NOVELSUncategorized

DIYAM 58

❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episode Fifty Eight : Murjanatu

Na dauke kaina gefe nace “tunda babu sakon da zaka bani, Allah ya bamu alkhairi” na juya zan tafi sai ya zagayo ta gabana ya tsaya yace “look into my eyes and tell me ba kya son ganina
and I promise you I will leave you alone” na daga ido na kalle shi amma muna hada ido sai nayi saurin sunkuyar da nawa idon kasa saboda wani zazzafan sako daya iso gare ni daga cikin idanunsa, sai na jawo fuskar hijab dina na rufe fuskata dashi, amma ina ganin duhunsa, sai naga ya sunkuyo dai dai fuskata yace murya can kasa “open your eyes and look into my eyes kice ‘sadauki bana son in sake ganin ka” sai na juya fuskata daya side din nace “ka bani hanya in wuce, ko ka manta na baro ƴata a daki ita kadai? And she needs me saboda babanta bayanan yana prison” sai ya gyara tsayuwar sa yace “hmmm. Gori zaki yi min kenan ko? Wai ‘ƴata'” ya fada yana kwaikwayon magana ta. Bance komai ba sai kuma yace “Subay’a will be fine, nayi miki wannan alkawarin. Na san ba zan taba replacing mahaifinta ba, amma zanyi duk iya kacin kokari na inga na bata duk abinda ya kamata uba ya bawa yarsa. Kar ki manta ina da training din rikon ɗan wani. Ban tashi da ubana ba duk kuwa da cewa yana raye, and still I have gotten the best fatherly care and love”

Na fahimci zancen Baffa yake, sai na bude fuskata ina kallonsa nace “hakane, amma banbancin ka da Subay’a shine shi Baffa bai rufe mahaifinka a prison ba sannan bai yi gidan gona a cikin gidan grandfather dinka ba. No child will ever forget that”. Ba tare dana kalleshi ba na wuce shi na koma ciki. 

Ina shiga na wuce Inna a palo na shiga daki ina jin zuciyata tana yi min zafi, haushin Sadauki nake ji kuma haushin kaina nake ji. Ji nake kamar wani dan karamin yaki akeyi tsakanin zuciyata da ƙwaƙwalwa ta ko wanne yana gaya min abinda zanyi. Sai na sake jawo jakata na kuma hada kayana kamar rannan na fita na samu Inna a dakinta tana sallah sai na zauna na jira ta sai data idar sannan ta juyo tana kallona, daga yanayin zaman da nayi tasan magana ce a bakina dan haka tace “ya akayi?” Nace “Inna, alfarma nake nema a gurin ki. Dan Allah Inna ina so ki fita daga maganar Sadauki” ta kalle ni da mamaki tace “ban gane ba? In fita daga maganar sa kamar yaya? Wacce maganar kenan?” Sai nayi shiru na kasa bata amsa sai tace “ba kya sonsa ne yanzu kuma?” Na girgiza kaina nace “kawai dai Inna ina son ajiye maganar sa a gefe sai zuwa lokacin da muka sake fahimtar juna tukunna. Kinga shekaru da yawa, abubuwa da yawa sun chanja. Ba lallai ne halayyar sa ta da ita ce a yanzu ba. Ni so nake ki bar mu ni da shi kiyi ta mana addu’a in Allah yasa muka fahimci juna sai mu sanar muku ku saka mana albarka” a juya kanta gefe tace “fushi kike dashi akan maganar Saghir ko?” Nayi shiru, sai ta cigaba “ruwansa ne in yaga dama ya yafe masa, ruwansa ne kuma in bai ga dama ba kuma yaki. Ni ba wai ina matsa miki ki kula shi ko ki aure shiba, ina kokarin gyara abinda na bata ne a baya, ina kokarin bashi abinda na hana shine a baya tare da fatan ko hakan zai rage min laifuffuka na a gurinsa da kuma a gurin ubangiji. Dan haka ni dai shi nake so ki aura, amma zabi yana gurinki in kince a’a bazan ji dadi ba amma ba zan matsa miki ba”.

Nace “Nagode Inna” sai kuma na gabatar mata da bukata ta tason zuwa gidan Mama. “Kwana biyu” ta ce min, naso ta barni inyi sati ko ma sati biyu amma taki, haka na hakura na dauki kaya set biyu da safe na tafi tunda ina son zuwan saboda ina so muyi shawara. 

Ina zuwa na tarar Rumaisa tazo, na saka ta a gaba da tsokana mai ciki mai ciki ita kuma tana ta jin kunyar Mama, sai da muka kebe tace “wai dama haka ake ji in ana da ciki?” Hmmm kawai nace mata a raina ina cewa wannan kukan dadi take yi, na tuna cikin twins ina 14 years, babu abinda na sani, ga babu miji babu iyaye. Na tuna cikin Subay’a yadda na sha wahalar laulayi, da gorin da Saghir yayi min wai daga an taba ni sai ciki. 

Sai da muka samu zama sannan na bawa Mama labarin cewa Sadauki fa ya dawo, bai dai furta direct ba amma ya nuna. Ta daga kafada tace “so? Ji nake murna zakiyi kuma naga kin bata rai” sai na gaya mata kuduri na akansa. 

“Ba wai bana son aurensa bane ba Mama, so nake ya kunce kullin da yayi da kansa, saboda jin dadin kansa kuma Subay’a” tace “so kike ya yafewa Saghir kudin da yake binsa?” Na girgiza kai nace “ba wannan kadai ba, so nake ya taimaka masa yayi solving drug case dinsa. Sadauki yana da power, zai iya jan wasu strings ayi closing case din Saghir na drugs, ko kuma ayi tracking Kabir a kama shi asaka shi ya amsa laifinsa. Bayan ya fito dashi kuma ina so ya bashi aikin yi, saboda nasan with that reputation babu ma’aikatar da zasu dauki Saghir aiki ballantana ya samu abinda zai rike yayansa”. Mama tace “anya kuwa Diyam wadannan sharadan naki basuyi tsauri ba? Wane ne zai je neman auren mace kuma tace masa sai ya fito da tsohon mijinta daga prison kuma ya bashi aiki? Anya kuwa kina ganin zai amsa?” Na girgiza kaina nace “ban sani ba Mama, shine kuma shawarar da nake so ki bani yadda zan saka Sadauki ya karbi wannan maganar. Ni dai abinda na sani shine zuciyar Sadauki tayi tauri da yawa, ya kasa yafewa wadanda yake ganin sun cutar dani da shi. Kuma nasan  gurin Sadauki Saghir yafi kowa baƙi, shi yasa nake so ya yafe masa kuma ya taimaka masa. Nasan in dai har ya iya yafewa Saghir to babu wanda ba zai yafewa ba, in dai har ya taimaka wa Saghir to babu wanda ba zai taimaka wa ba”.

Mama tayi shiru tana kallona sannan tace “zuciyarsa tana da tauri tabbas, ke ai kinsan haka tun kuna yara haka yake kuma sai rayuwa ta kara taurara shi. To ni a shawara ta ba juya masa baya zaki yi ba jawo shi kijinki zakiyi. Ki nuna masa irin son da kike masa ki bashi dama ya nuna miki nasa, to shi kansa ba zai san sanda zuciyar tasa zata rissina ba, abinda zaiyi ke kanki sai ya baki mamaki”.

Kwana na biyu gidan Mama na shirya zan koma gida Inna ta kirani. “Sadauki yazo dazu, na gaya masa kina nan gidan yau zaki dawo sai yace zai zo ya dauko ki” nace “to” a raina ina jin haushin mai yasa ba zai kira ni ya gaya min ba.

Sai bayan magrib sannan yazo, har na gaji da jira na kwanta a palo ina game a wayata sai ga kiransa “Aliyu” nayi tsaki sai kuma nayi murmushi na daga nayi sallama, ya amsa yace “na dauka ba zaki dauki wayar bama ai. Kin san ni yanzu tsoran ki nake ji fa” nace “naga alama kam. Amma ai ba yanzu ne ka fara tsoran nawa ba dama ka dade kana yi” sai yayi dariya, and I couldn’t remember the last time da yayi dariya irin haka. Nima sai nayi murmushi. Yace “ina waje, Please kar kice da Mama ni nazo dan kunyarta nake ji”  na tashi na shiga dakin Mama zan mata sallama tace “da daren nan” sai na sunkuyar da kaina nace “Sadauki ne yazo zamu tafi tare” tace “kuma babu gaisuwa? Ki ce masa ya shigo mana” na dauki waya na kira na gaya masa yace “ke ba’a sirri dake? Ban taba zuwa na gaishe ta ba sai kuma in zo in fitar mata da ƴa? Ni kunyar ta nake ji” nace “to ai in bance kai ne ba ba zata barni ba cewa zata yi dare yayi” a dolen sa ya shigo, yana ta sunkuyar da kai yana shafa keya, and I asked myself “wai me yasa maza in suna jin kunya suke shafa keyar su?”.

Bayan ya fita nayi wa Mama sallama na bishi a baya. A cikin mota na same shi a zaune a seat din driver. Sai ya bude min kofar gaba yayi min alamar in shigo da hannunsa. Na shiga na rufo kofar sai ya juyo yana kallo na, na sunkuyar da kaina kasa ina feeling uncomfortable. Motar naga kamar tayi mana kadan, space din tsakanin mu yayi kadan, ga motar ta cika da kamshinsa mai shiga har cikin ruhi. Sannan kuma gashi yana min murmushi.

Naji kamar in bude motar in fice. Bai kunna motar ba ya juyo yana kallona Yace “wai ke duk fushin ne haka? Me zanyi ne wai ayi min murmushi ko guda daya ne” sai na kara bata rai na turo baki yace “okay rashin kunyar tana nan ashe kenan. Na dauka an barwa Subay’a” sai ya tayar da motar muka bar gidan.

A hanya yace “kinsa naji kunyar Mama fa, banzo na gaishe ta ba sai da nazo zance” na kalle shi nace “zance? Gurin wa kaje zancen? A kano muke fa ba’a Maiduguri ba” ya dan bata rai kamar mai tunani sai kuma yayi dariya yace “ohhh okay, yanzu na gane wannan fushin na menene. Ai na gaya mata zan zo gurinki dama kuma tace in gaishe ki” nace “kar ma kayi tunanin da nake tunanin kana yi. It is not what you are thinking” yace “yes it is. Hausawa sunyi karin magana suka ce kishi kumallon mata, amma ke naki kishin aman gaskiya yake saka ki. Daga jin muna magana da Inna sai ki kama amai?” Na gane maganar da yake yi nayi saurin cewa “ba fa abinda kake tunani bane ba, bani da lafiya dama a lokacin. To ni ina ma ruwa na da aurenka” yace “okay idan rashin lafiya ta saki amai ita ce kuma ta saka daga nayi miki sannu kika rufe ni da fada?” Nace “kaga nifa bana son ake juya min magana ta” yace “shikenan, an daina” muka cigaba da tafiya sannan yace “na bata labarin ki. I told her ina son aurenki first and she agreed” ya fada yana kallona, nayi kamar ban jishi ba ina jin bacin raina yana karuwa, amma sai ya sake cewa “tana sonki sosai. Tace zata zo Nigeria karshen week din nan purposely saboda ta ganki” na saka hannuna na toshe kunnuwa na ina jin zaman motar duk ya ishe ni. Nace “stop the car” yace “why?” Nace “ko dai ka daina wannan maganar ko kuma ka tsayar da motar nan in fita in karasa a kafa” sai ya kama dariya yace “an daina your highness”.

Muna zuwa gida nayi masa godiya, kafin in bude kofar ya kira suna na “Diyam” na juyo ina kallonsa yace “Please in na kira ki ki dauka kinji. Say whatever you want to say in kin dauka din but please kar ki ƙi dauka”.

Ranar na jima banyi bacci ba ina juyi. Feeling a familiar warmth a cikin zuriya ta wanda a da naje tunanin ko ba gushe yanzu baya nan. Zuciyata da ƙwaƙwalwa ta suka cigaba da battle dinsa ni kuma na zama confused dan bansan wanne daga cikin su zan bi ba. My heart was telling me in kira Sadauki a waya, in bude masa zuciyata in gaya masa irin zurfin da soyayyar sa tayi a ruhina, while my mind was asking me to hold on, reminding me cewa ba lallai ne in Sadauki ya samu abinda yake so ni kuma ya bani abinda nake so ba.

Washegari da safe bayan na dawo daga islamiyya ya kirani, daga alama a office yake “kinci abinci? Me kika ci?” Nace “kosai Asma’u ta soya mana” yace “yan gayu. Ni kuma kinga yunwa nake ji babu wanda ya damu yace Sadauki ga abinci” nace “Sadauki ko Mr Abatcha?” Yayi dariya yace “all the same” nace “ni banga same ba. Sadaukin dana sani is different from this rich Mr Abatcha” yace “really? To fada min menene bambancin” nace “da farko dai Sadauki baya taba yin abinda zai bata ran Ummah ko Baffa. Ita kuwa Ummah a cikin masu hakuri ma ita daban Allah yayi ta, bata taba fada ballantana har ta kasa yafewa wadanda suka bata mata. Na tabbatar kuma zata so ace yayanta, ni da kai, munyi koyi da ita, ko da bamu zama irin ta ba sai mu kwatanta ko yaya ne” 

Ya jima shiru sannan yace “she was a good woman. The best. Bata bata wa kowa, in mutum ya bata mata ma sai tayi kamar bata gani ba duk kuwa da cewa ta gani ɗin. Har gida har daki za’a zo aci mutuncin ta ba tare data yi laifin komai ba and she will always looked at me and said “kar kayi magana, kar kace komai” and I will keep quiet. Amma ranar data mutu kinsan me Alhaji Babba yace? Cewa yayi ba za’a shigar da gawarta gidan mijinta ba as if she were some kind of trash” na goge hawayen daya taru a idona ina tuno wa da abinda ya faru a ranar data chanja gabaki dayan rayuwata. 

Nace “sai menene kuma? Hakan ai bai rage ta da komai ba a wajen ubangijin ta, kuma muna saka mata ran cewa yanzu tana gurin da yafi gidan nan kyau da daraja. Kuma nasan da ace zata kalle ka a yanzu zata ce “kar kayi magana, kar kace komai” saboda tana son ka zama mai hakuri mai yafiya irin wanda Allah yake so, Annabi kuma yake alfahari dasu” yace “nasan abinda kike so ki ce, so kike yi kice in yafe musu gabaki dayan su, amma abinda kika manta shine, su fa basu yi nadama ba har yau. Yes, Alhaji ya bani hakuri ranar nan amma daga ni har ke har shi munsan cewa tuban muzuru yayi, na saka shine a corner babu yadda zaiyi shi yasa ya bani hakuri amma a lokacin da yana da dama da ina juya bayana zai daɓa min wuka” 

Nace “na sani, amma wannan shi da ubangijin sa, ni da kai na damu ba dasu ba, zuciyarka nake fatan gyarawa and maybe a kokarin haka kaga tasu itama ta gyaru. Kasan abinda na fahimta? Babu abinda yafi saukarwa da mutum nadama irin idan wanda akayi wa sharri yayi sakayya da alkhairi. Take Inna as an example. Ba karamar nadama ce Inna tayi ba kuma a yanzu babu wanda take kaunar farantawa sama da kai” ya ajiye numfashi yace “kina so in yafe musu?” Nace “yes, amma badan ni zaka yafe ba. Dan Allah zaka yafe. Take your time and think over it. Kai da kanka zaka yanke shawarar yin abinda ya dace”. Sai ya chanja maganar “yanzu ya za’ayi a kawo min kosan nan zuwa office?”

Kamar wasa few days bayan nan da daddare ina shirin kwanciya ya kira ni “me kike shirya wa bakuwar ki ne?” Nace “wacce bakuwar kuma?” Yace “kin manta nace akwai wadda zata zi gurinki?” Naji duk nishadin dana ke ji ya kau, nayi shiru yace “gobe zata sauka. Jirgin safe. Ni ina da meeting about that time. Ki shirya sai in turo miki da mota kije ki dauko ra a airport” nace “ni kuma? To ni da bansan ta ba  ta yaya zan gane ta?” Yace “ki saka bakar doguwar riga ita kuma zata saka milk. You will know her when you see her” na hadiye abinda ya tsaya a kirjina nace “ya sunanta?” Yace “Murjanatu”.

Not edited. Sorry for the typos.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button