NOVELSUncategorized

DIYAM 72 & 73

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventy Two & Three :  A Perfectly Perfect Night

I was thinking about covid-19. Sai nake ganin da ace al’ummar duniya duk sun sani kuma sun bi umarnin fiyayyen halitta (S.A.W) a inda yake cewa idan
annoba tazo guri, wanda yake ciki kar ya fita wanda kuma yake waje kar ya shiga, da an bi haka da cutar bata kai matsayin da take a yanzu ba.

Chinese basu san wannan umarnin na annabi ba, amma mu munsani dan haka me yasa mu ba zamu bi ba dan dakushe yaduwar cutar?
Stay safe
Stay at home

Hannatu Sokoto da muka yi magana a last episode wata member ce ta group dina na WhatsApp, amma bata gyaran jiki, na saka sunanta ne kawai to honor her and for fun.
But Maman Fareeda is real, duk mai so zata iya kiranta.

Ta dora wayar a kirjinta ta lumshe idonta taba jin hawaye yana taruwa a idonta, sai data fahimci da gaske kukan zata yi sai ta mike da sauri zata shiga toilet sai suka hadu da Humairah tana fitowa ita kuma, ta tsaya tana kallon ta tace “wai kuka kike yi?” Sai Diyam taji sauran kukan data rike ya taho gabaki daga, ta juya bayanta tayi facing bango tana kokarin share hawayenta. Humairah ta fara dariya, abinda ya jawo hankalin yammatan da suke dakin suka taso suna tambayar abinda ya faru. Hannatu Sokoto ta shigo lokacin da Diyam take kokarin ture Humairah zata shiga toilet sai Hannatu tace “wai shiga kike so kiyi ki zauna a kan sassanyan tiles kiyi kuka zaki a toilet din? To dakata, bara in kawo miki garwashin wuta in dumama miki tiles din sai ki zauna kiyi ta kukan” duk suka kwashe da dariya, tace “a to, ni ba kukan ne damuwata ba, ni damuwata shine zama a sassanyan guri”. Da Diyam taga sun mayar da ita abar tsokana sai ta fice ta bar musu dakin. Daya dakin da yake kusa da inda suke ta shiga, wanda a da shine a matsayin dakin Sadauki sanda suna yara. Ta shiga ta rufe kofa ta jingina a jikin kofar tana kallon dakin da yanzu yaje a gyare tas amma babu komai a cikinsa sai carpet da akwatunan su Murjanatu da aka kawo dakin dan kar wancan ya cika da kaya. Ta rufe idonta hawayen yana cigaba da zarya a kuncinta, hawayen da ita kanta tasan na murna ne ba wai na bakin ciki ba. Sai yau ta tabbatar da cewa ana iya yin kukan dadi.

Ta bide idonta tana tuno lokacin da take shigowa dakin tayiwa Sadauki kaca-kaca dashi, ta yayyaga masa takardun sa ta hargitsa masa shinfidar sa, ko kuma tazo ta kwanta a shimfidar tayi ta baccin ta, amma bai taba ko daga mata murya da sunan fada ba. Da kuma sanda take zuwa ta saka shi a gaba yayi mata homework ko da kuwa shi baiyi nasa ba. She never thought da gaske one day zai zama mijint, duk kuwa da cewa tun kafin tasan ma’anar kalmar miji take cewa shine mijinta.

Anan dakin ta kwanta akan carpet. Ta lumshe idonta sai kuma tayi murmushi tana jin duk sauran problems dinta na rayuwa suna melting away. Ta zama matar Sadauki.

Tana nan kwance Rumaisa tazo gidan, ita ta shigo har dakin ta fita da ita palo sannan suka kafa tsokanar ta wai tayi kukan aure, sai kuma Falmata tayi mata kwalliya ta musamman aka shirya ta cikin tsadadden farin lace din da ta tanada saboda yau wanda tayi musu anko ita da Subay’a. Sannan suka fara daukan pictures, suka dauka anan sannan ta shiga part din Inna can ma suka daddauka da mutane ana ta taya ta murna da kuma yaba kyawun da tayi. Masu selfie nayi a waya, cameraman ma yana yin nasa.

Sai kuma ga sanarwar cewa ango yazo zasuyi pictures da amarya, nan kuma Diyam taji ita duniya babu wanda take kunya kamar Sadauki, ita sam bata dauka zaizo yin wani hoto da ita ba. Sai ta wayance ta koma part din Umma tayi zamanta amma tana jin alamar ya shigo kuma sai ta mike ta tsaya daga bakin kofa tana lekensa, yayi kyau sosai, a idon Diyam sai taga bata taba ganin mutum mai kyau irinsa  ba a rayuwar ta, yayi shigar farin yadi kal dashi tun daga hula har zuwa takalmi fuskarsa dauke da annuri wanda yake bayyanar da farin cikin da zuciyarsa take ciki. 

Tana kallo ya shiga gurin Inna, da alama gaisheta yaje yayi sai kuma gasu sun fito tare hannunsa rike da Subay’a, suka tsaya a tsakar gida suka yi pictures sai kuma Inna ta sa baki ta kira ta amma sai ta makale taki tafiya, sai Subay’a ta taho part din da sauri “mommy kizo kiga yadda uncle Sadauki yayi kyau, kizo kuyi hoto kafin ya tafi” Sa’adatu tayi dariya tace “chafdi, mai fitar da yaya Aliyu daga gidan nan ba tare da yaga Diyam ba ai babu shi a duniya”. Diyam ta kama hannun Subay’a amma kafin tayi magana sai gashi a tsaye a bakin kofa yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da idonta tana mamakin rashin kunya irin ta Sadauki da har ya keto mutane ya taho gurinta. Sai ya tako cikin tafiyar kasaita ya zo har gabanta ya tsaya yace “my wife” sai ta saki hannun Subay’a ta rufe fuskarta da sauri tana murmushi, taji yammatan gurin sun dauki shewa sannan kuma wata mata a tsakar gidan ta rangada guda. 

Sai kawai ji tayi ya kama hannunta ya fara jan ta zuwa waje, a dole ta nutsu ta bishi amma fukarta a kasa, ta kasa daga ido ta kalle shi duk da yadda zuciyarta take son ganin cikin idonsa, balle kuma ta kalli sauran jama’ar gurin. A kayi ta hotuna, suna tsaye wannan yazo a dauka wancan ma yazo a dauka har saida aka gama sannan ya kuma jan hannunta zuwa dakin daya dauko ta ya zaunar da ita yace da Murjanatu “kar kuda ya taba ta” sannan ya juya ya fita, sai a lokacin ta dago kanta ta bi bayansa da kallo, tana kallon yadda yake taking steps one after the other.

Sai da ya fita sannan kuma suka zo suka zagaye ta suna tsokana ‘mai tsoron miji’ ‘ta kasa kallon mijinta’ ‘dama fulani haka kuke?’ ita dai bata kula suba sai ta karbi wayar Asma’u wadda ta lura tana ta daukan pictures “kawo inga pictures din da kika dauka” ta bude hotunan da sauri tana scrolling tana neman wanda yafi fitowa sosai har ta samu, sai ta kwanta ta dunkule a guri daya ta zuba wa fuskarsa ido tana murmushi.

Humairah ce ta katse mata daydreaming dinta, tace “Bassam yazo fa, yana waje” sai ta ajiye wayar ta mike da sauri, ta kira Asma’u “akwai bako a waje, ki bude masa dakin baki ki kai shi can, sai kizo ki kai masa abinci da ruwa” sai Asma’u ta saka mayafin ta ta fita, amma kuma wajen a cike take da mutane maza da mata na ta gaggaisawa, sai kawai ta tsaya tana bin su da kallo tana son ta gani ko zata iya gane waye jikan sarkin Abuja a cikin su. Yana cikin mota ya hango ta fito daga gidan da yake tunanin nan ne gidan su Diyam, farko ya dauka Diyam din ce amma kuma yasan Diyam ba zata fito kofar gida cikin mutane ba tunda yau aka daura mata aure, sai kuma ya lura wannan bata kai Diyam maturity ba amma suna kama sosai sai fari da Diyam ta fita. Yana ganin yadda take yamutsa fuska, dafa dukkan alama zata yi tsiwa. Nan sai zuviyar shi ta bashi cewa wannan Asma’u ce, only sister din Diyam. Sai ya bude kofar motar ya fita yana kallon ta, sai yaga ta juyo ta kalle shi kamar wadda aka kira, suka tsaya suna kallon kallo sannan sai yaga ta doso shi. He likes yadda take tafiya, ya tabbatar bashi kadai ba sauran mazan da suke gurin ma ta ja hankalinsu. Ta tsaya dan nesa dashi kadan tace “Bassam?” Ya gyada kai yace “Asma’u ko?” Bata amsa ba sai tace “Adda tace ka shigo ciki” muryarta tayi masa dadi, sautin fulani. Sai ta juya tayi gaba. A zuciyarsa baya son shiga dan shi da a son ransa ne daga gurin daurin auren zai komawarsa dan dai Humairah ta nace sai yazo yayi wa Diyam Allah ya sanya alkhairi “dan ita kazo fa, ai ya kamata ku gaisa ko minti daya ne”. Amma yanzu da Asma’u take gabansa tana tafiya sai yaji cewa binta a baya ya zama wajibi a gare shi. Ya zare key din motar ya bita cikin gidan yaga ta tura kofar wani daki kafin a karasa shiga cikin gidan ta ce masa “Bismillah” sai ya shafa kai yana kallonta, shi ai ya dauka tare zasu shiga amma sai yaga ta juya ta shiga cikin gida ta barshi a tsaye. Wannan yasa dole ya shiga dakin ya zauna ya kama daddanna phone dinsa. Amma zuciyarsa tana tunanin ko zata dawo?

Bai jima ba sai gata ta shigo da sallama, tayi masa shimfidar abinci can gefe kadan sannan ta fara jera masa kayan ciye ciye iri iri har ta gama amma shi idanunsa a kanta suke ba wai a kan abinda take yi ba. Itama kuma tana jin idanuwan nasa akanta, dan kada ne ya rage bata yi barin abincin da take shiryawa ba. Sai data gama sannan ta mike, yayi saurin pretending kamar wayarsa yake dannawa tace masa “Bismillah, ga abinci. Adda zata fito ku gaisa” ya ajiye wayar sai kuma yace “thank you. Amma ki zauna mana kafin tazo din ko. Kinga ai sai ki tayani hira ko?” Sai ta dauke kanta, wannan mutumin neman magana yake yi kuma. Shi baisan zuciyarta bugawa take yi da wannan kallon nasa ba? Ga shi ya cika kyau da yawa. 

Ta girgiza kai tace “ina yin wani abu ne a cikin gidan” yace “Please, minti uku fa kawai. Kinga ni ban iya cin abinci ni kadai ba” he is a playboy, tayi deciding a zuciyarta, sai ta doshi kofa ba tare da ta kuma ce masa komai ba, har ta daga labule sai taji yace “an a lobbo sanne, Asma’u” sai ta juyo tana kallon sa, bata taba tsammanin bafulatani bane ba, mix din shi yayi yawa. Sai ta samu kanta da yin murmushi tace “miyetti” amma duk da haka bata zauna ba ta fita. Bata shirya yin wasa da zuciyarta ba.

Bai ci abincin ba tunda yaci a reception din da suka wuce daga gurin daurin aure. Aliyu ya gane shi kuma ya karbe shi sosai. Sai ya zuba juice ya sha, sannan ya koma ya zauna ana fatan Asma’u ta biyo yayarta su dawo tare. Amma sai ga Diyam tazo sanye da hijab tare da Humairah, suka gaisa tayi masa godiya shi kuma yayi mata fatan alkhairi sannan yace zai tafi. Yace “Asma’u tazo ta kwashe kayan abincin nan mana” Diyam tace “no, kar ka damu kayi tafiyar ka kawai, an jima za’a kwashe su” yace “a dauke dai yanzun ai sai yafi ko?” Ta tsaya kawai tana kallon sa sai yayi murmushi, ta daga gira tace “Asma’un?” Yace “sallama kawai zamuyi ba wani abu ba, dan Allah ki turo ta” Humairah tace “kar ka damu kani na, har phone number dinta zan karbo maka” yace “kash, shi yasa nake yinki over yayata”. Suna shiga ciki Humairah ta kwalla kiran Asma’u “kije kuyi sallama da kani na” sai Asma’u ta tura baki tana kallon Diyam, Diyam ta daga kafada tace “ina ruwa na, in kina son zuwa kije mana” kamar ba zata je ba, sai kuma ta zari mayafi ta tafi.

Bayan sallar azahar sai ga yan kawo lefe. Anan gida ya hargitse gaba daya ashe wai al’adar bare bari ne sai an daura aure ake kawo lefe. Akwatuna akwatuna, ga kuma wasu kayan a jakankuna. Lefen yakunshi akwatunan amarya set biyar, akwatin maman amarya (inna), akwatin kannen maman amarya(innaso), akwatin yan uwan baban amarya (bawaso),  sai sisters (Asma’u) sai na kawayen innarta (ya samma soye) sai na matan waliyinta (su Hajiya Babba da yalwati),  sai matan kawunnanta (kamu rawaye. Matar kawu isa da kuma su Hajiya Babba again)sai na  yan bayarwa (na rabo) sune a jakankuna, sai na wadda tayi mata kiso (Hannatu Sokoto) an bata atampopi da kudi. Tun a kofar gida aka fara nunawa maza tukunna aka shiga dashi cikin gida gurin su Inna. Wannan duk al’ada ce ta barebari. Fulani sai suka tsaya kallo da mamaki, wanda baya kusa ma sai da aka kira shi a waya yazo ya kashe kwarkwatar idonsa masu video coverage suna yi masu dauka a hotuna suna yi. 

Diyam kuwa tana cikin daki ta rufe kanta, ita kunyar yan uwan Sadauki take ji gashi taji ance gar da Yaya Ladi da yan’uwanta aka zo. Ana cikin haka sai ga Fauziyya ta shigo gidan tana rarraba idanu, da goyon yarinya a bayanta. Irin yadda gidan ya chanza rake kalla ga kuma uban kayan data gani mutane suna ta gani wanda ko ba’a fada ba tasan lefen Diyam ne. Amma data tuna wanda aka ce shi ya auri Diyam din sai taga wannan ba komai bane ba.

Ta tambaya aka raka ta har dakin da Diyam take. Diyam tana zaune da waya a hannunta tana kallon kiran Sadauki yana shigowa one after the other amma ta kasa dauka. Sai ganin shigowar Fauziyya tayi, ta tare ta da fara’a sosai sai Fauziyya tace “fushi nake yi fa, kin manta dani kuma wayar ki bata shiga kwata kwata” Diyam tace “Allah sarki, ba haka bane ba wallahi. Bana kasar ne ina UK ina karatu” Fauziyya ta gyada kai kawai. Ta tuna lokacin da Saghir ya fita da ita honeymoon America, a lokacin tana jin kamar duk duniya babu ya ita, tana yiwa Diyam dariya a ranta tana ganin cewa Diyam din tayi asara ashe ita asara zata samu. Rayuwa ta juya mata baya gabaki daya, komai ya tsaya mata. Dama a gurin maza take karbar yan kudade tana biyan buƙatar ta yanzu kuma tunda tayi deciding haifar cikin Saghir shikenan ta rasa costumers, bayan ta haihu kuma tana kallon fuskar jaririyar ta taji cewa ta gama yawon ta zubar kenan. Yan uwan Saghir sam basa taimaka mata kuma ta fahimci suma kansu taimakon suke nema, sun dai je sunga baby sanda ta haihu sai kuma Hajiya da take dan kiran ta tana tambayar lafiyar Anisa. Jin dadin ta daya ta samu aikin koyarwa a wata private school anan layin su. 

Diyam ta karbi Anisa tace “Masha Allah. Kinga dai yaran nan gaba ki dayan su kamar baban su suke yi”. Fauziyya tayi murmushi jin an yabi hasken rayuwarta, tace “ni fa bansan ma zakiyi aure ba, Hajiya Babba ta gaya min ana bikin kannen Saghir shine na shigar musu to a can ne nake ji ashe tare da naki ake yi” Diyam tayi murmushi kawai. Fauziyya tace “Allah ya sanya alkhairi” Diyam tace “ameen”. 

Ta dauko wayarta a karo na ba adadi tana kallon kiran Sadauki yana shigowa. Sai daya katse sannan tayi murmushi. Sai kuma ga Murjanatu ta shigo ta mika mata waya tace “yaya Aliyu yana kira” Diyam ta ture wayar tayi mata sighing “kunya” sai Murjanatu tayi dariya ta fita tana masa magana. Diyam ta kuma daukan wayarta sai sakon shi ya shigo.

Tunda Sadauki ya fita daga gidan yake kokarin ganin yayi waya da Diyam, yana so yaji muryarta. Da farko mutane ne suka hanashi samun sukunin yin hakan, daga baya kuma da ya samu ya kira sai taki dauka. Yayi yayi amma sai dai tayi ta ringing ta katse ba zata dauka ba. Da farko ya dauka bata kusa da wayar ne dan haka ya kira Murjanatu ya ce ta bata, amma sai taki karba, yana jin Murjanatu tana yi mata dariya sannan tace masa “yaya Aliyu kunyar ka fa take ji wai” sai yayi murmushi ya samu secluded guri ya zauna ya shiga WhatsApp ya tura mata “ke fillo” shiru at first, sai later kuma ta aiko masa da reply na emoji na harara. Yayi dariya shi kadai ya rubuta 
“wai da gaske kunyata kike ji? Tun yanzu?” 
“Kunya kuma? Wacce irin kunya?”
“Hmmm, really? So tell me, me yasa kika rufe idonki da na shigo gida? Me yasa kika ki yi min magana kuma me yasa kika ki daukan phone dina?”
“Bafa kunyarka nake ji ba. Fushi nake yi”
“Poor me, laifin me nayi?”
“Ba kai bane ba ka hanani rawa a gurin wushe-wushe” (imojin shagwaba)
Dariya “okay, yanzu dai rawa kike so ko?”
“Uhmmmm” 
“Shikenan. Kina bina bashin rawa”
“Da gaske?”
“Yes, but just me and you. Tonight.”

Tayi logging out da sauri. Feeling very nervous. Ina ma dai za’a daga kai amaryar nan zuwa gobe? Ko jibi?

Babu abinda aka fasa. Magrib tana yi aka saka ta ta sake wani wankan, wannan karon babu kwalliyar da aka yi mata sai atamfar da ta saka blue mai adon pink and white flowers. Sannan aka nada mata laffaya fara mai shara shara da adon blue and pink flowers. Humairah da Murjanatu ne suka shirya ta tsaf, sannan suka kamo hannunta suka taho da ita dakin Inna inda anan iyaye suke, Mama, Inna, Hajiya Rabi (matar Kawu Isa) sai kuma step sisters din su Inna su biyu. Ta zauna a tsakiyar su ta nannade kafafuwanta suka fara yi mata nasiha, idan waccan tayi ta gama sai waccan ta dauka itama tayi nata. Suka gama sannan suka yi doguwar addu’a suka shafa. Lokacin masu daukan amarya suka zo, yaya ladi, Mama (matar baban Sadauki) sai kannen Papa mata su biyu. 

Suna zuwa aka fara nuna musu kayan garar da aka hadawa Diyam. Komai da komai na kayan abinci an siya in abundance, ga kuma kayan gara dangin su alkaki, nakiya dubulan, gireba, cincin da sauran su komai a cikin manyan containers. Sai daaka nuna musu kayan suka gani suka saka albarka sannan aka zuba su a mota aka tafi dasu gidan Alhaji Bukar.

Diyam tana jinsu suka zauna suna ta barkwanci dasu Mama, sai taji dadin yadda taji ana magana tsakanin Inna da yaya ladi. Sai da suka gama sannan aka sake feshe ta da turare sannan maman su Murjanatu ta kama hannunta ta mike. A lokacin Subay’a ta shigo “mommy! Mommy wai aunty Asma’u tace tafiya zaki yi ki barni, Mommy ai tare zamu tafi ko?” Mama tayi saurin dauke ta ta fita da ita daga dakin tana ta rusa kuka, wannan shi ya kawo hawaye idon Diyam. Tun sanda za’a kai kayanta gidan Sadauki ta fara hada na Subay’a amma Inna tace “ba ki da hankali. In ma zaki tafi da ita ba yanzu ba. Kuma ke da zaki koma karatu menene amfanin tafiya da ita?”  

Ta fara kuka a hankali maman su Murjanatu tana tsokanar ta. Ita kuma tsokanar kara mata jin kunya take yi. A haka suka fita tana jiyo kukan Subay’a suka shiga mota ita da maman su Murjanatu da Mama, almustapha kuma yana driving suka tafi, sannan sauran motocin daukan amarya suka biyo bayan su.

Duk da fuskar ta tana rufe amma tana gane inda suke har suka je, a lokacin ta daina kukan Subay’a, suka fito aka saka ta tayi basmala ta kuma shiga gate din gidan da kafar dama sannan ta sake repeating sanda zata shiga cikin gidan. Tana shiga kamshi ya kaiwa hancinta ziyara, kamshi mai dadi, kamshin Maiduguri. 

Sama suka hau da ita suka kaita har cikin bedroom din da yake nata suka zaunar da ita, suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi. Sanda Mama zata tafi sai tace “Diyam yau ba zaki rike hannuna kice kar in tafi in barki ba?” Sai Diyam ta samu kanta da yin murmushi tare kuma da jin kunya. 

Humairah ce ta fara zuwa tayi mata sallama saboda a daren zata bi flight zuwa Abuja, daga nan kuma mutane suka fara watsewa a hankali gidan ya fara yin shiru. Su Murjanatu, Rumaisa da Asma’u ne karshen tafiya, sai da suka gyara mata duk inda aka bata suka kara tabbatar wa ko ina na gidan yana kamshi sannan suka yi mata sallama. Murjanatu tace “wato ko dan tayin nan ba zaki yi mana ba ko? Irin ki dan ce ‘ku zauna ku kwana mana tunda dare yayi?” Diyam ta matsa mata guri tace “Bismillah, zo ki kwanta a kusa dani” Rumaisa tace “har na tausaya miki Murjanatu. Ni dai kunga tafiya ta maigidana yana waje yana jirana tun dazu” Adama tace “kunsan wani abu? Yaya Aliyu fa yana cikin gidan nan duk wannan abin da ake yi. Naje part dinsa naji kofa a rufe kuma an bar key a jiki ta ciki” Murjanatu ta mike da sauri ta dauki handbag dinta “Allah ya bamu alkhairi” duk suka yi mata dariyar ta fiya tsoron Sadauki sannan suka fita gabaki dayan su a tare.

Tunda Diyam taji cewa Sadauki yana cikin gidan sai taji duk nervousness dinta ya dawo. Wayar ta har zamewa take yi daga hannunta tana faduwa kasa. Ta mike daga kan gadon tana karewa dakin kallo sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai taga tayi wani irin kyau har kyalli fatarta take yi duk kuwa da cewa babu ko digon kwalliya a fuskarta. Ta gyara zaman laffayar ta sannan ta bude kofar balcony din daya ke cikin bedroom dinta ta fita tana kallon yadda sama tayi tas sannan taurari suka cika ta. Sai tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta sannan ta koma cikin dakin ta murda kofar fita waje ta leka empty corridor sannan ta fita da sanda kamar marar gaskiya ta bude dakin da yake opposite nata taga shima irin nata ne sai girma da wancan dakin yafi wannan sai kuma banbancin colors. 

Shirun da gidan yayi ne yasa ta jiyo kamar motsin takun mutum yana tahowa inda take, sai tayi sauri ta karasa shiga cikin dakin ta haye can karshen gado ta rufe fuskarta da laffayar jikinta. Taji an bude kofar corridorn an shigo, sannan heavy footsteps suka taho zuwa dakin da take yayinda bugun zuciyarta ya karu, taji shigowarsa sannan taji kamshinsa. 

Ya dan jima a tsaye yana kallonta sannan ya karasa shigowa ya hawo kan gadon ya zauna akan kafafuwansa a gabanta yana kallon fuskarta ta cikin shara sharan laffayar ta sannan murya can kasa yace “Sadiyam”

Ta saka hannayenta da sauri ta kara rufe fuskarta tana murmushi. Sai ya saka nasa hannayen a saman nata yana shafa wa yace “hannayenki suna da kyau, kunshin yayi musu kyau sosai”. Tayi sauri ta juya tana kallon side. Sai yayi dariya yace “yanzu ni fuskar matar tawa ba za’a barni in gani ba?” Tace “sai ka biya tukunna” yayi murmushi ya jawo rose flower da ya shigo da ita a soke a bayan wandonsa a jikin rapping din an rubuta “loving you is all I ever know” ya mika mata ta karba da hannun dama, sai kuma ta miko masa hannun hagu tana murmushi, sai ya tuna lokacin da suna yara in ya bata sweet a hannu daya sai ta miko masa daya hannun shima ya bata. 

Sai ya saka hannu a aljihu ya dauko chocolate din twix ya saka mata a hannun. Yace “shikenan na biya?” Bata ce komai ba sai ya saka hannu biyu ya bude fuskarta ya sauke laffayar har kafadun ta. Ta dago kai a hankali suka hada ido yayi mata murmushi mai kyau sai ta kuma sunkuyar da idonta kasa itama tana murmushi ta fara bude chocolate din daya bata amma maimakon ta kai bakin ta sai ta kai nasa bakin. Ya rike hannunta a cikin nasa ya juyar dashi zuwa bakin ta ta fara gutsira sannan ya juyo da hannun zuwa nasa bakin shima ya gutsira. 

Sai da suka gama cin chocolate din su sannan ya jata suka mike a tare yace “let’s pray”. Dakin da aka kaita suka koma, shi ya fara shiga toilet yayo alwala sannan itama ta shiga. Sai ya ja musu jam’i a gurin da aka tanada a dakinta musamman dan sallah. Sukayi sallar isha’i tunda duk su biyun basu yi ba, sannan kuma suka yi sallar raka’a biyu ta godiya ga ubangiji a bisa cikar burinsu sannan ya juyo yana kallonta suka fara jero adduoi. Farko sun fara gabatar da godiya ga Allah sannan suka yi salati ga fiyayyen halitta (S.A.W) sai kuma sukayi addu’a ga mahaifansu da suka riga mu gidan gaskiya, Baffa da Ummah, suka roka musu gafara da ragamar ubangiji, sannan kuma suka yi addu’a ga mahaifansu da suke a raye tare da fatan tsahon rai a cikin kyakykyawar rayuwa. Sai kuma sukayi wa kansu addu’a, suka roki tabbatar alkhairin dake cikin auren su sannan suka roki tsari daga sharrin dake cikinsa. Suka yi addu’a ga yayan su, twins da suka rasu da fatan su zamo masu ceton mahaifansu sukayi addu’ar rayuwa mai kyau ga Subay’a sannan sukayi doguwar addu’ar a kan neman zuri’a ta gari mai albarka a tsakanin su.

In Sadauki ya dauko addu’a Diyam tana amsa masa da ameen in ya gaji sai ita kuma ta karba ta cigaba shi kuma yana amsa mata. A haka har suka kammala suka shafa. 

Kanta yana kasa tana kallon hannunta amma tasan ita yake kallo duk da bata kallonsa, sai ta murguda masa baki, yace “ni ko?” Ta daga gira. Ya mike tsaye yana cewa “zakiyi bayani ne yarinya” sai ya zauna a kan gado sannan kuma ya tafi da baya ya kwanta rigingine ya lumshe idonsa, tana zaune still a inda ya barta tana kallon sa ya jima a haka sannan ya juyo inda take ya bude idonsa a cikin nata yace “na gama komai ko?” Ta mike tsaye tace “sauranka kaza” yayi kamar zaiyi kuka “Please ni kam a yafe min kazar nan mana. Kinga na gaji fa, ga kuma dare yayi” ta makale kafada tana kallon sa. Ya mike zaune sannan ya mike tsaye yace “shikenan, in na fita waje aka sace ni kar kiyi kuka” ya juya ya fita ya barta ita kadai. 

Kayan jikinta ta cire, ta shiga toilet tayi refreshing sannan ta fito ta zauna tana shafa mai me sassanyan kamshi a duk ilahirin jikinta, tana yi tana kallon kofa a tsorace har ta gama ta saka underwears dinta ta kuma saka riga da dogon wando na bacci, rigar a sake take sosai amma ta tsaya ne a saman cibiya, wandon kuma dogo ne har kasa sai dai ya kama saman sosai ya kuma bude sosai daga kasa,  sannan ta hau kan gado ta dauko wayarta tana duba pictures. A lokacin ne sakon Sadauki ya shigo wayarta. 

“I owe you a dance, da kuma kazar amarci. Meet me in the garden please” 

Ta rufe idonta ta bude tana jin kamar zatayi zazzaɓi. Sai kuma ta mike ya dauki hijab ta saka masa turare ta saka sannan ta fita a nutse. Ta sauka kasa ta cikin corridorn daya raba palonsa na kasa da nata, inda anan ne stairs din hawa sama suke kuma anan ne front door da back door na gidan suke. Ta murda back door din ta fita doguwar veranda sannan ta sauka daga kan steps guda uku ta shiga garden. A tsaye ta hango shi, ya chanza dogayen kayan jikinsa zuwa shirt da wandon. Yayi shimfidar karamin carpet akan grass carpet din gurin ya zuba throw pillows akan carpet din sannan ya zagaye shinfidar da candles masu kyalkyali, a gefe kuma ga food warmers guda biyu da fruits da aka yi arranging dinsu a shape din heart. Ya taho ya tarye ta yana murmushi, ya jawo ta zuwa jikinsa ya rungume ta ta baya yana saka fuskarsa a ramin wuyanta yace “ga kaza an siyo, sai me kuma?” Ta juyo tana kallonsa tace “saura rawa ta” yace “with pleasure” sai ya zare hijab din jikinta ya ajiye a gefe ya juyo yana kallonta lokaci daya ya dauke numfashi saboda abinda ya gani, ya sani cewa tana da good figure but bai san cewa it is this good ba, ya jima tsaye yana jin tamkar ya samu paralises ita kuma tana ta sussunne kai, sai ya saka hannunsa na dama a waist dinta ya jawo ta sosai ya hade jikin su, daya hannun kuma yana shafo tun daga kan kananan kitsonta zuwa gadon bayan ta zuwa hips dinta, ta kwantar da kanta a tsakiyar kirjinsa tana jin cewa tamkar a nan ne aka halicceta, ta zagaye shi da hannayenta, tare suka sauke ajjiyar zuciya. Sai ya fara taking steps tare da ita a jikinsa, tamkar jikin nasu guda daya ne, three steps forward, two steps back. 

Ta lumshe idonta tana jinta kamar tana floating a cikin iska, kakkarfan jikinsa like a shield to her, his heart beat like a music to her ear. And he sang to her a cikin kunnen ta:

I found a love for me, Darling just dive right in, And follow my lead, Well I found a girl beautiful and sweet, I always knew you will be the someone waiting for me……
‘Cause we were just kids when we fell in love, Not knowing what it was, I will not give you up this time….
But darling, just kiss me slow, your heart is all I own, And in your eyes you’re holding mine……
Well I found a woman, stronger than anyone I know, She shares my dreams, I hope that someday I’ll share her home, I found a love, to carry more than just my secrets, To carry love, to carry children of our own
We are still kids, but we’re so in love, Fighting against all odds, I know we’ll be alright this time…
Darling, just hold my hand, Be my girl, I’ll be your man, I see my future in your eyes
Baby, I’m dancing in the dark, with you between my arms, Barefoot on the grass, listening to our favorite song, When I saw you in that dress, looking so beautiful
I don’t deserve this, darling, you look perfect tonight.
Songwriters: Edward Christopher Sheeran.

Lokaci daya ya tsaya, ya saka hannayensa biyu ya dago fuskarta daga kirjinta suna kallon juna for some seconds sannan ya sunkuya a hankali ya dora lips dinsa akan nata. Very slowly at first, very lightly that she hardly felt it, then it grows and it sends shiver data fara tun daga yatsun kafarta zuwa kwakwalwar ta tayi blocking dukkan tunanin ta, and she opens up to him, inviting him further in. 

A hankali hannayenta da suke sarke da juna a bayansa suka fara journey upward, daga bayansa zuwa wuyansa sannan zuwa kansa suna kara jawo shi closer, giving him more, accepting more.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button