NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 13

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
          *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)**Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


               *13*

Bayan an kai Izuddeen police station tafiya Baban Sa’adatu yayi ya kyale shi, tare da alkawarin kada a sake shi har sai ya fito masa da yarsa, ko da yan uwan su Izuddeen suka je duk iya bakin ƙoƙarin da suka yi don ganin an bada belinsa hakan ya gagara sbd dole sai babanta yana nan xa a kashe case din, haka suka taho suka kyale shi ba da don ransu ya so ba.
 Tunda ya bar police station bai xame ko ina ba sai gidansu Rukayya a kulle ya tarar da kofar gidan, wani irin bugun rashin mutunci ya riƙa yi, ummansu ce ta fito da kanta ta bude don ganin mai bugun, bata yi mamakin ganinsa a wannan yanayin ba, don ta san ko wanene malam Salisu kuma ta san kalar tijararsa baya ragawa kowa wannan dalilin yasa da yawan makota basa shiga harkarsa duk abinda zai yi sai dai su zuba masa ido.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Fuskarta a daure take tambayarsa “lafiya dai ko malam?” Shi ma a yatsine ya amsa mata “ina ‘yata da ku ka boye min?” cikin rashin fahimtar abinda yake nufi ta sake tambayarsa “Ban gane abinda kake nufi ba yi min dalla dalla yadda zan fahimta” gyara tsayuwa yayi “ina yarki Rukayya ita ce ta xuga min yata ta gudu ta bar gida ki fada mata wlh ta fadi inda Sa’adatu take ko kuma hukuma ta raba mu” wani kallo umma ta jefa masa wanda sai da ya shiga hankalinsa “Rukayya ba tada hannu wajen batan Sa’adatu mugun halinka da masifarka ita ta tunxurata ta gudu, kaje ka fara tuhumar kanka da matarka kafin ka tuhumi wasu, duk halin da yarka ta samu kanta a ciki kai ka fara jefata don haka kanka zaka zarga ba wasu ba” tana gama faɗar haka ta mayar da kofarta ta kulle ta bar shi tsaye yana naxari.

Gida ya koma yana ta masifa innah salamatu ce ta tarbe shi tana tambayarsa ko lafiya, faɗa mata yadda suka yi da Izuddeen da kuma mahaifiyar Rukayya yayi, zuga shi ta hau yi a kan kada ya yarda ya dauki mataki ta kuma bashi shawarar tafiya wajen Malam Jibo a kan yaxo a daura aure ko bata nan, in yaso idan ta dawo sai a kaita.
Yaji dadin wannan zugar da tayi masa, a nan take ya tashi ya nufi wajensa.
Tun a hanya yake ta tunanin Sa’adatu ya san dukkan halin da ya jefata a ciki shi ne sila amma ko kadan baya nadamar hakan sbd an riga an dasa masa tsanar yarinyar a xuciyarsa, kai tsaye makarantar sa ya wuce sai kuma bai same shi a can ba, don haka kai tsaye ya wuce gidansa, a  soro ya same yana lazimi bari yayi ya ƙarasa sannan suka gaisa.

Cikin karamci ya karɓe shi tare da shigar da shi shagon da ke soro sbd yadda ya ganshi ya san tattaunawar sirri ce ta kawo shi.

Zaunawa suka yi suna fuskantar juna kafin Baban Sa’adatu yayi magana Malam Jibo yace “ina muka kwana a maganar mu?” Cikin nuna tsananin damuwa yace “wlh Malam ina shirye-shiryen zuwa na sameka a kan maganar kwatsam shekaran jiya ta gudu” dafe kirji yayi “Ta gudu fa kace subhanallahi ya aka yi haka ta faru” jinjina kai yayi “Hudubar saurayi ce ta hure mata kunne shi ya yaudareta ya tunxurata ta gudu”

Shiru malam Jibo yayi yana tunani “To ai malam kai kayi sanya wajen tabbatuwar Maganar nan tun lokacin da ka same ni da maganar ya kamata a ce kayi wani abu amma kayi banxa da abin idan nayi maka magana sai kace zaka neme ni”

Mayar da ajiyar zuciya yayi “akasi aka samu malam kamar dauke min hankalina aka yi a kan maganar, ka gyara inda zaka ajiyeta na baka ita sadaka kada kayi lefe kada kayi komai sadaki ma na yafe maka xan bata dan wani abin idan ka shirya kayi min magana, gobe ko jibi nake so a daura aure” yana gama  maganar ya tashi. wani dadi ne ya sauka a zuciyar malam Jibo Allah ya bashi kifi daga sama gasashshe, yarinya kamar Sa’adatu ai abin alfaharinsa ne a ce ya aureta, godiya yayi masa har kofar gida ya rako shi suna ta tattauna maganar.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Har ya juya xai tafi ya sake juyowa “Au malam na manta ban fada maka ba” mayar da kallonsa yayi gare shi tare da cewa “ina jinka”

“Kada ka manta Sa’adatu ta ba yarinyar kirki bace ta riga ta saba da yawo banxa kana ganin xata iya xaman aure da kai?”

Wani murmushi malam Jibo yayi “Ba matsala don ka samu mafita aka yi auren nan ko?? To Sa’adatu ta shigo hannun da babu rabuwa har abada sai dai mutuwa, ko nan da can bata isa ta je ba sai dai idan ni na bata izni xata xauna tayi ibada kamar yadda kowacce mace take yi ka kwantar da hankalin ka”

Ba ƙaramin dadin maganar yaji ba yana farin ciki ya nufi gida don sanarwa innah salamatu.


Kada a manta da comment da share


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button