NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 2

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
          *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*



*2*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ko da na shiga daki a zaune na tarar da innah mamaki tare da fargaba ne suka cika zuciyata saboda yadda na ganta a zaune ga kuma damuwa bayyane a fuskar ta, da sauri na ƙarasa wajenta, tsugunnawa nayi tare da dafa kafarta “lafiya na ganki a zaune innah?” Kawar da kanta gefe tayi da alama bata so na fahimci halin da take ciki ba,  sake tambayarta nayi. “Dan Allah innah ki fada min damuwarki ni kadai na rage miki dan Allah ki fada min abinda ya sa ki kuka” share hawayen da ya cika idonta tayi “Babu komai Sa’adatu, amma tabbas ban ji dadin abinda kika janyo mana ba, da kin hakura Allah zai kawo mana hanyar da zamu samu abinci, bakin dan Allah ya tsaga baya hana shi abinci, da baki taɓa musu kayansu ba da duk haka bata faru ba, duk rashin mutuncin mutum bai isa ya keta alfarmarka ba matuƙar baka shiga gonarsa ba, haka zai ganka ya kyaleka, amma sanadin wannan kin janyo abinda za a yi ta goranta mana, shikenan sun samu topic din da zasu rika maimaita wa kullum, dan Allah ki xama mai gudun xuciya da yarda da ƙaddara Sa’adatu, duk halin da muke ciki Allah ya fi mu sani”

Ji nayi kwalla na shirin fito min daga idona a takaice nace “Haka ne innah insha Allah xan kiyaye dukkan abinda zai kawo matsala a tsakanin mu” ledar da ya salim ya bani na miƙa mata, ga wannan ya salim ne ya bani, kuma yace zai riƙa kawo mana abinci kullum mu riƙa hakura da na gidan nan.
Shiru innah tayi sannan tace “Ni fa bana son irin wannan Sa’adatu kin san halin uwar yaron nan sarai bata ƙi taci mana mutunci ba gaba ɗaya, ki dakatar da shi bana so ina zaman zamana a xo a daga min hankali”

“Insha Allah babu abinda xai faru innah ai shi ba shi da matsala kuma tsakaninsa da Allah yake taimakon mu”
bude ledar tayi gurasa ce da nama, godiya ta yiwa yaya salim tare da fatan Allah ya albarkaci rayuwarsa, sai da muka ci muka koshi sannan muka kwanta, amma abin mamaki sai bacci ya kauracewa idanuna maganganun da aka riƙa fada min ne suka rika dawo min cikin kunnuwana, tashi nayi na dauro alwala na fara jero nafilfili, bayan na idar na dauki Alkur’ani na karanta, sannan nayi addu’a Allah ya saukaka mana halin da muke ciki, daga lokacin naji nutsuwa ta lallube zuciyata bakina bai gushe da ambaton Allah ba, ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba.

Kiran sallar asuba ne ya tashe ni, da sauri na dauro alwala tashin innah nayi muka tada Sallah, azkhar muka rika yi har zuwa fitowar rana.

Ina daki ina shara naji ana kwala min kira, jikina na rawa na leka ta window don ganin mai kirana, umma ce mahaifiyarsa salim, a ladabce na amsa mata da “na’am umma”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Wani matsiyacin kallo ta bi ni da shi, “kada ki sake ce min umma domin ni ban haifi mai baƙin jini irinki ba, wato an rasa mai tayawa an ga dana kyakkyawa zaki makale masa ko to sam bazai yiwu ba, yanzu ma gargadi na karshe naxo yi miki babu ke babu salim, na yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninku, ki fita daga rayuwar dana idan ba haka ba kuma baxa tayi miki kyau ba, don baxa ki lalata min shi ba ki gurbata min rayuwarsa, kin shiga  kin fita har sai da yaron nan ya nace miki, gashi yanxu har hidima yake miki, to baxan lamunta ba saboda shi ba ubanki bane ba a kansa nauyin ki yake ba, uban naki ma ya kasa saboda mugun halinki da na uwarki, tun wuri ki kyale shi kafin na fito bainar jama’a na yaye miki rigar arziki”.

Duk maganar nan da take kaina na ƙasa na kasa dagowa sbd bakin ciki, haka ta gama ban-bamin masifarta ta koma ɓangaren su, taimakon da Allah yayi min ragowar matan gidan basu fito sun tayata ba amma nasan duk abinda ya faru da sa hannunsu.

A sanyaye na zame na xauna, cikin jimamin abinda ya faru dani naji innah na min magana “kiyi hakuri Sa’adatu ki daina damuwa Allah muke gayawa matsalolin mu shi muke fatan ya kawo mana dauki, tashi ki kintsa ki tafi makaranta Allah ya baki dukkan abinda kike nema”

Maganganun innah suna ratsa ni kuma suna da matukar tasiri ga rayuwata, ko naji abinda ake min ya dameni idan na tuna da nasihohin da take min sai zuciyata tayi sanyi, sbd innah mace ce mai tawakkali da yarda da dukkan abinda ya sameta na rayuwa, sannan bata yarda taje ta fadawa yan uwanta halin da take ciki ba,  wani lokacin ko tambayarta suka yi dangane da matsalolin gidanmu bata fada musu sai dai kawai tayi murmushi waɗannan dabi’un nata su suka sanya dukkan makota suke sonta. Kintsa kaina nayi na sanya kayana dai-dai na talaka Kasancewar duk kayan nawa sun mutu don rabon da baba yayi min dinki har na manta sai dai makota su tausaya min su bani kwance, allona na dauka na fita tare da yiwa innah sallama.

A soro na ci karo da matan gidanmu sun saka faifan gulamata suna ta tattauna abinda ya faru jiya suna ganina suka kara bada himma wajen zagina kawai dan naji raina ya ɓaci, ban kula da su ba na ratsa ta cikinsu na wuce, daya daga cikinsu naji na cewa “aikin kenan kullum a ɗauki uban allo a tafi makaranta kamar gaske, Allah yasa dai ana ganewa” umma ce ta karbi zancen “ina fa ake ganewa a yi sha’ani dai wai na birni ya cuci na ƙauye, da ana ganewa a rika sata gashi ana so a lalata min yaro” 

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Muryar A’isha kanwar salim naji “mu mun san inda ake xuwa ba wata makaranta ku ake rainawa hankali”
Ba karamin zafin kalmar da A’isha ta jefe ni da shi naji ba, wato kallon ma yar iska suke yi min.

Gidan su Rukayya na wuce don biya mata makaranta sbd na saba kullum tare da ita muke tafiya, dukkan mutane sun saba ganinmu tare idan ma ban biya mata ba duk wanda ya ganni sai ya tambayi inda take. Rukayya kawata ce tun muna kanana, duk da cewa ta dan girme ni amma mun yi matukar shakuwa da juna babu wanda yake jin tsakanin mu, babu wani abu da nake iya boye mata ita ma kuma haka, lokuta da dama idan aka bata min rai wajenta nake xuwa ta kwantar min da hankali, mutanen gidan mu sun yi iya bakin kokari wajen ganin sun zuga mahaifiyarta a kan ta raba mu, amma taki karbar kudirin su saboda ba yabon kai ba ina da nutsuwa da kamun kai kuma ba ni da yawan surutu sannan ban fiye shiga abinda bai shafe ni ba, wannan dalilin yasa mutane suke sona kuma suke son abota da ni.
Saka kaina nayi cikin gidan tare da sallama ban tarar da kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye na wuce daki, a kan gado na tarar da Rukayya tana ƙarasa haddarta don haka ban yi mata magana ba har sai da ta kammala karatunta sannan ta kula ni. “Sa’adatu lafiya yau na ganki a haka da alama ma kamar kuka kika yi” yaƙe nayi kawai saboda bana son na sake maimaita maganar, kawar da tambayar da tayi min nayi da “ina umma ban ji motsin ta ba lafiya?” 
“Yau da sassafe ta fita an kwantar da yar kanwarta a asibiti shi yasa baki ganta ba” 

“Ayya Allah ya bata lafiya” amsa min tayi da “ameen”
Sake jefo min tambayar dazu tayi “ki fada min abinda yake damunki Sa’adatu na sanki da zurfin ciki abu yana damunki baxa ki fada ba,kuma ga damuwa nan a idonki Ina gani, ki fada min komai kin san dai babu boye-boye a tsakanin mu”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Sai da ta yi min magiya sosai na fada mata sbd ban fiye son bude cikina ba musamman ma idan mutum baxai iya yi min maganin abinda yake damuna ba.
Kafin na fara faɗa mata har kwalla ta cika idona, rarrashina ta shiga yi har sai da hankalina ya kwanta na fada mata dukkan abinda ke faruwa da ni, tayi matuƙar tausaya min kasancewata yarinya mai kananun shekaru amma har na fara cin karo da matsalar masu yi min gorin aure, nasihohi tayi min tare da bani misalan da xasu kara min nutsuwa.

Sai da ta gama
 shiryawa sannan muka tafi makaranta.

08094136204

Domin karin bayani

A taimaka a rika comment a rika sharing

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button