Uncategorized

HAJNA 19-20

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 19-20

*********************

Bayan kwana biyu da yanke wannan hukuncin, sai ya zama Hajna bata da walwala a gidan su, kullum tana gida bata fita, ko ɗibar ruwa ma an hana ta zuwa, Baffa da kanshi yake fita ya ɗibo wani lokacin kuma ya samu yaro ya kawo musu, gashi tunda aka hana ta fita kullum sai sun yi faɗa da Qaseem, yau dai ta yanke hukuncin zata kira Fahna ta gaya mata duk abunda ke faruwa. 


       Wayar ta ta ɗauka ta kira Fahna, “hello Fahna”Hajna ta faɗa lokacin da Fahna ta ɗaga wayar, Fahna tace “hello ya kike Hajna “, “lafiya ƙalau Fahna, ke fa, ya kike?”, gaisawa suka yi, “Fahna wallahi ina cikin matsala, babba! “, Fahna tace “subahanallah me ya faru”, “Fahna Baffa ya hanani fita, ga shi Qaseem ya ƙi ya fahimce ni”Hajna ta faɗa, Fahna tace “kema da laifin ki, ki bari yau zan dawo gida sai muyi shawara “, hakan da ta faɗa yasa Hajna jin sassauci a zuciyar ta, sallama suka yi kowa ya kashe waya. 



   Da marece Fahna ta iso shinkafi,unguwar ajiyawa aka sauke ta, gida ta shiga, taci abinci tayi wanka, sannan ta nufi gidan su Hajna, in da ta samu Baffa a ƙofar gida, gaida shi tayi ya amsa sama-sama, a ranshi baya son kusancin Hajna da Fahna, amma ya zai yi, ɗiyar aminin shi ce, kuma gashi ba wanda yasan halin ta, idan ya hanata zuwa gidan shi mutane zasu zage shi, suce ai dan mahaifin ta ya rasu ne, bayan haka ma be kamata ya guje ta ba, baya da wani zaɓi da ya wuce ya taya Hajna da addu’a Allah ya tsare ta, wucewa tayi cikin gida, ɗakin Umma ta fara zuwa, gaisawa suka yi da ita, sannan ta nufi ɗakin Hajna. 


     A ɗaki ta same ta, murmushi Hajna tayi tace “har kin ƙaraso kenan? “, Fahna tace “eh dama ina da niyyar zuwa, shiyasa ban wani ɓata lokaci ba na zo, yanzu faɗa min minene”, Hajna tace “ Baffa ne “, “me ya faru” Fahna ta faɗa, nan Hajna ta kwashe labarin komai ta bata, Fahna tace “yanzu dama ɗaya kike da ita “, Hajna tace “wace irin dama ce”, Fahna tace “ki gudu ki bar gari “, Hajna tace “na gudu fa kika ce, inaa Fahna bazan iya ba”, Fahna tace “to kisa a ranki kin rasa Qaseem har abada “, shiru Hajna tayi na wani lokaci, Fahna tace “tunanin me kike yi, damar kenan gare ki”, Hajna tace “to Umma fa ya zanyi da ita, kinsan dai ba zata goyi bayan haka ba ko “, Fahna tace “to ai ba cewa nayi kiyi shawara da wani ba, kawai cewa nayi ki guda, sai da a tashi da safe baki”, Hajna tace “ ya Baffa na zai yi, Umma zata iya mutuwa saboda rashi na “, Fahna tace “ki daina damuwa akan su tunda kina son Qaseem ya kamata ki samu soyayyar shi, Umma zaki iya kiran ta daga baya, Baffa kuma idan kika auri Qaseem zai yafe miki ai”, shiru tayi domin ba zuciyar ta dama ta mata jagora, tabbas tana so ta samu soyayyar Qaseem, kuma tana so ta aure shi, gashi ba zata samu kusanci da Qaseem ba in dai bata gudu ba, ba kusanci ai ba maganar aure, amma ɗayar zuciyar ta na faɗa mata kar tayi haka, zata ruguza rayuwar ta ne, “Fahna zan yi tunani tukun, idan na yanke hukunci zan kira ki a waya “, Fahna tace “ai ina nan bazan koma ba sai kin yanke hukunci, ke dai kawai kiyi tunani mai kyau, yanzu dare nayi zan wuce gida gobe idan nazo zan ji hukuncin da kika yake”, “to shikenan Fahna “Hajna ta faɗa, Fahna tace “kar ki manta kina buƙatar soyayyar Qaseem” sannan ta fita daga ɗaki. 


    Da wannan tunanin Hajna kwanta kasancewar bata sallah, wayar ta, ta ɗauka ta kira Qaseem amma yana ta rejecting, maganar Fahna ce ta dawo mata a kunne “kar ki manta kina buƙatar soyayyar Qaseem!, kar ki manta kina buƙatar soyayyar Qaseem “, danne kunne ta tayi amma bata daina jin wannan sautin ba, haka ta dinga saƙe-saƙe, daga ƙarshe tayi murmushi jin ta samu mafita, barci tayi cikin kwanciyar hankali. 


 


    Washe gari da marece tana zaune tsakar gida tana gyara kayan miya, Fahna ta shigo, aiki ta taya ta suka ƙarasa, sannan suka ɗaura abincin marece, abinci suka kaiwa Umma ɗakin ta, sannan suka zuba nasu tare suka ci abinci, Umma da Baffa kuma suka ci a tare. 



   Ɗaki Fahna ta jawo Hajna suka shiga, “ke wai wani hukunci kika yanke? “Fahna ta faɗa tana zauna wa kan katifa, Hajna tace “na amince zan gudu, amma yanzu ya za’a yi”, Fahna tace wannan ba matsala bace tare zamu tafi, ke dai kawai ki fito cikin dare da misalin ƙarfe 

1:00 na dare lokacin Baffa yayi nisa a barci sai mu tafi”, Hajna tace “ina zan same ki? “, Fahna tace “bayan gidan mu, zan jira ki, kuma mota zata ɗauke mu zuwa gusau a daren nan, insha Allah”, Hajna tace “to shikenan nan, koma minene za muyi waya dake “, da haka suka yi sallama, Fahna ta tafi. 


    Hajna fargaba duk ya cika ta, a ɗayan ɓangaren akan soyayyar Qaseem ce, a ɗayan ɓangaren kuma aka soyayyar iyaye ce, zuciyar ta na faɗa mata kin riga kin samu soyayyar iyayen ki, yanzu ta Qaseem kike nema, ɗakin Umma ta shiga, yau Umma ba daɗi take jin jikin ta, bata meyasa ba, amma yau gaban ta faɗuwa yake yi, ta rasa dalili, tagumin da Umma tayi shi ya tada wa Hajna hankali, “ Umma ina fatan dai kina lafiya “Hajna ta faɗa, murmushi Umma tayi tace “Hajna lafiya na ƙalau kawai ina tunanin rayuwar gidan nan ne” Umma ta ɓoye wa Hajna fargaban da take ji, Hajna tace “kar ki damu Umma, watarana wannan rayuwar zata zama tarihi, kamar ba’a yi ba “, Umma tace “shiyasa kullum nake miki addu’a ki auri wanda zai kula da ke, mu mun tsufa ba jimawa mutuwa za muyi, amma ke yanzu kike da ƙuruciya, ina fatan Allah ya miki tsawon rai ki rayuwa da masoyan ki”, murmushi Hajna tayi a ranta tana jin son Umma har ranta, dan ta san Umma na matuƙar son ta, Umma uwace da ba kamar ta, kuma macecd ta gari a gurin mijin ta, Baffa zai iya bada shaidar nan, bata da raina abu, ko ya aka bata zata karɓa ta saka mishi albarka, a cewar ta kaɗan me albarka yafi dawa mara sa albarka, “Umma na tambaye ki zaki amsa min ” Hajna ta faɗa, Umma tace “eh ƴa ta me zai hana”, murmushi Hajna tayi tace “me zan yi duniya ki juya min baya “, Umma tace “babu abunda zaki yi na juya miki baya, Hajna in na juya miki baya wa zai so ki, hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka yadda shi”,, hawaye suka zubo daga idon Hajna tace “Umma duk abunda rayuwa ta canza, a kowane hali ni ɗinnan zan so da dukkannin rayuwa ta “, rugume ta Umma tayi suka sha kukan su, Umma na kukan son da take wa ƴar ta, ita kuma Hajna na kukan rabuwa da Umma. 



Anan zan dasa aya…….. 


Sai munji yadda Hajna zata gudu daga gidan su kuma ya zata yi da Qaseem, shi zai haƙura ko a’a. 



Muhaɗu a next chapter. 


Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya 

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button