DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL
Isa yace”Ammi kiyi hakuri, Sofia fa ta girma, Kuma ta girme ma Rahma kiga kenan dole a nunamata ta girma”
Sofia ta fashe da kuka tace” kiji fa Ammi, Yaya Aliyu tare yake tsaya mana abun, shine zakacemu na girma, kaje har Dubai kazo ma Rahma da Teddy nikuma Empty wlh Ammi da sake”
Mami tace” common shut that ur stupid mouth, ki girma bakisan ki girma ba”
Rahma tasa dariya tana ma Sofia gwalo..
“Ammi ki ganta ta na min gwalo ko?
Ammi ta Mike a fusace taje dinning ta dauko Teddy tace” tunda haka ne kema ki rasashi kenan har ki iya mata gwalo”
Idrees yace” yihakuri Ammi ki bar mata, itanefa autar, Sofia Kar ki damu za’a siyo mata nata”
Ta baka Mai harara tace” when?
Isa yace”Ammi duk ranar Dana koma”
“Baku isaba, yau Dina nakeson kasiya mata nata inhar Kuna neman zaman lafiya, toh yau nakeson Naga autar na da Teddy”
Mami tayi dariya taji tanakara son Ammi, har taiya fifita Yar kishiya akan nata, Allah sarki Ammi Mami ta fadi haka a zuciya ta, tace” Ammi ki shagwaba ta dayawa, Teddy na fa tana dasu bawai ta rasa bane, toh ima irishi takeson , ai’na za’a samu kalla Teddy Mai girma haka?
Sofia ta shagwabe fuska tace” Ammi akwai a ShopRite Wanda ma yafi wanan girma”
“Yawwa tashi kuje ya sanya Miki”
Jin Ammi ta fadi haka ta Mike da murnata ta dauko gyale ta yafa ta kalli Rahma ta mata gwalo tace”Kuma zanyi waya da Yaya Aliyu yazomin da Sari, zance Kar ya kawomiki”
Mami tace”oho dai”
Isa ya Mika ya na hararata Yana kwafa, Ammi tagani tace” lah Sofia maza dauko min mayafi na rakaku danaga Alama zai ita karya Mike a hanya”
Ya marairace fuska yace” haba Ammi ba abunda zan matafa”
Tace” yi min shiru nasan halika Sarai tashi muje”
Sofia ta Mika mata mayafi ta yafa, zasu fita Mami ta Mike Tace” da Allah kuda jirani na dauko handbag Dina, akwai small Shipp danakeso yi”
Sofia tana tafiya tace” Mami Meet us in the car, mun muyi gaba”
Bada jimawa ba, Mami ta fito suka shiga motar, motoci uku na guards na baya dasu masu rakiya, duk aka tada motoci zuwa ShopRite, suna isa , aka bude musu,Sofia tayi sauri ta shiga tayi hanya guri Saida Teddies da aka kilace su a glass manya manya dasu, Su Ammi na biye da ita, Mami kam guri shopping ta nufa, guri Saida Teddies badai nisa daga guri zamasa Sadik, Mami hartagama shopping, Sofia na na guri zaba teddy ruwa ido yahanata zaba da wuri, Isa na gefe yanaji kamar ya bugeta ba hali ga Ammi ta kasa ta sare tana kareta…
Sadik vannila ice cream ne a gabashi baiwani Sha sosai ba puzzle game na Mickey mouse yake ta hadawa…
Walid dake zaune ya Mike yace” bros zanje na sanyo tickets na movie di na kafi ya kare, zanbiya Kuma. Na sanya coins dun zamuyi game da boy”
Amir yayi murmushi yace”yawwa Walid Kama kana Raina, abunda nakeson fada kenan, sai ka dawo”
Walid ya wuce.
Amir ya Mike ya kalli Sadik yace”Boy let me use the toilet, don’t go anywhere” ya kada Mai hannu
Sadik ya kada Kai Yana murmushi, Amir yasha fa Mai Mai yace” sai na dawo, good boy”
Amir ya wuce suka barshi shi kadai zaune, afi mintina acikisu babu Wanda ya dawo, Walid ya sanyo tickets, gurin Sanya coins ne a cika shiyasa baidawo da wuri ba, Amir Kuma Yana fita daga toilet ya hadu da wani course mate nashi sunata zuba hira, a tunanishi Walid ya riga yadawo shiyasa ya kwantar da hankali shi suka cigaba da hira..
Sadik yahada puzzle har yagaji, shiru shiru aciki su babu Wanda ya dawo, har ya fara gyagadi, yajigana da chair dayake, har yayi bacci..
“Wai haryanzu bakusamu teddy da ya muku bane? Ammi ke Kuma ki tsaya biye ma shirmata” cewar Mami..
Isa ya harari Sofia yace” wlh kuwa Mami, ni da friends Dina zamu fita fa, ama Wana stupid girl din tana Bata min lokaci”
Sofia ta tura baki zatayi magana, Ammi ta tareta tace” yi shiru kallesu, natsu ki zabin Wanda ya ranki keso”
Sofia tayi murmushi tace”yawwa Ammi na”
Mami tace” uhmm kafi kugama dai bara na nemin guri na huta kafi ku Gama shirmeku”
Ammi tayi dariya tace”dayafi Miki”
Mami ta juya tabin gurin da kallo, bawasu mutani sosai a downstairs din anfi yawa a sama, tables da suka jera, two table’s ne daya ma an cikashi, ta kalli damata guri table dinsu Sadik, daka chair din Sadik ya Bata baya, Bata ga fuska yaro dake zaune a Kai ba tace” yawa nasamu guri zama, bazaiya juri tsayuwa ma shirmena na”
Ta karasa table din hankali ta na kansu Ammi, Mami tana murmushi, tana Alfahari da ita, a matsayi Yar uwa ta dauke ta ba kishiya ba,ta ja chair ta zauna tana kallo Sofia nata zuba shirme Ammi na biye mata, Nan taji Kara faduwa Abu kusa da’ita, ta Kai duba ta kasa taga Mai yafadi taga p-cap ne da puzzle game na robar , su fado lokaci daya ta tsuguna ta kwaso tace” Allah sarki Dan samari ba……..magana makale mata yayi , gabata yayi muguwar faduwa sakamako tozali datayi da fuskar Sadik daketa shara baccisa Hankali kwance, Ido Mami ta ware sosai Dan ta tabbatawa kanta abinda ta gani, da sauri cike da razana ta goge idota” Wai son ne kemin gizo Yana karami ko dai maikamadashi ne?
Jiki Mami na rawa ta Mike taje kusa da Sadik ta shafi fuskarshi abun mamaki ma Dan digo baki karami dake fuskar son nata duk yanadashi, abun da yakara razana ta Yana bacci murmushi dimples nashi suka Kara lotsewa gabadaya, jiki ta na rawa takai hannu ta tabo dimples din murya kuka tace” inalilahi waina ilaihi raju’un, hasbiyalahuu waniimal wakil, walahi son ne, Wana sonane, ko dai gizo yakemin ne Yana karamin?
Takara murza Ido da kyau ta bude taga tabbas ba gizo idonta kemanta ta fashe da kuka……
.. More comment more typing ❤️❤️❤️❤️❤️
Love you guys ????????????
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
DOCTOR ESSHA
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
WRITING BY
J Hajara
???? MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ???? ????️
*M.W.A*
_Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta Kuma Nishad’antar da masoya ta.????????
6️⃣8️⃣
Tycoon jiki na Bari cike da tashi hankali ya ciro wayarshi a aljihu shi ya bude ya dialing number Aliyu, buga daya Aliyu yayi picking, ya Soma gaidashi cike da girmamawa.
Tycoon bai amsa ciki baci rai yace” Aliyu kana ina ne?
Aliyu yaji tambaya a bazata yace” Daddy ina India mana na fadama ko ka Manta ne? Lafiya dai ko naji murya ka haka?
Tycoon tambaya ba murya na rawa yace” inasa gani ka, na baka na da three hours Aliyu ka dawo gida”
Aliyu ciki rudewa yanayi da daddy nashi yake sounding yace” Daddy laf……
Tycoon ya katse shi a tsawace yace” bana san ji wani tambaya daga baki ka I said just come back home”
Ya kashe waya kit, jikishi na karkawa yayi Kama zai fadi da sauri Ammi dake gefeshi ta tareshi ya zauna Yana kada Kai cike da damuwa….
Duk parlour akarasa Mai baki magana Dan duk a razane suke Aliyu ne da Dan Kai abun da mamaki yake..
Tycoon ya daga Kai ya kalli Sadik da duk ya tsorata da gani canzawa shi lokaci daya ya ka kula murmushi yace” come”
Yaki zuwa ya makale ma Isa a jiki Nan ya Soma kuka Wai zai su koma dashi guri mummyshi, lalashi duniya ama Sadik yakiyi shiru, da suka tambayi a ina mummy nashi take, ko amsa su baiyi ba ya cigaba da kukashi…
Aliyu naji Daddyshi ya kashe kira ya Soma bin waya da kallo, ya soma tambaya kanshi” mai yasamin Daddy? Ko dai workers nasu ne suke rikici basuyi aiki da ya kamata ba?
Ya ma kanshi tambaya da babu amsa, ya tabe baki ya Mike ya tada suhaima dake ta shara bacci a gefeshi, ya sanar Mata zan su koma Nigeria yanzu na. Suhaima ta Mike tana Bata fuska Tace” haba darling shekaran jiya fa mukanzo kace zamun koma da gagawa haka, ka Manta ne haryanzu fa baka Gama amsa medication naka ba”