DIYAM 67
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Seven: The Inheritance
Diyam ta ajiye wayar tana tunani, sati biyu da suka wuce Inna tace anyi relocating gidan gonar, sati biyu da suka wuce lokacin Sadauki bai ma yi
winning bet dinsu ba. This means yayi abinda yayi ne on his own account ba wai dan yayi winning bet din ba. Shin hakan yana nufin Saghir yana da hope?
Washegari Sadauki ya koma Nigeria. A airport Diyam ta marairaice masa kamar zatayi kuka shi kuma ya rikice. “Ki taho mu tafi. Sai ki dawo next week” tace “school kuma fa?” Yace “share school din nan, ai baku fara exams ba” sai ta tuna sanda yake hanata zuwa islamiyya, tace “so kake ayi min bulalar fashi ko?” Yace “waye zaiyi miki bulalar? Gaya min shi in fara yi masa tun kafin yayi miki” tayi dariya kawai tana tuno jibgar da ta sha a gurin Saghir, sai tace “ni yanzu mai duka na ai sai dai ruwan sama, ruwan saman ma sai na tsaya” yayi kasa da murya yace “in kin tsaya din ma I will shield you from it, like an umbrella” sai ta tuno sanda Inna ta kama su suna saukowa daga sama tazo zata dake su ya kare ta shi akayi ta dukan sa. He had been shielding her all his life. Ya katse mata tunanin ta ta hanyar langwabe kai yace “Please kizo mu tafi” ta makale kafada tace “naki, sai dai ka zauna anan” yace “ai kinsan maganar da zata mayar dani Nigeria. So nake fa ayi lokacin hutun ku sai mu dawo tare” ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, sai kuma tace “Inna ta gaya min zancen Alhaji Babba. An gode madallah Allah ya kara arziki” yace “ameen” sai kuma ya dauke kansa gefe kamar yana tunani yace “ina yammatan gidan? Su Murja kawarki wadanda kika yi min maganar su rannan akan har yanzu basuyi aure ba?” Diyam tace “suna nan. Muna waya da Murja ma. Wani abin ne?” Yace “ya maganar auren nasu” tace “suna jira dai. Last wayar da muka yi tace min zata tura saurayinta gurin Baba Sa’idu (mijin anty Fatima)” yace “idan kun sake waya kice mata zakiyi musu kayan daki, ita da sisters dinta” ta bude baki tana kallon sa yace “ke ba yayarsu bace ba, ke zakiyi musu kayan daki ai” ya dauke kai yace “in place of their brother”.
A kano bayan Sadauki yaje gurin Mama yaje ya gaya mata sun daidaita da Diyam, sai kuma ya nemi shawarar ta akan abinda ya dace yayi next. Sai ta nuna jin dadin ta sosai tace “ko ku fa, ai hakan yafi muku akan wannan zaman jiran da da kuka ce zaku yi” ya shafa kai yana murmushi. Tace “to yanzu abinda za’ayi shine zanje ni da kaina in samu Alhaji Babba, in yaso sai ya fadi ranar da za’a je a same su kai kuma sai ka fada a can gida sai su zo” yace “da nayi tunanin ko Kawu Isa, saboda kar a samu matsala da Alhaji Babba” Mama ta girgiza kai tace “babu matsala insha Allah. Shine Babba dan haka dole a bashi girman sa in ya karba shikenan in bai karba ba in yaso sai a je wani gurin a nema” suna cikin maganar sai Mukhtar yazo, suka yi hannu da Sadauki, Sadauki yace “ka yar dani Mukhtar, ko nema na bakayi” Mukhtar yayi dariya yace “ai ka zama yallabai ne yanzu, ka zama hukuma sai da lallashi” Sadauki yayi murmushi yace “sharri zaka yi min kenan ko? Zan samu time zaka ganni har gidanka”.
A Oxford da Diyam taje school sai taji babu dadi saboda ganin seat din Bassam empty. But sai taji dadi dan hakan yana nufin ya tafi gida kenan, ya tafi yaje ya gyara tsakanin sa da family dinsa. She just hope ba zai dade sosai ba saboda kar karatunsa ya samu matsala.
Kamar yadda Mama tayi alkawari, washegarin da Sadauki yaje ya same ta sai ta tafi gidan Alhaji Babba. As usual, bata ji dadin yadda ta samu gidan ba duk da dai a yanzu matan gidan sun fara yan sana’o’i, Hajiya Babba tana siyar da ruwan sanyi, lemo da kankara. Hajiya Yalwati kuma tana yin snacks, da wannan sana’ar suke kokarin ciyar da kansu da yayansu dan Alhaji Babba har yanzu kusan dashi da babu duk daya a gidan sai ma jigilar asibiti da suke tayi dashi, shi bai mutu ba shi kuma bai cigaba da rayuwa normal ba.
Taje suka gaisa da matan gidan sannan ta tafi dakin Alhaji. Yana nan har yanzu a dakin da Inna ta zauna bai koma part dinsa ba duk kuwa da cewa Sadauki ya saka an gyara part din tas batan an kwashe kajin. Ta gaishe shi ya tashi daga kwancen da yake ya amsa mata yana tambayarta lafiyar family dinta, kafin ta gabatar masa da abinda ya kawo ta sai cewa yayi “Hafsa ina Diyam, har yanzu bata zo gari ba?” Mama tace “bata zo ba. Basu samu hutu ba ai” ya mayar da kansa ya kwantar yace “Diyam yarinyar kirki ce mai son zumunci. Fatima ta gaya min abinda tayi wai taki auren shi wannan yaron da take ta nacin so tace lallai sai ya fito da Saghir tukunna zara aure shi. Banyi tsammanin haka ba, na dauka in ta juya bayanta ta bar Saghir a prison ba zata sake waigen inda yake ba, na dauka in ta samu cigaba a rayuwa ba zata sake tunanin halin da muke ciki ba. Ina so inga Diyam Hafsa, ina son in roki gafarar ta tun kafin lokaci na ya kare a duniya. Ina kuma son in roki gafarar Saghir. Ko ma menene Saghir ya zama ko ma menene Saghir yayi ko ake zargin yayi to laifi nane, nine na lalata rayuwar dana mafi soyuwa a zuciyata duk a tunanin soyayya ce nake nuna masa. Ina sane, ina sane da duk abinda Saghir yake yi nasan yana yi din amma sai in rufe idona in nuna tamkar ba zaiyi dinba saboda ina so in gaya wa kaina cewa ba zaiyi din ba. Banyi nadama a bisa tarbiyyar da nayi wa Saghir ba sai da na je gidan yari na ganshi tukunna” yayi shiru yana kokarin saisaita muryarsa saboda kukan da yaji yana neman ya kwace masa. Mama ta fara bashi hakuri “sai hakuri Alhaji, komai mukaddari ne komai rubutacce ne” yace “haka ne, amma komai yana da sila. Silar lalacewar Saghir kuma shine rashin tarbiyyar dani da mahaifiyar sa muka gaza bashi. Ba kuma mu tashi ganin sakamakon abin ba sai da ya zama babu abinda zamu iya yi akai. Bani da yadda zanyi in fito da Saghir daga inda yake, bani da kudi ko hanyar samun kudin da zan biya yaron nan kudinsa sannan bani da karfi na jiki dana aljihu da zan samo wannan yaron daya lika masa wadannan kwayoyi”
Yayi shiru yana tunani sannan yace “Hafsa, idan kunyi waya da Diyam ki nemar min gafararta dan ban tabbatar da zanyi tsahon ran ganin ta in roke ta da kaina ba, sannan kuma ki ce ina rokon alfarmarta akan ta janye waccan maganar ta kin cikawa kanta burin zuciyarta na auren Sadauki, ta aure shi indai tana sonsa, shi kuma ruwansa ne ya yafe wa Saghir ko kuma yaki yafe masa wannan zabin sa ne”.
Sai Mama taji dadi, dan haka sai ta rufe maganar sasantawar da aka samu tsakanin Sadauki da Diyam dan tana son alhajin ya ji dadi a ransa ya dauka tamkar shi ya sasanta su din, dan haka ta ki shigar masa da maganar auren da niyyar sai bayan kwana biyu sai ta dawo ta sake shigar masa da maganar. Ta kuma yi masa alkawarin kiran Diyam ta gaya mata sakonsa.
Sai dai tana mike wa sai ga Kawu Isa ya shigo dakin hannunsa rike da jariri. Ya wuce ta yaje chinyar Alhaji Babba ya ajiye masa yace “ga sakon Saghir nan. Nayi masa huduba da sunanka dan haka ina yi maka murna ka samu takwara” ya juya da sauri ya wuce Mama ba tare da ya kula mai take cewa ba ya fita. Ta juyo ta dawo gaban Alhaji tana kallon jaririn da take kwance kan cinyarsa yana ta jujjuya kai da alama abincinsa yake nema. Ko ba’a yi mata bayani ba ra fahimci cewa Suwaiba ce ta haihu kuma wannan shine dan gaba da fatihar data haifawa Saghir. Ta saka hannu ta shafi kan yaron tana kallon fuskarsa mai kama data Subay’a. Tace “Allah yayi maka albarka” Alhaji ya dago kansa daga kallon yaron shima yace “ameen. Ki kira min Hajiya Saratu a ciki”. Ga dai jika nan namiji Alhaji da Hajiya sun samu amma kuma shege.
Kafin Mama ta baro gidan sai data yi ta zarya zuwa gidan Kawu Isa akan ayi hakuri a mayar da yaron nan hannun uwarsa amma Kawu Isa yace sam bai san wannan maganar ba “ba zata shayar dashi ba” ya fada ya kuma maimaita wa. Ko samun ganin Suwaiba Mama bata yi ba, daga baya ma ta tabbatar bata gidan dan haka ta hakura amma tace “yaron dai jikan mune gabaki daya, kuma shi bashi ne yayi laifi ba dan haka bai kamata a hukunta shi akan laifin dashi bai san ma sanda aka aikata shi ba. Rashin shayar dashi ba zai goge cewa Suwaiba ce ta haife shi ba”.
Sai taje ta siyo baby formula da feeder ta dawo ta kawo wa Hajiya Babba. Ta tarar da ita ta goya dan jaririn da ya rare baki yana ta kwarara kuka. Ta mika mata tayi mata barka sannan ta koma tayi wa Alhaji sallama, sai yace “ki turo min Amina dan Allah” daga haka sukayi sallama.
Bata koma gida ba kuwa sai da ta je gurin Inna, ta fada mata duk yadda sukayi da Sadauki da kuma yadda suka yi da Alhaji da kuma abinda ya faru a gidan alhajin. Inna duk ta tayar da hankalinta nan take washegari ta dauki kudi ta shirya ita da Asma’u da Subay’a taje tayo siyayyar kayan babies sukaje gidan Alhaji Babba, ta kaiwa Hajiya Babba ta kuma yi mata barka ta dauki yaron da yasha madarar sa yana ta baccinsa tayi masa addu’a sannan taje gurin Alhaji.
Bayan sun gaisa yace mata “Amina idan kun yarda ke da yayanki ina so za’a zo a raba gadon usuman” Inna ta kalle shi da mamaki tace “wanne irin rabon gado kuma Alhaji?” Yace “an raba ne? Ai har yau ba’a raba ba. Kuma taba kudin da nayi ne ya haddasa min duk masifun da suka same ni. Tun da na shigo kano na fara neman kudi nake samun sa’a da nasara a rayuwata ban taba cin karo asara ba sai dana bi son zuciyata na taba kudin gadon nan. Kuma har yau ban biya ba, wannan shi yasa duk abinda nake dashi bashi da albarka, duk harkar neman kudi bana tarar da komai a ciki sai asara. Wannan kuma a duniya ne kadai, idan har ban biya ba to azaba tana can tana jirana a lahira. Na sani sarai, ina sane da duk abinda nakeyi son zuciyata kawai nake bi shi yasa na kasa gyarawa amma yanzu alhamdulillah rayuwa ta bani wata sabuwar damar gyara kurakurai na guda biyu. Zan fitar da hakkin usuman da yake kaina sannan kuma zan gyara kuskure na na tarbiyyar Saghir akan wannan yaron da aka haifa masa”.
Inna tace “mu ai Alhaji mun riga mun yafe maka rabon mu ni da yara da yake cikin abinda ka dauka, shima kuma Sadauki yace ya yafe kason mahaifiyarsa, sannan kuma ai kaima da sauran yan’uwa kuma da rabo a ciki sannan…..” Yace “muna dashi, hardo yana dashi, hatta yaya ladi mahaifiyar Zainab tana dashi. Yanzu bayan mutuwar hardo matar daya aura kafin rasuwarsa tana dashi. Mutanen da suke da hakki suna da yawa, wannan yafiyar ba zata sauke min nauyin nan ba”.
Tayi shiru tana lissafa maganar sa, sai yace “ina so azo ayi rabon gadon a bisa ka’ida. Zan bayar da complete kudin dana dauka, sai ayi wa gidan da kuke ciki kudi sannan a raba a bisa tsarin da addini ya tsara a bawa kowa rabonsa ko zan samu rayuwa ta dan sassauta min kafin in bar duniya kuma in samu sassauci a lahira” tayi tagumi tace “to a ina zaka samu kudin nan Alhaji?” Yayi murmushi yace “nan gidan da muke ciki shine kadai abinda ya rage min a duniya. Shi zan siyar. Kollere zan koma in cigaba da rikon sarautar da hardo ya mutu ya bari muka ki karba. Sauran abinda yayi min saura kuma sai in samu sana’ar yi a can wadda zata rike min iyalina a can din”.
Inna ta girgiza kai tace “ba zai kai ga haka bama Alhaji, insha Allah ba zai kai ga haka ba”.
Wasa wasa abu ya tabbata. Inna ta kira Diyam da Sadauki ta gaya musu abinda duk ake ciki, farko Diyam ta nuna rashin yardarta amma sai inna ta gaya mata cewa hakan shine dai dai “shima marigayin wannan wani sauke nauyi ne akayi masa”. Aka yiwa gidan Baffa kudi, a take Sadauki ya siya. Aka kuma yiwa gidan Alhaji Babba kudi aka siyar, ana siyarwa Diyam ta aiko da kudi tace a kama musu ko rent ne su zauna kafin komai ya zama settled. Sannan Alhaji Babba ya ware kudin garejin Baffa daya siyar aka hada da kudin gidan Baffa aka raba kudin cash, kowa aka danka masa nasa a hannunsa hatta amaryar da hardo yayi kafin rasuwarsa sai da aka fitar mata da nata a cikin kason Hardo aka aika mata dashi har Kollere.
Babu yadda Alhaji Babba baiyi ba akan son komawa Kollere amma yaya da yan uwa suka saka shi a gaba akan lallai ba zai koma ba. Dole ya zauna a gidan da Diyam ta aiko da kudi aka kama masa haya a unguwar Jaeen, suka koma gabaki daya shida iyalinsa. A lokacin ne kuma Diyam daga can ta aiko da kudurinta na son yiwa kannen Saghir su hudu wadanda suka isa aure kayan daki. Sai Alhaji Babba yace “ku gaya mata tazo sai a hada auren tare da nata”.
A bangaren Sadauki, yana ta son ya tunawa Mama da maganar da suka yi amma kunyar ta yakeji, sai yayi ta cewa Diyam wai ita ta kira Mama ta tuna mata, tayi dariya tace “wato nice marar kunya ko? To babu ruwana, tunda kaji tayi shiru tana da dalilinta”.
Sorry for keeping you guys waiting. Biki things. Enjoy your week.