DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Security ya nuna na mata wani wani kerere Mansion da girmashi kawai yayi Rabin angwan Tace” Thanks” ta tada motar gabata na tsanata faduwa ta runtse ido tana” inalilahi waina ilaihi raju’un” ta budesu tana kallo saiti gida, taga wani motar Mai tinted glass ya wuce ta gabasu zuwa ciki gida..
Daddy ya kalleta yace” karasa mana”
Ta hadiye wani yawu kut gabata na faduwa ta nufi bagaje gate din gida, suna isa dakanshi ya bude, suka sa Kai, suka sake cin karo da wani gate da securities ne birjik kala kala.. a sama gate din asa TYCOON RESIDENTS Essha saban rudewa ne yasa Bata karata Mai yake sama a rubece ba, duk tabin ta rude ta rasa dalili,Wana Second gate din na da tari security da kyar suka barsu suka shiga..Suna shiga Essha tayi parking kirjita na tsanata faduwa, ita da Daddy suka fito, daya daga ciki masu tsaro ya musu iso zuwa guest parlor.. suna zuwa Essha haka kawai jikita ya Soma rawa Kamar Mara gaskiya tanemi guri ta zauna.
Daddy yace” Kira number”
Ta dialing number bugu daya aka dauka, ta sanar mishi gasu a ciki gida.
Yace taba security dake tare dasu, ta minka ma security, bandai ji abunda Tycoon ya sanar mishi ba, security Kai kadai yake dagawa cike da girmamawa, Yana gama waya ya Mika ma Essha yace” ku biyoni” yayi gaba.
Essha suka mike suna biye dashi sai tafiya sukeyi harsu ka isa Babba part din gida, dayafi koina tsaruwa.
Essha tun kafi su isa ciki tasoma ji dariya Sadik, ciki rudewa ta Soma kwala Mai Kira, Sadik na kan cinyar Aliyu yaji ana kwala Mai Kira yagane murya na mummy shine ya Mike cike da murna yace” my mum’s voice, she’s here” ya Mike zai fita da gudu yaci karo dasu Fawaz da shigowansu kenan tare da matarshi, na kalli fuska matar da kyau abun mamaki Bestie nagani, Allah Mai iko..
Daga Fawaz har sumy baki suka bude cike da mamaki suna kalloshi, Fawaz ya murza Ido muryashi na rawa yace” what! Bud.. buddy!
Tycoon yataso ya dafashi yace” ba Buddy ka bane, gashi can”
Fawaz yadago yaga Aliyu zaune yace” Ammi Daddy Wana fa?
Ammi ta tsuke fuska Tace” sai ka tambayi Buddy naka gashi a zaune”
Ammi na rufe baki Security ya doka sallama suka amsa aka bashi izini shiga, ya shigo yace” Sir ga baki sun karaso”
Baigama rufe baki ba Daddy ya yaye curtains yashigo da sallama.. Sadik naganishi ya daka tsalle ya rugumeshi, dun yageneshi Yana gani hotuna shi a waya Mummy shi…
Yace”Grandpa I miss you, where is my mum?
Daddy ya waiyaya yaga Bata shigo ba yayi murmushi yace” yanzu zata iso”
Hankali kowa ya dawo kansu, Banda Aliyu da ya sukunyar da Kai yanaji zuciyarshi na buguwa…
Daddy ya gaisa dasu Tycoon yana musu godiya, Tycoon zai amsa
Essha ta shigo da sallama ta a hankali, Sadik ya sauko da gudushi ya rugume ta” Mummy, i surely knows that you will come, I miss you”
Essha ta Kara rugumeshi tana kuka yace” Mummy stop crying” ya share Mata haweye, ta Mike ya ja hannu ta Yana” Chaliye Mummy, mujhe bhok lagi hai( zo muje Mummy, inaji yunwa)..
Parlor sai kallosu suke gwani sha’awa, duk cikisu kuwa babu Wanda yaga fuskarta kanta a sukunye yake. .
Sadik yakara ja hannu zuwa hanya fita yace” Chaliye Mummy”
Ta rusuna a gabashi tace” baza mutafi yanzuba har sai ka ma Wanda suka taimaka ma godiya” ciki harshe turaci ta fada..
Sadik yayi murmushi yace” yawa mum, zo na nunamiki wani uncle, fuskar mu daya” Sadik ya fashe da dariya yayi sauri ya isa gaba Aliyu yace” hey uncle meet my mum”
Essha ta dago ta kalli Aliyu shima ya dago karaf idosu ya sarke ciki na juna, Aliyu ya Mike a zambure Yana nuna Essha na yaji kanshi na wani Sara Mai..
A kidime ciki tashi hankali zalla tsoro Essha ta saki gigitaciyar Kara da ya tsorata da kowa dake wajan, tamkar wacen ta zare ta Soma ja da baya itama ta na nunashi , ta kasa furta koda kalma daya labbata sai rawa suke tamkar maiji sanyi ciki sauri ta buya a baya Daddy ta Tana sauke ajiya Hadi da fashewa da wani riketace kuka ta runtse ido tana addu’a Allah yasa mafarki take.
Aliyu tsaye ya dafa kai, fuskarshi ya canza kala Kamar a mafarki yake gane komai na dawuwa mishi sabo, ya bude ido yaga komai na guri na mishi bibibbiyu jiri yake gani, Yana nuna Essha, gabadaya waje kallo yakoma kanshi su kansa fahimtar Mai yake nunawa..
Aliyu yayi baya zai Fadi Tycoon yayo kanshi da gudu da saura brothers nashi suka tareshi.
Suhaima ta hadiye wani kululu bakiciki tarasa gane maikefaruwa..
Aliyu a galabaice ya shifa nuna Essha dake boye a Daddy Yana cewa” Daddy Ammi, Es..shaa, Daddy Essha Dina gata yau a gabana” diff numfashi ya dauje, ya sume..
A razane Mami ta Sanya hannuwata bibibbiyu ta talofo fuskarshi……
???????????????????? Any errors u see I repeatam typing errors ne, and nobody is ferfect ????
Lovely fans nagode da kulawarku adduoiku nagode sosai ???????????? jiki Alhamdullila…
Love you guys ❣️❣️❣️