NOVELSUncategorized

DUKKAN TSANANI 15

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
           *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*



             *15*

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Su innah basu dawo daga ƙauyen da suka je a ranar ba, sai da suka yi kusan kwanaki uku a can, suna tattauna a kan yadda za a bullowa al’amarin Baban Sa’adatu, wasu daga cikin iyayenta har sun yanke shawarar a kashe auren tunda babu kwanciyar hankali a ciki ga zaluntarta da ake yi, wani kakan innar ne ya hana a kashe auren sbd shi mutum ne mai saukin kai da hangen nesa, yana duba yadda Sa’adatu zata kasance a bayan babu mahaifiyar ta a gidan, saboda a duk lokacin da suka kashe auren, tamkar sun kashe rayuwar Sa’adatun ne, a dalilin hakan xata iya fadawa cikin kunci da wahala saboda mahaifinta baxai taɓa bari ta zauna a hannun wani ba idan ba gidan shi ba, don haka dole a yi hakuri a zauna a haka don duba maslahar rayuwar yarinyar.

************
Zaune  Malam Jibo yake ya zuba uban tagumi yana jiran dawowar Baban Sa’adatu, don tunda yace masa xai je ya dawo har yanzu shiru babu labarinsa, sai duba hanya yake ko zai ganshi ya bullo, yayi zama ya fi na awa biyu da rabi babu labarin malam Salisu, kuma babu labarin waliyyanta, hakan yasa ya fusata ya tashi ya bar kofar gidan yana tafe yana masifa kawai don yaga ba shi da kudi ne kuma bai bashi komai ba shi yasa yayi masa wannan wulakancin amma zai ganar da shi kuskurensa, bude shagon gidansa yayi ya shiga ya zauna yana cigaba da ban-bamin faɗa.

Ko da Baban Sa’adatu yaxo bai ganshi ba hankalinsa ne ya tashi, ya san halin malam Jibo da fushi da zuciya watakila haushi yaji yayi tafiyarsa, a sanyaye ya zauna a kan tabarmar da ya shimfida yana jiran dawowarsa, har wajen sallar magariba bai dawo ba, wannan dalilin ya sanya shi nade tabarmar tare da xuwa gidan malam Jibo da kansa, a Kofar gida ya tsaya yana kwala masa kira, yana jinsa yayi banza da shi, yaro ya sake aikawa a fada masa cewa yazo yana kiransa, ko da yaron ya fada masa sai yace a koma a ce masa baxai samu fitowa ba, duk yadda ya so ya haɗu da shi yayi masa bayanin abinda ya tsare shi hakan ya garara don haka shi ma yayi fushi ya tafi gida.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A fusace ya shiga gida yana masifa “shi wannan mutumin ya san bai shirya auren yarinyar nan ba yasa nayi asarar kudin katifata da ledata, haka na tatike aljihuna ban bar ko sisi ba, gaskiya malam Jibo ba mutum bane na bashi yar tawa kyauta ya wulakanta ni, nima kuwa sai na wukakanta shi duk da abinda yake takama sai nayi maganinsa”

 Da rawar jiki innah salamatu ta karaso wajen sa “me kuma ya faru malam naga kana fada haka kai kaɗai” dafe kanshi yayi tare da hadiye wani ɓacin rai da ya tare masa a makogoro
 “wane ne kuwa banda malam Jibo mun kulla magana za a daura aure ƙarfe hudu ga shi har magariba tayi Babu shi babu dalilinsa naje gida na kira shi yaƙi fitowa ya san bai shirya auren ba yasa na fadawa yan uwana”
Jinjina kai innah salamatu tayi “Gaskiya malam kaine da laifi tun kafin lokacin malam jibo yazo kaine ka Kad’a kai kayi tafiyarka, neman duniyar nam an yi maka ba a samu inda kake ba” ajiyar zuciya yayi “to ai ba wani waje naje ba, naje ne na ƙarasa karbo gudunmawar da abokaina xasu bani sbd naga alama idan ban je da kaina ba, babu mai bani taimakon kwandala, don naga alama yarinyar nan ba tada goshi, ko sisi ban samu ba sai asara da nayi, gashi auren ma yana neman lalacewa”

Tabe baki innah salamatu tayi “aure yana nan daram babu inda xa shi don baxa mu yi jeran mu a banxa ba, kaje ka samu malam Jibo ku sasanta a sake saka ranar daura auren, tunda yau dai ta wuce Allah bai yarda an daura ba, ta sai a sake lale, ni a ganina ma fa uwar yarinyar nan ita ke bata abin sbd ba so take ba shi yasa ta tsaya tsayin daka take bin abin ta ƙarƙashin kasa don haka ku dage sai an yi ko bata so, idan bata auri jibon ba uban wa xata aura? yarinya irin wannan mummuna kamar a yanka a boye wukar ga uwa uba bakin hali, jibon ne maganinta shi xai saita ta”

Guri ya samu ya xauna ya haɗa kai da gwiwa duk wani shirinsa an rushe masa, amma xai yi kokari ya gyara komai, kafin sati mai kamawa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A ɓangaren malam jibo shi ma a damuwar yake bai ji daɗin abinda malam Salisu yayi masa ba, yau ya shirya tsaf don tarbar amaryarsa amma ya watsa masa ƙasa a ido, babban abinda ya fi damunsa habaicin da matansa ke yi masa a kan rashin daura auren, har dai yayi xuciya ya hakura da Sa’adatun gaba ɗaya, amma dole ya daure yaje ya bawa mahaifinta hakuri a kan a dawo a daura auren ko don ya huta da gori.

Bayan dawowar su innah bai fi da kwana biyu ba aka aiko daga gidan gwaggo Balaraba ana nemana, jikina har rawa yake sbd shaukin son ganin innata, tare da yaron da aka aiko muka tafi, tun daga soro nake jin tashin muryar Babana da alama wata tijarar ya ƙara xuwa yayi musu, da sand’a na shiga cikin dakin a  hankali cikin siririyar muryata da ta dashe sbd fargabar da ta cikata nayi sallama, gaba ɗaya kallo ya dawo kaina.

Su ma a sanyaye suka amsa min ina ganin innata bata dago ta kalleni ba, wanda na kasa fahimtar dalilin hakan, gefenta na samu na zauna duk na takure kamar mai jin sanyi, bi nayi na gaida kowa har da Baba Amma bai amsa min ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Dakin ne yayi shiru ana jiran a ji wanda zai fara magana amma babu wanda yace wani abu har sai da aka ɗauki wasu mintuna masu tsayi, gwaggo Balaraba ce ta fara bashi hakuri a kan abinda nayi masa tare da rokon ya mayar da innata dakinta kuma ya janye dukkan takurar da yayi mana.
Na lura da fuskarsa yaji dadin kiran sulhun da aka yi masa, fuskarsa bayyane da murmushi ya fara magana.

“Ba komai gwaggo komai ya wuce dama sharrin shaidan ne haka baxai sake faruwa ba, kuma a ja musu kunne duk su biyun sbd gaskiya basa jin maganata”

Nasiha su gwaggo suka yi min tare da innah a kan yin biyayya a bisa dukkan abinda ya umarce mu, tunda gaba dayanmu a karkashin sa muke kuma yardarsa muke nema.

Har aka yi maganar aka gama innah bata ce komai ba da alamu bata ji daɗin sulhun ba, kawai don an fi karfin ta ne shi yasa tayi shiru, don ta san ba canja xani xata yi ba ko ta koma ci-gaba xa a yi daga inda aka tsaya.

A lokacin ya nemi mu tafi tare da shi, gaba daya muka nuna kin amincewa da hakan, kyale mu yayi ya tafi tare da faɗa mana cewa lallai gobe mu taho gida.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Da farin ciki ya shiga gida a xuciyarsa yake fada duk burikan da yake son cika su a yanzu ne lokacin da zai cimma su tunda sun amince xasu dawo.

Yana fita na faɗa jikin innah ina kuka “me yasa kika amince mu koma hannun shi innah wlh baxa su canja ba watakila ma yanxun wani tuggun aka hado mana…… Dan Allah kice baxa mu koma ba innah”

Kuka nake mai cin rai ita ma innah haka, a ranar a can na kwana gaba ɗaya mun kasa gane kanmu banda kuka babu abinda muke yi kamar waɗanda zasu koma kurkuku haka muka ji.



Kada a manta da sharing da comment


*Jeeddahtulkhair????*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button