DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da gudu driver shi da saura security suka zo wajan, driver shi yakara sa zai karbi key , Aliyu ya tareshi yace” huta abinka na hutar da Kai , ni kadai zanje”
Driver yace” yallabai kayi hakuri , Alhaji ya hanani “
Aliyu yace” Kar kadamu Alhaji yasani” ya shiga ciki motar ya tada , Yana Kai second gate din gida yaga chief security a tsaye an tada motoci ana jirashi yayi ba, motoci sama da 20 lafiyayu, kowane guri mota an rubuta A TYCOON ( wato Aliyu tycoon) da plates number.
Aliyu da sauri ya sauka yace” kar wani ya kutsukura yabini acikiku”
Chief security yace” kayi hakuri sir, ama oga yace Kar mubar ka ,ka fita Kai kadai, so we have to follow his order”
Aliyu ya fusata yace” duk Wanda ya bini acikiku he’s going to be fired” suna ta rokoshi ama ko kallesu baiyi ba, su Ammi suna ciki gida basusa waina da ake tuyawaba, Aliyu ya tadda motar da gudu tsiya ya fice daga gates din , ya dauki hanyar kd ta nasarawa (safe trip Aliyu)
Kaduna
Essha tun asuba da ta farka tayi sallah, tafara hada Kaya, sai karfe Sha daya za su wuce, tana ta trying number hunaisat baishigaba, har ta hakura, ta fito ta gaida da su big mom, hajiya , yayya usma, daddy karami bai farka ba ,
Big mom ta lura da yanayita tace” daughter zo maiyasameki duk jiki a sanyaye, ko dai kifara kewa yaruwa naki ne” Essha ta daga Kai Alama eh
Tace” Kuma mom inata trying number ta baishiga, mom kice ma Yaya Usman yakaini”
Usman yace” Allah ba inda zankaiki, yariya sai so yawo”
Tace” mom kijishi fa “
Big mom tace” yihakuri Essha bai kamata kije da safe na ba , bayaku koma , za su kawo muku ziyara kijiko”
Eh ta daga Kai”
Jekiyi breakfast kizo Zaki rakani kasuwa”
Tace” yawwa mom”
Sha -daya cib cib suka shirya tafiya, su shiga motar Essha Kar ta tafi haka take ji, baba driver yaja motar suka dauki hanya LAFIA.
Suna tafiya a hanya, tsirori motaci ne kawai a hanya ba motoci Sosai, duk suyi shiru bakaji komai sai iska dake kadawa, hajiya da daddy karami duk suyi bacci, Essha ne kadai idon ta biyu, tanaji matsanaci faduwar gaba tarasa dalili, can sufara nisa, sukusa fita daga gari kaduna, motar su ne kadai a titi gaba da baya,ba kowa sai bishiyoyi , ta juya ta kalli taga tana bacci ta hankali kwance hk ma daddy karami, ta juya ga kallo titi taga guri yayi shuri ba’a ji motsi komai.
Can suyi nisa ta hango tawaga mutani su Kai goma, dukasu rike da manya makamai , tun daga kan Ak 47, Mai jigida har kasa su pistol, waesu Kuma na rike da adduna, su tare musu gaba mota, dukasu fuska su rufe da mask.
Bayanda baba driver yaiya dole yaja burki ya tsaya saboda su tare hanya.
Daddy karami da hajiya suna ji tsayuwar mota dukasu suka farka a firgice da Kuma ihu Essha dasu kaji, dukasu sai salati. Hajiya da Essha su fi kowa tsorata, daya daga ciki mutani ya daka musu tsawa yace ” Kuma na shiru kufi mu sanni Allah ne dakuke kiramana shi, oya common ku sauko daya baya daya” haka kuwa akayi sai Bari kawai sukeyi suga bindiga a kansu, wani ya shiga gaba yace” oya kubiyoni ” hajiya tafara rokosu tace” kuyi hakuri da Allah Kar ku cutar damu” Wanda ya saita ma hajiya bindiga akai yace” ke tsohuwa kina Kara magana magana zan fasa Miki bullet a kwakwalwa ki ” tayi tsit,
Su kaisu har ciki daji dake gefe titi, wani mutum ne zaune jibgege dashi, gabashi gawarwakine sukai goma Sha, sai wani tsoho da wani saurayi su rakube a gefe gwani tausayi,sai wata karama yariya zatakai shekara bakwai, daya bagare Kuma bukka ne.
Wanda ke zaune da Alama dai shine shugaba , ya daka musu tsawa yace” ku tsuguna”
Ai da sauri sukayi sauri tsuguna wa, balle da suka ga gawarwaki da ke gabanshi sukara tsorata.
Daddy karami yayi dauriya yace” da Allah in kudi kukeso ,zamu baku ama Kar kucutar damu”
Oga ya fashe da wani mahaukaci dariya sanda daji ya dauka yace” Alhaji mu bamu damu da kudiku ba , aiki Allah mu keyi, suna mu AURE KO RAI!
Dukasu suka daga Kai su ka kalleshi jikisu na Bari .
Hajiya tace” AURE KO RAI wani iri yaro , bamuganeba?
Ogan yace” tsohuwa kigamu na, ya nunasu duka, sukai 20, duka mu shegu ne, wato a haifemu ta hanya zina, wato Bata hanya Allah ba, irimu mutaso a ciki kaskatace rayuwa , mu Sha wuya rayuwa, gori kala kala ba Wanda ba musha ba , har ya jefamu ga wani hali, shiyasa muka yanke hukuci muka hada Wana kugiya, saboda mu aurar da duk wani Mara aure, shekara goma kenan da kafa kungiyana , so daya tak muke fita kowani shekara , Kuma duk Wanda yayi mana gardama , tush ya harba bullet a sama ,zamu kawar da shi a Dora duniya na, kuga gawarwaki na , ba’afi minti goma ba zuwa Sha hudu , suna da Rai kamar ku, ama sumin gardama , gashi yanzu Basu , bakuma Wanda zayakara ji labarisu, bamu da Imani ko tausayi, zuciyoyi mu Suri ga da su bushe, kuga bukka can , yanuna Wana bukka aciki amaremu suke tarewa” hhhhh yakara fashe dariya.
Su hajiya suka hada baki guri cewa inalilahi waina ilaihi raju’un su fadeshi ba adadi”
Oga yace” ku daina Kira mana Allah saboda aikishi mukeyi, ke Mai baki gown dina yanuna Essha, dake makale a jiki daddy karami, yace zona n yanmata”
Essha jiki na Bari tana girgiza Kai ,
Daddy karami yace” jeki Essha ba abunda zai saimeki”
Ta tashi ta a hankali Tana rufe Ido , dun ta tsorata dagani gawarwaki dake guri.
Oga yace” tsoro gawarwaki kikeji, Kai kuzo ku kwashe kwari na????, ku Kai can karshe daji ku zubar” ai nandana kamar jira suke yabasu umarni suka kwashe yace” kuje baki titi duk Wanda kuka gani ku daukoshi Nan ko waye”
Sukace” toh oga” suka wuce.
Essha jikita sai Bari yake Ido ta nafi da kwalla, ta rufe bakita da gyalle ta don Kar sauti kukata yafito.
Oga yace” Yan mata yasunaki ?
Ai da sauri ta amsa tace” ESSHA” murya ta na rawa.
Ogan yace ” ohh Essha suna Mai dadi, Allah sarki gaki kyakyawa duk Wanda yasamaiki ya more, Essha yau kadaraki ta fado , zamu Miki aure da ko ma waye????
Essha ta Kara fashe da kuka tace” da Allah ka taimakeni”
Yayi dariya yace” ya matsayi tsohuwa wajan aguki?
Tace” kakana ne”
Yace” Wana fa? Yanuna daddy karami. Tace uncle na” murya na rawa
Waena mutani fa? Ya nuna tsoho da saurayi da yariya dake guri
Tace” basan suba”
Oga yakira daya daga ciki yarashi yace” Kai kurmo?
Ya amsa da yadai oga? A murya mashaya.
Oga yace” sama tsohowa na bindiga “
Kurmo yace” an gama oga”
Essha tayi sauri ta rike mishi kafa , ta saki gyalleta ya fadi a kasa, gashi kana suka zubo har baya, Bata ko damu ta gyara ba sbd tana ciki tashi hankali , tace” da Allah Kar ku kasheta
Oga yace ” toh da sharadi , zamu aurar dake ga duk aka kawoshi na, kinsa maiyasa bamu hadaki da wacan ba yanuna saurayi, bai jira amsartaba yacigaba, saboda ango ne , Yana da aure Kuma mu shaida, inbaki Amince ce da bukatumuba , zamu kashe kakaki, uncle ki dake Kara kaki”
Daddy karami ya tsorata yace” kuyi hakuri ku kyalleta , ni ku aura Dani ama da Allah ku kyalleta”
Oga yayi dariya yace” Alhaji yara ka nawa ?
Daddy karami ya amsa da bakwai”
Oga yayi dariya yace ” mu budurwa da saurayi muke hadawa, muke aura dasu saboda sufi barna, Alhaji Inka Kara magana ana, toh lallai zamu kawar da Kai, ya juya ga Essha ya daka mata tsawa yace ” ki Amince ko ko so kike kiga mutuwar ahaliki”
Essha ta juya ga kallota ga hajiya da Daddy karami ta sukunyar da Kai kasa tana hawaye, tana zance zuci baza ta iya Bari a kashe hajiya da daddy karami ba, zata Amince.