Labaran Kannywood

Fim ba harkar kirki bace shiyasa “yan fim suke hatsarin Mota suke mutuwa – Dr Abdulaziz Idris

Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Dr Abdulaziz Idris Bauchi ya fadi wata magana akan “yan fim wadda tayi matukar tada hazo a wajen “yan fim din da kuma shafukan sada zumunta.

Malamin yace,harkar fim ba harkar kirki bace, shiyasa da yawa yawan “yan fim din suke hatsarin Mota suke mutuwa.

Sai dai bayan bullar bidiyon Malamin yana fadar haka,anyi cece kuce a shafukan sada zumunta musamman ma a shafin da aka saka bidiyon da kuma shafin Facebook.

Idan baku manta ba,tun a daya bidiyon da Malamin yace Kaf Kannywood babu mai Ilimin Addini,wasu da dama suka fiti suka kalubalance shi akan fadin haka din.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa, kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button