DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mummy ta ce” yihakuri hajiya kidaina kukana Ina ga baba su khamis sai yakaiku ko? Daddy ya amsa” bazai iya tuki ba, saboda Yana da ciwo a hannu, kawai yadan za’ayi za Kira baba driver yakaiku . Ya dauki waya yakira baba driver yace mishi yashirya zai Kai su hajiya kaduna, yace toh Alhaji ba matsala, da karfe nawa ne tafiya? Biyu ne toh Alhaji sai nazo.

Da misali karfe biyu su Essha su shirya tsaf za su dauki hanya kaduna kaduna gari governor.tasha dogo rigata na less Black yana da digo pink aciki, fuskana bawani makeup ama duk da haka ta fito, tayafa gyaleta Pink, takalmita hk, ta fito gwani sha’awa son kowa ki Wanda yarasa. Har zata shiga motar, sai ta tuna ta Manta da jaka Kuma a akwai wayata aciki da abubuwa da baza arasaba, ta fita da sauri ta shiga ta dauko.

Tana fita taci karo da mum nata rike da calendars da jaka da yawa na biki, ta Mika mata gashi kiba hunaisat, daddy yafito da bandir din hamsin hamsin yabata daya, ta amsa tayi godiya, daddy yace Essha banda yawo kinjiko ta gyada Kai, ta duba daya daga ciki jaka taga Kaya cinye cinye ne na biki.

Tace” gsky mummy na kiyi kokari. Abu fariciki ma tana duba baya jakakuna taga hotuna hunaisat da angota suyi kyau, a kasa Kuma asa Courtesy by Sis Essha.wow mum nagode, ta rugume meta, baba driver sai horn yake ta yi Alama tayi sauri, baya San dare yamusu a hanya, Kuma gashi yau Friday. Da sauri ta bude boat ta zuba Kaya ta shiga mota, mufeedat sai ihu takeyi zatabi ta, Walid da khairat har da gutu hawaye, daddy yajasu zuwa ciki, yace addu’a zakumusu, Allah yaqiya hanya ba kukaba, daker mum ta lalashi mufeedat tayi shiru sanan bacci ya bigge da ita.

Essha ta texting ma Khalid da bestie mun wuce, Khalid ne ya reply. Da Allah ya tsare hanya dear.


ABUJA, NIGERIA.

Wani tamgameme gida ne na gani a fada, girmashi kamar mansion, na lura duk girma angwan ba gida da yakai Wana girma da haduwa, baki gate din kuwa duk security ne, gaba da baya, dukanisu sanye da black suits. Ciki gida Kuma ba’a magana dun ciki kamar outside country,

Gida ALHAJI UMAR TYCOON kenan, shaharare Dan kasuwa, Kuma cikake Dan boko, daya nimi yataka dangote a kudi, da shahara, yakai yakawo ma yayi kwari suna tun daga kasar mu Nigeria har kasa waje, bawanda zaka tambaya waye Alhaji Umar tycoon baisaniba, koda karami yaro ne,

Alhaji Umar tycoon bafilatanine, da asali jahar Nasarawa , haifafar gari uke, mahaifishi shine sarki gari, subiyu aka Haifa, Tycoon da kanishi Mai mulki gari a yanzu, Mai martaba Yusuf isa, a babba masauratana Mai take Yakanaji. Maihifisu ya jima da rasuwa.

Saboda shahara shi a kasuwanci ne yasa abokainashi suka masa suna TYCOON(tycoon na nufi babba business man).

Matashi biyu, hajiya hajara itace uwargida anakirata da Ammi, sai hajiya Khadija, itace amarya anakirata da Mami.

Duk tari dukiyanshi nan yarashi bakwai kacal Allah ya azurtashi dasu, alhamdullila dai toh, don a zamani yanzu wani ma na nema baisamu ba .

Yara Ammi uku, Aliyu, rukaya anakirata da siyama,sai autarsu Sofia, Mami na da hudu, idriss , fauziyya, Isa, sai hammatul Rahman suna kirata da Rahman,

Duka yarashi a kasa waje sukayi karatu.

Aliyu ne babba cikisu, shine Dan gaba goshi tycoon, sbd Aliyu akwai hankali da biyaya, da tun yana karami aka fitar dashi wajen saudia, yayi shekara goma cib, sanan tycoon ya yawuce dashi Russian , idriss yagama karatun law, Babba barista ne Mai zama kanshi, sai fauziyya Tana aure da yaro governor katsina state, sai rukkaya, babba ma’aikaciyar gomanati wace kasa ke dama da ita, sai Isa yagama karatun shi, ya dawo gida service, Yana service a illori, sai Sofia da rahma suna mataki secondary, suna jss2 a Turkish international School dake abuja.

Yara gida suna da tarbiya Sosai, ga ilmi addini, basu da raini ko Kuma kaskatar da talaka kamar yanda waesu yara masu kudi keyi.

Mahaifiyar Aliyu wato Ammi, Yar kaduna ce, family house nata na kaduna, yayita uku, uncle bello, uncle Fahad, uncle auwal, mahaifisu ne kadai a raye, suna kirata da ummi( kaka Aliyu).

Yau ko wani Dan family din tycoon na gida, sbd yau za’atarbi shalale baba, kowa a family din sai murna sukeyi yau big brother Aliyu zai dawo.

Yanmata family su Sha wanka, masu aiki sai safa da marwa kawai sukeyi a goge nan a gogecan, so ke Wana Dora wancan, kamar za’ayi sukai dari, haka aketa jera abinci yafi kala ashiri a kan dinning,

Da misali karfe biyu jirgisu zai sauko, Aliyu shekarashi shida kenan rabon shi da Nigeria, sai yau zai shigo kasarshi ta gado.
Akala shekarunshi sunkai talati da daya.

NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA

Sai jijiniyar mota kawai kakeji a airport.
Motoci su Kai talati kowani baya mota ansa TYCOON baro baro da number shi.
Yau dakashi yazo airport don tarba shaleleshi, duk sun fito ana jira isorwashi.

Can a jirgi , mutani nata sauka, can na hangi wani hadade guy yafito, kyakyawa na karshe, ko shi yayi kansa iya yanda zaiyi kenan, Aliyu kenan,

Aliyu fari ne ama ba kal ba, dogone ama ba zankaleleba, dai dai, shi ba ramame bane ba Kuma Mai kiba ba, a tsayakiyake da kirjisa me fadi normal, hanci sa Mai kyau da tsari, baiyi tsini can da yawa ba, gashin kasa, Wanda ya yarashi luf dashi, baki ga santsi da laushi kamar na India, gira sa Mai yawa ga kyau, idanu na Dara dara, farare kal kal, habarsa Mai Dan tsayi, bakisa das dan daidai, lips dinsa su ba pink ama kamar light pink, ya bude baki yayi murmushi hakoransa Yar yar, farare kal kal, ga wani dimple nasa Yar ciki Yana lotsawa gwani sha’awa, fatarsa kuwa shar2, subhanallahi Aliyu yagama haduwa.

Jikishi sanye yake da black jeans, da top fari, kafarna kuwa tasha????farare, hannu shi kuwa zobe azurfane, sai agogo rolex, sai kamshi ketashi.

A hankali yake sauka a matakalar jirgi, a kasa zuciya shi yace Alhamdullila.

Doctor Essha
????‍⚕️
Written by j hajara

1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣

Yace” Alhamdullila yau na shaki iska kasana” yacigaba da sauka a hankali, Yana kan sauka yaji wani muguwar faduwa gaba, nandana yariga karato inalilahi waina ilaihi raju’un. Haryaji ya daina ji.

Yana waigawa ya hangi su Ammi da dad.can gefe daya security ne, ai nandanna ya hada fuska, don shi arayuwashi yatsani ya farka ya ga security Dina, suna daga ciki dalilai da bayaso zuwa Nigeria, anashi tsari, security kamar takura rayuwane.

Aliyu Yana da sanyi amfa a kwai zuciya inkatabashi, ga tausayi da jikan Dan Adam, ko duma yayi girma kasa waje ama baya shaye shaye, baya Nima mata, mata ma Basu a agender nashi.

Sai kwanaki ne yariyar aboki daddyshi suka hadu a Russian, Tana nacce mishi Wai Tana sonshi.

Sunata SUHAIMA, suhaima yargatace, duk abunda ta keso daddy ta na mata, kyakyawa ce a fuska, ama ba diri ta tafi kamar pencil????.

Tana gayama daddy yazo yasamu tycoon, yaminshi magana,????dayake abokanaine. Yace” ba damuwa zai ma Aliyu magana, shi Kuma Aliyu duk abun daddy shi yasashi yanabi, shiyasa yace ya amince da aure.

Suhaima tana makale mishi har yasoma saki jikida ita, har ayi musu bayko,ansa Rana, aure sai nan da wata uku tukun.

Aliyu nada abokanai gudu hudu Wanda yake ji dasu, Kuma duka atare sukayi karatu,

Haydar namesake nashi, Suleiman, hafiz, fawaz. Aliyu da Hafiz su karata business,fawaz da haydar medicine, Suleiman civil engineer.
dukasu mazauna abujane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button