NOVELSUncategorized

DIYAM 70 & 71

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episodes Seventy & Seventy One : The Wedding

The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah’s wish is 100%. Wanne ya
kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne? 

Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur’ani da Azkar, mu  yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma’aikatan lafiya suka kafa.

Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.

Diyam……………

Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri’ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.

Tayi masa kyakykyawan murmushi tace “hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci” yace “Ameen, Mrs Abatcha” ta harare shi, “bana so” yace “okay, madam kike so?” Ta mike tsaye kamar zata yi kuka “bana so wallahi” ya mike shima yana mata dariya “gaya min to, me yasa ba kya so?” Tace “sai in ji na zama kamar wata katuwar ƙedara, wai Madam” yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace “to me kike so ince miki?” Ta juya ido tace “Diyam” yace “Sadiyam” tayi masa gwalo tace “sholoki” sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay’a tana waigensa. Ya daga murya yace “zan kama ki ne ai, not now but on the 25th” bata waigo ta kalleshi ba but she blushed. 

Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa “time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu” Diyam ta mike straight tana cewa “Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai” ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay’a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan.

A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay’a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma’u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace “ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari” kafin tayi masa godiya sai yace “birth year din ki shine pin din” ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace “bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki”.

Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa “kar ki karya ni” Asma’u ma ta kankame ta tana cewa “nayi missing dinki, sosai Adda ta” Diyam ta kalleta tace “oh, Asma’u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja” Asma’u ta fara buga kafa tana cewa “shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina” ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa “yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?” Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma’u yake kamar wata jaririya.

Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba’a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma’u da Subay’a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama.

Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace “sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba”. Tare da Asma’u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al’umma for his misfortune. Da fara’a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa “munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?” Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri “Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu” yace “ameen” ya dora da “ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa” ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. “Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba”.

Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam. 

A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace “Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?” Sai ya girgiza kansa yace “uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama’a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri’ar da zasu fito daga gareta?” Diyam tayi shiru tana tunani sai tace “Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?” Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace “yaushe Saghir din zai fito?” Diyam tace “very soon, insha Allah” sai yace “Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu”.

A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace “Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?” Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace “Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad” Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da ɗa musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba’a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba.

Sai Diyam tayi tunani akan lalacewar zumuncin zamani. Babban dalili a fahimtarta shine son kan mu da muke dashi da kuma nuna son yayan mu a fili. Yes, an sani kowa yana son dansa amma hausawa sunce kaso naka ne duniya ta kishi ka kuma ki naka duniya ta so shi. Duba misalin uwa in ta kama danta tana duka idan yayi laifi, sai kuga mutane sun tafi da gudu sun karbe shi a hannunta suna bata hakuri suna kuma lallashinsa. Amma idan da ace zaiyi laifin ta goyi bayansa ta nuna cewa ba laifi yayi ba sai kuga mutane suna yi musu tsinuwa daga ita har shi. Daga nan kuma zasu fara ja baya dasu, zasu yanke zumunci dasu, in yayi laifin ma babu mai kwabar sa babu mai hana shi. Wannan tsarin na daga ni sai yayana shine tsarin daya tarwatsa zumunci. 

A gidan Mama suka kai har dare. Diyam ta tambayeta shawara akan kayan dakin da zata yiwa su Murja, shin ta siya musu kayan ne ko kuma ta basu kudi kowa ya siya da kansa? Sai Mama tace “ina ganin ki sai musu furnitures, sai kuma ki basu kudin da zasu sai sauran kayayyakin anfaninsu tunda kowa da irin taste din ta” nan suka yanke shawarar irin kayan da za’a siya da kuma adadin kudin da za’a basu. Sannan Mama tace “to ke kuma fa? Menene naki shirin?” Diyam ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta. Mama tace “ba kunya zaki tsaya ji ba fa, magana zaki yi sosai. Dan ba kya gari ne da tuntuni ya kamata a fara yi miki gyaran jiki da sauran abubuwa. Amma tunda kin dawo yanzu zamu fara insha Allah. Kinga akwai tsumin Maman Fareeda shine gatan da ake yiwa ko wacce amaryar da za’ayi aurenta a yanzu, ko matan auren ma zasu iya amfani dashi, very pure and natural babu algus. Ga number dinta nan zan baki ki kirata kiyi order zata kawo miki har gida kiyi ta sha kuma sai ki ajiye number din daga baya ma kya cigaba da karba” ta karantowa Diyam number din kamar haka “07033742833”.

Sai kuma ta nemi Diyam ta sanarwa da Sadauki cewa zasu zo ganin gida ita da Aunty Fatima dan su san yawan kayan da za’a siyo. Amma da daddare da Diyam tana waya da Sadauki ta gaya masa sai yayi dariya yace “wanne kayan za’a siyo? Ki ce musu suyi hakuri nayi musu shigar sauri har na bayar da order kayan gida gabaki daya, za’a sa komai da komai, sai dai in an gama sakawa sai suzo su gani in akwai gyara suyi mana” da Diyam ta gayawa inna sai ta kama fada “wannan wanne irin abu ne? To wannan kudin da suka kawo a cikin jaka kuma me zamuyi dashi?” 

Rumaisa tazo har gida suna maganar gyaran jiki da Diyam. Tace “akwai Hajiya Hannatu Sokoto, mutuniyar Sokoto ce amma ta zauna a sudan dan haka ta iya gyaran jiki sosai kuma duk kayan ta ma daga sudan take zuwa da abinta, nima wata matar abokin abban Najma (babynta) ce take bani labarin ta, aikinta akwai tsada dan matan manyan mutane kadai suke iya hiring dinta amma kuma fa akwai kyau dan saita mayar dake tamkar jaririya, Sadauki kuwa in ya shigo hannun ki to kuwa ya kade har ganyensa” ta karashe maganar tana dariya. Diyam ta dungure ta, sai kuma tace “to kisa a hada ni da ita mana” Rumaisa ta harare ta tace “au, na dauka ai ba kya so”.

Tunda aka hada Diyam da Hannatu Sokoto shikenan komai ya chanja mata, matar ta karbi kudade da yawa a gurin Diyam amma fa tana fara aiki akanta, Diyam tasan cewa she is worth it. Kullum sai tazo kuma kullum da kalar gyaran da take yi wa Diyam. Tun daga kan gashin kanta zuwa faratan yan yatsun hannayenta da kafafuwanta babu abinda gyaran bai shafa ba. Yau a shafe ta da wancan a wanke da wannan gobe a saka ta tsugunna akan wancan turaren jibi kuma a bata wannan ace ta liƙa ta kuma yi tsarki da wancan. Gata kuma a jika ta gabaki dayanta a wanke ta. Har bakin Diyam sai da akayi masa gyara na musamman yadda zai bada wani sihirtaccen kamshi. Ga kuma tsumin maman fareeda (07033742833) da Diyam ta kira aka kawo mata shi har gida, wanda tana sha sau daya ta tabbatar wannan bana wasa bane ba dan haka tayi wa number din kyakykyawan ajiya dan gaba.

A gefe guda kuma tayi dinkuna na fitar biki. Duk da dai ita har yanzu tana nan akan bakanta na cewa ba zata yi taro ba, wanda inna zata yi kawai ya wadatar.

Sadauki kuma a nasa bangaren baya samun zama sam. Kullum yana cikin zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Kano. Family dinsa duk sun taho daga Canada suna Maiduguri suna nasu shirin. Kamar yadda Murjanatu ta fada, lokacin da suka gabatar masa da jerin events din da suke son yi na biki sai yace “no, kuyi parties dinku ku kadai amma ni ba za’a fitar min da mata ana tallata ta a duniya ba” duk suka juya suna kallon Murjanatu ita kuma ta daga kafada tace “I told you so”. Abinda kawai Sadauki ya yarda za’ayi shine wushe-wushe, wanda yake bikin al’ada na kanuri. Sai mother’s eve da Mama zata yi washegarin kai amarya dan a nuna wa yan uwa amarya itama kuma ta san su.

On impulse Diyam ta kira Humairah, matar yayan Bassam ta tuna mata zancen bikinta. “Ban sani ba ko zaki samu zuwa?” Humairah tace “what are you talking about? Zan zo mana, ai ina lissafe da lokacin dama already na tambaya har an barni ma. Insha Allah kwana ma zanyi tare dani za’a kai ki gidan Mr Abatcha” sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Ana bugo kati Diyam ta sake tura mata, sannan kuma ta tura mata na daurin aure tace “ki nunawa Bassam ko zai samu damar zuwa”.

Satin biki yazo, su Mama sunje sunga gidan Diyam kuma babu abinda suka gyara saboda babu abin gyarawar, sai dawowa da sukayi suna rike baki suna bada labarin aljannar duniyar da suka gani. Mama tace “har Subay’a anyi mata dakinta, da set din gadonta da komai na bukatar ta”. Ranar talata Diyam tayi baki, Sa’adatu, Falmata, Fanna da Adama gabaki dayan su da akwatinan su “tunda yaki yarda muyi dinner da luncheon da bridal shower da cocktail party gwara mu dawo gidan su amaryar mu zauna muyi ta kallonta” inji Murjanatu tana turo baki. Diyam tayi murmushi tana taryen su with open arms, da alama shi kansa yayan nasu bai san da zuwan su ba tunda bai gaya mata ba. A ranar ne sauran sisters din Sadauki suka fara ganin Diyam a zahiri, gashi kuma dama tasha gyara sai abun yayi musu duka biyu. Adama tace “gaskiya pictures basa yi miki adalci Diyam, you are much more beautiful in person” Murjanatu ta kama hannunta tana shafawa tace “what’s the secret? So kike ki kashe min yaya na ko?”.

Part din Ummah Inna tasa aka shirya musu aka yi musu shimfidu aka saka musu duk abubuwan bukata sannan aka kai musu kayansu can suka sauka. Sai Diyam itama ta koma can tare da Subay’a da Asma’u suka barwa Inna da yan uwanta da suka fara zuwa daga Kollere part dinta. Wasa wasa sai ga gida yana kara cika. Kusan duk wanda yazo daga Kollere sai yace a nan zai sauka, da Asma’u ta tambayi wata mai yasa basa tafiya gidan Alhaji Babba shi da yake auren yaya hudu? sai tace “haba yar nan, kowa ai yana son dan maiko maiko ko?” Jin haka yasa Inna ta aikawa da Hajiya yalwati kudi da kayan abinci tace saboda baki.

Kamun amare (su Murja) an saka shi ranar Alhamis, juma’a kuma angwaye sun shirya dinner su da amaren su da kawayen amare. Assabar za’ayi daurin aure, wanda shine za’a hada dana Diyam, Alhaji Babba ya bawa Kawu Isa waliccin yaran duk su hudun shi kuma zaiyi waliccin Diyam. Ranar assabar din ne kuma za’ayi yini sannan da daddare akai amare.

A bangaren Diyam kuma babu kamu, babu dinner, sai wushe-wushe ranar friday sai daurin aure assabar da safe sannan inna tayi yinin ta anan gida da daddare kuma akai amarya. But, ranar laraba sai ga mutane daga Maiduguri wai sunzo kawo kudin cin-cin, aka tarye su sosai aka kuma karrama su amma kuma akayi ta mamakin wannan al’ada ta cin cin. Mama tace “to yanzu cin cin din zamu zo mu soya ko kuma me?”.

Alhamis da safe Hannatu Sokoto tayi wa Diyam kunshi ja da baki mai dan karen kyau, sannan kuma tayi mata kitso shuku kanana kanana, duk a cikin aikinta ne. Da yamma Diyam ta shirya tayi simple kwalliyarta cikin atamfa riga da plain zani ta dauki in-laws dinta suka tafi gidan aunty Fatima inda a can ne za’ayi kamun wadancan amaren. Amma Diyam tana zuwa sai kallo ya koma sama, kowa ya kalle ta sai ya sake waigo wa “wai Diyam ce wannan?” “Diyam ke ce kuwa?” Har sai data gaji dan haka kafin a gama ma ta gudo ta dawo gida. Tun a daren Sadauki ya gaya mata zasuyi baki washegari.

Washegari Friday, da wuri Humairah tazo gidan, hakan ba karamin faranta ran Diyam yayi ba. Suka hadu da Rumaisa, Rufaida, su Murjanatu da kuma Asma’u. A ranar Kasusu (yan uwan ango) suka zo gari, gidan Alhaji Bukar suka sauka, daga nan kuma suka taho gidan su Diyam kawo kayan gaisuwar uwar amarya. Set guda akayo wa Inna na kaya tamkar wanda aka hado mata lefe, sai kuma kayan kunshi iri iri wadansu ma ko sunan su su Inna basu taba ji ba. Su kuma anan gidan suka hada musu goma sha tara ta arziki na nau ikan kayan ciye ciye, fura da nono kam ba’a maganar ta saboda tambarin su na fulani, sai gurasa ita kuma shedar su kanawa ne, sai kuma sauran abinciccika da kala kalar nama da drinks har sai da suka ci suka bari suka kuma yi takeaway. Da zasu tafi suke tsokanar su Sa’adatu “wato dan kunyi yaya shine kuka tare anan? To sai ku bita har gidan mijin kuyi mata zaman daki” Asma’u tayi saurin cewa “nice yar zaman daki ai”.

Daga nan kuma sai aka fara shirye-shiryen wushe-wushe (bangajiya). A gurin taro na Meena event center anyi decorating gurin da traditional costume na barebari. Falmata, wadda take registered beautician ita ce ta zauna ta tsarawa Diyam kwalliya sannan suka nannade ta da flowery laffaya mai kalolin red and blue. Su kuma yammatan duk sunyi kwalliyar blue shadda da akayiwa dinkin riga three quarters da skirt, sai kuma suka yafa jan mayafi. Duk abinda suke yi Diyam tana jin sune kawai, amma ita hankalinta yafi tafiya ne akan murnar yau zata ga Sadauki, dan rabonta da ganin sa tun ranar Monday daya tafi Maiduguri zai taya Papa shirye shiryen saukar bakinsa da zasu zo daurin aure.

Bayan magrib motoci suka zo akayi ta diban mutane ana kai su, kowa cewa yake yi zaije saboda kowa yana son yaga wannan al’ada ta barebari sannan kuma kowa yana son cin dadi. Lol

Sai da aka gama kwasar mutane saura Diyam da yammatan ta sannan Sadauki yazo daukan ta. Aka kawo kuma wata motar da zata dauki kawayenta. Ya kira ta yace ta fito su tafi, ai kuwa duk su fanna suka taho rakiya da kuma tsegumi. Suka hango motar daya zo da ita, tun daga motar suka fahimci cewa yau a shiryen sa yake, Al- Mustapha ne a seat din driver, kuma dama yana daga cikin samarin Murjanatu dan haka ta bude seat din kusa dashi ta zauna. Diyam kuma aka bude mata baya inda Sadauki yake zaune ta shiga ta zauna kusa dashi aka rufe kofar. Adama ta zagaya side din da yake tayi knocking window, ya sauke glass yana kallon ta yace “ya akayi?” Tace “yaya Aliyu dan Allah in shigo? In zauna a tsakiyar ku kaga waccan motar kamar ba zata ishe mu ba” ta karashe maganar tana kokarin yin dariya, bai ce mata komai ba sai tayi winding up glass din yana murmushi yace “yaran nan so suke su mayar dani kakan……” Sai kuma maganar ta makale ya kasa kammalawa saboda juyo wa da yayi suka hada ido da Diyam da take kallon sa saboda kyawun da yayi mata ko kuma maybe dan bata saba ganin sa da manyan kaya bane ba?. Bakin sa ya motsa a hankali amma Diyam bata ji mai yace ba, sai ta tambayeshi. Yace “tasbihi nake yi ga Allah, mahaliccin kyawawan surori” ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta sai yabi hannun da kallo, idanunsa suka sauka akan tsararren kunshin da yake kwance akan farar fatarta. Yace “wadda tayi kunshin nan ko nawa aka biya ta taci kudinta” Diyam tayi masa fari da ido tace “harda kitso tayi min” yace “may I see it?” Ta makale kafada tace “not today” yace “gobe ne dai kadai ta rage min. Amma ban sani ba ko zan kai goben? Dan wannan abin da kike min da ido bana jin zai barni in yi bacci yau” dariya suka ji Murjanatu tayi daga gaba, Sadauki ya kalle ta yace “ko kiyi shiru ko kuma a sauke ki ki hau napep” Al-mustapha ya dan waigo yace “amarya, ni ko gaisawa ma ba’a bari munyi dake ba” Sadauki yace “hey! Juya ka kalli gabanka, don’t go about looking at something that is not yours” Murjanatu tace “an fara, yau zanga yadda za’ayi wannan taron” Sadauki yace “kinyi shiru ne ko kuma ayi packing ki fita?” Al-Mustapha yace “in ka sauke ta sai dai ka zagayo ka ja motar ka da kanka” Diyam dai tana jinsu tana ta murmushi. Ita kanta tasan tayi kyau kuma tasan yau za’ayi rigima da Sadauki duk kuwa da cewa komai nata a rufe yake fuskarta da hannayenta ne kawai a bude.

Suna packing ya miko mata hannu yana murmushi, ta makale kafada sai ya langwabe kai yace “Please” sai ta saka hannunta a cikin nasa, ya juya hannun sannan ya saka fingers dinsa a tsakankanin nata yana kallon yadda hannayen nasu suka yi kyau sosai together,  perfect match for each other, kamar dama a haka aka halicce su.

Suka fita suka jera a tare suka tafi gurin da aka tanada saboda su, Diyam idanuwanta a kasa tana jin tsananin kunyar mutanen gurin. Tun daga bakin mota ake turara su da turaren wuta iri iri masu kamshi kala kala har suka je suka zauna sannan aka sake zagaye su da turarukan wuta. Nan take aka fara gabatar da shagali wanda ita Diyam ba fahimta take yi sosai ba saboda hannun da yake rike da nata kuma tayi dabarar kwacewa ta kasa. Ga kuma idanuwa guda biyu a kanta suna kallon duk wani motsi nata. Ta dan kalle shi tace “hey…….stop looking at me like that” ya daga gira yace “ko? Saboda me? Baki san ni maye bane ba? Ko baki da labari?” tayi murmushi tace “kar ka bari Inna taji ka” yace “am serious fa, kin dauka wasa nake yi ko? Ina tausaya miki ranar da zaki fahimci a inda tawa maitar take” ta sake kokarin karbar hannunta ta kasa. Yace “wannan hannun tunda kika bani shi kuma ya zama nawa, sai sanda nayi niyya zan baki aron sa” ta sake cewa “ni ka daina kallo na” ya bata rai yace “ba fa ke nake kallo ba, lips dinki nake kalla wondering what they taste like” taji kamar zata nutse a gurin, tace “wayyo Ummah”. 

Anyi rawa sosai, rawar barebari, yan’uwa da abokan Sadauki ne suka fara yi sai kuma na Diyam sukayi joining dinsu suna koya, sai kuma suka koya musu suma irin tasu rawar ta fulani. Amma Diyam ko motawa daga seat dinta Sadauki bai bari tayi ba ballantana ta saka ran yin rawa. Duk wanda yazo gurin su daukan hoto kuwa indai namiji ne to Sadauki zai ce masa “zagayo ta side dina” sai suyi dariya gaba daya. And Diyam wondered, anya kuwa Sadauki zai barta ta koma school?

Sai after 11 suka tashi, shima dan dare yayi ne ba wai dan sun gaji ba. Da kyar Sadauki ya bar Diyam ta shiga gida, shi ji yake kamar su yi ta zama a mota har gari ya waye, gani yake kamar gobe ba zata yi ba. 

A ranar duk su biyun babu wanda yayi bacci. Kwanciya suka yi da wayoyinsu a kunnuwansu suna bitar rayuwar su, yarintarsu, rabuwarsu, da kuma sake haduwarsu. Diyam ta bashi labarin sanda take lekensa ta window lokacin da Saghir ya kawo shi gidan su. Yace “ohhhh, ashe shi yasa naji kamar zan fadi, ashe idanuwa ne suka yi min yawa”. Sai da dare ya raba sannan suka yi shawarar gabatar da salloli da addu’ar neman alkhairi a cikin sabuwar rayuwar da zasu shiga gobe. A kan sallayinsu suka karasa kwana. Sai da suka yi sallar asuba sannan Diyam ta kwanta, amma kuma ba wai bacci tayi ba likimo kawai tayi tana jin su Humairah dasu Murjanatu suna ta hirarrakin su suna dariya har gari ya waye. Bata tashi ba sai da Hannatu Sokoto ta zo ta tashe ta tana cewa “gwara da kikayi baccin ai, shi bacci yana kara fito da kyawun mutum” sai ta ajiye mata special dahuwar kazar da tayo mata daga gida, ta zauna ta cinye tas sannan ta kora da tsumin maman fareeda (07033742833), tana ci suna hirar su da Humairah suna kuma jiyo hayaniya a tsakar gida maza suna ta shirye-shiryen  tafiya daurin aure. A lokacin Bassam ya kira Humairah ya gaya mata ya shigo gari amma ya zarce venue din daurin auren, Alfurqan Mosque.

Kafin ta gama Hannatu Sokoto ta shirya mata ruwan wanka dan haka ta shiga tayi wanka tafito, tana zama a gaban mirror message din Sadauki ya shigo wayarta.

Dear Mrs Abatcha
Alhamdulillah. I am now yours and you are mine.
Signed
Mrs Abatcha

Ai mun gama ko?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button