NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 12

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*


              *12*


Gudu nake cin karfina kamar zan tashi sama burina kawai na bace daga inda suke, Mutane sai bi na da kallon mamaki suke sbd ganin budurwa kamata na gudu abin mamakin ne, har sai da naga nayi nisa da su sosai sannan na samu nutsuwa, tsayawa nayi don na huta, a bakin wata bishiya na zauna ina ta maida numfashi, sai da na dawo na huta sosai sannan na ci-gaba da tafiya, nayi tunanin na gudu gidan wata kakata kanwar Baba tunda tana sona sosai na san xata rufa min asiri, amma sai fasa sbd idan suka bincika zasu iya gano ni a can, yanke shawarar tafiya gidan kanwar innah nayi Adda saratu, ban bata lokaci ba na kama hanyar tafiya gidanta.

***********

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A ɓangaren kannen kakan Sa’adatu kuwa basu ankara bata nan ba sai da aka zo shiga mota, ɗaya daga cikin su ne ya lura da bacewar ta, a firgice ya dubi ragowar yan uwan tafiyar tasa “yarinyar nan fa bata nan kamar gudu tayi” 
Da sauri suka baxu a cikin tashar kowa yana duba inda Sa’adatu ta shiga, ga mamakinsu sam basu ganta ba hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, a tunaninsu ko gida ta koma abinka da mutanen karkara duk cikinsu babu mai waya ballantana su kira gidansu su ji ko nan ta dawo, haka suka hakura suka ƙara koma gidan su Sa’adatu ko xasu sameta.

A Kofar gida suka ci karo da mahaifinta kallon mamaki ya bi su da shi gami da mikewa tsaye yana tambayarsu “Baba lafiya naga kun dawo?” Girgiza kai dattijon yayi “Hmmm Salisu yarinyar nan sai ta Allah kawai, don duk inda kake neman shu’uma ta kai, sai da ta san yadda tayi ta gudu sannan hankalinta ya kwanta, a gaskiya kayi sakaci da tarbiyyar yarka, tunda ta saba da yawo zai yi wuya ko aure tayi ta zauna”
Dafe kai mahaifin Sa’adatu yayi wani gumin tashin hankali ne ya riƙa yanko masa, cikin sarkewar harshe yake magana “ko ma menene uwarta ce ta fara jawowa ita ce ta dorata a tafarkin da take yanxu, sannan wannan kawar tata ita ma ta taimaka wajen lalacewar ta shi ma saurayin haka”
 jajanta masa suka riƙa yi ko gidan basu sake shiga ba suka kama hanyar ƙauyen su.

A fusace ya shiga gida tun daga soro yake kwalawa innar Sa’adatu kira mutanen gidan na jin irin kiran da yake yi mata suka fito saboda sun san ci mata mutunci zai yi, cikin kakkausar murya ya fara magana
 “Burinki na son lalacewar Sa’adatu ya cika kin hure mata kunne ta bi saurayi yawon iskanci, dokar da na saka kin karyata, duk shirina a kan yarinyar nan kin xuga min, tunda haka kika zaba mu zuba, a cikin minti biyu nake so ki tattara kayanki ki bar min gidana idan kinga kin xauna a gidan nan sai dai idan tare da Sa’a ku ka dawo”
 jikin innah a sanyaye ta miƙe ta shiga haɗa kayanta ita abin yayi mata dad’i dama ta gaji da wannan zaman kaskancin da take yi, kullum cikin xagi da cin zarafi, yanzu fargabarta ɗaya bata san inda yarta take ba, ta san Sa’adatu da kamun kai baxa tayi wani abu da zai xubar mata da mutuncinta ba amma duk da haka tana jin ba daɗi a ranta saboda sharrin xamani.

Mutanen gidan sai murna suke suna ta habaici Sa’adatu ta tafi yawon iskanci. Innah salamatu ke cewa
 “Yadda kika fita kin fita kenan ba dawowa mun ci gida ni da yayana” ko kallonta innah bata yi ba ta fice ta kyale su.

A soro taci karo da salim, har ƙasa ya tsugunna ya gaidata cikin farin ciki ta amsa, tambayarta ya hau yi “ina zuwa innah na ganki da kaya haka” labarin abinda ya faru da Sa’adatu ta bashi, ransa yayi matuƙar ɓaci, hakuri ya riƙa bawa innah kada ta saka damuwar hakan a ranta wata rana komai xai wuce, ɗari biyu ya bata yace ta hau mota.

A fusace ya shiga cikin gidan, innah salamatu na ganinsa ta hau magana “yauwa Gara da Allah ya kawo ka, ana yi maka gata ana raba ka da yar iskar yarinyar nan kana nacewa to gashi nan dai yanzu ta gudu”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ba ƙaramin zafin maganar innah salamatu yaji ba, salim yaro ne mai tarbiyya baya yiwa manya rashin kunya amma yau tunda ta tsokano shi sai ya mayar mata da martani cikin fushi yake mata magana “ina ruwan ki dani indai kin san irin wannan maganar xaki rika fada kada ki sake yi min magana Sa’adatu yar uwata ce ta fi ki kusa da ni, duk rintsi duk wuya dole a ce kanwata ce, don haka sai na damu da dukkan halin da take ciki, duk ba ku kuka tunxarata ta aikata abinda ta aikata yanzu ba, kun hanata abinci kun hanata walwala kun hanata wanda take so, kun jefeta da zina wanda ina da yakinin duk tafi yayanku tarbiyya,  sannan sbd zalunci yanxu kun dauke ta kun ce sai kun mayar da ita kauye, ya ku ke so tayi da rayuwarta, shi kenan so kuke yi ta zauna ku kasheta da baƙin ciki”

Dakinsa ya wuce ya kyaleta ta saki baki tana mamakin maganganun salim, tanbayar kanta take yaushe yaron nan yayi baki haka?? Lallai idan ba su yi taka tsantsan ba wata rana zai kwance musu aiki.

 Dakinsa ya shiga yana xuwa ya faɗa kan ƙaramar katifarsa, kwanciyar rigingine yayi yana tunanin rayuwar Sa’adatu, yayi alkawarin indai yana doran ƙasa baxai bari ta tagayyara ba.


Shi kuwa baban Sa’adatu tun bayan fitar innah daga gidan shima ya fita, bai xarce ko ina ba sai gidan su Izuddeen, a Kofar gida ya same shi tare da abokansa suna hira bai lura da xuwansa ba sai kawai ji yayi an shako shi ta baya, cike da mamaki ya juya don ganin wanda ya riƙe shi haka.
Baban Sa’adatu ya gani yana yi masa kallo mai cike da tsana, a ladabce yace “lafiya Baba??” Wani kallo yayi masa tare da cewa “lafiyar kenan, ina ka boye min yata, ka fito min da Sa’adatu ?” 

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A razane yace “ban gane Abinda kake nufi ba”
“Zaka san baka gane abinda nake nufi ba idan ka ji ka a hannun hukuma” abokan Izuddeen ne suka fara tambayar baban Sa’adatu “malam mai ya faru haka kaxo ka shake shi, a matsayinka na babban mutum ai bai kamata ka kama shi da kokawa ba, tunda a haife ka haife shi” cika shi yayi yana haki “wannan yaron da ku ke gani azzalumi ne ya lalata min ‘ya sannan yanzu ya hure mata kunne ta gudu watakila ma shi ne ya boye ta” kallon kallo suka hau yi kowa yana mamakin abinda yake faɗa, kasa magana suka yi sbd maganar ta daure musu kai, mayar da kallonsu ga Izuddeen suka yi.
“Gaskiya ne abinda ya faɗa?”
Shi kuma saboda takaici ya kasa magana sai dai ja da idanunsa suka yi, sai da ya gama tijara sannan ya tafi ya kyale su, binsa suka yi da kallo har ya kule.

Komawa suka yi suka zauna suna tambayar Izuddeen “menene alaƙarka da wannan mutumin ɗan tijara , gashi ya xo har kofar gida xai zubar maka da mutunci”

Labarin soyayyarsu da Sa’adatu ya hau basu dukkansu sun fahimci halin mahaifin nata, kuma sun gano cewa ba kaunar yar tasa yake yi ba, gaba daya suka shiga gida suka shaidawa Mama yadda suka yi da malam Salisu, ba ƙaramin takaici taji ba saboda abinda yayi masa, a wannan lokacin ta tashi ta shiga wajen mahaifin Izuddeen ta shaida masa abinda ke faruwa, tunda dama ya san Izuddeen na san yar aurensu da yarinyar, shi ma ransa ya ɓaci sosai, sa wa yayi aka kira shi ya tambaye shi yadda suka yi.
Cike da tausasawa da kamala yake magana.
“Faɗa min gaskiyar abinda ya haɗa ka da wannan mutumin, bana so ka rage min komai kuma bana so kayi min karya” kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana.

“Wlh Baba tun bayan korar da yayi min daga gidan sa ban sake komawa ba, kuma bana waya da yarsa hasali ma na cireta daga rayuwata, yanzu kuma kawai ina zaune sai yaxo ya shake ni wai na fito masa da yarsa da na boye, kuma ko abokaina za a tambaya babu macen da take shigo min dakina ku ma nasan zaku yi min wannan shaidar”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Shiru mahaifinsa yayi yana nazarin maganganunsa, “tashi kaje xan sake neman ka”

Cike da ladabi ya tashi fitarsa kofar gida kenan yaga Baban Sa’adatu tare da yan sanda, yana ganinsu ya tsaya don ya san bakinsa ne, suna karasowa ya nuna shi, tafiya suka yi da shi sauran abokansa ne suka je gida suka faɗa an tafi da Izuddeen, ana tafiya da shi suka bi bayansa su da ragowar yayan gidansu.

Kada a manta da comment da share


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button