar gaskiya sai irin su Bilkisun saboda Kinga babanta wani me itama tsaye take…. Ba wani babanta wallahi ko Yar gidan malam shehu ce tunda Anwar na sonta shikenan…..Kuma idan Kun tuna zuwanta ance sun Sha fada sosai da ita dashi tun farko ta nuna Bata tsoronsa, ke kuwa mufeeda ke ce Kika bayar da kanki yaushe Zaki ringa bin namiji Kuma guy kamar Anwar kema ai kinsan kin siya ma kanki buhun wulaknci.
    Tana kokarin parking Aisha sauko daga napep ta shigo da gudu…… Wai kin daki mufeeda?
Ta fada tana shessheka , ta fito motar, ta bi su mustapha ( body guard ) da harara tayi ciki tana fadin Aisha yarinyar nan Bata da tarbiyya Kuma duk laifin Anwar ne…Anwar Kuma? Shi meye nasa aciki?
Ta hayayyako Mata tafi karfinsa ne da bazai ce ta kyalesa ba? Me yasa sauran Yan matansa ke tsoronsa ita kadai ce zakakka????
Amma Yanzu kinji yanda ake Mata Allah ya Kara a school? Wallahi mufeeda ta shiga uku ko kunya ta isheta kinji labarin da ake yi kuwa?… Maryam ta kallesu ya akayi ne? Tana kwance falo suka shigo
Ta cire hijab ta fada bedroom dinta…. Aisha ta zauna…wallahi Bilkisu ta nakada ma mufeeda tsinannen duka har tana cire Mata hular gashi..ta karasa maganar tana kyalkyatar dariya.. Maryam ta tashi zaune bani in Sha…..
Hmm yarinyar nan ta debo ruwan dafa kanta Wai inba ita jakka ba waye zai shiga shirgin Anwar da Bilkisu soyayyar da kowa ji yake da kansa, soyayyar da sukeyi ma juna ta gadara wa ita ta shiga tsakani????
  ….ta danyi kasa da murya Wai kinsan an daura musu Aure Ashe?
Maryam ta zaro ido…. Tayi saurin Dora yatsa a lebe alamar tayi shiru….
Haba nidai wallahi nayi mamaki abun fa akwai alamar tambaya…. Kuma kin San waye Anwar?
Ta zaro ido tana girgiza Kai alamar a’a…. *Hamza bushara*….. Ta kwalalo ido ta dafe kirji..kice wallahi.
Tayi Yar dariya wallahi kuwa ta budo Mata waya duba ki gani… A nuna Mata. Ta Kara zaro ido… Bilkisu ta sani?
Tayi dariya wallahi ta sani yarinyar can hmmm kibar ta kawai….. *Bushara* Maryam ta maimaita… Yanzu Bushara takeyi ma wannan iskancin Aisha….. Aisha ta kama dariya fitowarta yasa duk sukayi shiru….
Ta zauna bisa kujera Maryam kinyi break?
Eh, ta fada a darare….
Aisha tace naji ana Kiran wayar ki kuwa…. Ta janyo jakar sai kawai tayi tsoki ta wurgar…. Bazaki dauka ba?
Kyaleshi Anwar ne….. Maryam ta zaro ido..
Aisha tace me yasa bazaki dauka ba?
Me zance mishi?
Duk wannan hatsaniyar waye ya janyota?…… Meye laifin sa Bilkisu?
Ta Sha mur, Aisha har Yanzu Ina mamakin me yasa yarinyar nan ta kasa rabuwa dashi?
Kina ganin ba laifinsa bane??
Ba laifin sa bane….. Ta Mike tare da buga tsoki tayi kitchen……yunwa nakeji Maryam Ina masu aikin?
Maryam ta kalli Aisha itama ta kalleta Aisha ta kyalkyace da dariya Maryam kuwa kasa darawa tayi. Ta rike Baki *Bushara*….. Kut!
  Ya kalli sadeeq nifa wannan fitinar yasa naso na mayar da ita Abuja kaga Yanzu da alama ni ne nayi laifi…. Sadeeq yayi murmushi ai dole taji haushin ka mufeeda ta kasa kyaleka itama tana nuna bata tsoronka kaga kuwa Bilkisu Dole ta tuhumeka….
… sadeeq ya zanyi da yarinyar Nan? Wulakancin duniya wane ke ban Mata ba?…. Duk da Haka ya kamata kayi wani Abu da zata kyaleka… Kamar ya? Dukanta zanyi?
Zagi na gidan duniya na Mata amma Bata da zuciya domin Allah meye laifina?
Ka barta zuwa anjima kilan ta dauka….. Bilkisun? Tabbb, yarinyar nan wuyar lallashi gareta Yanzu kaga Ni ta janyo mun jidali shegiya…. Sadeeq ya kwashe da dariya….

 Soyayyar ku na birgeni nawan…. Ya Kai mishi duka wane birgewa Dan ubanka ana ba juna wahala….Au Ashe Kai ma ka San Haka… Sadeeq ko zaka je ka bata hakuri ?
Eh, Amma Bari ayi sallah tukun…. Wai mu Dan ubanka baka kawo Mana masu girki ba?
… ……. Ba wani Mai girki da Zan kawo, Ni nafi son ta dafa mun…. To ka kirata a waya ko ka Mata text…. Bari dai ta huce.
Ya harareshi to ai kaga irin wannan ranar da aka kafsa fada mune Masha wuya ko?….
Ya Mike Bari na dafa indomie…. Please zanci…. Baka cinta Dan ubanka..ya wuce Yana banka mishi harara.
   Sadeeq yasha tsayuwar Shi taki fitowa, inda Allah ya taimakeshi suna da lecture four…….
Tana fitowa ta Kira mustapha.. kuyi wa Allah basai Kun bini ba Allah Yana tare Dani, bana bukatar tsaronku don kuwa bana wasa da addu’a…
   Ya danyi murmushi toh Hajiya,….tana fita suka rufa Mata baya…..
  Yana tsaye bakin kofa, ko kallonsa batayi ba ta wuce tana Zama shima ya zauna…. Ajin yayi tsit kowa ya maida hankalin sa wurin su don kuwa basa gajiya da dramar su. ….
Wai fushin na menene Bilkisu?
Ta harareshi kawai.
Yayi murmushi ke me yasa kin na son dauran laifi babu gaira?…… Au Ashe ma baka da laifi ko?
Me yasa har yau mufeeda ta kasa kyaleka, saboda me baka son ta daina kulaka????
Ya daga hannuwa sama na rantse da Allah Ina so ta kyaleni Bilkisu baki ganin irin wulakancin da nake ma yarinyar can Amma taki zuwa???….. Kuma shine ke nuna tafi karfinka?
….. Zaiyi magana malamin ya shigo…..
Ya dauko wayarsa ya rubuta Mata text a WhatsApp…
“`kiyi hakuri please“`
Ya Dan zunguro ta galla mishi harara ya Mata nuni da baki cewar ta duba Wayarta……
Ta tura mishi da harara….
Ya rubuta “` please sorry I don’t want to see you pissed off“`
Taki magana.
Ya Kara rubuta Mata..
“`You snubbed your husband?“` tare da imoji na zare ido.
Ta Kara tura mishi harara
“` sai ya tura Mata kuka“`
Ta Dan kalleshi ya langwabar da Kai ya rubuta… “` wallahi Zan yi maganin ta please am sorry“`
Ta danyi shiru sai ta rubuta mishi “` it’s okay“`
Yayi saurin tura Mata “` Oya smile na“`
Ta Dan kalleshi ya sakar Mata murmushi… Sai kawai ta duke tana Yar dariya.

Malamin na fita ya hawo table ya zauna gabanta Yana Yar dariya *Mun shirya ko?*
Ta danyi murmushi.
Sai ki koyan abinda akayi tunda kin Hana ni naji komai… Ta harare Shi Nima halan naji?
Ya kyalkyace da dariya gaskiya wannan semester din akwai damuwa Anya Zaki Bari na ringa ganewa?
Ta Kara mishi harara…  
Kun shirya ko? Ni an kyaleni cikin Rana daga Biko ya kalli Anwar Dan ubanka ka Kara Sanya ni cikin shirginku sai naci ubanka….. Tayi kasa da Kai tana murmushi Shi Kuma ya Kama dariya.
Suleiman yazo zai wuce Anwar yayi saurin rikoshi ranka ya dade idan ba hello ai akwai daga hannu ko?
Ya danyi murmushi ya Mika mishi hannu ya kalli Bilkisu, Hajia Allah yasa Allkhairi… Amin Suleiman Dan Allah ara mana abinda akayi Yanzu idan ka rubuta….. Anwar yayi fit ya fizge littafin ni zaka ba Alhaji ba ita ba.
Yabar masu book din ya wuce Yana Yar dariya….
Anwar kenan, yau kuma Suleiman kakeyi wa magana????
Ya Dan Sosa Kai gayen Yana bani tausayi wallahi duk wulakancin da na mishi a masallaci idan muka fito wallahi sai ya bani hannu…. Ta ce hmmm.
 Ya dan harareta ba hakan Yana nufin fa Zaki ringa kulashi ba fa….. Amma ai ma gaisa ko?
Eh, Amma idan kin saka nikaf, Wai yau me ya hana ki Sanya? Ya zaro ido……
Ta langabe Kai kamar zata mishi kuka Anwar Dan Allah ka saukaka mun da nikaf…… Wallahi sai kin saka ya dire Yana masifa…kammm idan Kika Kara fitowa babu nikaf wallahi sai kin koma Koda kuwa za ayi test ko exam….. Shikenan naji ta fada tana zumburo Baki.
  Muje ki ajiyeni gida…
 Wai Kai duk motocin da na gani gidanku fa…. Yayi murmushi kawai.
Ta haraeshi Wai Kai an fada ma har Yanzu ba’asan waye Kai ba?
Ya watsa hannuwa tare da daga kafada…. Ta danyi dariya tana son wannan move din…. 
Ungo kaja mu toh,
Yayi gaba abinsa bai ko kalleta ba…….
Ta bude suka shiga ta bata wuta…. Duk aka bisu da ido….. Ba karamin tafiya sukeyi da zukatan dalibai da malamai ba, ya kalleta Yana dariya waya koya Miki mota haka?
Ta mishi banza, ya kwantar da sit ya Dora kafa bisa dash board yayi filo da hannuwansa kinji kunya ta Hana mufeeda shigowa school?
Ta galla mishi harara sai kaje ka shigo da ita ai….. Ya runtse ido Yana dariya.
  Taci gaba da hararar sa tana magana watau Kai hankalin ka na gunta kana bin kwaf kwaf…. Ke rufan asiri ya tashi da sauri wallahi da wasa nakeyi zolayace….. Hey nawaoooo….
Ta kawar da Kai kawai .
  Ya canza maganar da cewa, me Zaki dafa mun yau?
Ta yi shiru.
Kinji?
Har abinci Zan maka?
Eh Mana, kiyi mun tuwo please kinzo da manshanu?
Ta ce um.
Amma anan zanzo inci kinji ko?
Ta kalleshi da sauri yayi Yar dariya ko ke Zaki kawon gidana na jiraki?……… Taci wani uban birki ji kake kuuuuuuu….????✍????
*Zainab wowo mamar Abdallah*????????


*YOU ARE THE BEST AMONG BESTEST, ALAWIYYA NASIR*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button