DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL
Daddy aranshi yace” wani amsa yaka mata ya ba bawa Allah na? Kai na ma fasa gayamishi abunda yafaru” baice uffan ba ya Mike yabar office din fuska cike da damuwa..
Yana fita Dr Abbas ya tabe baki yace” tundama iriku bakusan gaskiya, kullum Kuna tsakiyar yaraku Kuna washe musu hakora Wai shi so????, Kaya sai Wanda suka sa, Tayays bara’aji sha’awa yi musu fyade ba, toh kawace da yanta ma na kusan rabasu very soon “ya kada hannu..
Daddy na fita magaganu Dr Abbas ne ke masa yawo akai, sai tambayar kansa yake” ayya Dr Abbas ne kuwa amintace makwabcishi, shine yake gayaminshi haka, bai tayashi jaje ba, bai Kuma San kan magana ba shine ya yake hukuci, hmmm yayi ajiya zuciya, Yana gode ma Allah a yanda kaddara nashi yariya yanzo a haka , da aure akanta komai ya faru.. yama kanshi alkawari baya family shi bawanda zai gayama ko da kuwa abokaina shi ne, dun yasa tabas bawanda zai yarda da zanceshi, ya bar ma Allah komai, ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi……
Ur comment is my strength ????????
Comment &share????????????????
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
DOCTOR ESSHA
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
WRITING BY
J Hajara
???? MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ???? ????️
Kungiya d’aya tamkar da dubu. masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.????????
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣
Ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi, ya nufi daki da aka kwantar da Essha,Yana kaiwa baki kofar suka ci karo da daddy karami da haryanzu kuka yake, daddy ya kalleshi duk ya hargizai yajashi gefe suka zauna a kujeru da aka jera agefe dakuna. Baya su zauna. Daddy ya kalleshi yayi ajiya zuciya yace” yakamata ka daina kuka na haka duk abunda yasamu bawa mukadarine daga Allah, yanzu kawai munjira farkawata”
“Yaya kunya hada Id……
Daddy ya daga mishi hannu yace” ya’isa haka, Kar ka Manta fa duk abunda yasamu bawa haka Allah ya rubuta mishi, ni musulmi ne kaima haka, Kuma duk muyi Imani da kaddara, Ina Kara godema Allah ba keta mata haddi sukayi ba, aure suka hada rokona ana shine Allah yasa ya zamto alkhari, idan da rabo za su hadu tom, dun ace matar mutum kabarisa, fatana Allah yaba Essha lafiya da juriya”
Daddy k ya amsa da ameen yaji dadi kalamai daddy, sukara kwantar mishi da hankali, suna zaune suyi jungum sanda aka Kira sallah magarib suka Mike zuwa masalaci dake ciki asibiti.
Har akayi isha’i, Essha Bata farka ba, mummy na makale a gefeta , wata likita daban tazo takara dubata ta tabatar musu cewa suyi na bada jimawa ba zata farka.Dare ya tsala dukasu ba bu Wanda ya runtsa mummy da Daddy, hajiya da daddy k tun baya isha’i, Bala driver ya wuce dasu gida dun su huta.. Essha kuwa can tsarka dare ta farka batama gane kosu wa ye akanta sai kuka take tana fisge fisge tana magaganu” hajiya kuce mishi ya sakeni wlh basan aure, na tsaneshi, mugu ne, hajiya ki taimakeni”
Daddy da gudu yaje yakira likita dake da duty a daren yana zuwa ya mata allura bacci, mummy kam tayi kuka da Bata tabayishiba..
Washe gari sai misali 1:30pm na Rana Essha ta farka.” Alhamdullila ta farka” maganar nurse din data zo dubanta ta ratsa dodo kunnuwansu haka yasasu juyowa a hautsune Dan gani zahiri abun da kunnuwasu suka jiye musu” Tabbas ta farka” mummy ta fada lokaci da idanuwansu suka hade waje daya, da sauri ta karasa wajenta tana ” Essha daddy” ta fada Tana kokari ruko hannu ta, Essha ta Mike da ga kwance da sauri ta rugume mummy ta, ta fashe da wani kuka Mai kashe jiki Mai sauraro, mummy ma haweye takeyi tana shafa kwantace gashi ta da ya gaji da hargitsewa.
“Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life” ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi ” Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa …. Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka” daddy why me? Why? Why?
Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace” ya’isa haka Essha daddy, ki daina ai’bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma’aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA” yaja mata kumatu yayi murmushi ” ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke”
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya, Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace” Essha zanje sallah ankira zuhur”
” Ni ma zanyi sallah daddy” ta fada Tana share hawaye , tun jiya banyi sallah ba”
” Toh mummy ki da antyki zasu tamaika miki” ya fice da sauri baison ya rasa jam’i.
Nurse din ta kalli mummy tace” hajiya bara na taimaka mata dun ba’ason tayi kwakara motsi saboda dinki dake jikita”
Essha ta makale kafada ta tura baki tace” uhm uhm mummy nane zata taimakamin”
Nurse tayi murmushi ta shafa kanta tace” okay beauty badamuwa Bari na baku waje” ta fice..
Mummy ta Mike ta dauki flask din da hajiya suka kawo da safe, tafasheshe ruwa ne dam , tashiga toilet ta juye a baho wanka, da taimako anty zainab ta kaita toilet, ta zuba gishiri kadan ta Kara surka ruwa, sanda suka Kai ruwa Rana Essha ta Amince ta shiga ruwa zafi, ihuta yagama cika asibiti, kuka tasaki da Karfi tana Kira hajiya da daddy ta su zo su taimaketa, Wai balle Essha iyaye raki.. sanda mummy ta tabbatar ta gasu sosai sanan ta cire ta tasata tayi wanka janaba ta Dora alwala tafito, tan Dan ji dama dama, Dakar take takawa mummy na rike da ita, har su ka Kai baki gado, haweye kawai take sharewa ta hura baki, ita kadai tasan yanda takeji a zuciya ta, sai tsine Aliyu takeyi, yasha Allah yaisa ba adadi.
Mummy ta shimfidar mata daddurma tabata riga da skirt na atamfa tasa da hijab , a zaune duk ta Rama sallolita tana hawaye..
ABUJA
Gari na wayewa ummi tasa su a gaba sai fada take musu” tun jiya nagaya muku cewa su shafi Aliyu ama kuka ki yarda da batuna, gashi har su na nema sumishi illa, Allah sarki bawa , Yana ban tausayi , ke Kuma aljana Essha, Allah yama jikana kataga karfe dake” Mami ta amsa da ameen sanan tace” ummi maiye mafita?
Ummi ta rike haiba tace” mafita kenan ana sallamorshi atara malamai Yan ruqiya kawai suriga mishi tofi har tasakeshi”
Tycoon ya Mike yace” ummi ni zan wuce asibiti”
Tace” bamugama magana ba”
Yace” duk abunda kika ga yadace shi za a yi, sai na dawo”
Mami ta Mike tace” jirani na dauko mayafi na muje”
Yace” sai ki fitoh”
Suna isa asibiti Tycoon ko yaji ra a bude minshi kofa ya bude kofar da kanshi, guards na gani hk da sauri suka bi bayashi ya dakatar dasu.. I C U ya wuce Mami na biye dashi, suka Tara a canza ma Aliyu room an cireshi a I C U. Mami tayi ajiya zuciya tace” Alhamdullila son yasamu sauki tunda acireshi a ICU” tana magana saiga haydar yamusu iso zuwa harzuwa daki da Aliyu yake , Allah sarki, Hafiz suna na a zaune su zuba uba tagumi harsu dan fada kamar a jikisu ciwo yake, Tycoon ya binsu daya baya suka yi musabaha cike da girmamawa suka gaida mummy ta amsa .