NOVELSUncategorized

DIYAM 68

DIYAM Chapter 68
Save the Date

Yace “eh nasan tana da dalilin ta shi yasa ni kuma na
kasa zuwa in tuna mata. Am just scared Diyam, tsoro
nake yi kar a sake hana min ke a karo na biyu. Bansan me
zanyi ba wannan karon” tace “babu wanda zai hana mu

juna Aliyu. In har kaga ba’ayi ba to kuwa tabbas Allah bai
rubuta za’ayi ba. Waliyai na ne su amma basu kadai bane
waliyai na in sunki zamu iya zuwa Kollere mu……” Yace
“no, no Diyam. Ba su kadai ne waliyan ki ba amma sune
shakikan Baffa, kamar yadda kika fada haka ne Baffa zaiji
dadi idan muka sasanta tsakanin mu da su. Kuma ni ba
zanzo in zama sanadiyyar rabuwarki da yanuwanki ba but
am not going to give you up, not now not ever. Dan haka
zamu jira in ta kai ga cewa ni zan kuma durkusawa Alhaji
Babba zan durkusa din” sai ya dan yi dariya yace “the
table have been turning so past yanzu kuma na dawo ni
nake nema a gurinsa” ta taya shi dariyar sannan tace “in
lokacin durkusawar yazo, call me sai mu durkusa tare ni
da kai because we are in this together”.
Washegari sai ga wayar Mama. Ta gayawa Diyam duk
abinda sukayi da Alhaji Babba tace “na bashi wannan
damar ne saboda naga yadda yayi nadamar abinda yayi,
so nake ya nemi Sadauki da kansa ya gyara kuskuren da
yayi da kansa. Yanzu yace yana so kizo gari dan yana son
neman yafiyarki, sannan kuma yace kice da Sadauki ya
turo, in yaso sai a hada dana su Murja ayi gabadaya”
Diyam ta lumshe idonta tana jin wani irin farin ciki marar
misaltuwa a zuciyarta wanda har sai daya saka hawaye ya
taru a idon ta. Mama tace “kinyi shiru kuma, me zance
masa?” Ta dan goge hawayen idonta tana jin zuciyarta
fari kal kamar takarda, rabon data ji wannan feeling din
tun Baffa yana da rai, tun tana carefree teenager, tun
lokacin da Sadauki yake zuwa gurinta a school suyi ta
bayyana wa junansu abinda yake zukatan su.
Amma sai taji kunyar Mama tace “mun kusa fara exams
yanzu Mama, ba zan iya tahowa gida ba amma muna yin
hutu zan taho sai in samu alhajin, duk da dai ni na riga na
yafe masa tuntuni” Mama tace “to Allah ya bada sa’a.
Maganar Sadaukin fa?” Diyam tace “duk yadda akayi
Mama” Mama tace “ki gaya masa ya tura gurin Alhaji
Babba, sai asa rana tare daba su murjan. Yaushe kuke so
a saka?” Diyam ta sake yin shiru sai da Mama ta maimaita
sannan tace “duk sanda aka ce dai dai ne” Mama tace “in
aka saka lokacin hutun ku ai yayi ko?” Diyam ta sake yin
shiru tana murmushi amma a ranta tana lissafa kwana
nawa ya rage ayi hutun.Mama tace “shikenan tunda ba
zakiyi magana ba, shi bara in kira shi in tambayeshi” s
Suna yin sallama Diyam tayi saurin kiran Sadauki ta gaya
masa yadda sukayi da Mama, yace “tare dana su Murja
kika ce?” Tace “eh, haka tace min” ya girgiza kai yace “I
don’t like that. Nafi son ranar bikinki ya kasance all about
you not you and someone else, nafi son in an ganki ace
‘ga amaryar can’ kar ace ‘ga daya daga cikin amaren nan’
nafi son ki samu cikakkiyar kulawa daga kowa ba wai ki
samu divided attention ba. Dan haka zan gaya mata ayi
nasu first, later in an huta sai ayi namu”
Tun da ya fara magana take murmushi har sai daya gama
sannan tace “I don’t need attention din mutane, attention
dinka nake so, in nayi kwalliya ban damu da a yaba ko ayi
comparing dina da wasu ba as long as kai ka yaba as long
as a gurinka babu wadda ta kai ni. Besides, ni ba biki
zanyi ba, daurin aure kawai za’a hada da nasu, ni a gida
zanyi zamana kawai sai wanda ya shigo aka gaisa kawai
shikenan. Ban damu da having a big wedding ba as long
as kaine angon that’s all that matters, tunda nasan a
gurinka zan samu more than abinda na samu a wancan
auren” a can kasan makogwaron sa yace “more of what?”
Tace “everything” yace “like?” Tace “caring” yace “and?”
Tace “tunda nace everything ai ina nufin everything ko?
Sai na lissafa maka?” Yayi dariya yace “so nake ki fada da
bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke
nema da kanki” ta bata rai tace “abinda kake nufi fa ni ba
shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing”
yace “zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake
nufi” tace “ni ban san me kake nufi ba fa” yace “to in baki
sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke
ba?” Tayi rolling eyes dinta tace “good night Aliyu” yace
“ashe tsoro na kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana”
tace “ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school
gobe” yace “hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I
will still demand to know that ‘everything’ da kika fada, ko
ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you”.
Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana
kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe
idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa
yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune
sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan
ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da
zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma school, sai
ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar
su school yana neman weekend mai perfect date for their
wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday.
Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to
have a perfect birthday gift for his 30th birthday.
Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma
maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta
tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata
abinda Diyam tace mata “duk sanda aka saka dai-dai ne
Mama” ta tabe baki tace “ai shikenan, idan manyan sunzo
ayi magana dasu”.
Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu
Alhaji Babagana wanda yake kani ne a gurin Papa kuma
shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya
nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai
sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka
fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa
sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan’uwa suje su
hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka
gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya
keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi “kana ganin ba
za’a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon”
Sadauki yace “babu matsala in sha Allah, tunda wannan
karon ai sune da kansu suka nemi azo din”.
Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun
gurin yaya ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da
Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin
more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke
kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da
fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana
maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace “Diyam din
dai Aliyu?” Ya dago kai yana kallon ta yace “Diyam din dai.
Ko kina kishi ne?” Ta tabe baki tace “ni dai daka hakura da
Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik
ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da
gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar
da yan’uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta
mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?” Ya daga
kafada yace “ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in
anyi auren da ita zan zauna bada yan’uwanta ba” Hajiya
Dije, cousin din Yaya Ladi tace “amma duk da haka Aliyu,
ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka
kara da ita” sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a
hannu fuskarsa da murmushi yace “kar ku damu, bayan
anyi auren da sayi daya zan dawo nan sai in aure ku duk
ku biyun a rana daya” yaya ladi ta tabe baki dan tasan
shirishitar da maganar yake yi, tace “to ai shikenan,
uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura” ya
durkusa a gabanta yace “kisa mana albarka kawai ke dai.
Kiyi mana fatan alheri” ta dafa kansa tace “Allah ya sanya
alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade
duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri’a mai
albarka” yayi kyakykyawan murmushi yace “yanzu kika yi
magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina,
ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata”.
A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri,
aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da,
Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu
abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su
masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an
karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo
sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta
hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun
saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin
waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su
yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai
rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu
yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa
ba shida mahaifiyar sa?
Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da
dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar
Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa
ya gyara masa yace “dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne
kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi
dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni
amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu
aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da
damar” Alhaji Babba yace “mun bawa Aliyu auren Halima.
Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana” Alhaji
Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a
gaban Alhaji Babba yace “a shirye muka zo. Kuma munzo
da ranar mu amincewar ku kawai muke nema” sai ya fadi
ranar da Sadauki ya gaya masa, yace “lokacin yarinyar
tana hutu” babu musu kowa ya amince da hakan, sannan
suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai
kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi
musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar
tsokana dan mayar da abin wasa.
Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke
cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da
kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama
jakar da aka bashi yace “ga abinda suka kawo” Mama ta
bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace “wannan kudin
sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi
ba” Kawu Isa yace “nima dai naso ince haka, amma sai
naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru” Inna
tace “ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan
sun mika masa ne saboda shine Babba” Abban Rumaisa
ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin
tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace “tunda an riga an
karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta
saka musu ita mu kuma tayi musu addu’a shikenan”. Sai
Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi
sannan ya tafi.
Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message
“save the date. 25th August”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button