DIYAM 7
By
Maman Maama
Episode Seven : The Phone Call
Tun daga ranar Diyam da Bassam suka hade, kullum a school suna tare duk ya
daina kula friends dinsa ita kuma dama bata dasu, daga school kuma zai wuce gurin aikinsa, anan zai samu kudin kashewa gobe. Sosai yake jin dadinsa hankalinsa kwance as if bashi da wani problem.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ranar Thursday suna lunch a cafeteria kamar kullum, Diyam ta tambaye shi “can you tell me about that not laughing situation da kace kana ciki? Because I can see yanzu kana dariyar” dariyar yayi sannan kuma ya hade rai yana jujjuya abincin gabansa yace “I got fired” ta zaro ido tana mamaki, fuskanta cike da concern tace “daga gurin aikinka? When?” Yace “no, ba daga gurin aikina ba, I got fired from my family” ta hade rai tace “your family? Ta yaya za’ayi familyn mutum su kore shi? Me kayi Bassam? What happened?” muryarta tana breaking kamar zata yi kuka ta tambaye shi, ba tare daya kalleta ba yace “nayi laifi, babban laifi, maimakon in tsaya in fuskanci hukunci na kuma sai na gudu na kama daki a hotel nayi zamana. When I did that na saka ran kwana biyu ba zasu wuce ba mami na da Daddy na zasu zo kasar nan, nayi tsammanin zasu zo har dakin da nake, nayi tsammanin karbar wadansu kyawawan mari daga Daddy na kuma yi tsammanin in samu nasiha daga mami amma shiru, basu zo ba ballantana su fada min cewa nayi ba dai dai ba ballantana su kaini gurin Aunty na da nayi wa laifi su saka ni in bata hakuri” ya dago ido yana kallonta cikin ido yace “basu zo ba ba kuma su kira ni ba, they just cut me up, basu zo ba ballantana suyi min maganin problem dina, at least ko shawara ce su bani”. Tana kallonsa tace “wanne problem ne kenan? Your smoking problem?” Ya girgiza kai yace “basu san wannan ba ai” sai kuma ya bata labarin feelings dinsa for Khausar, da kuma yadda ya tarar tana dating cousin dinsa Ayan, tun daya fara bata ce komai ba har sai daya gama sannan tace “how old are you Bassam? You know nothing about love, do you? That girl doesn’t love you, cigaba da jan magana tsakanin ka da ita ba abinda zai yi sai bata zumuncin dake tsakanin ku. Kuma ni a fahimtata familyn ka ba wai cutting dinka off suka yi ba, suna keeping tabs on you tabbas tunda su suka haife ka and they love you. They just want you to grow up, they want you to make the right decision by yourself daga nan sai su san hukuncin da zasu yanke maka. Kafin Mami da Daddy su zo su baka shawara ni ga tawa, ka koma gurin auntyn ka wadda kayi wa laifi kaje ka bata hakuri on your on ba wai sai ance maka kaje ba, ka bawa cousin dinka hakuri kuyi shaking hands kabar maganar Khausar, you don’t know what God has planned for you”.
Yayi murmushi yace “I guess you are right, maybe wadda zan samu nan gaba tafi Khausar komai” ya karashe maganar yana kashe mata ido daya. Tayi saurin dauke kanta tana jin zuciyarta tana bugawa da karfi. A take taji abincin ya fita daga kanta, ta ture plate din ta mike tace masa zata je class in ya gama ya same ta a can, ya bita da kallo har ta fita yana mamakin me ya chanja mata mood.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A ranar haka ta wuni tana jin ranta babu dadi, kar dai abinda take tunani akan Bassam haka ne, kar dai he is developing feelings for her, kar dai abinda Murjanatu ta fada rannan gaskiya ne, cewa she is playing with fire. Tana zuwa gida ta tarar da abinda yafi wannan daga mata hankali. Murjanatu ta gani zaune ta zuba uban tagumi, ya yarda jakar hannun ta ta zauna a gabanta cike da concern tace “Fanna? Lfy?” Ta dago tana kallonta tace “yaya ya kira yanzu, wai in gayawa Judith ta hada kayanta ta bar gidan nan kafin weekend” Diyam ta mike “au wai har yanzu bai bar maganar Judith ba? Me ta tsare masa? Akanshi take zaune? Ni ba zan iya korar Judith ba tunda babu abinda tayi min, dama baki gaya masa sakona na ranar nan ba?” Murjanatu tace “ni na ce miki bazan iya gaya masa ba Diyam tsoro nake ji” Diyam tace “mala’ikan mutuwa ne shi da zaki ke tsoronsa?” Daga haka ta figo wayarta daga cikin jaka and for the first time tun zuwan ta kasar ta danna number dinsa, bugu daya ya dauka, bata ko saurare shi ba ta fara zazzaga bala’i “wanne irin mutum ne kai wai? When will you stop playing god? When will you stop making decisions a rayuwar mutane? This is my life and I asked you to stay out of it” I nutse yace “Diyam….” Ta katse shi “kar ma ka gwada yimin dadin baki, bazan kori Judith ba and that is final” yace “am sorry dear, I was just trying to..” tace “trying to protect me? To kayi hakuri but I don’t need your protection” ya sake cewa “I was just trying to…..to provoke you into calling me” sai ya kyalkyale da dariya. Ta tsaya tana kallon wayar da mamaki, sannan ta kalli Murjanatu taga ta durkushe a kujera tana ta kyalkyala dariya harda rike ciki, sannan tayi realising abinda ya faru.
Ta jefar da wayar kamar wadda aka ciza sannan ta dafe kanta da hannu biyu tace “oh God, Murjanatu what have you done?” Da gudu Murjanatu ta mike ta shige daki tana dariya ta rufo kofa. Diyam ta zauna akan kujera ta dauki wayar da har yanzu take a kunne tace “this is cheating” har yanzu da dariya a muryarsa yace “kin tuna abinda kika ce min ranar da zaki bar Nigeria? Kin tuna alkawarin da muka yi dake cewa in dai kika dauki waya da hannunki kika kira ni to nayi winning, zan yanke duk hukuncin dana ga dama” ta sake cewa cikin raunanniyar murya, “but this is cheating” yace “in life, my dear, cheating is allowed once in a while” sannan ya kuma dariya yace “see you on Saturday” ya katse wayar.
Ta kife kanta a kujera tana jin hawayenta yana jika kujerar, sai da tayi kukanta ta gama sannan ta dago ta dauki wayarta ta tura masa message
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“You always claimed that you play your games fair and square, but this is not fair”
Bayan yan mintina reply ya shigo mata
“Nothing is fair my dear, life in itself is not fair, you just have to be smart and have eyes like an eagle’s so that you won’t get cheated on. My regards to your lips”.
Comments dinku suna kadan, shi yasa typing yake kadan