NOVELSUncategorized

DIYAM 59 & 60

❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episodes Fifty Nine & Sixty : The Answers

Da safe na gayawa Inna sakon Sadauki. Tace “to fa! Sai kije ki dauko ta din. Anan zata sauka ne ko kuma a wani gurin daban?” Nace “nima ban
sani ba inna” sai tace “to ki kira shi ki Fjtambayeshi mana, in nan zata sauka ai gwara mu sani dan ayi mata abinci ko?” Na kasa kiransa saboda ji nayi duk haushinsa nake ji, sai na tura masa text “a nan zata sauka?” Sai da na fito daga wanka naga reply dinsa, “bakuwar ki ce ba tawa ba. Besides, ni gwauro ne bani da gurin da zan sauke ta”.

Karfe goma da rabi yace min jirgin su zai sauka. Karfe goma driver yazo yana jirana. Asma’u tana school Subay’a ma haka, dan haka dole na shirya ni kadai na fita ina ta bace bacen rai. Sai 10:30 muka je airport din a raina ina cewa ‘in sun sauka ma ta jira, da waye ya gayyace ta zuwa wajena?” Sai kuma nayi rashin sa’a jirginsu yayi delay dan haka sai da muka jira ma sannan suka sauka. Ina tsaye da bakar rigata da ya umarce ni in saka idona akan kofa ina ganin masu fitowa, mostly turawa ne maza da mata, sai few blacks suma kuma yawanci maza ne sai kuma wasu family da suka fito tare. Sannan na hango ta ta taho, tun daga nema na ganeta saboda kalar rigar jikinta. Waya a makale a kunnenta tana magana tana murmushin da yake bayyana hakoranta, naji kirjina ya buga da karfi a lokacin da zuciyata ta ayyana min wanda suke wayar dashi. 

Ta fito waje sosai tana dan dube dube, idonta ya sauka a kaina sai naga ta sake fadada murmushin ta ta katse kiran sannan ta taho inda nake. I was suppose to like nima in tafi inda take sai mu hadu a hanya amma sai nayi tsayuwata pretending as if ban gane taba har ta karaso gaba na tana murmushi tace “Diyam?” Sai kuma na kirkiro murmushi nayi mata ina studying dinta. Baka ce, mai matsakaicin jiki kyakykyawar gaske and every part of her was screaming “I am rich” dan kallo daya zaka yi mata kasan cewa bata san wata kalma wai ita wahala ba. And something caught my attention, kalar skin dinta, manyan fararen idanuwanta, shape din fuskarta da kuma yanayin murmushin ta irin na Sadauki ne. Na tambayi kaina “are they related? Ko hadin gida za’ayi musu?”

Na kirkiro murmushi nace “Murjanatu?” Sai tayi dariya, ta saka phone dinta a cikin karamar jakar da take rataye a kafadarta sannan sai kawai naga ta rungume ni, ta sake ni tana kara kallona tace “wow, you are even more beautiful in person than yadda aka kwatanta min ke” na danyi dariya ina tunanin tsaurin ido na Sadauki da zai zauna yayi wa budurwarsa description dina. Nace “welcome to kano, fatan dai baki sha wahala sosai ba” ta yarfe hannu tace “zafi, haka kullum in muka je Maiduguri nake fama. Kamar ace an ciro mutum daga cikin freezer ne an saka shi a cikin oven. Na kan tambayi Adama, wai haka kaji sukeji in ana gasa su? irin frozen chicken din nan kuma a saka su a oven” nayi dariya a raina ina cewa wannan surutu ne da ita. 

Drivern da muka zo dashi ya zo ya fara jan akwatin ta ni kuma sai na mika hannu da niyyar in karbi jakar hannunta amma sai taki bani tace “rufa min asiri, so kike yaya ya gasa ni kamar gyada?” Na maimaita kalmar yaya a raina. So they are related da gaske.

Muna tafiya veil din kanta ya fado kafadarta ya bayyana gyararren gashin kanta, but sai naga bata damu data gyara ba har sai da ni da kaina na gyara mata. She just thank me casually muka cigaba da tafiya.

A hanya muka dan taba hira, duk da dai da yawa daga hirar ita takeyi, a lokacin take gaya min cewa wannan ne zuwan ta kano na farko “in munzo Nigeria gida muke zuwa, Maiduguri, sai Abuja sometimes, mun dai taba zuwa Kaduna once” jin haka sai na fara yi mata bayanin guraren da muke wucewa a hanya, and she looked very interested. 

Da muka je gida ina kallonta ina jiran inga tayi wa gidan mu wani kallo haka, ko kuma in an bata abinci inji tayi wani comment marar kyau amma sai naga sam babu abinda ya dame ta, she is the most down to earth person I have ever met. Ta zauna ta harde kafa tana ta cin tarin abincin da Inna ta jera mata tana kuma yiwa Inna hira. Sai tace “ina ‘yar Asama? Kullum sai an bamu labarin Yar Asama da Diyam, Diyam this Diyam that. Ko kaya muka saka sai yace “ku kun mayar da kanku turawa, kuyi ta saka kananan kaya, why can’t you dress like Diyam?” Ta fada tana kwaikwayon yadda Sadauki yake maganar sa.

Na kai mata kayanta dakina sannan na hada mata ruwan wanka a toilet nace tayi wanka ta huta. Bata tashi ba sai da Asma’u ta dawo daga school, ina jin Inna tana yi mata bayanin bakuwar da akayi sai kuwa naga ta tura baki tana kunkuni, Inna tayi mata warning kar ta sake tayi mata wata magana marar dadi.

Na shiga daki na tarar ta tashi daga bacci tana sallah, na zauna ina jira har ta idar sannan na tambayeta ko da akwai abinda take so. Kafin ta bani amsa Asma’u ta shigo tace “nazo gaishe da matar yayana” sai naga Murjanatu ta kalle ni sai ta cigaba da nineke abin sallah. Asma’u ta sake cewa “matar yaya barka da zuwa” sai Murjanatu ta kalle ni tace “ana miki magana” nace “ke take gaisarwa fa” sai tace “matar yaya naji tace, wanne yayan?” Na gyara zamana ina so inyi confirming suspicio dina Nace “Sadauki mana” ta dan bata fuska tace “waye Sadauki?” Na sunkuyar da kai nace “Aliyu, mu anan Sadauki muke ce masa” cikin mamaki tace “yaya Aliyu? Nice matar tasa kuma?” Nace “well, not legally yet, yace dai an bashi ke an kusa biki” sai ta zauna a bakin gado ta dafe kanta tana dariya tana kallona tace “tsokanar ki yake, he is my brother, my half brother, baban mu daya”. 

Har dare Murjanatu tana ta tsokana ta. Ina jinsu suna waya da Sadauki tana bashi labari suna dariya sai na harare ta daga ita har wayar tata, ina jinta ta gaya masa wai ina hararar ta sai naga ta saito ni da wayar kamar zata min hoto sai na rufe fuskata ita kuma tayi ta min hotuna a haka.

Sosai Murjanatu ta sake a gidan mu, nan take muka kulla kawance mai kyau a tsakanin mu. Tana ta yimin hirar gidan su, Papa, Mama, Adama, Sa’adatu, Yani. Amma ban taba yi mata tambaya a kansu ba, na saka a raina cewa Sadauki ne ya kamata ya bani labarin su. Na fahimci kuma tana tsoron Sadauki, duk da kuwa na kanga suna yin waya suyi hira amma kamar bata taba ketare maganar sa, bata yi masa musu, kuma tana bani girma sosai saboda shi.

Ranar nan bayan Murjanatu ta kwana uku da zuwa muna waya dashi tace gobe mu shirya gabaki daya zai zo mu fita yawo “mu zagaya da Fanna taga garin Kano” nace “Fanna?” Yace “yes, Murjanatu. We call her that a gida”. 

Ina gaya musu sai murna, nan da nan Asma’u ta fara making list na guraren da zamuje, aka fara ware kayan da za’a saka da irin kwalliyar da za’ayi. Murjanatu ta kalleni ina yi musu dariya tace “gobe sai na yi miki kwalliya. Asma’u zata rike min ke in kinki tsayawa”.

Na dauka wasa suke sai washegarin na fito daga wanka sai gasu da make up kit, nace bana so amma haka suka tilasta min suka yi min kwalliya. Na dauko abaya ta na saka sai Murjanatu ta tsaya tana kallo na tace “wannan rigar is too loose, bai fitar da duk abinda ya kamata ya fitar ba bayan kuma akwai abin” sai ta dauko wani belt a kayanta ta daura min, na kalli kaina a mirror naga yadda hips dina suka fito sosai, ni kaina bansan ina dasu har haka ba, sai na girgiza kaina nace “bazan iya fita haka ba. Mutane zasu ke kallona fa” sai ta dan dake ni a kafada tace “dalla in sun kalle kin sai me kuma? Ke wallahi halin ku daya da yaya Aliyu yanzu zaku fara wa’azi” nayi dariya kawai amma na hakura ne kawai dan bana so in gwale ta amma ni nasan bazan iya sakewa ba sam. 

Muna gamawa yazo, muka fita ni dai ina ta rabe rabe a bayansu. Muna fita muka hango motarsa duk da bama ganinsa but I felt his eyes on me sai na kara buya a bayan Murjanatu ina jin kamar zan gurde in fadi har muka karaso inda yake, Murjanatu ta bude min kofar gaba tace “entere” nayi murmushi na shiga ina jin still idanuwansa a kaina amma na kasa kallon side din da yake, sai naji yayi gyaran murya yace da Murjanatu “koma ciki ki samo mata hijab” sai ta kama bubbuga kafa a kasa kamar mai shirin kuka sai yayi mata tsawa “are you still there?” Da sauri ta koma cikin gida.

Nayi kasa da idona ina wasa da fingers dina, still feeling his eyes on me. Sai yace “kinyi kyau sosai Halima. But I can’t let people see you like this. Ina da kishi da yawa I might end up fasa wa wani hanci akan hanya. In son samu nane ma bayan hijab har nikab zaki saka ki rufe fuskarki” tunda ya fara magana nake murmushi, ina jin feeling mai dadi a raina cewa nima ina da value. Sai na tuno da ranar da Saghir yake fito min da gashina “let’s show them abinda matansu basu dashi”.

Ta kawo min hijab din na saka ya saka hannu ya gyara min fuskar hijab din sannan yace “that’s much better” sai kuma ya leka waje yace da Asma’u da Murjanatu “duk wadda bata shigo ba zamu tafi mu barta” da sauri suka bude baya suka shigo suna dariya.

Yawo mukayi sosai a garin kano, har gidan sarki sai da muka je muka shiga ta kofar gudu muka fito ta kofar arewa muka ga grand central mosque. Muka je gidan mesium muka je gidan makama da gidan mutan da. Muka hau badala, muka hau dutsen dala da gwauron dutse. Muka je har government house muka yi zagaye a ciki muka fito sannan muka tafi Abatcha Motors.

Murjanatu tace “yau dai finally zanga wannan precious Abatcha Motors din da yake rike yayana a Nigeria. Ko da yake ban sani ba ko ba shi kadai bane yake rike shi ba” ta fada tana mintsini na ta baya. Na juya na harare ta shi kuma yana mana dariya muka shiga building din. 

Da yake weekend ne duk babu ma’aikata sai security kamar zasu ci mutum. Muna zuwa suka taso kamar zasu durkusa mana ni dai duk sai naji inajin nauyin su. Ya saka su bude ko’ina a gurin sannan yace dasu Murjanatu su zagaya duk inda suke so mu kuma sai ya saka aka kawo mana kujeru gaban wani fountain muka zauna. 

Sannan ya dauko waya yayi kira, da alama abinci yayi mana order. Sai kuma yace min “ranar nan, you asked me some questions. Are you ready for the answers?” Na tuno tambayoyin da nayi masa farkon zuwa na office dinsa. Sai nace “eh. Ina son sani please”. Yace “okay. Let’s start from the beginning”.

“Tun farko na san cewa Alhaji Bukar ne ya hada auren Ummah da mahaifina, amma bamu taba maganar dashi ba saboda ganin kamar umman bata so”.

“Sunan mahaifina Alhaji Umar Mustapha Abatcha” nayi saurin cewa “Alhaji Umar Mustapha dai wanda muke jin labarin sa?” Ya gyada kai yace “shifa. Family din Mustapha Abatcha family ne da yayi suna ba’a Maiduguri ba kadai har ma da sauran Nigeriya. Suna da kudi tun asalinsu but kudin Umar Mustapha daban ne dana sauran. Tun yana saurayi ya mallaki kudin da shi kansa mahaifinsa a lokacin bashi da su. Harkar man fetur yakeyi yi, tun yana yin gidajen man fetur a gari gari har ta kai shi ga fara siyan rijiyoyin man fetur din gabaki ɗaya. Bashi da lokacin aure, dan haka ya jima baiyi ba, wannan yasa yan’uwansa, musamman da yake duk yan uba yake dasu dan shi kadai ne a gurin mahaifiyarsa, suka sako shi a gaba, suna saka ran in ya mutu suci kudi. A lokacin ne Alhaji Bukar, tsohon amininsa da sukayi secondary school tare yayi masa tayin auren bafulatanar yarinya Zainab. Shi kuma sai ya karba yana ganin tunda ba auren soyayya bane ba ba zata ke demanding time dinsa ba. Ta gaya masa labarin wanda take so aka raba su and he was sympathetic, yana nuna mata kulawa sosai ita kuma ta kwantar da hankalin ta sukayi zamansu lafiya a nan family house dinsu dake Maiduguri. A haka har ta samu ciki. A lokacin ne kuna ya fara business da Canada yana exporting crude oil daga Nigeria zuwa Canada wanda har yanzu shine sana’arsa, a yanzu yana daya daga cikin manyan dealers na crude oil a kasar Canada. 

Tunda zainabu ta samu ciki shikenan kuma sai al’amurra suka cabe mata, gashi lokacin baya zama a kasar ita kuma taji duk duniya babu inda ta tsana irin gidan aurenta, babu wanda bata son gani kamar mijinta, babu kuma abinda take son rabuwa dashi irin cikin jikinta. Ta zama kamar mahaukaciya, sai ta fita da gudu sai an bita ana kamota ana dawo da ita gida, wani lokacin kuma sai ta zauna tayi ta dukan cikin wai sai ta kashe abinda yake ciki. Alhaji Umar yana zuwa ya ganta a wannan halin yasan asiri ne dan haka ya hada malamai aka zauna addu’a da magungunan karya sihiri akayi tayi mata, in abun ya lafa kwana biyu sai ya dawo. Ta sha wahala sosai. Ranar nan cikin dare suna bacci ta tashi tafita ko dan kwali babu ta kama doguwar katangar gidan da aka zagaye da waya da kwalabe amma a haka ta haura ta var gidan cikin jinin ciwuwwukan da taji, Alhaji Umar yana tashi yaga bata nan ya fito yayi ta nema babu wanda ya ganta sai ya dauki mota ya fita hankali a tashe. Cikin ikon Allah sai ya samo ta tana ta tafiya kamar zautacciya a kamata da kyar ya saka a mota daga nan sai airport. A can ya samu yayi mata adduoin ta dawo hankalinta ya sako ta a jirgi ta taho Kano ya kira Alhaji Bukar ya gaya masa, shi kuma sai ya koma ya nuna cewa bai same ta ba. Akayi ta nema har da cigiya a gidajen radio daga baya aka hakura.

Ita kuma ta dawo gurin yaya ladi ta zauna a kano. Har ta samu lafiya sosai aka tabbatar duk sihirin dake jikinta ya fita. Anan ta haife ni, Alhaji Umar yazo da kansa yayi min huduba da suna Aliyu “saboda ka zama jarumi ya sa na saka maka Aliyu” daga nan sai ya datse igiyar aurensa da zainabu, ya kuma roki Alhaji Bukar cewa ya nemo wannan wanda take so din yayi kokarin hada su aure, bayan an samo Baffa kuma Alhaji Umar da kansa ya bashi amana ta. “Dan Allah ka rike shi tamkar kai ka haife shi. Ɗa na kowa ne ai, wata kila ma kai zaiyiwa rana bani ba. Ni dai kawai ina son shi da mahaifiyarsa su kasance safe”. Through all those years da nake gurin Baffa ashe duk Alhaji Umar yana biye da rayuwata, kuma yace ko da sau daya Baffa bai taba neman wani taimako daga gare shi ba.

To bayan rasuwar Umma da Baffa, bayan na koma gidan Alhaji Bukar, sai yake gaya min cewa ya gaya wa mahaifina zancen rasuwar, amma baya kasar a lokacin yasan da zaizo gaisuwa ma amma yace a gayamin in saka rana da kaina sanda na ke ganin am ready in gaya masa zaizo Nigeria sai mu hadu a Maiduguri. I fixed the date, sai muka tafi. But cikin rashin sa’a sai ya zamanto shi din wani abu yarike shi a can kasar da yake zaune, Canada, dan haka bai samu tahowa da wuri ba. Ban sami kowa a Maiduguri ba sai step grandmother dina a uncles dina. A lokacin ne kuma kika kirani da maganar za’a hada aurenki da Saghir. Nan take naso in yi musu dan karamin hauka a gidan na dage akan lallai sai an taho anzo Kano an nema min auren ki. Duk kallona suke kamar tababbe, irin suna ganin ban isa aure ba ai. Aka kira Papa aka gaya masa yace a rabu dani, wanne irin aure kuma? Sai na karbi wayar na gaya masa ko dai ya ajiye koma me takeyi yazo ya nema min aurenki ko kuma in kama gabana kuma babu wanda zai kuma jin labari na. Sai na gaya masa ko wa cece ke da dangantakar mu. Wannan ne ya ja hankalinsa. Sai ya bani hakuri akan cewa ba zai iya zuwa ba sai dai mu taho tare da Alhaji Babagana, daya daga cikin uncles dina. Muka taho din kuwa and you know what happened a gidan Alhaji Babba. Sanda muka fita I was beyond broken. Sai nace bazan koma Maiduguri ba, a gidan Alhaji Bukar zan zauna. Na zauna gidan Alhaji Bukar trying to find a solution amma na rasa ko daya, babu irin tunanin da banyi ba ciki kuwa har da in shirya mana visa tare zuwa Canada sai in dauke ki mu tafi can mu cigaba da rayuwar mu. But sai na tuno da kalaman Baffa da yake cewa ba yaso ya bani aurenki in dai babu amincewar Inna a ciki, nasan kuma yadda Inna bata sona in na dauke ki zata hada daga ni har ke ne ta tsine mana kuma ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwa. And I didn’t want to put you through that. Sai na fara bincike ta karkashin kasa, Alhaji Babagana ya bani kudi sosai kafin ya koma Maiduguri dan haka bani da matsalar kudi, I followed Alhaji Babba, I watched him a lokacin da ya siyar da garejin Baffa, I also watched him lokacin da ya siyar da filina, I watched him lokacin daya siya wa dansa gida na bishi har gidan na gani. But bayan ya tafi sai na tsaya ina studying gidan, bai yi min ba kwata kwata. Unguwar was deserted dan haka babu security kenan, ko menene zai samu mutum a gidan babu wanda zai sani. Na haura na shiga har cikin gidan sai naga locks din kofofin ba masu kyau bane sosai sai naje na siyo wasu na dawo na cire wadancan na saka sababbin da kaina. But still ban gamsu ba dan nasan wannan mijin naki ba lallai yake zama a gida bake kadai zai ke bari so I hired a gate man for you. Malam Iliyasu” na kalle shi da sauri nace “Malam Iliyasu dai maigadin gidan Saghir?” Yace “yes. Tsohon soja ne yana gadi anan kusa da gidan Alhaji Bukar to sai wanda yake yi wa gadin ya rasu. So I took him zuwa unguwar na nuna masa gidan, mukayi sa’a Saghir din yazo sai na nuna masa shi nace yaje ya nuna masa cewa gurin zama yake nema, yana son zaiyi masa gadi free of charge abinda yake so kawai a bashi dakin mai gadi ya zauna anan. And he took the bait. Nace yace masa free ne dan na fahimci babu yaren da Saghir yake ganewa sosai irin na kudi. So, Malam iliyasu yayi muku gadi, ni nake biyansa duk wata, in return shi kuma yana supplying dina with information musamman abinda ya shafi lafiyar ki”

Ban bar kano ba sai da nayi attending daurin aurenku da Saghir. Daga nan airport na wuce straight na tafi Maiduguri ina zuwa kuma na tarar takarduna sun gama haduwa zuwa Canada dan haka kwana na daya a Maiduguri na tafi Ottawa, capital din Canada inda anan ne mahaifina yake zaune da iyalinsa. 

I had been holding on, ina ta gayawa kaina cewa ba gaskiya bane ba, cewa ban rasa ki da gaske ba, but sai a jirgin nayi loosing din sauran hope dina. Gani nake yi na rabu dake kenan har abada and I couldn’t picture my life without you, gani nake babu wani sauran meaning a rayuwata. Daga airport maimakon gida sai asibiti aka wuce dani, ji nake kamar tsaga kirjina akeyi da wuka ana yankar zuciyata sala sala. Mahaifin da naci burin gani sai a asibiti na ganshi and the first thing da ya fada min shine “are you this weak? Do you really want to die saboda mace?” Nace “she is not just any woman. She is mine and they took her from me” yace “to me zakayi akai? Zaka kwanta ka mutu ne while tana can tana sabuwar rayuwa da wani ko kuma zaka tashi ka rayu and show them that abinda sukayi is wrong?” And I decided, maybe gwara in rayu din, maybe one day I will be able to see you again, and get you justice from whoever wrong you. 

But it was easier said than done. A watannin farko na aurenki I spent more time in hospital than at home. In ina gidan ma kuma ina daki a rufe. Bana kula kowa bana yi wa kowa magana. All I kept thinking about was you, you and you. Kullum tunani na a wanne hali kike ciki? Kinyi missing dina ko kuma kinyi accepting auren ki kin cigaba da rayuwarki da mijinki. Na kira Malam Iliyasu sai yake gaya min cewa Saghir yayi tafiya sai ke kadai a gidan tare da wata mata. And the agonizing months suka wuce, the most terrible times of my life. Ranar nan ina gida da rana kawai sai ga wayar Malam Iliyasu, nayi mamaki dan nasan cewa dare ne ku a wajenku na dauka sai naji cikin tashin hankali ya na gaya min wai baki da lafiya, shi yana ganin ma kamar kin mutu dan yaga maigidan ya dauko ki cikin jini ya saka ki a mota ya fita dake. Papa yana office dan haka message kawai na tura masa na dauki kudi da passport na tafi airport. Ban samu jirgi zuwa kano ba sai Abuja. Sai dana shiga Abuja sannan na samu wani zuwa kano ina shiga kano na kira Malam Iliyasu yace min shi bashi da wani labari tunda kuka fita shiru, sai na wuce gidan Alhaji Babba, na shiga har compound din gidan saboda yadda nake jin raina I was beyond caring akan me zai faru in aka ganni. Amma sai na tarar da gidan a hargitse, hankali na ya tashi and I asked wani mai kula da flowers sai yace min ai gobara ce Alhaji yayi duk shagunan sana’arsa sun kone kurmus babu abinda ya tsira dashi. Sai na tambayeshi game da matar Saghir, sai yace haihuwa ce kika yi amma yaran sun mutu, ke kuma an kaiki asibiti amma baisan wanne asibitin ba. Muna cikin magana Inna ta shigo gidan, ta wuce mu ba tare da ta ganni ba kuma na lura hankalinta a tashe yake, ta shiga cikin gidan ta sake fitowa sai na tura wanda muke tare nace yaje ya tambaye ta ya mai jiki? Anan naji sunan asibitin da kike, ana bukatar jini kuma ita ta rasa kowa duk gidan suna gurin Alhaji da yake asibiti shima. Sai na fice ba tare data ganni ba, na je asibitin da kike na nemo dakin da kike na shiga har ciki na ganki. You were sleeping, kamar allurar bacci aka yi miki. Kin kumbura sosai kinyi fari tas. I stayed a dakin for a while ina ganin kamar in na fita bazan dawo in tarar dake da rai ba but i knew dole inyi wani abu sai na tafi nace Inna ce ta turo ni in biya kudi kuma a dauki jini na, akwai wadda a gurin ta tambayeni ko nine mijinki and it pained me to say no. Aka gwada jini na and luckily sai yayi matching da naki” 

Na katse shi “wait, wai kai ka bani jini ranar nan a asibiti?” Yayi murmushi “naki fadar kaina ne saboda nasan yadda Inna bata sona zata iya cewa ba za’a karba ba dan kar in shafa miki maita or something like that”

Kullum ina zuwa in duba ki. Na tabbatar kina samun sauki sosai, ranar nan saura kadan Mama ta ganni na buya duk I doubt ko ta ganni ma zata gane ni saboda ni kaina nasan I looked terrible. Ranar nan nazo sai akace min a ranar za’a sallame ki. Sai na tsaya and I saw you sanda kuka fito, ke da Inna da Saghir da wadansu mata. Kuka shiga motar Saghir ke da Inna kuka tafi and I kept following you a kafa sai danja ta tsayar daku har na karaso inda kuke and I did what I shouldn’t have done, nayi miki magana”

Da sauri nace “I knew it. Nasan kai na gani amma inna tace wai aljanu ne suka bude min ido”. Yayi murmushi. Ban kyauta ba na sani bai kamata inyi wa matar wani magana ba but I did it. 

A ranar na koma Abuja daga nan kuma na koma Canada. A cikin jirgin nayi making decision cewa it is time to move on, tunda ke gashi har kin haihu, seven months after the wedding har kin haihu. Dan haka ina zuwa gida na samu Papa nace “am ready to move on yanzu” yace “good. Sai ka tafi makaranta kayi mechanical engineering dinka” sai nace “ina son karatu amma nafi son business, in yaso sai in hada da karatun da business din duka” yace zai saka ni a harkar Mai, but sai nace masa bana son aiki under him, I want something of my own, yadda zan making name for myself ba wai in jingina dashi ba. Na dauka zaiji babu dadi but sai naga yayi murna, yace wannan ya nuna masa how strong I am. Sai yayi signing check ya bani yace in cike kudin da nake ganin zasu ishe ni in kafa kaina. Na rubuta na mika masa sai ya yaga check din yace “wannan kudin da zan bawa wani ne in tazo neman taimako gurina. Ba kudin da zan bawa tilon dana ya kafa business ba. Sai ya sake signing wani ya miko min yace “multiply that by hundred, ka rubuta kaje ka karba. Allah yasa albarka a ciki”.

That was the beginning of Abatcha Motors. I chose Kano saboda in samu damar keeping eyes on you. Cikin few months aka gama komai na fara hiring ma’aikata. A lokacin ne Malam iliyasu yake gaya min cewa kuna cikin matsalar kudi dan yaga aba ta fitar da kayan gidan ana siyarwa. So, I talked to someone who talked to someone har aka gayawa Alhaji Babba cewa ga sabon company nan ana daukan ma’aikata and luckily shi kuma Saghir ya dauko takardunsa ya fito neman aiki a lokacin sai aka turo min shi. A gurin interview din dana yi masa ne na tabbatar cewa bai sanni ba. I gave him a job. Amma ba job bane ba dan baya ma cikin list of staff dina. Salary dinsa daban nake bashi and his salary was just like me giving you money. Ina bashi kudin dana san ya isa ya kula dake. 

Ina gab da komawa Canada ne sai yazo office dina yana ta complain wai matarsa ce zata haihu kuma doctors sunce ba zata iya haihuwa ba sai dai ayi mata aiki, gashi sunyo masa bill na kudi da yawa. I was scared kar yazo yaki biyan kudin ki zo ki samu matsala so I paid the money. Har na kara masa da kudin ragon suna da sauran hidima, ranar da za’ayi aikin na kwana ina miki addu’ar nasara, I wanted to go and see you but nasan hakan ba dai dai bane ba sai na hakura nace ya kirani in anyi and I asked him ya sakawa yarinyar Subay’a hoping hakan zai faranta miki ranki.

Daga nan na koma school. Carleton University of Canada. Anan nayi karatu tsahon shekaru biyar na fita da matsayin mechanical engineer. A wannan shekarun ne muka yi bonding sosai da yan uwana. My four sisters, Sa’adatu, Yani, Fanna da auta Adama, wadanda Papa ya bani task din koya musu hankali dan zaman kasar turawa ya saka duk sun koma suma kamar turawan. Yanayin shigarsu da yanayin mu’amalar su. I treated them with fire, but sometimes kuma sai inyi musu sanyi muyi ta wasa da dariya. Maman su kuma ta bani goyon baya sosai gurin koya musu hankali dan dama yanayin nasu duk yana damunta itama turancin ne yasa bata iya tsawatar musu.

All those years, nayi iyakacin kokari na dan ganin na cire ki a zuciya ta amma abin ya faskara. Nayi addu’a, nayi azumi nayi sadaka duk da wannan niyar, daga baya sai na saka a raina cewa wannan shine kaddara ta, zan rayu da sanki a zuciyata amma bazan rayu dake ba. Ban dauka cewa babu abinda ya ragu na sonki a zuciyata ba sai dana dawo, ranar da staff dina sukayi surprising dina da party, I saw you there, I tried pretending but then I saw him holding your hand and I couldn’t take it, nasan in ban bar gurin ba zan iya rufe shi da duka dan haka na gudu”

Then one day ina dakina na hotel ana ruwan sama, har na fara shirin bacci sai ga wayar Malam Iliyasu yace min mamanki da kanwarki sunzo gidan Saghir ya kore su, ga dare gashi ana ruwa yana jin tsoron kar wani abu ya faru dasu. I left everything na hau mota na taho unguwar ina tafiya ina dubawa, hankalina a tashe ina tsoron kar in zama too late, sai gasu nan kuwa na gansu already har sun fada hannun mugaye. I couldn’t imagine me zai faru da Asma’u idan da Allah bai sa Malam Iliyasu ya kirawo ni ba. That was when I decided to sue Alhaji Babba for garejin Baffa da filina. Tunda rashin mutumci suke ji I decided to show them rashin mutunci”.

“Wannan shi yayi stating chain of events din da har suka kai ga rufe Saghir”

“Ina so ki fahimci cewa ban rufe Saghir dan in aure ki ba. Yes, I loved you, I love you and I will take your love with me to my grave but da ace zaman lafiya kuke yi da Saghir da babu abinda bazanyi ba dan ganin cewa zamanku ya dore a tare. I would have given everything in dai zakiyi farin ciki. But after na fahimci irin zaman da kuke yi, after what he said a gaba na ba tare dako digon nadama a muryarsa ba, after ke da kanki kin gaya min cewa ba kya son komawa gidansa then I won’t let you. Yes, na barwa Saghir kudina intentionally saboda ina so ya dauka, saboda ina son in samu hujjar rufe shi yayi paying for abinda ya aikata. But I didn’t force his hands. Shi yayi making decision din dauka da kansa. And that’s what took him to prison bani ba”.

“Yanzu na dawo gurinki Diyam. Ina neman aurenki bisa yardarki. Yes, nasan shekaru sunja ba lallai ne kina da feelings for me a yanzu ba. Amma ina so ki fada min abinda yake ranki, in kika karbi offer ta ta aure I will surely be the happiest man on earth, in kuma kika ki karba I will be heart broken maybe fiye ma da wancan karon but I will respect your wish. Bazan matsa miki ba ba kuma zan bari a matsa miki ba”.

Ina jiran amsar ki.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button